Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Ita kuwa tana fita ta kama hanyan class dinsu tana fadin”kam lallaima mutumin nan wani wai yana sona?..to ni ko rasa miji nayi me zanyi da inyamuri Allah na tuba…Allah ya kiyaye na auri dan yaro ma kamanshi wlh..aini matar manya ce ba matar irinsu kananun yara ba..dan rainin wayo kawai”.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
32
Da misalin 9 na dare yana zaune dinning yasa abincinshi a gaba amma ko loma daya ya kasa kaiwa bakinshi…goshi ya dafe da both hannayenshi yanatunanin abubuwanda suka faru…kawai gani yake dalilin kauracewa yan uwan daddy da yayi Allah yakeson ya hukuntashi da ita…shi gani yake wnn abun da yakeji gameda ita yayi yawa…tunda yayi mgn da ita zuwa yanxu bai samu peace of mind ba sbd yanda tayi reacting da yace yana sonta..kawai tasa mishi kuka sbd da gaske ta tsaneshi ne ko kuwa sbd tsabagen ta6ara da yake dawainiya da ita…yayi zurfi cikin tunani har baisan sanda Mummy tazo ta zauna kusadashi ba sai hannunta da yaji ta dafa shoulder dinshi..da sauri ya dawo hayyacinshi tareda daukan spoon dake nan cikin abincin nashi da sauri ya shiga cin abincin kamar mayunwaci..bayason ta gane halinda yake ciki baisan kuma ta riga ta gano ba…batace mishi komai ba sai kallon yanda yake tunkuda abincin take tana jira ya gama suyi mgn dan yau ko yaki ko yaso saiya sanar da ita damuwarshi…tausayi yake bata yanda yake kokarin 6oye suffering dinshi bayan bayyanawa kadai ne maslaha…bata katse mishi cin abinci ba saida ya gama ya kora da drink snn ta kira sunanshi…kasa amsawa yayi sai juyawa da yayi yana kallonta…kallonshi takeyi itama sosai tace”Bobby wai meye matsalarka?..why kake kokarin 6oye abunda ba kai ka dorama kanka ba kuma 6oyewan bazai haifar maka da komai ba..kanaso ciwon zucia ya kamaka sbd wnn damuwan daka dorama kanka ne?..baka tunanin halinda ni da ‘yan uwanka zamu shiga idan wani abu ya faru dakai?..duk bakayi wnn tunanin ba kake kokarin cutar da kanka koh?..”shiru kawai yayi yana kallonta yasan duk mgnr data fada gaskia ne..da gaske abunda yakeji bashi ya dorama kanshi ba..kuma kokarin 6oye hakan ba abunda zai haifar mashi sai dana sani amma ya zaiyi?..soyayya ne Allah ya jarabceshi dashi na yarinyar nan kwata kwata bai ganin zata soshi..shi kuma so yake ya yakiceta daga zuciyarshi amma zuciyar taki bashi hadin kai dama tun ba yanxu ba yasan zuciyarshi tafi shi kanshi taurin kai sbd yanda yayita kokarin dakatar da abun tun yana dan karami abun bai yiwu ba har yanxu aka kawo wnn matakin…yasan yanxu tana gama makaranta kilan a hadata da wani ta aura ko kuma ta fitoda wanda takeso tunda tasha fada mishi ita tanada wanda zata aura…tunanin hakan yasa yaji wani irin nauyi a cikin zuciyarshi…idonshi suka kada sukayi jaa har wani shinning suke sbd dan kwalla daya cikosu…da sauri ya kifa kanshi jikin Mummy ya sauke wani ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya koshi…numfashinshi ma da kyar yake shaqa sbd kokarin 6oye hawayenshi da yake…baison Mummy ta gani shiyasa yayi haka amma yasan da kyar ma idan bata gani ba…saida ya dauki almost 3 minutes a haka kafin ya dago daga jikin nata yana sauke kanshi kasa…wnn raunin da yake zuwa mishi duk yayi mgn da itane bayaso shiyasa bai cika son yin mgnr da itaba..da akwai wani irin rauni da karyewar zuciya dake zuwa ma mutum duk yake gaban mahaifiyarshi idan ya tsinci kanshi cikin wani yanayi mara dadi…baisan ko kowa haka yakeji ba amma shidai haka yake tun yana dan karaminshi…hannu Mummy takai ta dago fuskanshi tana kallon idanunshi da har yanxun suke shinning sbd hawaye da suka kuma taruwa a ciki tace”let them out son..zakaji sauki”..da sauri ya sauke kanshi yana sake kokarin mayar dasu amma wnn karon sai yaji kamar turosu akeyi da gayya dan haka ya sake maida kanshi jikinta da sauri daidai lokacin kuma hawayen suka silalo kan fuskanshi…bayanshi Mummy ta shiga shafawa a hankali itama nata muryan a raunane tace”cry as much as u want zaka samu sauki”..shidai bai iya cewa komai ba sai hawaye da har yanxu basu dena zubowa fuskanshi ba…mamaki da haushin kanshi suka dirar mishi lokaci guda…shi kanshi he can’t remember when last ya zubar da hawaye da idonshi amma wai yanxu shine ke kuka sbd karamar yarinya..wnn wace irin jarabawa ce?..some months back idan kace mishi zai kamu da soyayya kuma har yayi kuka sbd wata mace kallon you are not normal zaiyi maka amma yanxun gashi dumu dumu cikin soyayya snn kuma gashi yanata kwararar da hawaye abunda zai iya cewa rabonshi dayi tun bayan rasuwar mahaifinshi…Allah ma yasoshi ba kowa a wurin da kunya zaiji wlh…Mummy ce tasa hannu ta dagoshi tana goge mishi hawayen da yayi saura fuskanshi kafin tace”fadamin..what exactly happened?..”hannunta ya kama duka biyun yana dubanta cikin voice dinshi daya fara disashewa yace”she doesn’t love me Mummy..she despise me..da bakinta tacemin tanada wanda zata au..”kasa karasawa yayi sbd wani abu dayazo ya tokare mishi wuya..sake dora kanshi yayi shoulder dinta yana jujjuaya kan nashi from side to side yace”mutuwa zanyi Mummy…wlh duk ranan da ta auri wani i won’t survive zuciyata bugawa zatayi in mutu Mummy ki taimakamin please!..”rungumeshi Mummy tayi itama nan take hawaye suka ciko idanunta tace”u won’t die inshaAllah..Bi’iznillah batada mijin aure sai kai sbd haka ka kwantar da hankalinka”…girgiza kai yacigaba dayi yace”Mummy wlh i can’t..dan bakisan yanda mukayi da ita bane..she even cried da nace ina sonta kuma nasan halinta Mummy da gaske bata kaunata shiyasa takemin haka…bansan meyasa Allah zai…”bai karasa ba Mummy tayi saurin rufe mishi baki tana cewa”karkayi sa6o Bobby..kayi hakuri mubi komai a sannu inshaAllah komai zai wuce..komai zai zama tarihi”…wani numfashi ya sauke mai karfi tareda fadin”Allahumma Ameen Mummy..Allah sa ya zama history kaman yanda kikace”..tace”Ameen InshaAllah..yanxu tunda ka gama cin abincin ka samu kaje ka kwanta naji jikinka da zafi anya ma zaka iya bacci a haka kuwa?..kodai muje asibiti?..”girgiza mata kanshi yayi kafin a hankali yace”don’t bother haka yakeyi dama”..da mamaki tace”u mean haka kake kwana da fever kullum kuma bakayi kokarin kayi wani abu ba?..”dagowa yayi ya kamo hannunta yace”Mummy ai bai dade da farawa ba..for the past few weeks ne kawai and inashan magani”..girgiza kai Mummy keyi tace”ban yadda ba..nasan ba maganinda kakesha”..yace”da gaske inasha Mummy..kinsan bazanyi wasa da lafiyana ba”…tace”ya kamata dai kar kayi wasa dashi din idan kuma baso kake Lamido tace batason mai yawan rashin lafia ba”..da murmushi ta karasa mgnr aikam shima saiga wani hadadden murmushi kwance akan fuskanshi…Lamido kawai da aka kira yaji kaman anyi mishi gagarumin kyauta wnn baisan yanda zaiji duk akace ta zama matarshi ba…ganin yanda Mummy ta tsareshi da ido sai ya mike yayi mata sallama ya kama hanyar Flat dinshi…da kallo Mummy ta bishi tausayinshi na sake kamata..ta tabbata authentic so yakema yarinyar nan har tunda taga yayi abunda ita kanta ta manta yaushe rabonda yayi shine hawaye…addu’anta bai wuce Allah ya karkato da hankalin yarinyar kanshi ba snn yasa ayi komai da komai cikin sauki da kwanciyar hankali.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button