Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari karfe bakwai ta kira Bobby tace mishi gata nan zuwa gidan nasu..da kanshi ya fita bakin gate ya shigo dasu mota guda itama tayo itada yaranta…a parlor suka zauna gaba dayansu kafin ta shiga kallonsu one by one idonta na cikowa da hawaye tace”why plss?..idan kun kauracewa kowa sbd laifinda akai maku ni me nayi?..meyasa bakuyi tunanin halinda zan shiga ba”..da sauri Bobby yace”Aunty kiyi hakuri dan Allah..it was all my faul..nine na yanke duk wani alaqa daku kuma na hana kowa ya nemeku sbd ciwon abubuwanda akayi mana..nasan bai kamata na hada dake ba amma ina neman yafiyarki on behalf of all of us kiyi hakuri please!..”ya karasa mgn yana hade hannayenshi wuri daya…dan murmushi ta saki da wet face dinta kafin ta yafitoshi da hannunta alaman yazo..ba musu ya taso daga inda yake ya dawo kusada ita..yana zama ta daddage ta rankwashi kanshi tana fadin”this is ur punishment”..dafe kan yayi da sauri yana murmushin jin dadi..at least yasan yanxu ta yafe mishi…aunty sumy ma murmushin takeyi da hawayenta…itama Auntyn Munu bata dena hawayen ba ta sake fadin”ina Mummy?..”Sab ne ya amsada”tana gida”..kallonshi take tanaso tace gida ina?..sai aunty sumy tace”Kano”..kuyawa tayi tana kallonta da mamaki tace”u mean all this while kano kuke zaune?..”aunty sumy ta gyada mata kai alaman yes…tace”ikon Allah..kinga Allah ne kawai baiyi zamu hadu daku ba sbd nima kusan watanmu 6 da komawa Kano da zama”..Bobby yace”yanxu knn kano kuke?..”tace”kano muke..bari inyi introducing dinku wa kids dinku”…da sauri Bobby yace”haba sai kace bamu sansu ba”..ya nuna babban cikinsu da bazai wuce mate din Sab ba yace”ga ma sunan Daddy”..aunty Munubiya tace”umhum..”ya nuna mai bi masa yace”shi kuma wnn Habeeb”..nanma kai ta sake gydawa tana kallonshi…ya nuna ‘yar macen da bazatafi sa’ar Miemie ba yace”ga Nusaiba..wnn kuma itace bansan sunanta ba”…daria sukayi gaba dayansu ganin da gaske bai manta su din ba…Aunty Munubiya tace”ita wnn dama bai zama lallai ku santa ba”..juyawa tayi tana duban yarinyar tace”baby yama sunanki?..”da sauri yarinyar tace”sunana Nadia Usman”…wara idanu sukayi gaba daya jin sunan Mummynsu nema da yarinyar…Bobby ya kalleta yanaso yace da gaske sunan Mummy ta saka ko kuma coincidence ne..kamar tasan me yake shirin tambaya tace”yes sunan Mom dinku nasa mata…inaso ta dauko kyakykyawan hali da hakuri irin na mahaifiyarku and Alhamdulillah ta dauka”..shiru kawai sukayi kowa cikeda Mamaki…ilham da taji yarinyar ta fadi sunanta amma ita baace ta fadi nata ba tace”nima Sunana Nadia Isma’il”..a take suka kwashe da daria jin mgnr nata…Aunty Munu ta janyota jikinta tana murmushi tace”da gaske kema Nadia ne sunanki?..”da sauri Ilham tace”yes amma ana cemin Ilham”..rungumeta Aunty Munubiya tayi tana cigaba da murmushi…daga nan kuma sai labari ya 6arke tskaninsu…kowa ya shiga bada labarin bayan saduwa..farin ciki suke sosai na sake haduwa da juna after six long years…a tare sukayi breakfast daga nan kuma suka nufi asibiti gaba dayansu.

Waziri na zaune tun safe ko bacci ya kasa komawa sai tambaya yake wai da gaske ‘ya’yan Attahir dinshi ya gani ko kuwa dai mafarki ne kaman yanda ya sabayi?..mutum uku daga cikin yaranshi dake wurin dai babu wanda ya bashi gamsashshen amsa don basu san ko su dinne sukazo da gaske ko kuma a mafarkin dai ya gansu shine yake zargin a gaske ne…suna shigowa dakin gaba daya hankalinshi ya koma kansu..kallonsu yake yayinda hawaye ke zarya kan fuskanshi..gabi yake bai masu adalci ba daya kasa nemansu duk shekarun nan amma saidai ba laifinshi bane..babu wanda baisa ya nemosu cikin yaranshi ba amma kowa da labari daya yake dawo mishi cewa ba’a gansu ba..shi kuma ba lafia ne dashi dazaije neman nasu da kanshi ba…yanxu kuma da yake ganinsu gabanshi sai yaga kaman ba gaske ba…da hannu yayi musu alama da suka karasa inda yake…ba musu suka isa suka tsaya jikin gadon nashi…kallonsu yakeyi daya bayan daya yana sakejin kewar mahaifinsu na rufeshi..hannu yakai ya kamo hannun Bobby dake nan kusa dashi muryanshi ba rawa yace”Attahiru..”kawai sai ya rungumeshi yana cigaba da hawaye…ya janyo Sab da other hand dinshi duk ya rungumesu yana zubda hawaye..Sab ma hawayen yake likewise su Aunty Munubiya da Aunty Sumy dake tsaye gefe…Bobby kuwa wani irin different feeling yakeji tattare dashi..bai taba tunanin zasu samu tarba daga wajen waziri balle har yayi kuka sbd farin cikin ganinsu ba…ganin yanda yake kuka kawai ya isa ya gane ba karamar wahala yasha na rashinsu a tareda shi ba..nan take ya sakejin rashin kyautuwar abunda yayi..wani irin tausayi da kuma kaunar kakan nashi suka taru suka cika mashi zuciya..sun dade rungume da juna kafin ya sakesu yana duban Aunty Sumy dasu Miemie suma yace su karaso kusa dashi..suna karasawa haka ya dinga binsu yana runguma ko kalma daya ya kasa furtawa sbd farin ciki..sun dauki lokaci mai tsaho a haka kafin Waziri da har yanxun ya kasa barinsu subar kusa dashi ya shiga neman yafiyar su kan abubuwanda ya aikatawa mahaifiyarsu..ya kuma rokesu da susa mahaifiyarsu itama ta yafe mishi…a take duk sukace sub yafe hadda Bobby da yake sake jin tausayin kakan nasu…yanda yaga yanayi musu ba karamin tausyi ya bashi ba…ya rasa inda zai sanyasu sbd farin ciki duk wanda ya shigo kuwa saiya nuna mishi su a matsayin iyalan Attahir dinshi…uncles dinsu wajen mutum biyar sukazo asibitin and duk cikinsu ba wanda waziri bai nuna masa su yana cewa sun dawo gareshi ba..sbd tsabar farin ciki lokaci daya ciwon daya dade yana fama dashi ya samu saukinshi fiyeda zato dan har hakan yaba doctor dinshi mamaki…koda sukazo tafiya hanasu yayi yace bai gaji da ganinsu ba…haka sukacigaba da zama kowa yana bashi labarin bayan rabuwa…Aunty Sumy da Aunty Munubiya suka tafi gida zasuyi girki su kawo tareda yaran..Sab shima sai yabi Taheer da yayi driving nasu zuwa gidan…ya rage daga Bobby sai kakan nashi a dakin…tambayoyi sosai Waziri keyi mishi na duk abubda ya shafi rayuwarsu shi kuma yana bashi labari daki daki…sunyi nisa cikin labarinsu sosai aka turo kofar Lamido da daddy sai wani yayan daddyn suka shigo dakin a tare…da mamaki Bobby ya daga kai yana kallonsu sai kuma ya mike daga inda yake zaune yana musu murmushi yace”barkan ku da zuwa”..daddy ma kallonshi yayi da murmushi yace”Attahir kana nan knn?..”yace”ina nan daddy..Bismillah ku zauna”..karasawa ciki sukayi suka zauna Lamido da Waziri suka fara gaisawa..baya sun gama su daddy ma suka gaisa da Waziri tareda tambayarshi ya jiki yace jiki yayi sauki…daddy na duban mahaifinshi yace”Baffa wnn shine Proprietor din makarantar su Aysha ai..dan wajen Col Attahir ne”..da mamaki Lamido yace”ikon Allah..yanxu wnn karamin Attahir ne yayi girma haka?..”cikin farin ciki waziri yace”tareda yan uwanshi sukazo tun jiya..ashe duk tsahon lokacin nan suna kano bamuda labari”..gyada kai Lamido keyi yana cewa”ikon Allah knn..Allah ya jikan Attahiru”..gaba daya suka amsa da Ameen..dakin ya danyi shiru kafin Lamido dake duban Bobby yace”kace kasan amaryata knn?..”murmushi kawai Bobby yayi kai a kasa..Lamido ya sake cewa”batajin mgn koh?..nasan kilan kuna can kuna fama da ita”..wnn karon daria ya danyi jin abunda Lamidon da kanshi ya fada still dai baiyi mgn ba…wato ita dai ko yan uwanta ba wanda baisan fitinanniya bace…nan take kuma sai akalar tunaninshi ta koma kacokam kanta yaji duk wani iri yau throughout baiji muryanta ba..ya kamata kuma ya kirata ko don ya bata labarin yau yaga Lamido..hira sosai ya barke tsakaninsu shidai nashi murmushi ne kawai sai idan waiziri ya tambayeshi wani abu ya bada amsa…gaba daya hankali da tunanin nashi sun koma kanta kuma..so yake suyi suyi su tafi shima ya dan samu ya fita waje ya kirata amma basu suka bar asibitin ba sai dab da magrib..bayan ya rakasu yayi sallah masallaci snn ya koma ciki nan kuma ya samu su Aunty Munubiya sun dawo suna cikin dakin…lalla6awa yayi zai fita waziri daya ankara dashi ya dawo dashi wai bai yadda ko nan da can yaje ya barshi ba…haka yayita zaune suna labari duk hankalinshi yayi kanta…sai da kyar suka samu waiziri ya yadda su tafi don da farko cewa yayi saidai Bobby da Sab su zauna su kawan dashi amma sbd ganin wanda ke kwana dashi yazo and bazaiji dadi ba sai suka lalla6ashi tareda alqawarin zasu dawo gobe kafin su wuce kano…ko sanar dashi tafiyan nasu ma basuyi ba sbd basusan kalan rigiman da zaiyi musu ba don sun fahimci yana fama da ita in excess.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button