Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari haka tazo office din nashi fuskan nan cunkus dashi kaman bata taba daria ba…sbd presence na Dr Aslam yasa bai nemi jin dalilin fushin nata ba yayi mata posting dinta kawai ta tafi…ranan har ya bar hospital din bai sake sanyata idonshi ba…washegari ma same thing happens kuma har ward din da take yaje bai sameta ba..duk jinshi yake wani iri da bai samu ganinta ba…a haka suka cinye satin nan tas bai sake ganin Lamido ba…damuwan da ya shiga a dalilin haka har mamaki yake bashi…yaudai yayi alqawarin dukma ina take zuwa ta 6oye idan ta ganshi sai ya nemota tunda ya tabbata zai iya samun matsala wajen bacci matukar bai sanyata a idonshi ba…cikin toilet dinsu aka ganota wai ashe tana hangoshi ya taho sai tayi wuf ta fada bandaki kuma bazata fito ba har sai ya fita..yaudai asirinta ya tonu dan har office dinshi yajata snn yace ta zauna suyi mgn..idanunshi a kanta kaman yau ya fara ganinta yace”why are u doing this?..”dan turo baki tayi tace”ba kaine ba”..yace”me nayi?..”ta sake turo bakin batace komai ba..shi kuma ajiyar zuciya ya sauke mai karfi kafin yayi lowering voice dinshi sosai yace”to kiyi hakuri”…dagowa tayi ya kalleshi da mamaki…ya sake cewa”kinji?..”murmushi ne ya kwace mata ganin yanda ya maida face dinshi abun tausayi…murmushin shima ya saki mai kyau yana kallon dimples dinta da yakejin kaman ya saka finger dinshi a wurin…ya sake yin kasa da murya yace”kin hakura?..”tace”eh mana..amma zaka denamin masifa koh?..”kallonta ya tsaya yi for some minutes kafin ya sauke numfashi yace”idan kin nutsu kin dena aikata abunda zanyi maki masifan ba?..”murmushin dai ta kara saki tareda fadin”na dena”.
Bayan sati hudu…
Tuni sun gama posting dinsu sun koma makaranta…’yan year 3 su besty kenan tuni suma sun rubuta Hospital Final exam dinsu wanda sukayi passing sune suka fara rubuta council exam cikin satin nan…gaba daya Aysha ta zama wata iri daga ita har Billy ba karamin missing Sa’eed suka fara ba tun ma kafin ya tafi…kuka kuwa yana shanshi dan kullum ne idan suka hadu sai anyi mishi kukan nan hadda Billy data kasance abokiyar rigimarshi…shi kanshi shima ji yake kaman yayi kukan amma bazaiyi ba sbd namiji da dauriya aka sanshi amma only Allah knows yanda yakejin zafin rabuwa da zaiyi dasu…ranan Thursday bayan ya fito daga exams yaje hostel ya kwashesu suka fita wai yanaso su ragema juna radadin rabuwa da sukeji…duk inda yasan suna so saida ya kaisu including market da Lamido bata da burin da ya wuce ta shiga kasuwa a kano idan ta koma Gombe tayita bada labarin taje kwari taje sabon gari taje singa taje wambai taje bakin asibiti saidai wnn karon yawon sam baya masu armashi as kowa yanada damuwa cikin ranshi…a takaice sun shafe almost 3 hours suna abu daya kafin daga bisani ya saukesu gidan Hajia itama kuwa hadda dan kwallarta wai ta kusa dena ganinsu tunda Sa’eed zai tafi…kuka sosai sukasha a gidan nata kafin ya sake daukansu sai hostel dinsu..a bakin hostel din ma sun kwashi lokaci mai tsayi yanata aikin rarrashi da basu baki amma har suka rabu baiga alaman zasu dena kuka ba…the next day which is friday ranan sukayi final exam ma’ana sun gama da council saura waiting results kuma…ranan ma haka suka hada kai sunata faman kuka a cikin makaranta har mutane na kallonsu…saida akayi da gaske snn aka samu suka daina kukan yayi musu rakiya da kanshi har cikin hostel dinsu.
Washegari Saturday tun safe Bobby ke kiran wayarta sbd saqo da babanta ya aiko mata dashi amma bata dauki waya ba…saida ya kiraya kusan sau shida snn yayi sa’a ta dauka…kafin yayi mgn Billy tace”sir nice..batada lafia ne bazata iya daukan waya ba”…zaro idanu yayi sosai hankalinshi a tashe sosai yace”meya sameta?..”a takaice Billy tace”fever..”yace”kun kaita clinic?..”tace”sir kasan halinta ai..taki yadda”…da sauri yace”kice mata nace ku sameni a clinic yanxun nan”..Billy ta amsa da”toh..”snn ta ajiye wayar tana duban Aysha da tun daxu ta kudundune cikin bargo ko oxygen na kirki bata shaka…as usual sai da kyar da sidin goshi ta samu ta mike suka tafi clinici din…tun kafin su shiga Bobby dake zaune cikin motanshi ya hangosu..gabanshi yaji ya fadi da yaga situation da take ciki dan ko tafiya ma da kyar take yinshi ga wani irin haske da yaga ta kara tun daga nan inda yake…bude motan yayi kawai ya fita kafin su karasa ya iskosu hankalinshi a kanta yace”kin tabbata only fever ke damunta?..”Billy tace”maybe baza’a rasa headache ba tunda kuka taita yi har yasa mata zazza6i”..kallonta kawai yayi kamar zai tambayi dalilin kukan sai kuma ya fasa…Billy ta sake cewa”sir ciki zamu shiga?..”girgiza kai yayi hankalinshi gaba daya na ga Aysha data samu wuri ta zauna tana sauke numfashi yace”i think saidai muje hospital sbd inaso ayi mata test shi kuma lab din nan ciki sun tashi..ki sata a mota kawai”…ba musu Billy ta sake kamata zuwa inda motarshi yake ta sakata a back seat snn ta rufe kofar…karasowa yayi shima ya shiga yana dubanta yace”ke bazaki jeba?..”girgiza kai Billy tayi tana murmushi tace”no sir..inaso inyi mata girki kafin ku dawo”..gyada kai kawai yayi ya rufe glass dinshi snn ya tada motar suka tafi Billy ta bisu da kallo tana fadin”love birds”.????
Kai tsaye Freedom ya nufa da ita…yana shiga ciki ko parking daidai bai tsaya yi ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin asibitin…few minutes later ya dawo tareda wasu nurses mata guda biyu suna tura trolley bed…bude motan yayi matan suka taimaka mata ta fito suka dorata kan trolleyn snn suka shiga ciki…direct office dinshi suka kaita suka dorata kan bed da yake scanning da other examinations akai snn suka fita…maida kofa yayi ya rufe bayan sun fita ya shiga takawa a hankali zuwa inda take…idanunta yaga a kulle amma still hawaye basu dena fitowa daga cikinsu ba…hannu yakai forehead dinta yaji akwai zafi sosai dan haka ya koma seat dinshi yayi using landline ya kira lab yace a kawo mashi sample bottle…babu wasting of time aka kawo mashi..ya bude wani drawer nan cikin office din nashi ya dauko 5cc syringe da tourniquet kana ya koma inda take…hannunta ya kama a hankali ya daura tourniquet din a jiki aikuwa da sauri ta bude idanu tana kallonshi..ya wani hade rai tareda rike hannun nata da kyau dan yasan tsaf zata iya sawa yaji mata ciwo snn ya soka needle din cikin vein dinta…wani irin kara data saki saira kiris ya ya zare needle din daga jikinta sbd shiganshi da karan nata yayi…haka tana buge buge tana kuka ya dauki sample din nata ya zuba cikin sample bottle da aka kawo snn ya bada yace mp/widal yakeso ayi mashi yanxun nan…bayan fitar mutumin yayi checking vital signs dinta yaga all normal snn ya koma seat dinshi ya zauna waiting for the results…ana kawo mishi ya duba yaga da akwai malaria kadan babu typhoid dan haka ya rubuta drugs da injection da zaiyi mata ya bada aka amso mashi a pharmacy…saida ya gama withdrawing alluran da zaiyi mata snn ya karasa inda take yana tunanin ta yanda zaiyi alluran nan ba tareda ta tara mishi jama’a ba..kallonta kawai yakeyi yanda bacci ya fara daukanta yasan yanxu yana tashinta tayi ido hudu da allura ba karamin rikicewa zatayi ba…hannu yakai forehead dinta ta bude idon a hankali…tana ganin injection a hannunshi ta mike zaune da sauri idonta na cikowa da hawaye tace”Allura zakaimin?..”shiru yayi yana kallonta duk sai yaji ta bashi tausayi yanda tayi tambayar…zaunawa yayi kusada ita yana kallonta a hankali yace”bakya so?.”da sauri ta hau gyada kai tana goge hawayenta…yace”amma Aysha alluran ne kadai zai saukar da wnn temperaturen naki da wuri?..bakiji yanda jikinki yayi zafi ba?..”ta shiga yarfa hannayenta hawaye na ambaliya fuskanta tace”nidai banson allura”…kallonta yacigaba dayi not knowing what to do or say…harga Allah yafison ya mata allura sbd fevern zaifi sauka da wuri amma kuma tausayi take bashi da wnn kukan da takeyi…lalla6ata ya shigayi da bata baki amma sai botsarewa take wai ita baza’a mata allura ba…nan kuma yayi abunda bayaso wato forcing dinta dan matseta yayi yayi mata alluran tanata rizgar kuka tana ihu bai saurara ba saida ya gama…sai kuma ya hadata da jikinshi ganin yanda legs dinta ke trembling murya can kasa yace”am so sorry”..kuka kawai take har breathe dinta yana kamar zai dauke…zaunar da ita yayi kan gadon shima ya zana gefe tareda cupping fuskanta yana kallon cute face dinta yace”stop crying mana..yanxu fevern zai sauka kinji?..am sorry”…kasa ce mishi komai tayi sai hawaye da sukaki tsayawa…Bobby ya lumshe ido ya bude shima kaman zaisa mata kukan yace”nace fa am sorry Aysher..kukan ya isa haka mana”..hannu takai tana goge tears din nata baisan lokacinda ya daga hannunshi ba kawai sai ganinsu yayi akan fuskanta yana goge mata tears din…saida ya gama snn ya sake kasa da murya yace”zakici abinci?..”girgiza mishi kai tayi tana turo baki shi kuma ya saki murmushi kafin yace”toki kwanta abinki..idan fevern ya sauka sai in maidaki hostel”…batayi masa musu ba ta juya masa baya ta kwanta shi kuma ya sake lumshe ido yanajin wani abun mai kamada magnet na kokarin janshi gareta…ganin ta cure legs dinta wuri daya ya janyo kujera ya zauna bayan ya gyara mata kafan sai ya tallabi cheeks dinshi yana kallonta…ta dauki almost an hour tana bacci shi kuma yana nan zaune inda yake yana kallonta..he just can’t take his eyes off her baisan meyasa ba…he drives pleasure staring at her..har wani smile yake saka akai akai ba tareda saninshi ba…a hankali yaga ta fara mosti kaman zata bude ido saita fasa ta wani turo baki inda kasan idonta biyu…daria sosai ya saki ganin yanda ta turo bakin..ya lumshe ido tareda kai hannunshi a hankali ya aza kan lips din nata sai kuma ya janye da sauri yana yarfa hannun idanunshi a kanta sbd wani abu da yaji kaman electric shock…sake juyawa tayi nan hulan dake kanta ya zame tareda faduwa kasa black silky hair dinta da bata cika yima kitso ba ya bayyana…saida breathe dinshi ya dauke na wucin gadi ganin gashin nata…da dadewa yasan tanada gashi tunda ya ta6a ganin kan nata amma sai yaga kaman daga wancan lokacin zuwa yanxu an kara mishi tsayi da baqi dan har wani daukan idonshi yakeyi…sake lumshe idonshi yayi a karo na ba adadi kawai sai ya mike daga wurin ya koma kan sofa ya zauna because abubuwan nan da yakeji bana lafia bane ya sani…tsaf zai iya mancewa ya aikata abunda daga baya zaizo yana regretting so it’s better he leaves kafin azo a samu matsala…haka yayaita zaune yana duban agogo saida tayi baccin 3 hours cur snn ta tashi tana wani yatsine fuska kaman wanda taga poopoo…mikewa yayi daga inda yake zaune ya karasa kusada ita yana dubanta with concern yace”how are u feeling now?..”a hankali tace”da sauki..inajin yunwa”..murmushi ya saki tareda sunkuyawa ya dauko hulanta dake kasa ya mika mata yana cewa”ki shiga bathroom ki farayin brush kafin a kawo abincin”…batayi mishi musu ba ta sauko daga gadon zuwa bathroom dinshi…da mouth wash tayi amfani da wanke bakinta snn ta dauro alwala ta fito rikeda hulan nata a hannu…kallon gashinta daya sauka shoulders dinta yayi yace”ya kika cire hulan kuma?..”turo baki tayi ta mayar da hulan batace komai ba…carpet ya shimfida mata da kanshi snn ya dakko jilbab dinta daya cire mata daxu shima ya mika mata..amsa tayi ta zura ta tayar da sallah shi kuma ya koma ya zauna waiting for abincin da yayi mata order yazo…tana idar da sallah ta sake dubanshi tana kwabe fuska tace”yunwa fa nakeji”…murmushi ya kara saki yace”Aysher ki kara hakuri mana..nayi ordern abincin ne and nasan suna hanya inshaAllah”…gyarawa tayi zata kwanta nan kan carpet din yayi sauri tasowa daga inda yake yace”karki kwanta kasa”..ba musu ta mike ta koma gado…bayan few minutes akayi delivering abincin nata dan haka ya mika mata gaba daya snn ya zauna yana kallonta…ita kuwa cik abincinta take hankali kwance sai kallon dimples dinta dake lotsawa idan tana tauna abincin yake…ba kanta ya fara ganin dimples ba amma nata kullum shi yake tempting dinshi yaji kaman yaje yasa finger dinshi a wurin…tana gama cin abincin tasha drink din kadan snn ya bata drugs suma tasha badon tanaso ba…saida yaga ta nustu ta dawo hayyacinta snn yace”can we talk now?..”kallonshi tayi batace komai ba…shi kuma yana kallon eyes dinta da sukayi luhu luhu sbd kukan da taci yace mata”what happened to ur eyes?..”raurau tayi da ido zatasa mishi kuka yace”I didn’t ask u to cry…cewa nayi meya samu idonki?..”tana kwabe fuska tace”kuka nayi”…”kuka?..”ya maimaita abunda ta fada kafin yace”me aka maki kikai kuka da har ya sanya maki zazza6i haka?..”lumshe ido tayi nan hawayen dake ciki suka silalo kan fuskanta tace”Bestie ne zai tafi”…cak yaji komai nashi ya tsaya including breathe dinshi…nan take face dinshi ya sauka murya a dakile yace”sbd shi kike kuka knn?..”cigaba da kukanta take tace”tafiya fa zaiyi ya barmu…ba sun gama council ba”..a kufule ya mike zuwa inda ya ajiye wayoyinshi yace”sai ki bishi ai”…harara ta watsawa bayanshi tana turo baki…ya dauki wayoyinshi daya ajiye nan wurin snn ya kama hanya zai fita yace mata”fito mu tafi”…da kallo kawai ta bishi tana mamakinshi..har yanxu bata bar mamakin yanda he can change forms in a blink of an eye ba..he can be nice for a second and become annoying the other second…shiyasa kwata kwata bata gane mashi…mikewa tayi ta zura jilbab dinta snn ta fita daga office din..a bakin kofa ta sameshi yana ganin ta fito yayi locking office dinshi snn ya wuce parking space…motanshi ya bude ya shiga itama tana karasowa ta shiga sai turo baki take…bayan sun dauki hanya ta dan saci kallonshi ganin yana driving..tunda suke bata ta6a ganin ya tuka kanshi ba saidai yayi d’urum a baya mota ana driving dinshi yau kuma wane salon ne yasa shi driving din oho?…motan yayi tsit ba abunda kakeji sai sanyin ac dake tashi…wayanshi dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing…yayi connecting Bluetooth snn ya daga..daga daya 6angaren da igbo Mummy tace”Bobby where are u?..”shima da igbo din yace mata”ina kan hanya Mummy..what happened?..”tace”jikin yarinyar nan ne naga kaman gaba yakeyi wlh..ko asibitin zamu kawota?..”yace”aah Mummy gani nan zuwa gidan yanxu”..Mummy tace”to kayi sauri dan Allah”..yace”toh..”snn ta kashe kiran…Lamido data kasa kunne tana jinsu bata fahimci komai a zancen nasu ba tace”kilan mamarshi ce”…yaji abunda ta fada sarai kulata ne kawai baiyi don a yanda ta kular dashi tsaf zai iya kwada mata mari wlh…haka ta ringa baza ido tana kalle kalle har suka iso kafar gidansu…maimakon ya shiga da motar ciki sai yayi parking a nan waje ya bude motar ya fita ya wani sake hade ranshi yace”saura kuma ki fito daga ciki kiga me zanyi maki”…tabe baki tayi ta kauda kai shi kuma ya juya ya nufi gate..kwankwasawa yayi mai gadi na lekowa yaga shine ya bude mishi da sauri ya shige cikin gidan…Lamido na ganin ya shiga ta bude motar ta fito tana karema gidan nasu kallo tace”ai wlh saina fito na bawa idona abinci”..sake juyawa tayi tana kallon zabgegen mansion din tana girgiza kai tace”gaskia mutumin nan me kudi ne..ji gida kaman ba’a Naija ba ni Aisha”..karasawa tayi jikin gate din ta shiga lekawa ta wata ‘yar karamar kofa kamar daga sama taji an danne mata horn ta bayanta…a rikice ta matsa daga wurin tana kallon motar dake kokarin shiga gidan sai tayi saurin komawa inda motarshi yake kafin ta shiga taji ance”yammata”..juyawa tayi tana kallon matar duk sai taji kunya ya kamata tana leka musu gida..ta shiga washe baki tace”ina..ina yini”..aunty sumy ta bude mota ta fito zuwa inda take tana kallonta da fara’a tace”lafia lau yammata..zaki shiga ciki ne?..”da sauri tace”aah tareda proprietor muke shine nake jiranshi”..ta karasa mgnr duka daburce kaman matsoraciya…aunty sumy ta saki smile jik tareda Bobby suke tace”to mu shiga daga ciki mana saiki jirashi a can”..tun kafin ta rufe baki Aysha tace”aa ba saina shiga ba wlh..yace kar in shiga”..dafa shoulder dinta aunty sumy tayi tace”karki damu bazaiyi maki komai bafa..aini nace ki shiga sbd haka muje plss”…narkewa tayi tana kallonta kafin tayi mgn aunty sumy ta sake fadin”please!..”haka nan ta bita suka cikin gidan ba don tanaso ba…mai gadi taba key ya shigo mata da motar snn suka wuce…matar ce tayi mata kwarjini wlh amma ita sam bata son shiga yazo yana wulakantata…suna shiga compound ta ware idonta tana kallon lafcecen compound din dake zube da uban motoci kaman na siyarwa..cikin ranta tace”babban burin inyamuri a dunia kenan..a danqara gida snn a hau motoci”..ganin bata daga kafa aunty sumy ta kama hannunta suka nufi entrance…basu samu kowa central parlor ba dan haka direct ta nufi parlon Mummy da ita…Mummy na zaune da Ilham akan cinyarta shi kuma yana rikeda hannun ilham din yanayi mata alluran jijiya..yarinyar tayi luf jikin Mummy sai sauke numfashi take…saida suka isa ciki aunty sumy ta saki hannunta tana doka wani uban murmushi tace”Mummy ga bakuwa na kawo maki”…dagowa Mummy tayi tana kallon yarinyar da kanta ke kasa kafin tace”to bismillah zauna kinji bakuwa”..karasawa tayi ta zauna a hankali har yanxun kanta yana kasa…Bobby da sai yanxun ya gama mata alluran yana dago kanshi yayi ido biyu da ita tana zaune kusada aunty sumy sai wani sussunne kai take…cikeda mamaki sosai yake kallonta yace”ke bakida hankali ne?..waya baki izinin shigowa gidan nan?..”juyawa Mummy tayi tana dubanshi tace”ka santa ne?..”dauke kai yayi yana huci ya kasa cewa komai…tambayoyin nan ne bai shirya amsawa ba shiyasa yace tayi zamanta cikin mota amma sbd tsabar rashin ji irin nata saida ta fito…yanxu shknn yasan ya shiga uku da tambayoyi a wurin su Mummy…ganin bazaice komai ba aunty sumy tace”ganinta nayi fa a cikin motarshi shine na tambayeta tace tare dashi suke amma yace ta zauna nan cikin mota karta fito”..juyawa Mummy ta sakeyi ta kalleshi sai taga ya sake hade rai yana muzurai sai ta maida dubanta ga Aysha da har yanxun kanta ke a kasa lokaci daya ta saki wani murmushi dan tasan zaiyi wuya idan ba itace Lamido ba dan haka tace”yammata meye sunanki?..”a hankali tace”Aysha”..Mummy ta shiga gyada kai tace”MashaAllah Aysha me babban suna ce ashe?..”daga kai kawai Lamido tayi tanajin kamar ta saki fitsari a wando sbd yanda takejin idanun Bobby nata kaiwa da kawowa a kanta..ko baa fada ba tasan kallonta yake…Miemie ce ta shigo parlon rikeda tea data hadoma Ilham..tana karasowa ta mikawa Mummy snn ta zauna tana kallon Aysha dake zaune tace”Mummy bakuwa mukayi?..”Mummy da har yanxu bata bar smiling ba tace”wlh bakuwa mukayi Miemie”..Miemie ta matsa kusada ita tace”sannu da zuwa ina yini?..”dan dagowa Aysha tayi ta kalleta kafin tace”lafia lau”..wara ido Miemie tayi da taga face dinta tace”laa Mummy ai na ta6a ganinta a FCNM wall…”bata samu karasawa ba sbd wani kallo da Bobby ya watsa mata ba shiri taja bakinta yai tsit..aunty sumy da tun daxu take kallonshi ganin yanda duk yabi ya takura kanshi kawai ta saki murmushi..ita bata ta6a ganin mai hali irin na Bobby ba wlh..kiri kiri ga abu kana sonshi amma wai kake kaiwa kasuwa?…mikewa Mummy tayi ta ba aunty sumy tea din Ilham tace”ki bata tasha”..snn ta karasa inda Malama A’ee take zaune ta kama hannunta ta mike tsaye snn ta jata zuwa dakinta tace”tashi muje mu gaisa ‘yata”…daga haka suka shige bedroom din Mummy..Bobby yabisu da kallo kaman idanunshi zasu koma jikin kofar dakin…hankalinshi yaji ya tashi kardai Mummy taje ta fadama yarinyar nan abunda zaisa ta rainashi fa..gabanshi har wani faduwa yakeyi wlh…kaman wanda aka tsikara yabi bayansu zuwa dakin da sauri kamar zai tashi sama…