Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiko Bobby yana shiga Flat dinshi kulle kofanshi yayi ya wuce direct zuwa bedroom dinshi…bayan yayi wanka yasa pyjamas dinshi snn ya kwanta ya dora wayanshi kan kirji wani sashe na zuciyarshi sai azalzalanshi yake ya kirata ko muryanta yaji yasan zai danji sauki yayinda daya sashen kuma yake cewa idan har ya kirata bayan duk wulakancin da tayi mishi daxu to ya tabbata a kirashi da mara zuciya…shiru yayi gamida runtse ido yanajin shawarwarin da ko wane sashe na zuciyar ke bashi…shi kanshi yayi na’am da kin kiran nata dan haka ya sake kulle ido ya lullu6e da duvet shi a lallai bacci yakeso ya daukeshi sbd kwata kwata bayason yawan tunanin nan da yake amma kememe bacci yace baiga daman daukanshi ba..haka ya karaci juyi yana rungume pillow daga karshe dai dole kasa daurewa yayi saida ya danna mata kira…har ya gama ringing bata dauka ba dan haka ya sake kira..yana gab da katsewa ta daga cikin magagin bacci tace”baby ka bari in tashi daga bacci sai muyi waya kaji?..”wani irin abu yaji yazo ya tokareshi a wuya har numfashinshi na barazanar daukewa…bai iya ce mata komai ba ya kashe wayarshi gaba daya…ita kuma jin baice komai ba ta dago wayan tana kallon screen sai taga proprietor a jiki nan take baccin dake idonta ya wartsake ta wani zare ido tareda fadin”na shiga uku”…sam bata duba wanda ya kira ba tayi zaton shine tunda daxun yace mata idan ya isa gida zai kirata..hankalinta taji ya tashi tasan yanxu da kyar idan basuyi rigima dashi ba..sake kiran wayanshi tayi amma har ya gama ringing bai dauka ba..data sake kira kuma sai taji wayan gaba dayanta ma swicth off…haka nan ta hakura ta kwanta tana tunanin yanda zasu kwashe dashi gobe…shi kuma Bobby tsabar 6acin rai ne ya hanashi mgn…sbd wulakanci shine zai kirata ta wani kirashi da sunan saurayinta sbd bata da hankali..haushin kanshi ka yaji ya kamashi ga zafi da zuciyarshi ke mishi..shidai ya hakura da yarinyar nan kawai inyaso idanma mutuwa zaiyi sbd ya mutu amma bi’iznillah bazai sake nuna yanada wani feeling gameda itaba tunda ita batasan mutuncin hakan ba…wnn daren ma kamar sauran saida dare ya tsala sosai snn ya samu bacci.

Washegari Thursday ranan shiga college dinshi ne amma yana sane yace bazaije ba sbd bama yaso ya ganta ballantana ya karya alkawarin daya daukan ma kanshi…ko a gida bai zauna ba ya shirya ya tafi hospital sbd yasan idan Mummy ta ganshi a gida zata tashi hankalinta ne and shima kanshi yana bukatar ya fita ko dan wani wurin ne yaje at least zai shaki fresh air.
Lamido na shigowa makaranta ta nufi office dinshi kaman yanda yace kullum taje ta gaidashi da safe and ita kanta tanada bukatar yin mgn dashi akn abunda ya faru jiya..ga mamakinta bata sameshi office dinba haka ta koma class tana sake trying numbershi yana shiga amma bai dauka ba…suna fitowa break ta sake komawa office din nashi still baya nan kuma tanata kiran wayanshi har ta gaji bai dauka ba…hankalinta ya tashi sosai tasan yanxu kilan yace zai hadata da daddy…tasan dan abu karami ke 6ata mishi rai amma ita ai bada niyua tayi ba…ranar har suka bar school bata ganshi ba kuma bai dauki wayanta ba…hankalinta ya tashi fiyeda yanda take zato duk sai taji wani iri dan tunda suke bai ta6ayi mata haka ba…a ‘yan kwanakin nan da yake mata mutunchi ta fara fahimtan waye shi…sure tasan yanada fada amma kuma yanada kirki and yasan darajan mace…gaba daua jinta take wani iri addu’anta bai wuce Allah yasa kada ya hada da daddy ba.
Washegari friday same thing happens shima har suka tashi Lamido na nemanshi bata ganshi ba wayanshi kuma tun yana kin dauka har ya fara rejecting call din…hankalinta yayi mugun tashi har hakan yaso bata mamaki dan bata taba tunanin zata damu haka ba…da dadewa tasan ta saba dashi amma batasan sabon yakai hakaba sai yanxu…koda yake bataso ya hadata da daddy ne shiyasa hankalinta yaki kwanciya…a takaice saida ta kwashi three days tana nemanshi bata samu ganinshi ba…ranan Sunday tana zaune dakinsu itca kadai saida ta bari Billy ta fita snn ta kira Nur a waya sbd tasan idan sukayi mgn a gabanta zatacigaba da cewa soyayya ne tsakaninta dashi ita kuma bata son haka..yana dauka tace”sir dama ina neman proprietor ne”..Nur yace”baki sameshi a waya ba?..”a hankali tace”baya dauka”..da mamaki Nur yace”ban gane baya dauka ba?..”tace”sir inata kira bai dauka..rejecting call dinma yakeyi”..Nur ya danyi shiru for some minutes before yayi adding”kinyi mishi laifi knn?..”a hankali tace”sir kawaifa kirana yayi bansan shi bane na zata baby ne shknn fa yaketa fushi dani har yanxu..kuma sir ni ina tsoron kar ya hadani da daddyna”..shiru Nur yayi yana saurarnta yana murmushi…addu’a yake Allah yasa itama ta damu dashi koda baikai rabin damuwar da yayi da itaba..saida ya gama smiling dinshi before yace”bani two minustes inyi mgn dashi”..a hankali tace”toh”snn ta kashe wayar…suna gama mgn Nur ya dannawa Bobby kira..ringing biyu ana uku ya daga da sallama…Nur yace”maza ina ka shigane kwana biyu?..”Bobby yace”wlh banjin dadi ne shiyasa kajini shiru..ya aiki”..”Alhamdulillah kana gida ne?..”Nur ya tambayeshi kai tsaye shi kuma ya amsa da fadin”no ina hospital”…da sauri yace”ohk gani nan zuwa asibitin yanxu..bakada lafia ne naji muryanka somehow?..”ajiyar zuciya Bobby ya saki before saying”sai kazo din dai kawai”..Nur ya amsa da”ohk”..daga haka kowa ya ajiye waya..sake kiran Lamido Nur yayi tana dauka yace”munyi mgn dashi yace yana hospital yanxu haka..ko zaki shirya in kaiki?..”shiru tayi tana nazari for a while sai kuma a hankali tace”toh..”yace”ki shirya yanxu gani nan zuwa”..ta sake amsawa da”toh..”snn ta kashe wayar..mikewa tayi ta dora dogon hijab akan jessy da straight skirt dake jikinta..tazo fita daga dakin saiga Billy ta shigo ciki..kallonta takeyi from sama zuwa kasa tana ta6e baki tace”ina kuma aka nufa hakia indo?..fushin ya kare knn?..”wani irin harara Aysha ta watsa mata snn ta bangajeta ta fice daga dakin Billy ta bita da kallo baki bude tana cewa”anya kuwa Lamido batada aljanu?..”

A hankali take tafiya har ta iso first gate na hostel din dan haka Nur na karasowa bai karasa ciki ba yayi picking dinta a nan suka wuce…suna hanya da yaga yanda tayi shiru ta zubama spot daya ido yace”duk Dr Bobby ya sanyaki a damuwa koh?..”da sauri ta daga kai tana cewa”eh mana..kumafa ni banga abun jin haushi a mgnr dana fada ba”..murmushi Nur yayi yana girgiza kai cikin ranshi yace”ai bazaki ganiba dama”..daga haka ba wanda ya sake mgn cikinsu har suka iso Freedom…yana gama parking duk suka bude mota suka fita zuwa cikin asibitin…saida sukazo daidai office dinshi taji wani irin faduwar gaba ya risketa..ko wane kalan masifa zai sauke mata oho?…Nur ne ya fara tura kofar ya shiga kafin itama tabi bayanshi…Bobby dake kwance kan sofa ya bude idanu a hankali ya saukesu kan Nur then back to Lamido dake tsaye bayanshi sai faman sunkuyar dakai take…da sauri ya mike zaune yana kallonta da kyau duk idanun nan a waje kaman yaga abun tsoro..yakai hannu yana murza idanuwan nashi wai ya tabbatar ba mafarki yake ba ba kuma gizo take mishi kmr yanda ta saba ba..ganin da gaske itam ce nan tsaye a gabanshi baisan sanda ya wani daure fuska yana kallonta ba…a hankali tayi kasa da idonta tanajin yanda tsatstareta da wnn idanun…kafin tayi mgn ya nuna mata kofa yace”out of my office”..da sauri ta dago tana kallonshi wnn karon shi ya kawar da nashi idon kafin ya sake fadin”i said ki fitarmin daga office”…kafin tayi mgn Nur yace”Haba Bobby”..k kallonshi baiyi ba ya sake nuna mata kofa ita kuma tayi tsaye taki tafia kawai sai ya dafe head dinshi da hannu bibbiyu yana sauke numfashi…ganin haka Nur ya dan matsa kusada ita murya can kasa yace”karki yadda kibar office din nan ba tareda kun daidaita dashi ba..idan yacigaba dayi maki masifa kawai kuka zakisa shknn kinyi maganinshi”..yana gama fadan haka ya juya ya bar office din..jin karar kofa ya sashi bude ido sbd yana tunanin itace ta fita amma sai yaga Nur ne…sake dawo da kallonshi yayi gareta murya can kasa yace”ba cewa nayi kibar min office ba?..”da sauri tace”sir dan Allah kayi hakuri”..girgiza mata kanshi yayi yace”kimin laifi ne kike bani hakuri?..”kwabe fuska tayi zatasa kuka tace”nifa bansan kaine ba Allah”..kallonta kawai yake ganin zata fara mishi kuka bayan ba abunda yayi mata..shi baisan dalilinda yasa ma Nur ya daukota ya kawo mashi ita har nan ba..ajiyar zuciya ya sauke gamida dauke kanshi daga gareta ya sake komawa ya kwanta kan sofa…ita kuma ganin yanda yaba banza ajiyarta sai ta daddage ta rushe da kuka kmr yanda Nur yace tayi..da dadewa tasan bayason kuka tasan kuma shine kadai abunda zatayi ya saurareta…sake runtse ido yayi jin yanda take mishi kuka ya dauki throw pillow ya danne face dinshi dashi wai ko zai denajin kukan nata amma a banza..da dane ya tabbata ko zata shekara tana kuka a gabanshi bazai dameshi ba amma yanxu wani irin rauni kukan nata ke haifar mashi..sai yaga kaman yayi mata wani abun alhalin kuma ba uwar da yayi mata..har cikin zuciyarshi yakejin kukan..kasa daurewa yayi ya mike zaune yana kallonta da idonshi da sukayi red yace mata”wani abun nayi maki da zaki sani a gaba kina kuka?..”cikin kuka tace”sir kaine fa kaki hakura”..yace”cewa nayi ban hakura ba?..ni bakiyimin laifin komai ba kawai kije I don’t want to see u”..haushi sosai mgnrshi ya bata dan haka ta juya a fusace zata bar office din garin sauri ta take hijab dinta dake jan kasa aikuwa ta tafi luu saura kiris ta fadi Bobby yayi hanzarin mikewa ya tareta a jikinshi…ta runste ido tana sauke numfashi dan yanda ta gama tsorata ta gama sadakarwa zata jita a kasa sai kuma taji ba haka ba…shi kam kallonta kawai yakeyi kaman an aikoshi…the more ya kalleta the more yake sake ganin asalin beauty dinta wanda da bai cika gani ba sam…zuciyarshi yaji tayi wani tattarewa ta dunkule waje daya sai wani irin harbawa take da mugun karfi…ya lumshe ido ya bude still yana kallon yanda har yanxu ta kasa bude idanunta baisan ya akayi ba kawai shidai yaji ya hadata da jikinshi..rungumeta yayi da kyau yana sauke numfashi a jere kaman wanda yayi race tareda lumshe ido yanajin wani irin mixed feeling tattare dashi…Lamido kuwa mutuwar tsaye tayi jin yanda ya cacimeta sbd tsabar tsorata kasa ko motsi tayi balle tayi kokarin kwatan kanta..Bobby kuwa is far gone sam bai ankara da abunda ya aikata ba saida yaji ta fara mutsu mutsu a jikinshi..sakinta yayi da sauri yakai hannu ya dafe head dinshi tareda fadawa kan sofa…sai sauke ajiyar zuciya yake kmr wanda yayi tsere..he just can’t believe what happened..he can’t believe he hugged her after all alqawuran daya daukan ma kanshi…runtse ido yayi yana salati dama abunda yske gudu knn shiyasa tun farko yace ta tafi amma taki tafiya…yasan idan yacigaba da ganinta abubuwanda yake 6oyewa suna iya kokarin tona mashi asiri and now see what happened..ya kasa controlling kanshi har yayi hugging nata wanda yakeda tabbacin mutuncinshi ja iya zubewa a idonta…Aysha kuwa shiru tayi ta kurawa spot daya ido kawai tana mamakin abunda yayi mata…gani take kodai aljanu sun shafeshi ko kuma yana fama da serious rashin lafia tunda ga alama nan ta gani yanda yake dafe da kanshi..kuma tasan yana cikin hankalinshi bazai aikata abunda ya aikata ba for she trust him..tasan yanda suke rigima dashi ko wani ya gani tareda ita so ta tabbata bazaiyi hugging dinta for his selfish interest ba..kilan yayi haka ne don ya taimaketa ko kuma sbd wani abu dake dawainiya sam bata kawo wai da gaske sonta yake ba…ganin har yanxu bai motsa ba ta karasa a hankali ta zauna kan one of kujerun office din tana dubanshi murya a hankali tace”sir ai ka hakura koh?..”a hankali ya bude ido yana kallonta..ta wani sake langabewa tace”nace fa bansan kaine ba”..gyada kai kawai yayi kafin ya safe maida eyes dinshi ya rufe..tace”kuma bazaka fadama daddy ba?..”nan ma kan ya daga mata without saying anything..shiru sukayi a office din shi yanajin kaman ya fallasa mata asirin zuciyarshi ita kuma tana tunanin wane irin ciwo ke damunshi da duk yabi ya canxashi haka?..mikewa tayi tana murmushi tace”sir zan tafi”…kai kawai ya sake daga mata ta juya ta fita shi kuma ya sake dafe kanshi yana cije lips dinshi…baisan garin ya yayi loosing control dinshi ba wlh..Allah dai yasa yarinyar nan batayi masa muguwar fahimta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button