Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
40
Tana shiga daki wayanta ta dauka ta sake dialing number Hamma amma bai shiga ba..ta kira na daddy shima bai shiga ba na Ammi ma bai shiga ba..duk hankalinta yabi ya tashi taji bata son zaman kanon ma gaba daya..ko ba yanxu zasu tafi Saudi ba itadai gara mata ta koma ko Bauchi ne gidan aunty fiddausi akan dai ta zauna gidansu wnn mutumin daya fara bata tsoro yanxu..gaba daya abubuwan da yayi mata sun kasa bajewa daga kwanyarta..yanda ya furta i love u din nan har yanxun bata denajin echo dinshi cikin ears dinta ba..kuma ta tabbata this time around da gaske yake..da gaske yake tunda har yanayinshi taga gaba daya ya sauya and she saw wani abu cikin idanunshi wanda ko kusa bata fatan sake ganin makamancinshi…ba Kano kadai ya fita daga ranta ba har FCNM din taji ta tsaneta da daddy zai yadda ya maidata Gombe da tafi kowa farin ciki da hakan amma tasan ko rasuwa zatayi daddy bazai canxa mata makaranta ba especially not yanxu da take dab da kammalawa…bayan sallah suna gama hutu zasu tafi Clinical posting daga nan kuma saura musu semester daya su gama ta huta da alakakai..duk ranan da akace ta gama FCNM kuwa tana tunanin bazata sake tako kafarata ta kawo Kano ba duk kuwa da tarin kaunar da takewa garin amma bazata iya da halin proprietor dinsu ba..she remember yanda Prof ya nace kan Bobby sonta yakeyi hakama Billy ita kuma tanata cewa ba sonta yakeyi ba ashe duk sun fita gaskia…abubuwa da dama sai yanxu suka shiga dawowa kwanyarta suna kuma sake tabbatar da lallai da gaske proprietor sonta yake saidai ita ko kusa ko alama bataji wai zata soshi ba saidai tausayi daya bata..kawai dai zaiyita wahalar da kanshi ne daga baya ya hakura tunda dai tasan da hankalinta da komai bazata fara zabanshi a matsahin miji ba bayan ba kalan bakin halinshi da bata sani ba.

Bayan duk sun kammala iftar dinsu suka mike zuwa parlor kafin sallahn isha..ya rage daga Mummy sai Bobby da har yanxun ke dafe da head dinshi a dinning din…kama hannunshi Mummy tayi cikin tsananin tausayinshi tace”dan Allah ka ragema kanka damuwan nan Bobby”..tana rufe baki ya dago jajayen eyes dinshi dake nan kaman ana hura musu wuta yace”bansan yanda zanyi in dena ba Mummy..ya zanyi plss?..”yana rufe baki tace”ka fawwalawa Allah komai..ka kuma yi imanin cewa idan Aysha matar ka ce zaka aureta likewise idan ba matarka bace duk wnn kunchi da damuwan bai isa yasa ka sameta ba”..dagowa yayi yana kokarin boye tarin damuwar dake kan fuskanshi yace”shikenan Mummy amma pls can i see her this once?..i just wanted to make sure bata tareda yunwa ne kinga azumi akeyi and ina kallo daxun ba wani abincin kirki taci ba”..mikewa Mummy tayi tana cewa”don’t worry i will take care of that”..da sauri yace”Mummy please..idan ban ganta ba bazan iya bacci ba wlh”..kallonshi Mummy tayi kawai ta ksa mgn..tausayi yake bata sosai..da ganin yanda ya jigata za’a san dama abun ya dade yana cinshi a zuci yanxun ne kawai ya fito sbd kasa cigaba da boyewa da yayi..bata sake hanashi ba ta kama hannunshi suka nufi flat dinta…a tare suka shiga dakinda take tayi saurin mikewa daga kwancen da take tana kallonsu…Mummy ce tace mata”anya kin koshi da abincin nan kuwa Aysha?..idan kina son wani abu ki fada a kawo maki”..girgiza kai ta shigayi da sauri tana cewa”Allah na koshi Mummy”..kallonta Mummy tayi kmr zata sake mgn sai kuma ta saki hannun Bobby tareda juyawa ta fita daga dakin..tana fita ya karasa ciki da sauri yana dubanta a raunane yace”if sbd mgnr dana fada ne yasa kika kasa cin abinci am sorry.. ki fadi duk abunda kikeso i will go out in samo maki yanxun”..girgiza mishi kai kawai tayi tareda komawa ta kwanta murya can kasa tace”na koshi”..legs dinshi yaji sunyi wani irin sanyi kmr bazasu daukeshi ba..murya a hankali ya kira sunanta ta mike tana kallonshi kawai sai ya juya ya fita daga dakin yana jin kanshi na sarawa da karfi…magani kadai ya iya sha snn ya hau gado ya kwanta tareda lumshe ido yana addu’an Allah ya kawo bacci ya daukeshi ko zai samu saukin halinda yake ciki…dukda maganin da yasha baccin bai samu daukarshi da wuri ba sai can kuma ya daukeshi ba tareda saninshi ba…ana kiran sallahn isha ya farka tareda sake dauro alwala ya wuce masjid..bai dawo ba saida suka idar da taraweeh still ya sake komawa daki ya kwanta tun daga nan kuma bai sake tashi ba saida alarm din wayanshi ya buga alaman time din sahoor yayi knn…mikewa yayi da sauri ya sauka daga gadon tareda fadawa bathroom yayi brushing ya fito kai tsaye ya fita zuwa flat din Mummy…yau ko nafilar dare bai iya tashi yayi ba sbd maganin bacci da yasha..a parlor sukayi karo da ita tana ganinshi tace”yauwa ka tashi?..”yace”na tashi..Mummy kin tasheta?..”murmushi Mummy ta saki tana kama hannunshi tace”na tasar maka ita Bobby..nama kai mata abincinta can dakin saida ta fara ci na fito”..ajiyar zuciya ya sauke gamida lumshe idonshi yace”Mummy kar kina fita taki ci fa”..hannunshi Mummy ta kama suka fita daga parlon tana ce mishi”zataci inshaAllah..believe me”..kai kawai ya gyada mata har suka fita…nashi abincin shima ta hada ta kawo mashi snn itama ta zauna cin nata..shi kuwa kasa cin abincin ma yayi gaba daya hankalinshi ya tafi wurinta..bayan mintina kadan ya mike yace ma Mummy zaije yayi nafilah kafin time din subhi yayi..batayi masa musu ba barshi dukda tasan kafin yayi sallahn sai ya fara zuwa inda Aysha tukunna…ilai kuwa yana shiga direct dakin da take ya wuce…ya sameta da mug din tea a hannu tana sha baisan lokacinda ya sauke wani ajiyar zuciya ba..kallonta ya danyi for like 5 mins snn ya juya ya fita don yasan ko yayi mata mgn ma zaiy wahala ta amsa mashi hakan kuma yana iya sa zuciyarshi ta hauro yazo yana mata abunda bai kamata ba.

Karfe goma na safiyar ranar Aunty Munubiya tazo gidan tareda yaranta..gaba daya sun cika parlon Mummy suna labari har Aysha da Mummy tasa dole aka kirata ta fito itama ake labarin da ita..dukda ba wani abu take cewa ba tana sauraronsu tana murmushi..ga Miemie da Nusaiba da suka sanyata tsakiya sun cikata da surutu kmr ba azumi suke ba…dukda labarin da sukey hankalin Mummy na kanta taga yanda take dan smiling idan an fadi abun daria sai hankalinta ya dan kwanta at least dai bata cikin damuwa yanxu…Bobby na fitowa ta wani hade girar sama dana kasa kmr ba ita ke smiling a while ago ba.. ya karasa ciki ya zauna suna gaisawa da Aunty Munu kmr bazai ce mata komai ba shima nashi face din daure can kuma ya kasa hakura yace”come and speak to ur dad”..kallonshi tayi taga shima ya daure fuska saida gabanta ya fadi da ganin fuskan nashi…tayi kasa da kai kmr bata jishi ba shi kuma ya sake cewa”ba dake nake mgn bane?..”mikewa tayi a hankali tana turo baki shima ya mike maimakon ya hadata dashi din sai ya kama hanyar fita itama dole tabi bayanshi kafin ya zazzaga mata masifa kuma…Mummy da mamaki ta bishi da kallo ganin har yanxu bazai dena hade ma yarinyar nan rai ba bayan duk wahalan da yakesha kanta…yana fita kai tsaye motarshi ya nufa ya bude front seat yana kallonta har ta karaso ta shiga ya rufe kofar snn shima ya zagaya ya shiga tareda tayar da motar ya figeta da wani irin gudu suka fita daga gidan…cikin tashin hankali ta juya tana kallonshi taga fuskan nan ba sarari sai ma sake tamkeshi da yayi kmr namijin saniya..kasa cewa komai tayi ta dauke kai daga gareshi…gudu yakeyi sosai ba tareda yasan shi kanshi ina ya dosa ba..kawai haushi yakeji da zata dinga treating dinshi like this sbd yace yana sonta bayan ya tabbata ko bestynta baza tayi treating dinshi haka ba ballantana kuma ace wnn tsohon saurayin nata…ganin yanda yake tsere da motoci akan titi kawai ta fashe mishi da kuka..yanzu idan yaje ya zubar dasu ya zasuyi?..kuka takeyi wiwi yana jinta baice komai ba bai kuma dakata da gudun da yakeyi ba dukda yanda kukan nata ke neman karyar mishi da zucia amma haka ya dake…saida yaje can Arean Naibawa ya hau fly over yabi titinda zai maidashi hotoro snn ya samu silent area da ba motoci ke wucewa sosai ba yayi parking nan wurin yana kallonta…lumshe ido yayi jin kukan nan nata yake har cikin ranshi..duk wnn zafin da ya fito dashi sai ya nemeshi ya rasa kukan nan da takeyi duk ya wargaza su…a hankali yake dubanta murya a matukar raunane yace”do u want to kill me?..so kike kiga karshena koh?..”shiru batace komai ba..ya sake cewa”am asking u..kinaso kisamun ciwon zucia sbd kinga na damu dake ne?..”dagowa tayi tana wiping tears dinta ta girgiza masa kai alamar aah..yace”then why are u doing this?..why are u punishing me like this?..na fada maki if sbd abubuwanda na maki a baya ne u are free to punish me amma am begging u to stop giving me tough times haka nan..na wahala mana..ko a haka kika barni i’ve learnt my lessons and ko a mafarki bazan sake yunkurin hurting dinki ba plss”..kallonshi kawai take ba tareda tace komai ba..kamo hannunta yayi da sauri ya dora kan chest dinshi yace”feel my heartbeat kiji..bai sake bugawa normal ba tun daga ranan dana fara sonki”..dakatawa yayi tareda dora kanshi kan hannun data yace”Aysha help me plss..am about going crazy”..kallonshi kawai Aysha keyi gabanta na tsananta faduwa…for the very first time taji ya mugun bata tausayi yau..ta yadda da gaske son nata yakeyi amma ita fa tana sonshi?..hannunta taji ya fara sagewa sbd kanshi daya dora akai dan haka ta shiga kokarin kwatan hannun ya sake mata shi da sauri ya dago kai yana kokarin maida tashin hankalin dake fuskanshi yace” am sorry”..yarfa hannun ta shiga yi kafin a hankali tace”it’s ohk”..shiru sukayi na wani lokaci kafin Bobby yace”zan baki enough time kije kiyi tunani akai..i promise bazan sake disturbing dinki da mgnr ba amma do help me plss..help me out of this whole mess”..kallonshi har yanxun takeyi tanajin zuciyarta na karyewa..tausayi yake bata fiyeda tunaninta amma ya zatayi?..tasan idan tayiwa baby haka bata mai adalci ba..koda tana son Bobby bai kamata ta wulakanta shi ba ballantana ba sonshi takeyi ba tausayi kawai yake bata…yana gama mgn ya gyara zamanshi snn ya dauki phone dinshi yayi dialing number daddy…yana fara ringing ya mika mata wayar ta amsa tareda karashi a kunne…tanajin yayi picking tayi saurin cewa”daddy ina kwana”..yace”lafia lau..meya samu wayarki ne Najeeb yace tun safe yake kira bai shiga ba”..a hankali tace”kilan network ne..nima tun jiya ina kira bana samunshi”..daddy yace”shknn..yanzu ki zama cikin shiri zuwa gobe flight dinku zai tashi inshaAllah..shima Najeeb din a gobe zai iso”..nan da nan face sinta ya washe da tsananin farin ciki tace”to daddy..Allah ya kawoshi lafia”..daddy yace”Ameen”..snn sukayi sallama..ta mika mashi wayarshi tana cigaba da murmushi tace”thank u”..kallonta kawai yayi bai iya cewa komai ba…ya amsa wayan ya ajiye snn ya tada motar suka cigaba da tafia…bakin wani mall taga yayi parking snn ya bude motar ya fita..after few minutes ya dawo da leda a hannunshi ya ajiye back seat snn ya shiga ya sake tada motar suka wuce..har yanxun babu mai cewa wani abu a cikinsu..shi gaba daya tunaninshi yanaga neman hanyar da zaibi don ya samu soyayyarta yayinda ita kuma nata tunanin ke ga tafiyar da zasuyi gobe zuwa saudi sai kuma asalin tausayinshi daya fara damunta…har suka isa gida ba wanda yayi mgn cikinsu..bayan ya gama parking ya dauko ledan da ya ajiye a baya ya mika mata ba tareda cewa komai ba..batayi gaddama ba ta amsa ta duba sai taga abaya ne a ciki da wani zundumemen hijab da ta tabbata sai yakai mata har kasa..da dan murmushi ta dubeshi tana fadin”thank u”..bude motar yayi ya fita ya saki dan guntun smile shima kafin yace”u are welcome”..daga haka ya wuce gaba tana binshi a baya har cikin gidan…har yanxu suna nan zaune a parlor ya karasa ciki ya zauna ita kuma Aysha gaishesu tayi snn ta wuce daki don Allah Allah takey ta kira Billy da besty ta sanar musu tafiyanta gobe ne…Aunty Munubiya ta bita da kallo har ta shiga flat din Mummy snn ta juya tana kallon Bobby dake zaune kusada ita..ya saki dan murmushi yana shafa kai baidai ce mata komai ba…itama bata ce komai din ba ta maida hankali ga hiran da suke wanda mostly na zuwa Gombe da zasuyi ne cikin sallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button