Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranan Thursday suna kwance hostel bayan sun fito daga exams kowa tana fama da azuminta musamman Lamido da sai juyi takeyi kan gado wai tanajin yunwa…sbd tsabar haushi Billy ko tanka maka tabayi ba har ta gama surutunta ta hakura…tana nan kwance har bacci ya fara daukanta taji wayanta na ringing…hannu ta mika ta dauko wayan daga kan study table dinta tareda dagawa takai kunne…muryan Sa’eed taji na fadin”my bestyyyyyy”…wani irin mikewa zaune tayi da sauri tana zare idanu tace”besty is this really you?..”full of excitement yace mata”its me besty…ur very own best friend”..tun kafin ya rufe baki ta wani turo baki tace”ba wani my very own best friend..yanzu tsakani da Allah haka ake rayuwa besty?..tunda ka tafi ba hello ba hy kaman dama ka gaji damu”…tana rufe baki shima yace”dadina da besty rigima wlh..to yanxu dai ku fito gani bakin gate ina jiranku”.. sake zare idanuwanta tayi tamkar wanda tayi gamo da aljani tace”are u serious besty?.”yace”come outside mana zaki gani ai”..daga haka ya kashe wayar ita kuma ta diro daga kan gadon ta rarumi hijab dinta ta zura snn ta karasa gadon Billy ta fara tashinta daga bacci…a fusace ta mike zaune tana cewa”Lamido wai meye baka plss?..meyasa bakyaso kiga nayi bacci a hostel din nan”..kama hannunta Aysha tayi ta mikar da ita tsaye ta dauko mata hijab ta mika mata snn tace”wai besty ne yazo yana bakin gate..kinji dan rainin hankali zaizo ko fada mana baiyi ba”…tabe baki Billy tayi tana kokarin momawa gadonta don sake kwanciya tace”kuma shine zaki tasheni daga bacci sai kace besty na ne yazo?..”sake kamata Aysha tayi ta shiga turata waje tana cewa”ai wlh baki isaba sai kinje”..daga haka ta ja hannunta suka fita daga dakin bayan Billy ta zura hijab dinta itama…suna fita suka hangoshi daidai inda ya saba tsayuwa idan yazo dan haka suka nufi wurin da sauri…har suka karaso inda yake kallonsu yakeyi yana murmushi…bai taba sanin da akwai friendship irin wanda yake tsakaninshi da su biyun nan ba…jinsu yake a jikinshi tamkar sun zama family…suna karasowa Lamido data wano hade girar sama dana kasa tace”nidai ba kulaka zanyi ba wlh”..murmushi ya saki kafin yace”idan besty taki kulani kuma ai sai in samu matsala..yanxun kiyi hakuri mu zauna sai in fada maku uzuri na nasan kema idan kikaji zaki hakura ki dena fushi”…ba musu gaba daya suka nufi inda suka saba zama nan cikin hostel din as usual…bayan sun zauna ya shiga musu bayanin tafiya sukayi zuwa Canada tareda Dad dinshi shine dalilinda yasa basu samunshi a waya…shima kuma bai samu yayi roaming ba and bai hau social media ba har suka dawo shiyasa sukajishi tsit kmr baya existing…kmr yanda ya fada kuwa nan da nan ta sauko daga fushin nata sai kuma aka hau labari na yaushe gamo..hatta Billy da ba wani dasawa sukeyi ba yau labari na musamman sukeyi dashi sbd missing juna da sukayi…bashi yabar hostel din ba sai around 4 yace su shirya kafin magrib zaizo ya daukesu su fita don akwai special iftar daya hada masu for the three of them…murna wajensu kmr ba gobe haka suka koma hostel kowa ta fara shirin fita tunda yace before magrib din zaizo yayi picking dinsu.
6 nayi kuma yazo yayi picking dinsu sai Cilantro…wurin har wani decoration yasa akayi mashi specially for them dama already yayi reserving so daga su sai su zasuyi iftar dinsu…tun kafin asha ruwa aka cika masu gabansu da kayan ciye ciye iri iri…sunata hiransu abunsu har aka kira sallah Sa’eed ruwa kadai yasha ya wuce masallacin dake nan ciki yayinda su kuma suka gabatar da sallahrsu a inda suke…yana dawowa suka shiga iftar dinsu hankali kwance kowa ka gani cikinsu is full of happiness and excitemet sbd kada cewa tareda junansu after a long period of time…Sa’eed sai snapping dinsu yakeyi wani su biyu kadai wani kuma yayi musu selfie gaba daya..a takaice sunyi having fun dinsu yanda ya kamata suna barin wurin kuma ya kaisu gidan Hajia nan ma taji dadin gani su sosai daga nan kuma yayi musu siyayyan kayan kwalam snn yayi dropping nasu a hostel as usual.
A daren ranar Dr Bobby yana parlonshi yana karatun Qur’ani kiran daddy ya shigo wayanshi…ajiye alqur’anin yayi tareda dagan wayan da sallama..bayan sun gaisa daddy yace”wani nauyin dai zan sake dora maka son Allah yasa bazaka gaji dani ba”..da murmushi Bobby yace”not at all sir..ka fadi kome kakeso zaayi inshaAllah”..cikeda jin dadin amsan daya bashi daddy yace”nagode sosai Attahir…mgnr Aysha ne dama gobe zasu gama exams koh?.”yace”yeah gobe zasu gama”…daddy yace”so nake if it’s ok by you ka kaita wajen mahaifiyarka ta kwana biyu zuwa sunday wanda zasu tafi dashi ne har yanxun Passport dinshi bai zama ready ba amma yacemin zuwa sunday komai zai zama ready inshaAllah..banson ta koma Gombe ne snn ta sake dawowa Kano tunda dole ta kano flight dinsu zai tashi”…da sauri Bobby yace”no problem sir..zan kawota inshaAllah”..daddy yace”i hope dai ba wani matsala koh?..”yana gyada kanshi yace”babu wani matsala inshaAllah”..murmushi daddy ya kara saki kafin yace”to nagode sosai Attahir..zuwa sunday din komai inshaAllah zai zama ready ita dama passport da visa dinta duk basuda matsala so ticket kawai zaa sai mata”…gyada kai kawai yakeyi yama rasa abunda ya kamata yace…sallama sukayi snn daddy ya kashe waya..shima ya ajiye nashi yana sakin wani numfashi da karfi gamida dafe kanshi…farin ciki ya kamata yayi sbd zata dawo kusa dashi amma what he’s feeling is not close to farin ciki at all…yasan zamanta a kusa dashi din ba abunda zai amfaneshi dashi saima karin damuwa da zai sanya mishi tunda yasan ba sonshi takeyi ba…duk sai yaji damuwan da ya fara raguwa a tare dashi yana neman dawowa sabo…dunia yanxu babu abunda ke bata ranshi kmr idan ya tuna yarinyar nan bata daukeshi a bakin komai ba bata kaunarshi…dukda har yanzun ba bai furta mata yana sonta ba yasan ko a can kasan zuciyarta babu wani abu makamancin sonshi shiyasa idan ya tuna haka yakejin kmr zai hadiye zucia ya mutu…ganin damuwan na nema yi mishi yawa sai ya dauki alqur’aninshi yacigaba da karatun da yakeyi…nan take kuma yaji ya samu saukin damuwar daya fara rufeshi.
Washegari bayan ya gama shiryawa kafin ya fita ya nufi Flat din Mummy dan sanar da ita yanda sukayi da daddy jiya…tana zaune itama tana karatu ya shigo dakin..ya karasa kusada ita ya zauna har takai aya snn ta rufe Qur’an din tana dubashi tace”har ka fito?..”yace”na fito Mummy..dama wata mgn ce nazo muyi dake”..Mummy tace”to ina jinka”..saida ya lumshe ido ya bude kafin a hankali yace”baban Aysher ne dama yace in kawota tayi kwana biyu a nan wai wanda zasu wuce Saudi dashi passport dinshi bai gama zama ready ba”..full of excitement Mummy ta wara idanu tana cewa”da gaske?..to Allah ya kawota lfy yaushe zasu gama exam din?..”a takaice yace mata”yau”..sake wara idanu tayi tana murmushi tace”to Allah ya kawota lfy kace mishi babu wani matsala zatayi zamanta tare damu a nan”…kallonta kawai yakeyi ganin how happy she is kawai sbd zatazo gidan tayi kwana biyu…baisan meyasa ba shidai tun jiya da aka fadi mgnr nan yakejin jikinshi wani iri kmr dai ba nashi ba…Mummy ta kamo hannunshi tana dubanshi da kyau tace”wnn damuwan kuma na menene Bobby?..”dan matsala yayi ya dora kanshi kan shoulder dinta murya can kasan makoshinshi yace”bata sona Mummy..har yanxun bata kaunata dan Allah Mummy me zanyi mata ta soni..ko bai kai yanda nake sonta ba at least itama ta soni”…Mummy dake rikeda hannunshi tace”inaji a jikina zaka auri yarinyar nan kawai ka kwantar da hankalinka”..sake lafewa yayi a jikinta yace”na gaji ne Mummy..na gaji da chasing dinta tana nuna banida muhimmanci a wurinta..Allah kadai yasan halin da nake ciki these days ko bacci wahala yakemin..ji nake idan abubuwa suka cigaba da tafia a haka mutuwa zanyi”..girgiza kai Mummy ta shiga yi tace”nace maka ka dena fadin haka amma ba kaji..ajiye duk wani pride and ego dinka zakayi a gefe ka fada mata how feel..tell her that you love her and you can die for her amma ba kazo kana tambaya yanda zakayi ba”..lumshe ido kawai yayi yana sauke numfashi da kyar..baisan meyasa when it comes to love yakejin brain dinshi na toshewa ba..gaba daya sai yaji ya rasa me ya kamata yayi…abu daya daya sani shine ya dena chasing dinta infact yama dena nuna yana son nata tunda batasan yanayi ba.