Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
29
Kallonshi Aysha keyi ganin yanda ya dafe goshi ya lumshe ido aikuwa ta daddage ta maka masa wani harara sai gashi karaf ya bude idon nashi…ta wani zaro ido hadda dora hannu a bakinta tace”sir i swear bada kai nakeba”..bai iya cewa komai ba sai kallonta da yakeyi nan kuma tayi kasa da idanunta tanajin idanun nashi har cikin brain dinta…ta rasa meyasa har yanxun ta kasa sabawa da idanun mutumin nan..sam bata kaunar ya zuba mata su sbd sawa suke tanajin wani iri wlh..sai su saka nutsuwar da baka shirya masa ba…shiko Bobby kallon nata yakeyi yana tattaro duk wani abu da yasan yanaji akanta yana dorasu cikin idon nashi wai ko Allah zaisa taga illar da take nemanyi mishi ta zubar da makamanta…sun dauki lokaci mai tsaho a haka har zaman wurin ya fara isanta kafin kuma taji yace”bani wayarki?..”juyawa tayi ta kalleshi sai kuma ta kwar da idon da sauri ta zaro wayan da aljihunta ta mika mashi..ya amsa ya duba sai yaga babu key a jiki dan haka kai tsaye whatsApp dinta ya shiga yayi deleting gaba daya status dinta daga nan ya shiga gallery nan ma yayi marking all pictures dinsu na kaduna yayi deleting snn ya shiga bin duk wani picture da sukayi itada besty yana deleting dinsu…a garin haka yaci karo da wani da sukayi itada Prof ya zuba mata ido yana kallonta da murmushi itama tana murmushin aka dauki picture din…wani abu mai daci yaji yazo ya tokareshi a makoshi..sai yayi zuru yana kallon pic din yana sakejin zuciyashi ma tafarfasa amma bai nuna mata ba yayi deleting pic din ya muma cigaba da abunda yake…bayan ya gama da wnn foldern ya fito ya shiga wani sai yaci karo da pictures din ‘yan Manchester rututu musamman Pogba dan nashi sunfi na kowa yawa a matsayinshi na best player dinta…tsayawa kawai yayi yana kallon pics din kaman gunki..yana yin minimizing ya sake cin karo da hoton pogba akan screen din wayan nata datayi making as wallpaper ai baisan lokacin da yayi wurgi da wayan nata ya fadi kasa ba…Lamido ta wara ido tana kallonshi idonta kmr zasu fado don mamaki kawai sai taga ya mike ya fada bathroom ya wani buga kofan da mugun karfinda saida ya tsorata ta…jiki na rawa ta mike ta fita daga office din ko takan wayanta da yayi rugu rugu a kasa batabi ba…shiko yana shiga samun wuri yayi ya zauna yana dafe head dinshi wani azababben kunchi na sake rufar mishi…ya tabbata da yaci gaba da zama a wurin nan ita kanta yana iya yin ball da ita sbd kuncin da yakeji…ashe rashin hankalin nata har yakai ta ringa tsayawa tana hoto da ko wane banza and to top it all har tara hotunan ‘yan kwallo takeyi a wayarta kaman ta hada wani abu dasu?..hadda wani sanya picture din namiji a wall paper dinta wai meke damun yarinyar nan ne kam?..waye wani Pogba da take mugun sonshi haka?..me akai akayishi ma gaba daya..anya kuwa yarinyar nan bata samu ta6in kwakwalwa ba?..idan ba haka ba why zatana abubuwanda ba kowace mace ce keyi ba..meya hada mace da kallon ball idan ba tsabar rashin hankali ba…saida ya dauki lokaci mai tsaho nan cikin bathroom kafin ya fito..bai sameta a office din ba amma wayanta na nan inda yayi wurgi dashi sai yanxu kuma yaga bai kamata ya fasa mata waya ba..kaman yayi overreacting amma shi kanshi ba laifinshi bane baisan meyasa yake kasa controlling abuna yakeji akanta ba…gaba daya ma sai yaji dana sanin zuwa college din yake at the first place kawai sai ya juya ya fita daga office ba tareda yabi takan wayan daya farfasa mata ba.

Karfe hudu da kusan rabi ya baro hospital kai tsaye yacema driver ya kaishi FCNM zai shiga hostel yayi wani abu…driver ya dauki hanyan college din shi kuma Bobby yayi relaxing a back seat idanunshi lumshe yana sake sake cikin ranshi…tun daxu yasa aka kawo mashi sabon waya irin nata sak shine yakeso yakai mata tun kafin taje ta fara yamadidi dashi cewar ya fasa mata waya…bakin kokarinshi kawai yake na ganin abunda yakeji bai kwantar dashi ba amma ko Allah yasan ba karamin mawuyacin hali yake ciki ba…suna isa cikin hostel din yasa akayi mishi mgn da daya daga cikin matrons dinsu ya bata wayan bayan yace mata ta bada a kaiwa Lamido…daga haka gida ya koma dan ko ganinta bai sonyi ballantana ta sakeyin wani abun zuciyarshi tazo tana bugawa…koda ya koma gida yaki kwanciya kokari yakeyi sosai ya yaki abunda yakeji gameda ita yasan yana bari ya kwanta shknn ciwo zai samu galaba a kanshi.

Haka kwanaki sukaita tafiya suna zama weeks..weeks kuma suna zama watanni har suka fara second semester exams…zuwa yanxu Bobby ya tabbata ko ba sonta yakeba to definitely he’s attracted to her and tunanin hakan kadai yana iya samai zazza6i sbd tsabar takaici…zuciyarshi kwata kwata bata mai adalci ba amma alqawari ne ya daukan ma kanshi bazai bari koma me yakeji a kanta yayi tasiri a zuciyarshi ba…da wnn alkawari ya samu yake yaqar abunda yakeji dukda cewa ba karamin wahala bane yake bawa kanshi…har suka gama exam suka tafi hutu bai sata a idanunshi ba hakan kuma ba karamin tada hankalinshi yayi ba abun har mamaki ya bashi…da farko gani yake kaman rashin ganin nata shine mafi a’ala amma zuwa yanxu ya tabbatar idan ba ganin nata yayi ba yana iya samun gagarumin problem…haka a daddafe suka cinye two weeks dinsu na holidays zasu dawo school Sunday..Monday kuma kowa ta fara zuwa Clinical Area…baisan hospital da za’ayi posting nata ba dan haka yau Saturday yana barin Hospital ya kira Nur yace yanaso su hadu a College that yanada mgnr da yakeso suyi dashi..Nur baiyi masa musu ba yace su hadu a college din…karfe biyar saura ya shiga cikin makarantan a lokacin ma ko Nur din bai karaso ba dan haka ya jirashi nan cikin mota ya karaso snn suka wuce office din Nur din gaba daya…bayan sun zauna Nur yace”to Dr Bobby ina sauraronka”…ajiyar zucia Bobby ya sauke yana tunanin ta inda ya kamata ya fara dan bayason iskancin Nur ko kadan dan haka ya dinke fuskanshi tsaf yana wani babbasarwa snn kai tsaye yace mishi”wane Hospital akayi posting Lamido?..”Nur yayi kuri da ido yana kallonshi yana daria cikin zuciyarshi yana tausayi abokin nashi amma bai nuna mishi komai ba a fili yace”well ina tunanin bazai wuce General Hospital ba..kasan rural posting ne”…da sauri Bobby yace”inaso a dawo da ita Freedom”…kallonshi dai Nur yacigaba dayi yana tuno ranan da tazo tace a canxa mata posting amma yace baza’a canxa ba yanxu kuma gashi da kanshi yakeso a canxa mata posting din..kamar zai tsokaneshi sai ya tuna yanda sukayi dasu Mummy dan haka ya basar tareda fadin”shknn zanyi mgn da isaac zaa canxa mata inshaAllah”…wani ajiyar zucia Bobby ya saki sai yaji kaman an sauke mashi wani nauyi…yanada reasons da yasa yace a kawota Freedom sbd yasan ba hankali ta cika ba kilan zuwa zatayi taita kule kulen maza tana abunda bai kamata ba shiyasa yake sonta a kusa dashi yanda zaisa mata ido…Nur dai nata kallonshi yana kunshe daria a haka sukayi sallama kowa ya shiga motarshi ya wuce.

Washegari misalin 12 suka iso makaranta tareda Hamma daya dawo dasu as usual…kowa taje ta duba posting dinta suna murna zasuje rural posting amma sai sukaga an sake posting dinsu Freedom again…aikuwa gaba daya murnan da suke ciki sai ya koma ciki musamman Lamido da ko kadan last posting da tayi a Freedom din bataji dadinshi ba infact that was the most difficult and boring posting data ta6ayi a rayuwarta..lokaci daya duk wnn farin cikin na tafi rural ya koma ciki…kallon Billy tayi tana wani misti misti da ido sbd 6acin rai tace”zo muje mu samu provost mu fada mashi wlh..kan me za’a wani sake kaimu Freedom bayan ko last time can mukaje”…girgiza kai Billy tayi tace”nidai babu inda zanje and ina bakin shawaran kema ki hakura kawai..if u could remember last time ma kinje a canxa maki posting din hakan bai yiwu ba so yanxun ma ba canxa maki zasuyi ba”..sake hade rai Aysha tayi tace”amma nidai an cuceni wlh..dukma wanda ya bada shawaran a barmu a Freedom Allah ya isa tsakanina dashi wlh”…dan murmushi Bily ta saki kafin tace”nasan bazai wuce proprietor ba”..Aysha dai batace komai ba haka suka karasa cikin hostel kowa rai a 6ace.
Ranan Monday tun seven Bobby ya bar gida zuwa Hospital ko breakfast bai iya tsayawa yayi ba duk yanda Mummy taso yayi hakan kuwa…so kawai yake ya sanyata idonshi ko zai samu ya cike wasu gurabe da yakejinsu so empty a cikin zuciyarshi…su kuma basu karaso Hospital ba sai after eight…bus dinsu na gama parking duk suka firfito zuwa cikin asibitin kowa sanyefa uniform dinshi…daga bakin office dinshi ya hangosu suna tafia and duk yawan nan nasu idanunshi basu sauka kan kowa ba sai ita..nan take kuma yaji wani irin sanyi mai hade da zafi yana mamaye zuciyarshi..shi sanyin dai na ganinta da yayi ne after a long period of time while shi kuma zafin na jin ciwon yanda tazo asibitin ne daga ita sai dan hijab dinsu na uniform da ko chest dinsu bai gama rufewa ba…wasu sukan dora hijab ko mayafi akai idan anzo makaranta ko asibiti sai a cire amma Lamido koda wasa bai ta6a ganin tayi irin wnn ba…haka take yawonta a college da hospital tana tallata surar jikinta kowanne jick and jerk yana kallo…gashi ya kasa dauke idanun a kanta tunda yake bai ta6a jin ciwon kananun hijabs din nan nasu ba sai yau..gaba daya jikinta a waje yake sararin Allah…har sukazo suka wuceshi bai dena kallonta ba saida suka shiga office din da za’a yi musu posting…already yayi mgn da CNO yace ayi posting dinta theatre yanda zai dinga samun ganinta sosai..idan basuda aiki kuma ta tafi Office dinshi dan yasan tsaf zai iya zuwa ya samu tana hira da doc Gabriel ko doc Vivian…kaman yanda ya tsara din kuwa haka akayi..tanaji anyi posting dinta theatre hankalinta yakai kololuwar tashi dan har yanxu bata mance suman da tayi last time da suka shiga theater ba..sbd tsabar wulakanci duk fadin asibitin nan a rasa inda za’ayi posting dinta sai theater?..aiko billahillazhi bazata zauna a theater ba saidai duk abunda za’ayi ayi…suna barin office din kowa ya nufi various post dinshi including Billy dake maternity…ita kuma sai ta nufi office dinshi da nufin ta hadashi Allah annabi yasa a canxa mata posting…da sallama ta shiga ciki kanta a kasa ta gaisheshi…ya shiga binta da kallo sama da kasa yana wani 6ata rai kaman baiji dadin ganinya ba ya nuna hijab din jikinta yace”shi wnn mezai hana ki cireshi sai ki dinga yawonki a haka kawai”..kallonshi takeyi kallo irin na mamaki jin mgnr daya fada kafin tace”sir in cire hijab dina fa kake nufi”..a fusace yace”to meye amfaninshi tunda dama jikin naki kikeso a gani ai saiki cireshi kawai yanda zaa samu daman kallon jikin naki da kyau”…daure fuska tayi tana turo jin inda zancen nashi ya dosa tace”nidai bazan iya yawo babu hijab ba”…yace”if u are referring wnn abun dake jikinki to a hijab then you are deceiving yourself..ke ko irin asa babban hijab akan uniform baki iyaba..u always come out like this kamar dai tallan jikin naki kike”…sake daure fuska tayi jin maganganun da yake fada..indirectly fa zaginta yakeyi knn?..ita batasan ma tsautsayin daya kawota office dinshi ba tunda tasan halinshi and bazai ta6a canxawa ba…juyawa tayi zata fita a fusace yace”come back here”..ba yanda ta iya haka ta juyo ta dawo tana tutturo baki…mikewa yayi ya shiga wani kofa dake office din can sai gashi ya dawo da coffee hijab mai girma a hannunshi yana zuwa ya mika mata…batayi musu ba ta kar6a saidai fuskan nan har yanxu ba fus…komawa seat dinshi yayi ya zauna ita kuma ta sake juyawa zata fita yace”dawo kisa hijab din nan”…kaman zatayi kuka ta dawo ta zura hijabin..shi kuma yana zaune yana kallonta har wani dan murmushi ya saki ganin hijab din yayi covering dinta yanda yakeso yace”perfect…now seat saiki fadi meke tafe dake?..”zaunawa tayi tana sake marairaicewa tace”Sir dan Allah so nake kayi mgn CNO a daukeni daga theatre..tsoro nakeji wlh”…murmushi sosai ya saki wanda har ya bata mamaki dan zaiyi wahala kaga murmushinshi shiyasa idan yayi ma sai ta ganshi wani daban kmr ba proprietor data sani ba…saida ya gama smiling dinshi snn ya sake relaxing kan seat dinshi yana kallonta kamar ba gobe yace”yanxu me kikeso inyi Lamido?..”da sauri ta sake dagowa tana kallonshi dan ita wlh bata ta6aji ya kirata da Lamido ba..ko sunanta ma ita baya kira saidai yace ke ko wani abu amma yau shine da kiranta Lamido?..duk yau sai taga kaman bashi ba..kaman canxashi akayi sbd yanda yake behaving is so unlike him…ganin yanda tayi wani zuru tana kallonshi sai yadan hade rai yace”meye?..”da sauri tace”sir cewa fa kayi Lamido”…ya sake hade ran yace”eh ba hakane sunanki ba?..ko kinfi so kiji nace Aysher?..”wani mamakin ya sake kamata da alama yau dai Dr Bobby na cikin farin ciki…saita dan saki smile itama kafin tace”sir you are in a good mood today”..yana cigaba da smiling dinshi yace”of course..rabona da jin farin ciki kaman na yau har na mance”..dan wara idanu tayi irin abun mamakin nan sai kuma tacigaba da smile dinta tana gyada kanta tace”to sir albarkacin farin cikin da kake ciki kayi mgn a canxa min posting dan Allah”…girgiza mata kanshi yayi in a serious tone yace”no..kawai kiyi hakuri kije tunda can aka kaiki”…kaman zatasa kuka tace”sir suma fa nakeyi idan naga ana yayyanka mutum”…murmushi ya kara saki before yace”zaki dena inshaAllah..kuma I promise idan naga kin maida hankali kin nutsu sosai da kaina zanyi posting naki inda kikeso?..”nan da nan face dinta ya washe da fara’a tace”dan Allah da gaske?..”yace”yea i mean it..kawai so nake inga kin nutsu”…yana rufe baki kuwa ta hau gyada kanta tana fadin”nama nutsu tun yanxu wlh..i will be behaving gently”…yace”ni kuma zanyi posting naki inda kikeso”…sake gyada mashi kai tayi tana murmushi sai kallon yanda shima ya kasa dena murmushin take…mamaki take ashe haka murmushi ke bala’in mishi kyau amma baya yi?..kam ai da itace ta gane murmushi nayi mata irin kyan da yake mishi da kullum cikin murmushi zata kasance wlh koda cikin bacci ne kuwa…shi kuma kallonta kawai yake yanajin yanda yau ta ware dashi ba tsoro ba fargaba ko 6acin rai a tattare da ita…shi kanshi so yake ya gina kyakyawan alaqa tsakaninshi da ita yanda ko sun koma college bazata na gudunshi ba snn bazata na daure mashi fuska ba…yayi na’am da wnn shawara na zuciyarshi dan haka ya daura damarar gina shakuwa tsakaninshi da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button