Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
31
Yana shiga ya marairaicewa Mummy yace”Mummy dan girman Allah mu tafi..bama ta da lafia shine na kaita asibiti”…murmushi Mummy tayi kafin tace”to ka jiramu a waje yanxun nan zata fito”..da sauri ya canxa yare yace”Mummy me zaki fada mata?..”da yaren itama tace”akwai abunda kake 6oyewa wanda bakaso ta sani ne?..”girgiza kai yayi da sauri duk yabi uzzurawa kanshi babu gaira babu dalili…kofa Mummy ta nuna mishi alaman ya fita haka ya juya ya bar dakin yana sake sake…bayan fitarshi Mummy ta dawo da dubanta ga Aysha tace”zauna mana Aysha”..maimakon ta zauna saita risina har kasa tana kallon kasan tace”Ina yini”..Mummy ta amsa da”lafia lau..ya karatu?..”tace”Alhamdulillah”..Mummy tace”to dawo nan ki zauna tunda mun gama gaisawa”..ba musu ta mike ta zauna inda ta nuna mata…kallonta kawai Mummy keyi taji ta shiga ranta sosai…irin wnn kyau da take dashi ai ba Bobby ba kowane namiji ma yana iya samun matsala idan aka jarabceshi da qaunarta…tana cigaba da dubanta tace”da gaske bakida lafia?..”kai kawai ta iya dagawa…Mummy tace”to Allah ya baki lafia..yanxu bari a kawo maki abinci kici”..da sauri tace”wlh mama na koshi banajin yunwa”…Mummy ba girgiza kai tace”aah dole kici wani abu”..daga haka ta kwaloma Miemie kira…tana shiga Mummy tace”jeki kawo mata abinci”…kafin ta fita Aysha tace”wlh ban dade da cin abinci ba banajin yunwa”..Mummy tace”to shknn dukda haka dai ko tafiya sai kinyi dashi…Miemie ki samu abu ki zubo mata pepper chicken sai ki hada mata da lemo”..ba musu Miemie ta fita don yin yanda aka sata…suna nan zaune ta dawo da wani bag mai kyau datasa pepper chicken din a ciki…Mummy tace”to ki rike mata saiki rakata waje dashi”..a hankali tace”toh..”snn ta juya ta fita…mikewa Mummy tayi zuwa wadrobe dinta ta dauko wasu turaruka masu kyau guda biyu ta zuba mata su cikin dan karamin jaka mai kyau snn ta bude drawernta ta dauko two sets na sarkoki suma masu azabar kyau duk ta zubasu cikin jakan…hajia indo dai tana zaune kai a kasa kamar munafuka..hannunta Mummy ta kama suka fita daga dakin…Bobby daketa safa da marwa ya juya yana kallonsu kamar idonshi zasu fadi kasa..saida daria ya subucewa Mummy sbd ganin yanda duk yabi ya addabi kanshi ba gaira ba dalili..shi kuma ya wani kwabe fuska da igbo yace”Mummy me kike ce mata dan Allah?..”bayan ta staida dariyarta tace”gata nan ka maidata kuma wlh ban yadda kayi mata fada ba Bobby..idan kayi kuma zai dawo kunnena”..daure fuska kawai yayi baice komai ba…aunty sumy ma ta fito daga dakinta rikeda wani dan box mai kyau tana karasowa ta mikama Aysha tana murmushi tace”to ga wnn Aysha..i hope zaki sake kawo mana ziyara?..”murmushi kawai tayi bata iya amsawa ba duk sun sata jin wani iri wlh..sunada kirki sosai unlike Proprietor da sukayi hannun riga da kirki…ta amsa abun tayi godia..Mummy tace”ai zai sake kawota mu gaisa”..aunty sumy tace”kwarai kuwa..idan ma bai kawota Mummy da kaina zanje har hostel dinsu in dauko mana ita”..shidai yana fsaye fuskan nan a tamke baice musu kala ba…after long surutunsu finally ya samu aka bashi ita suka fita..Miemie ta rakata har mota da kayanta ta zuba mata su back seat snn ta zaga inda take da nufin tayi mata sallama Bobby dake cika yana batsewa ya wani 6alla mata harara tareda fadin”bar nan”..ba shiri ta koma ciki tana turo baki…tada motar yayi da wani irin gudu suka bar layin nasu..Ita dai a tsorace take sai rarraba idanu take…suna hanya wayanta ya fara ringing ganin wanda ke kira sai tayi silencing wayar taki dauka sbd gudun masifanshi…sake kira akayi ta kuma sawa a silent shi kuma ganin batada niyyar dagawa yakai dubanshi kan wayar dake cinyanta sai yaga baby boo kan screen aikuwa ya sake dinke fuskanshi tsaf yana sake figan motan a guje kmr zai tashi sama…gani take kaman tsoron dunian nan a kanta ya sauka wnn uban gudun da yake idan yaje ya watsar dasu fa?..bata dai ce masa komai ba har suka isa gate din hostel…ya cire mata lock ba tarefa ya kalleta ba yace”fita”..da sauri ta kama kofar zata bude sai kuma taji yace”bana hanaki kiramin wani besty idan muna mgn ba?..ke wato bakyajin mgn koh?..”da sauri tace”kayi hakuri”..yace”sbd kinga banaso shiyasa kike fada wato koma me zanyi inyi koh?..”ta dan lankwasa wuya tace”sir nace fa kayi hakuri”…dauke kanshi yayi daga gareta yace”fitamin daga mota”..ta sake langabewa tana kwabe fuskanta tace”sir i said am sorry mana..kayi hakuri bazan kara ba”…juyo da kanshi yayi yana kallonta yace”idan kika kara inyi maki me?..”hannu takai tana shafa cheeks dinta kafin a hankali tace”ka mareni”..murmushi kawai ya saki tareda jinginar da kanshi jikin kujera..dama yasan fushin ma ba wani iyawa zaiyi da ita ba..itama murmushin ta saki tace”sir kacigaba da smiling dan Allah..yana maka kyau”..bude idonshi yayi ya zubasu a kanta..wasu sabbin al’amura yakeji suna zagayawa cikin jini da tsokarshi…mikewa yayi daga inda ya jingina still yana dubanta ina serious note yace”da gaske banason jin wani besty ko waye a bakinki..banaso idan kuma kika sake kiramin shi muna mgn marinki zanyi kaman yanda kika fada”..murmushi take tace”bazan ma kara ba inshaAllah”..yace”shknn u can go..and make sure kinsha drugs dinshi akan lokaci kuma banda skipping idan ba haka ba kuma alluran da bakiso shi za’a kuma yi maki”…bude motar tayi ta fita still tana murmushi tace”aah banason allura zansha maganin..saida safe”..kanshi kawai ya iya daga mata snn ta juya ta tafi bayan ta kwashi kayanta dake baya…saida yaga shiganta ciki snn yaja motarshi ya kara gaba.

Tun daga wnn ranan suka sake dinkewa abunsu…tanajin magananshi sosai and hakan ba karamin farantawa Bobby yake ba..zuwa yanxu ya gama admitting ya kamu da soyayya..soyayya kuma na bafulatana data fito daga jihar Gombe..what a miracle..tunda yake bai ta6a tunanin zaiso wata mace ba ballantana ‘yar Gombe amma ita sai yaga kaman turota akayi dan tazo ta wargaza duk wani tanadi da alqawura da yayima kanshi…shida yake shiga college only Thursdays da Fridays amma yanxu kusan kullum sai ya shiga sbd kawai ya samu ya ganta domin ganin nata shine kadai samun nustuwarshi…yanayi mata sonda shi kanshi bai tunanin yana yiwa kanshi amma har yanxu ya kasa nuna mata dukda yasan wani lokacin actions dinshi suna nunawa sbd kasa controlling kanshi da yake amma ita kota fahimta bata ta6a nuna mishi ba…abu biyu dake damunshi sune na farko amanarta da mahaifinta ya bashi yana gudun kada mgnr sonda yake mata ya fita shi kuma mahaifinta yaga kamar bai rike mashi amana ba tunda har shi da kanshi zaice yana sonta..sai na biyun kuma shine Gombe..bayan kasancewarta ‘yar Gombe muma tazo a bafulatana..har yanxu bai mance yanda ‘yan uwan dad dinsu fulani sukayi treating Mummy ba..shima yana tsoron kada yaje neman aurenta ace dan inyamura ne shi baza’a bashi ba..ga kuma su kansu ‘yan uwan daddyn da matukar zaiyi aure dole saiya nemi inda suke sbd su shige mishi gaba kan mgnr saidai sam baiji zai iya zuwa ya samesu ba..har yanxu yana nan akan bakanshi na babushi babusu amma kuma tayaya zai samu auren Lamido ba tareda sa hannunsu ba?..gaba daya ya zama wani iri yanxu ko abincin kirki baici..aiyukan nashi ka neman tsaywa suke cak sbd damuwar da yake ciki..har dan ramewa yayi sbd tunani..Mummy tayi tayi dashi ya sanar mata abunda ke damunshi amma kullum mgnrshi daya shine babu komai…ganin yana neman rasa nutsuwarshi yau dai ya yanke shawaran zaije ya samu Nur suyi mgn ko yanada solution da zai bashi…gashi itama yarinyar wahalar dashi takeyi these days baisan laifin da yayi ba duk ya kirata a waya bata dauka…hankalinshi ba karamin tashi yayi ba yau kusan 5 days knn baiji muryanta ba kuma bai ganta ba dan haka yake jin kanshi kaman mara lafia..baisan meyasa take mishi irin wnn ba..haka nan babu laifin zaune babu na tsaye saita dauke mishi wuta sai yayita binta yana lallashi snn zai samu kanta amma this time around yace bazai ske nemanta ba inyaso sonta yayi ajalinshi shima sai ya samu ya huta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button