Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kwana biyar…
Da sallama ya shigo parlon Mummy ya sameta zaune tana answering call…karasawa ciki yayi ya zauna nan kusada ita saida ta gama wayan ya wani kwa6e fuska yana dubanta yace”Mummy am back..Mummy yunwa nakeji wlh ni yanxu duk kin deddena sona”…dan murmushi ta saki tana kallonshi..cikin ‘yan kwanakin nan ta fahimci yana cikin farin ciki..batasan ko sun daidata da yarinyar ba amma she’s happy seeing him like this…sake kwa6e fuska yayi yace”kuma Mummy ko ki tambayeni yanda mukayi da Lamido”..murmushi ta saki tana kama hannunshi tace”ai nasan tunda na ganka cikin farin ciki these days kilan kun gama daidaitawa da ita”..tana rufe baki yace”a ina?..we are still patching things up dai..kawai inaso tasoni koda baikai wanda nake mata ba”…sake damke hannunshi Mummy tayi tace”zata soka inshaAllah..just continue being a good guy”…murmushi ya saki mai kyau yana shafa lallausan gashin kanshi yace”Allahumma Ameen Mummy..I can’t wait to see that”…dan rankwashi Mummy ta kai mashi a kai tana cewa”rashin kunya kou?..”dafe kan yayi yana dan saki kara yace”ouchh..Mummy da zafi fa”..dungure mishi kai tayi tana hararanshi tace”Comot for this place”..murmushi ya kara saki ya wani makale mata kafada…kallonshi kawai tacigaba dayi full of excitement..seeing him like this really gladdens her heart and she prays Allah yasa ya dore har karshen rayuwarshi…Allah ya mallaka mashi yarinyar nan idan har ta kasance alkhairi a gareshi…ganin yanda taketa kallonshi sai ya dan 6ata fuska yace”Mummy wnn kallon fa?..”murmushinta ta fadada tana fadin”am just suprised and impressed..My Bobby is in love i can’t believe this”..murmushi shima ga kara saki yana cigaba da shafa gashin kanshi kaman zaisa kuka yace”Mummy manaaaaa..am shy plss”..daria ta saki sosai kafin tace”ba wani u are shy bayan har rowarta kake mana..tun yaushe nace maka ka sake kawo mana ita mu gaisa amma baka kawota ba”…yana cigaba da smiling yace”zan kawota Mummy inshaAllah..amma dan Allah idan tazo kar kice mata wani abun plss”..murmushi take tace”bakaso ta sani?..”gyada mata kai yayi tareda cewa”not now”..Mummy tace”dont worry she won’t know anything..yanxun dai take these”..ta zaro wasu papers dake bayanta ta mika mashi…amsa yayi yana dubanta yace”Mummy meye su?..”a takaice tace”ur flight tickets”..kallonta yayi da sauri cikin mamakin abunda tace..kafin ma ya tambayi na meye ta sake cewa”to Abuja”..kallonta kawai yake full of surprise..a hankali yace”Mummy badai ke da kanki kikaje airport siyo mana tickets ba?..”harara ta watsa mishi tace”it’s non of ur business..nasan ba son zuwa kuke ba ai shiyasa nayi maku haka..sai kuje ku fara shiri flight dinku is tomorrow by 4″..kallonta kawai yake kafin ya koma kallon tickets din…na gaba dayansu ne including Miemie da Ilham…sbd tsabar mamaki kasa ce mata komai yayi..shi wlh da yaji shiru ta dena mgnr ma yayi tunanin mantawa tayi ashe tana sane ido kawai ta zuba musu…numfashi ya sauke yana cigaba da duban tickets din shidai Allah ya sani ba son zuwa Abujan nan yake ba..sam baison tafiyan shi baima san ta ina zasu fara ba idan sukayi ido da ido da Wazirin shin gaisuwa za’a fara ko kuwa kallon kallo zasuyi a tsakaninsu…itadai Mummy mikewa tayi ta shiga bedroom dinta shima yaja jiki a hankali ya fita daga parlon nata..knn dai gobe i yanxu suna can Abuja tareda Waziri..what the heck shi baisan ma da wane ido zasu kallesu ba wlh..sam baisan ya haduwan nasu zai kasance ba.
Washegari ko fita baiyi ba dan Mummy hanawa tayi..haka ta tsaresu gaba daya kowa ya dauki kayanshi set daya tunda gobe zasu dawo…Bobby na fitowa daga Flat dinshi ta kalleshi from head to toe kafin ta mike zuwa insa yake tana cewa”koma kasa manyan kaya”…kwabe fuska yayi yace”manyan kaya kuma Mummy?..”tace”yes haka nace..hanga dalilinda zaisa ka tafi wajen grandpa dinka haka ba”…kallonta Bobby yake kaman zaisa kuka yace”Haba Mummy kaman wanda zaije wajen surkai?..”kama hannunshi tayi suka koma Flat din nashi tana fadin”komai abunka bazaka tafi a hakaba wlh..kuma idan ma kayan daka dauka na gobe irin wnn ne then ka sake wasu”…kasa cewa komai yayi suna shiga bedroom kawai ya shiga closet dinshi ya sako wani coffee yadi mai taushi ba tareda yasa hula ba ya fito yace”Mummy amma dan girman Allah ba saina sa hula ba koh?..”kallonshi tayi taga yanda yayi kyau saita saki smile kafin tace”da kasan yanda manyan kaya ke maka kyau da ka dena saka wnn suits din wlh..now wuce muje time na kurewa”..ba yanda ya iya haka ya wuce gaba Mummy tabiyoshi a baya…a central parlor suka tadda sauran suma gaba daya sun fito kowa ya gama shiryawa…haka ta hada kansu suka fita zatayi musu rakiya airport..aunty sumy da Mummy da kuma Miemie suna motan Mummy da driver ke tukawa..shi kuma Bobby yana tareda Ilham da Sab shima cikin nashi motan…duk ranshi a 6ace yake sbd tafiyar nan nunawa ne kawai baiyi sbd Mummy…bayan sun isa airport duk dukayi sallama da ita har zasu wuce Bobby ya sake dawowa inda take yana dubanta kaman wanda zaisa kuka yace”yanxu Mummy ke kadaifa zamu tafi mu bari a gidan..dan Allah ni in dawo su su tafi sbd kar a barki ke kadai”..girgiza kai Mummy tayi tana jan cheeks dinshi tace”nafa fada maka ba abunda zai faru ai akwai masu aiki a gidan”…turo baki yayi yace”nidai dukda haka u take care of yourself”..wnn karon rungumeshi tayi gamida manna mishi kiss a forehead dinshi tace”zan kula inshaAllah..Allah ya kaimin ku lafia ya dawo daku lafia”..a hankali ya amsa da Ameen..da sauri Sab ya matso kusa dasu yana cewa”Mummy nima bakiyi hugging dina ba”..bude mishi hannu Mummy tayi yace”come here dan autana”..da gudunshi kuwa ya fada jikinta kafin ta maida hannu ta rungumeshi snn ta dagoshi shima ta manna mishi kiss a goshinshi…daga nan kuma sai Miemie da Ilham suma duk suka dawo tayi musu aunty sumy dai ba tsaye tana kallonsu…Ilham ce ta kalli mamanta snn ta kalli Mummy tace”Mummy to saura aunty”..dungure mata kai Mummy tayi tace”wa yake ta wani aunty…auntyn da ta girma”..daria gaba daya suka saka nan kuma aka fara announcing passengers su zama ready jirgi ya kusa tashi..a gurguje suka sake sallama snn suka wuce itama Mummy ta shiga motanta driver yaja suka koma gida.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
34
Karfe biyar da wani abu jirginsu ya sauka Nanmdi Azikiwe International Airport Abuja…wani Friend dinshi mai suna Dr Fariq ne yazo ya daukesu daga airport din zuwa Freedom Medical College inda ya ware ma kanshi apartment guda sbd irin wnn lokacin…apartment din na dauke da babban parlor guda daya sai three bedrooms inda shi ya dauki daya Sab ya dauki daya su aunty sumy ma suka dauki daya…gaba dayansu ba wani mai cikakken walwala cikinsu kowa yake kawai yakeyi amma ta ciki na ciki…tunani da kuma zullumin yanda haduwarsu da ‘yan uwan mahaifinsu zai kasance bayan kusan shekaru shidda suke…aunty sumy dai addu’a take Allah yasa karshen komai ke yazo while shi kuma Bobby jikinshi ke bashi ko sunje dinma Waziri ba accepting nasu zaiyi ba har yanxu..kawai ya riga ya sawa kanshi tunda baiyi kokarin sawa a nemosu har tsahon wnn lokacin kilan ba baya sonsu ne..ko kuma bai shirya kar6ansu a matsayin jikokinshi ba…Dr Fariq ne yayo musu takeaway na abinci ya kawo musu dukda basa tareda yunwa…Mummy dake can gida hankalinta gaba daya yana kansu ta kira Bobby tana tambayan ya suka sauka…yace sun sauka lafia sai sunyi sallahn magrib zasuje can asibitin da wazirin yake..dadi taji sosai tareda sa musu albarka..har tausayi yaji ta bashi sbd yanda take mgn..ya tabbata ita kanta tana cikin zullum ko waziri basan amince dasu ba…saida sukayi sallahn magrib kaman yanda yace snn gaba daya suka fito suka nufi asibitinda waziri yake cikin motan Dr Fariq da Bobby ya tuka da kanshi…koda suka shigo cikin asibitin saida gaban kowa ya fadi including Bobby da baisan dalilin faduwar gaban ba…bayan sun fito daga mota suka nufi cikin asibitin da yake nan kaman ba dare ba sbd hasken dake ta ko ina…daida suka tambayi wani sub staff room 105 yayi directing dinsu har zuwa can…a kofar dakin suka tsaya suna kallon kallo an rasa wanda zai fara karfin halin shiga a cikinsu..aunty sumy ce tayi murmushin yake tareda tura kofar a hankali ta shiga da sallama suma duk sai sukabi bayanta…yana kwance kan gado idanunshi a rufe da alama bacci yakeyi..sai wani dan matashi dake zaune kan kujera daga dam gefenshi…kallon kallo aka shigayi tsakaninsu da matashin shi yana musu kallon kamar ya sansu amma ya kasa tuna a ina suma suna mishi kallon saidai ya kasance jika a wajen waziri domin kaf yayanshi sun sansu amd bashida karamin yaro kamarshi…wuri ya nuna musu suka zauna yana kokarin dora murmushi kan fuskanshi yace”sannunku da zuwa”..aunty sumy ta amsa da”yauwa sannu..ya mai jiki?..”yace”Alhamdulillah ya samu sauki”..gyada kai kawai tayi kafin tace”Allah ya kara sauki”..daga nan kuma sai dakin yayi shiru ba wanda ya sake mgn cikinsu…a hankali Bobby ya daga ido yana kallon tsohon da a kallon farko za’a gane jininshi ne sbd kamanninshi daya dauko..mahaifinsu na kama da waziri sosai shima kuma Bobbyn sai ya dauko mahaifinshi…kallonshi kawai yake yana tuna duk abubuwanda suka faru a baya sai yaji ranshi na 6aci..da sauri ya dauke kanshi tareda mikewa tsaye da hannayenshi a aljihu yace”i think we should leave tunda bacci yakeyi da safe sai mu dawo”..babu wanda yayi masa musu cikinsu duk suka mike da nufin su fita sai kawai sukaji am turo kafar dakin wata mata ta shigo sanyeda katon hijab da glass a idanunta…tana dora idanu a kansu ta saki ledan dake hannunta tana zare idanu sosai a kansu bakinta yana motsi alaman she wants to say something…da sauri ta karasa inda suke ta shiga nunasu da finger dinta daya bayan daya har yanxu bakinta bai bar motswa ba amma ko kalma daya yaki fita daga bakin…ta tsayar da idanunta kan Bobby da shima yayi kasake yana kallonta kawai saita rungumeshi hawaye na saukowa fuskanta tace”Bobby is this realy you?..anya ba mafarki nake ba?..”hannunshi yakai shima ya zagayeta dasu snn a hankali yace mata”you are not dreaming”..dagowa tayi tana kallonshi har yanxu bata bar hawaye ba..takai hannayenta tayi cupping fuskanshi dasu tana cewa”my son..where have u been?..ina kuka shiga kuka 6oye nayita wahalar nemanku ban sameku ba?..”kafin yace wani abu ta sakeshi tareda matsawa inda Sabeer shima tayi hugging nashi tightly tana cewa”Sabeer..Sab kaine ka girma haka?..kaine ka zama saurayi haka?..zaka iya tuna ni?..”duk a lokaci daya ta jero mai wadan nan tambayoyin sbd tsabar shock data shiga na ganinsu..bata ta6a tsammanin ganinsu a nan ba..tayi wahalar nemansu na tsahon shekaru amma da yake ita mace ce kuma ba mazauniyar kano ba sai ta kasa samunsu har daga baya ta hakura…shima ta dagoshi tana cupping fuskanshi still tana zubda hawaye tace”baka ganeni ba koh?..”a hankali Sab dake hawaye shima yace”na ganeki”..tace”then wacece ni?..”da sauri yace”Our only aunt…Aunty Munubiya”..yana karasawa ta sake rungumeshi tana fashewa da kuka…su aunty sumy ba gefe suma suna nasu kukan dan hatta Bobby dakeda taurin zuciya yau saida yaji kaman ya zubar da hawayen shima sbd maganganun da take…bayan ta saki Sab saita isa ga aunty sumy…kallon juna suka shigayi kowacce hawaye na tsere a fuskarta ko pump albarka…a tare suka wani rungume juna kowacce tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya…saida suka dauki lokaci mai tsaho haka kafin su sake dagowa suna kallon juna..aunty Munubiya ta saki murmushi da wet face dinta tana dubansu Miemie tace”mu grand kids…haka kuka girma kuma?..”kallonta kawai suke ba wanda yace uffan…hannu ta bude musu tace”come to me kuni?..”ai tun bata rufe baki ba suka karaso da gudu suma suka fada jikinta…shidai wanda ke jinyar Waziri yayi kasake yana kallonsu kaman ya samu movie…hayaniyar da sukeyi ya tada Waziri kawai sai jin tarinshi sukayi..da sauri duk suka karasa inda yake..shi kuma idanunshi na kan Bobby ya shiga kokarin nunashi da hannunshi amma ya kasa…Aunty Munu ta karasa gareshi tana kama hannun nashi tace”Baffa sune..iyalan Attahir dinka ne suka dawo gareka”…har yanxu idanunshi na kan Bobby sai kokarin mgn yakeyi amma ya kasa..a hankali ya dawo da kallonshi ga aunty sumy da Sab kawai sai wani tari ya sake turnukeshi har numfashinshi nayi kaman zai dauke…Bobby da yaga haka baisan lokacinda ya karasa kusa dashi da sauri ta kama hannunshi ba…har yanxu kallonshi wazir yake ya kasa dena kokarin yin mgn dukda breathe dinshi da yake kaman zai dauke..da sauri aunty Munubiya ta fita sai gata ta daw tareda doctor…taimakon gaggawa ya shiga bashi har yanxun hannunshi na rikeda na Bobby daya kasa sakewa…doctor ya samu ya daidaita breathe dinshi snn ya mishi alluran bacci sbd yaga idan ba haka akayi masa ba bazai ta6a dena yunkurin mgn ba and yana bukatar hutu dan haka ya juya garesu yace”you all shoulf go outside plss..he needs to rest bansan ya akayi ma aka barku kukazo har kuka cika dakin ba haka”…ba wanda ya kulashi har ya juya ya fita..suma hada kansu sukayi gaba daya sukayi waje don ya samu enough rest kaman gabda doctor ya fada…suna fita aunty Munubiya tace”amma dai zaku jira har lokacin da zai tashi koh?..”Bobby yace”no zamu dawo safe..yanxu hutu yake bukata”..gyada kai tayi tana kokarin dakatar da hawayen idonta tace”ya kamata mu zauna muyi mgn sosai..a ina kuka sauka?..”aunty sumy tace”Gwagwalada”..zaro wayanta tayi ta mika mata tace”sakamin numberki da safe zanzo inda kuke muyi mgn”..ba musu aunty sumy ta amsa wayan ta saka mata digits dinta snn ta mika mata tayi saving..ta sake mikawa Bobby shima tace ya saka mata nata dan haka ya saka still ta karba tayi saving snn tayi musu rakiya har bakin motarsu tareda alqawin zatazo gidansu gobe da safe su tattauna kafin suzo asibitin…haka suka tafi jikin kowa a sanyaye…gaba daya wani irin feeling sukeji tattare dasu…Aunty Munubiya only sis din mahaifinsu ce..ita kadai ce sis dinshi da suke uwa daya uba daya sauran duk uba kadai suka hada…ko a da can sunsan Aunty Munu bata daya daga cikin wanda suka tsani Mummy dan ko itama Mummyn tana fada…sai yanxu Bobby yaji rashin dacewar abunda yayi at least ita ya kamata su nemeta tunda yasan mai kaunarsu ce kuma bai zama lallai ta iya binciko inda suke ba tunda ita mace ce dole sawa zatayi a bincika mata…for the very first time yaji kaman bai kyauta ba abunda yayi..yaji gaba daya bai kamata ita su kasa nemanta ba duba da kasancewarta qanwar babansu…sai yaji guilty conscience ya rufeshi..tabbas bai kyauta ba abunda yayi mata domin daga yanayin yanda tayita kuka daga ganinsu yasan ba karamin missing nasu tayi ba..kilan ma tayita faman neman inda suke bata gansu ba…har suka karasa gida bai bar tunane tunanen nan ba…suma gaba daya sauran kowa da tunaninda yake dan haka suna karasawa gida kowa dakinshi ya kama yana sake tuntuntuni.