Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

U people should include me in ur prayers plss..am seriously sick????????bana son nayi keeping naku waiting shiyasa nayi wnn amma if kun jini shiru gobe kuyimun uzuri plss…ina gama warwarewa zuwa jibi zaku jini..thanks and love u all❤️

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
37
Yana shiga bedroom dinshi direct ya wuce bathroom bayan ya rage kayan jikinshi…wanka yayi sharp sharp ya fito zuwa closet ya saka pyjamas har zai kwanta sai kuma yaga he needs to see her ko don sbd ya tabbata taci abinci…fita yayi daga dakin zuwa flat din Mummy..ganin ba kowa a parlorn ya nufi dakinda take ciki..kan gado ya isketa zaune da zumbulelen hijab dinta tayi tagumi da hannunta…ya karasa ciki da sauri ya zauna kusada ita kafin yace”what again?..”kallonshi ta danyi sai kuma ta dauke kai tana turo baki…yakai hannu ya juyoda fuskan nata gareshi yana kallonta yace”Lamido plss..menene ya faru again?..nayi maki wani abun ne?..”girgiza kai ta shiga yi kmr zata fara hawaye tace”ni bacci zanyi”..ajiyar zuciya ya sauke mai karfi yana kallonta..har kullum yana mamakin yanda hawaye sam baiyi mata wahala..kan dan karamin abu zata fara kuka kuma saika rantse wani gagarumin laifin akayi mata…ganin ta juya tana neman kwanciya yayi saurin dakatar da ita da fadin”ki tsaya to kici abinci plss”..ture hannunshi tayi tana cigaba da turo mishi baki tace”ni na koshi”..daga haka ta juya mishi baya ta kwanta abunta shi kuma sai yayi zaune yana binta da ido..baisan ta inda ya kamata ya fara rokonta taci abinci ba..yasan ko a hostel din ma da kyar idan taci wani abun shi kuma baiso ta kwana da yunwa ko kadan..suna zaune haka Mummy ta shigo dakin rikeda sabon dogon riga na bacci a hannunta…tana ganinta a kwance taga tea kuma a ajiye tace”Aysha bakisha tea din ba?..”mikewa tayi da sauri tana sunkuyar da kai tace”yanxu zansha”..daga haka takai hannu ta dauki mug din tea din ta kai bakinta ta fara sha…Bobby sai kallonta yakeyi yanajin wani irin relieve sbd shan tean da take..wato sbd shine yayi mata mgn tace bazata sha ba amma da yake yanxu Mummy ne shine ta dauka tana sha..shi ko a hakan ma yaji dadi at least dai bazata kwana da yunwa ba…tunda ta kada mug din a baki bata ajiye ba saida ta shanye Mummy ta karasa tana mika mata rigar hannunta tace”to ga wnn ki sa zuwa safiya..naga bakici omalet din bama”..a hankali tace”na koshi”..Mummy tace”to amsa rigan kisa..idan kina bukatar wani abun karkiji komai kizo ki fadamin kinji?..”kai kawai ta gyada tareda amsan rigan..Mummy ta maida dubanta ga Bobby dake kallonta har yanzu tace”to tashi muje kaima ka samu ka kwanta”..baiyi mata musu ba ya mike suka fita daga dakin..suna zuwa parlor ya wani marairaice yace”Mummy kina ganin zata iya kwana ita kadai kuwa?..”kamo hannunshi Mummy tayi tana murmushi tace”bana son a takurata ne shi yasa na barta ita kadai..ka kwantar da hankalinka nothing will happen inshaAllah ba gani nan kusa da ita ba?..”gyada mata kanshi yayi kafin ya rungumeta yana cewa”nagode sosai Mummy”..tace”nima nagode..yanxu kaje ka kwanta saida safe”..dagowa yayi yana kallonta da murmushi yace”ka chi fo”..murmushin itama takeyi mishi tace”ka chi boo”..sake rungumeta yayi hadda yi mata peck kafin ya juya ya fita Mummy tabi shi da kallo tana cigaba da smiling..zata iya rantsewa rabon da ta ganshi cikin farin ciki irin wnn har ta manta..fatanta bai wuce Allah ya daidaita tsakaninshi da yarinyar ba..ta fuskanci so ne yakeyi mata matsananci.

Washegari ringing din wayanshi ne ya tada shi daga baccin da ya koma bayan yayi wanka…ya mike zaune a hankali yana murza ido ya dakko wayan ya daga tareda karashi a kunne ba tareda ko sunan wanda ke kiran ya duba ba..muryan waziri yaji yana fadin”Attahiru”..da sauri ya wartsake daga baccin yana sake rike wayan da kyau yace”Baffa kaine?..”Waziri yace”nine Attahiru..ya kukaje gida?..”yace”mun sauka lafia Baffah..ya kafin jiki?..”yace”jiki yayi kyau sosai cikin satin nan nake sa ran komawa Gombe..ya mahaifiyar taku take?..”yace”tana lafia Baffa..na fada mata sakonka kuma tace ta yafe maka duk abunda ya faru”..waziri yace”nagode sosai amma dukda haka ka kai mata Waya inason mgn da ita”..da sauri ya diro daga gadon yana fadin”ohk bari in bata”..daga haka ya fita zuwa flat din Mummy…a bedroom dinta ya sameta ya mika mata wayan da sauri yana cewa”Mummy Waziri ne ke mgn”..a hankali ta karba wayan tareda komawa ta zauna kan sofa tana gaisheshi…ko gaisuwar nata bai amsa ba ya shiga bata hakuri da neman yafiyarta kan duk abubuwa daya aikata mata a baya…nan da nan Mummy data fara hawaye tace ta yafe mishi dunia da lahira dama ita bata taba rikeshi a rai ba…sun jima sosai suna mgn duk akan abubuwanda suka faru a baya..Mummy tace zataje Abuja da kanta ta dubashi itama yace ba sai tazo ba shima cikin satin nan zai koma Gombe and yanaso ya fara biyowa Kano yaga inda suke…Bobby dai na zaune yana kallon Mummy data kasa dena zubda hawaye har suka gama wayan…mika mashi wayan tayi tana share hawayen idonta tace”ka gani ko Bobby?..yanxu ka yadda da abunda nake fada?..”kama hannunta yayi kafin a hankali yace”na yadda Mummy..shiyasa hausawa suke cewa abunda babba ya gano yaro ko ya hau kan tsauni bazai iya ganoshi ba…ni kaina nayi mamakin irin tarbar da muka samu a wurinshi..ban taba zaton yana sonmu har haka ba sai yanxu Mummy..kuma duk laifina ne dana hana ku mu’amala dasu”..ya karasa mgn da wani irin rauni a muryanshi..kamo hannunshi itama tayi tana kallon cikin idonshi tace”ka bar damun kanka anything happpens for a reason..kilan hakan ya faru ne sbd ya zama darasi wa mutane irinka wanda basu yafe laifi komai qanqantarshi da kuma masu yanke zumunta..yanxun tunda komai ya wuce mu bar tunawa dashi sai muyi duba zuwa ga future kuma”..kissing hannunta dake rike da nashi yayi yana fadin”shiyasa nake sonki Mummy..Allah ya yafe mana baki daya”..tana murmushi ta amsa da Ameen sai kuma tace”kaga yanxu kuna daidatawa da Aysha sai ayi mgnr aure kawai..nasan waziri bazaiki nema maka aurenta ba”..da sauri yace”and Mummy kinsan me?..da Lamido da Waziri fa abokan juna ne?..na hadu dasu a Abuja sunzo dubashi tareda dad dinta”..Mummy tace”ai ba abota kadai ne a tsakaninsu ba..akwai alaqa mai karfi tsakanin ahalin Lamido dana Waziri tun zamanin yarinta..alaqa ne irin na gidan sarauta so inshaAllah bazasuki baka aurenta ba”..Bobby daya kasa dena smiling sbd farin ciki yace”Allahumma Ameen Mummy..Allah ya amsa bakinki”..dungure mishi kai tayi tana hararanshi tace”mara kunya kawai…ya jikin nata ma?..”yace”Mummy ai ke za’a tambaya ya jikinta tunda a flat dinki ta kwana”..Mummy tace”ai nayi tunanin wurinta ka fara zuwa kafin kazo nan”..da sauri ya shiga girgiza kai har yanzu bai dena smiling ba yace”haba Mummy..haka nan sai in fara shiga mata daki this early morning?..”mikewa Mummy tayi tace”ai gwara da bakaje ba sbd kada ka fada mata daki tana bacci..yanxun muje mu duba jikin nata”…baice komai ba ya mike suka fita dan Allah ya sani tun daxu dama yakeson zuwa ya ganta…zaune suka sameta gaban mirror tana shafa cream a jikinta Allah yaso da hijab dinta a jiki da shknn haka wnn mutumin zai gama ganin jikinta…ajiye cream din tayi tareda mikewa a hankali ta koma gefen gado tana kokarin durkusawa tace”Mama ina kwana”..Mummy ta mikar da ita tsaye tana cewa”ki dena wnn durkuson keda baki da lafia..ya kafan naki?..”a hankali tace”yayi sauki”..Mummy tace”kin tabbata yayi sauki?..”ta daga mata kai alama Eh..kamata Mummy tayi ta zauna gefen gadon snn ta isa ga wardrobe din dakin ta dakko wani sabon abaya data ajiye mata nan ciki tun jiya ta mika mata rigar tace”maza ki shiga bathroom kisa sai ki fito muje muyi breakfast koh?..”ba musu ta amsa rigan snn ta juya ta shiga bathroom…bayan mintina uku ta fito sanyeda rigar da yayi matukar amsarta…ta yafa mayafin a kanta sai kyawunta ya fito sosai kmr balarabiya…kallonta kawai Bobby keyi harta karaso ciki ta zauna kanta kasa..dukda ba kallonshi takeyi ba zata iya rantsuwa kallonta yake sbd yanda takejin eyes dinshi na zagayawa a jikinta..ba tareda ta kalli inda yakeba tace”ina kwana”..ko jin abunda ta fada ma baiyi ba hankalinshi gaba daya yayi nisa yana kallonta…saida Mummy ta tabashi snn yayi firgigit ya dawo hayyacinshi yana shafa kai…tace”bakaji ana gaisheka bane?..”shafa kan yacigaba dayi yana dan murmushi yace”am..la..lafia lau”..mikewa Mummy tayi tareda kama hannun Aysha tace”to taso muje muyi breakfast daughter”..ba musu ta mike ta shiga binta suka fita daga dakin Bobby ya sauke wani wawan ajiyar zucia yana cigaba da shafa kai..wai me yake damunshi ne haka?..meke faruwa dashi?..mikewa yayi daga kashe shima ya fita daga dakin…a dinning ya samesu gaba daya…Miemie na zaune kusada Aysha sai zuba mata dan banzan surutu take ita kuma tana murmushi sai ta ganta kmr Husna…karasawa Bobby yayi ya zauna yanata kallon dimples dinta dake fitowa sbd murmushin da take..sai yaji kaman an yaye mashi duk wani baqin ciki da yake tare dashi an musanya mashi da farin ciki..ganin murmushin nan nata kadai ya isa yasa ya mance da duk wani damuwa daya tsinci kanshi a ciki…Anty Sumy da Sab da Mummy sai satan kallonshi suke suna dariya..gaba dayansu zuwa yanxu ba wanda baisan irin son da yake mata ba…Miemie ce tayi serving dinsu kmr kullum snn kowa ya shiga cin abincinshi..Lamido dai a hankali takeci dan ko Allah yasan jinta takeyi a takure wlh..gashi ta baro wayanta a can hostel da ko baby saita kira ya rage mata damuwa..kafanta kuwa ya warke garau sai dan abunda baza’a rasa ba…ita ta riga kowa gamawa amma bata tashi ba saida Miemie ta gama suka mike tare..suna tashin kuma wayan Bobby daya ajiye kan table ya fara ringing..yana dubawa yaga daddy ne ke kira dan haka ya mike shima ya koma parlor ya zauna idanunshi a kanta yayi picking da sallamar..a daya bangaren daddy yace”Ameen wa’alaika salaam Attahir..ya aiki?..”cikeda respect yace”Alhamdulillah daddy..ya naka aikin?..”daddy yace”mun gode Allah..ya jikin Aysha?..daxun na kira wayanta ai Bilkisu ke sanar dani kuna asibiti”da sauri yace”eh tama ji sauki daddy..bayan na gama mata treatment sai na kawota nan gida wajen mahaifiyata ta kwana sbd dare yayi lokacin”…daddy yace”MashaAllah sannu da kokari kaji Attahir..Allah ya maka albarka”..Bobby ya amsa da”Ameen Ameen..bari na bata wayan kuyi mgn”…daddy baice komai ba shi kuma ya mike zuwa inda take ya mika mata wayar…kara tayi tareda kaiwa kunnenta a hankali tace”daddy goodmorning”..yace”morning..ya kafan naki?..”tace”ya warke..daddy ina su Yusra?..”daddy yace”gasu”..daga haka ya mika masu wayan Husna ce ta fara cewa”hello Addah”..Aysha ta saki wani murmushi kafin tace”sunanki Yusra dama?..”a fusace Husna tace”idan bakiyi haka ba ai ba kece Adda ba..ga Yusran nan ai sai kuje kuyita yi”..dariya ta saki wanda bata shirya ba..Husna badai saurin hawa ba wlh..sam bata iya wasa ba…kmr daga sama taji muryan Yusra na fadin”Addatah”..nan da nan ta sake sakin wani murmushi tana cewa”habibty na..ya kike ya school”..tace”lafia lau Addah ya ciwonki?..Adda Billy tace mana baki da lafia kin kwana asibiti”…tana cigaba da murmushi tace”hakane amma yanxu na warke habibty..ina Hamma na?..”tace”Daddy ya aikeshi Bauchi..Ammi ma tace idan zamu tafi Umrah zamu biy..”bata karasa ba taji tayi shiru and zata iya rantsewa dakatar da ita akayi..tana jin muryan Husna a background tana cewa”ke Yusra ba Ammi tace kada mu fada mata ba?..”daga haka kuma sai taji an kashe wayar..ta dagota da sauri tana dubanshi duk ta wani maraifaice ta mika mashi wayan tace”sake kiramin dan Allah”..amsa wayan yayi yana kallon yanda ta tsuke fuskanta yace”wnn kuma na menene?..”da sauri tace”cewa fa tayi wai zasu je Umrah su barni”..yace”kuma saiki yadda da mgnr ta..ba yarinya baice?..”girgiza kai takeyi tace”da gaske ne wlh..ai dama duk Ramadhan muna zuwa..nidai ka sake kiramin inji”..bai sake cewa komai ba yayi dialing number ya mika mata..a maimakon Yusra sai taji daddy ne ya dauka..tayi shiru tana tunanin me zata ce sai taji yace”bakida abun cewa ne?..”runtse idonta tayi tanajin kaman ta rushe da kuka tace”ba..komai”..yace”then sai anjima..Allah ya kara sauki”..daga haka daddy ya kashe wayar shi..itama ta mika mashi nashi tana sake daure fuska kai kace wani gagarumin laifi akayi mata…tasan wlh da kyar idan ba da gaske Umran zasuje ba..ai dama suna zuwa da azumi and idan ba mantawa tayi ba yau baifi saura one week a fara azumin ba…ta rufe fuska da hannayenta kmr zata fara kuka Bobby yayi saurin rike hannayen nata yana girgiza mata kanshi yace”dont cry plss..inshaAllah ba inda zasuje su barki”..bata iya cewa komai ba sai bude fuska da tayi nan kuma yaga ba kukan takeba…daidai nan su Mummy suka shigo parlorn ganin yanda taci kunu Mummy tace”Subhanallah meya faru haka?.”a hankali yake duban Mummyn yace”wai ‘yan gidansu zasuje umrah banda ita”..Mummy ta zauna nan kusada ita tana dubanta da kyau tace”haba stop frowning ur face mana daughter ba sai Azumi zaaje umran ba?..”Aysha ta gyada kai alamar Eh..Mummy tace”then don’t cry inshaAllah baza suje su barki ba kinji?..kiyi hakuri”…su aunty Sumy dai na zaune suna kallon ikon Allah..cikin ranta fadi take”lallai Bobby zaiyi fama da shagwaba a wurin nan”..shi kuwa gogan kallonta kawai yakeyi yana mamakin yanda batayi kuka ba..shidai Allah ya kawo ranar da zaiga ta dena saurin kukan nata..ya rasa wace irin shagwabace da ita wlh…bayan ta dan saki fuskanta ya mike zuwa Flat dinshi ya sake shiryawa ya fito…har lokacin suna zaune parlorn sai janta da hira suke…yana duban iwacth dake hannunshi yace”Mummy bari in maida ta hostel in dawo”..Mummy tace”dan wuri haka?..baka bari sai zuwa yamma?..”yace”gwara in maida ta yanxu sbd kada tayi missing lectures dinta..ba dadewa zanyi ba ina ajiye ta zan dawo”…Mummy tace”to shknn Allah ya tsare..Aysha sai yaushe kuma?..”shiru tayi kanta a kasa..Mummy dake murmushi tace”idan inason ganinki zan cema Bobby ya kawoki mu gaisa..Allah ya kara sauki kinji?..”a hankali tace”Ameen..nagode Allah ya kara girma”…da murmushi Mummy tace”babu komai daughter”..juyawa tayi ga aunty Sumy itama tayi mata godia..duk suka bita da adduan samun sauki snn Miemie tayi mata rakia har compound bayan sun cikata da abubuwa iri iri…driver dake zaman jiranshi a compound yana ganin fitowarsu ya mike da sauri zuwa inda motar da zasu fita yake…Bobby na karasawa ya mika mashi hannu yace”bani kyes din kayi zamanka yanxu zanje in dawo”..da sauri ya mika mashi key din tareda komawa ya zauna..shi kuma ya bude motar ya shiga itama ta shiga bayan Miemie ta sa mata kayanta a booth yaja motar suka tafi…baisan meyasa sam bayason driver yayi driving dinshi idan yana tareda ita ba..gani yake kaman zaiyita kallonta ne ta mirror shi yasa yafi gane yayi driving da kanshi idan yana tareda ita…har suka iso hostel babu wanda yace komai a ciki su…ta bude motar zata fita bayan tayi mishi godia ya dauko ledan wani magani ya bata yana cewa”kici gaba da shafawa a kafan har zuwa lokacin da zai dena ciwon”..karba tayi tace mishi”nagode”..ba tareda kallonshi ba..shi kuma kallon nashi yakeso tayi amma sam taki yin Hakan kmr dai tasan yanda yake son ganin fuskanta da kyau…bai takura ta ba yace ta shiga ciki tasa uniform sai ta fito ya ajiyeta area classes..ba musu ta shiga ciki tasa uniform din snn ta fito ya sake maidata cikin school din…har wajen class dinsu yayi parking snn ta bude motar ta fita bayan ta sake mishi godia shi kuma yaja motar ya koma gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button