Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari Billy ta koma gida ya rage daga su sai su a gidan…Ammi na kitchen sunata shirin tarban daddy da zai dawo daga Abuja yau…hankalin Aysha duk ba jikinta yake ba as tunda sukayi waya da baby daxun ya daga mata hankali..cewa yake wai indai tana sonshi da gaske saita bashi daman yazo ya nemi aurenta kafin holidays dinsu ya kare idan kuma ta sake dakatar dashi zai dauki hakan da tayi as bata sonshi…hankalinta ya tashi sosai Allah ya sani bata san ta ina zata fara cema daddy za’azo neman aurenta ba..gashi duka duka hutun nasu saura one week ya kare..yanxun daga ina zata fara ne?..tun daxun take tunanin kota fara sanarda Ammi ita kuma ta sanar da daddy amma tsananin tsoro ya hanata tayi hakan dan Allah ya sani itadai tsoron abunda zaije ya dawo take..kilan ma cewa za’ay ba karatu takeyi a Kano ba soyayyanta kawau take..shi kuma baby duk yabi ya birkice mata ko wayanta ma ya dena dauka…a waya ta kira Billy tayi mata bayanin komai ita kuma ta bata shawaran taje ta fadama Ammi duk yanda sukayi da ita saita fadama babyn..tayi na’am da wnn shawara na Billy dan haka bayan ta fito daga kitchen kai tsaye ta bita zuaa bedroom dinta…tana kokarin shiga wanka Aysha ta shigo dakin..Ammi ta shiga binta da kallo ganin yanda tayi wani sanyi kmr ba ita ba tace”menene?..”karasawa tayi ta zauna gefen gado tana duban Ammin fuska a marairaice tace”Ammi mgn nakeso muyi”..komawa Ammi tayi ta zauna tana fuskantarta tace”to ina jinki”..a hankali ta sake dagowa ta kalleta sai kuma tayi kasa da idonta tace”Ammi dama..da akwai wani mutumi da muka hadu dashi a kano”..kallonta Ammi keyi tanaso taji inda zancen nata ya dosa tace”umhum cigaba mana”..saida ta hadiye wani yawu snn tacigaba”Ammi dama cewa yayi yana sona kuma da gaske aurena zaiyi..nace bazan kawoshi gida ba saina gama school shine daxu yace shidai dole yanaso ya turo ayi tambaya kafin na koma makaranta”..ta sakeyin shiru ta kurawa Ammi ido tanaso taga reaction dinta…ganin kallonta itama Ammin keyi tayi saurin cewa”kuma wlh Ammi bani nace mishi ya turo ba..da kanshi yace zaizo wai a fara saninshi a gida”..sauke ajiyar zucia Ammi tayi kafin tace”ke kina sonshi ne?..”shiru tayi tana kallonta..Ammi tace”magana fa nake miki”..a hankali tace”eh..”Ammi tace”shikenan kije zanyi magana da daddy idan ya dawo sai a fadama Lamido ya basu ranar da zasuzo..da yake ke mara hankali ce shine kikaje kika fara kulashi ba tareda ya turo gidanku ba”..itadai shiru tayi kanta kasa dan bata taba zaton Ammi ba fada zatayi mata ba..koda yake dama ance duk wata uwa mace da zarar yarinyarta ta girma batada burin da ya wuce ta sadata da dakin mijinta saidai idan lokaci baiyi ba…wnn mgn na mutane kuwa haka yake don ga alama nan ta gani wajen Ammi…mikewa tayi ta fita daga dakin bayan Ammi ta salameta..cikeda farin cikinta ta kira Prof ta sanar dashi yanda sukayi da Ammi..murna wajenshi tamkar bai taba aure ba…suna gama waya ta kira Billy itama ta sanar mata sai kuma ta jiye wayar tareda fadawa duniyar tunani..babu wanda ya fado mata a rai sai proprietor.. ta tabbata zai shiga mawuyacin hali idan yaji wnn labarin..to amma ita ba sonshi takeyi ba kuma bazata iya auren mai shekarunshi ba..tafi son babban mutum daya kusan haifanta yanda zataje taci duniyarta da tsinke…ta lumshe ido tana sake lafewa kan pillow incident dinsu ya shiga dawowa brain dinta…she remeber how he hold and tell her yana sonta morethan anything…how he made it clear cewa idan ta auri wani mutuwa zaiyi..then she remember his jealousy..ta tabbata level of jealousy dinshi yafi na baby sosai sbd yanda ko wani yaga yana kallonta kishi yakeji…abubuwa da dama ta shiga tunawa game dashi tun daga ranar daya fara mata allura har zuwa lokacin festival da Presentation da abubuwan da ya dinga nunawa a lokacin…ajiyar zucia ta sauke da gaske mgnr Billy haka yake kilan tun ranar daya fara ganinta yake sonta ganewa ne batayi ba…sai yanzu take ganin tsagwaron kishi cikin duk wnn abubuwan da yayi mata a baya…sake juyawa tayi tana rungumar pillow ta tuna how his Mom and siblings treated her time da taje gidansu..they are the most kind and nicest people she’ve ever come across..sunada karamci sosai likewise shi kanshi Bobbyn saidai shi yanada matsala daya which is masifa da shegen taurin kai…gaba daya tunaninta ranar sai ya tattara ya koma kanshi da ahalinshi kuma ta rasa dalilin hakan don dai ita bata taba tsayawa tunaninshi bama balle kuma na family dinsh..sai yanxu take ganin rashin dacewar amsan data bashi ranar..sam bata kyauta ba..ko bata sonshi bai kamata tana walakanta shi ba ko don sbd karamcinshi a gareta..yanada kirki sosai and yana sonta da gaske..duk sai taji wnn tunane tunanem sun addabeta sun hanata sukuni.
Tun safe kowa ya fito parlon waziri suka gaidashi kmr yanda suka saba gashi har za’a fara breakfast Bobby bai fito ba…parlon nashi a cike yake da Uncles din su Bobby maza da yaransu sai Aunty Munubiya dasu Aunty Sumy suma duk suna nan…Waziri ne ya dubi daya daga cikin jikokinshi yace”Khalid je daki ka dubamun Attahir kaga meya hanashi fitowa har yanxu”..ba musu khalid din ya mike zuwa dakinda aka sauki Bobby..a kwance ya iskeshi can karshen gado ya wani dukunkune kanshi cikin duvet sai rawan sanyi yake…da sauri ya haura kan gadon tareda yaye duvet din yaji jikinshi akwai zafi sosai dan haka ya sauka da sauri ya fita daga dakin yaje ya sanar da waizir..hankalinshi ya tashi sosai dan ko Mummy bazata kaishi tashin hankali ba..mikewa yayi kai tsaye zuwa dakin nashi..ya zauna gefen gadon tareda kai hannu yayi feeling temperature dinshi yaji zafi sosai..dan haka yace a fito da mota su tafi asibiti..ba yanda wasu daga yaranshi basuyi ba kan ya bari a kira doctor yazo ya dubashi amma yace sam bazai iya jira har sai likita yazo ba..ba yanda suka iya dole haka aka fito da mota suka wuce asibitin daga shi sai Bobby sai daya daga cikin cousins dinshi da kuma Uncle dinshi.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
42
Suna shiga asibitin family doctor dinsu ya fara dubashi su kuma suka jira a waje..babu yanda khalid da wani uncle din su Bobby mai suna Lukman basuyi da waziri kan suje waiting room ya zauna ba amma yaki haka yayita kai kawo a reception cikin tsananin tashin hankali kai kace Attahir dinshi ne na asali baida lafia…after like 15 mina doctor ya fito daga dakinda yake..tun kafin ya karaso inda suke waziri yayi saurin juyawa yana dubanshi cikin tashin hankalin dake karuwa a tareda shi yace”ya jikin nashi?..”a nutse doc yace”ya samu bacci yanxu”..waziri yace”amma meyake damunshi?..”daga kafada yayi before yace”well da akwai tests daya kamata a mashi amma dole saiya tashi daga bacci..for now dai few examinations da nayi masa ya tabbatar mun da cewa yana tareda damuwa snn da akwai mgn da yake kokarin fada ban gane me yake nufi ba..ina ganin idan akwai mahaifi ko mahaifiyarshi a kusa ya kamata a kirasu ko su zasu fahimci me yakeso ya fada”..sbd tsabar tashin hankali waziri har wani jiri yaji ya daukeshi kaman zai fadi..uncle lukman dake bayanshi yayi saurin tareshi yana fadin”Dan Allah Baffa ka kwantar da hankalinka..zai samu lafia inshaAllah”..girgiza kanshi yakeyi cikin tashin hankali…bayaso ya rasashi kmr yanda ya rasa mahaifinshi..gani yake kaman wani abu zai faru dashi..ganin halinda ya shiga doctor yace u shiga dashi ciki shi kanshi yana bukatar hutu a yanzu..ba musu suka shiga dashi inda Bobbyn yake kwance..kujera ya samu ya zauna snn ya dubi khalid dake tsaye kusada uncle lukman yace”ka koma gida ka taho da Nadia yanxun nan..kace ma Munubiya da Sumayya suma ina son ganinsu a nan”..da sauri khalid ya juya ya fita don tahowa dasu din…uncle lukman ya karasa ciki ya zauna shima ya zubama Bobbyn ido yana kallo kmr yanda waziri ma ke kallonshi…yana kwance kan gado hannayenshi dafe da forehead dinshi..numfashinshi na fita da sauri dalilin haka chest dinshi keta sama da kasa…kana ganin yanda face dinshi ke a yatsine zakasan ba dadin baccin yakeji ba…bayan 30 mins khalid ya dawo asibitin tareda su Mummy kmr yanda Waziri ya bukata…a rikice suka shigo dakin gaba daya su ukun musamman aunty sumy da Aunty Munubiya duk a figirce suke kmr ance rasuwa yayi Bobbyn..Mummy kuma tayi kokari sosai wajen 6oye tashin hankalin da ta shiga na ganin halinda Bobbynta ke ciki sbd presence na waziri da kuma qanin mahaifinshi a wurin…karasawa ciki tayi ta zauna tana duban waziri kafin tayi mgn ya rigata”likita yace Attahiru na tareda damuwa..kinada masaniya akan abunda ks damunshi?..”shiru Mummy tayi tana tunani..duk dunia dai tasan damuwar Bobby guda daya ne kuma shine Lamido…amma ya kamata ta fadama waziri ba tareda sanin takamaiman dalilinda ya jefashi cikin wnn halin ba?..muryan waziri ya dawo da ita daga tunaninda take..yace”idan kinsan wani abu na damunshi ki fadamin..banaso shima in rasashi kmr yanda na rasa mahaifinshi”..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace”eh to da akwai wata yarinya da nasan yana sonta saidai ban saniba ko sanadinta ne ya fada wnn halin”…shima ajiyar zucia ya sauke kafin yayi mgn Bobby yayi wani irin mosti da saida gadon da yake kwance akai ya motsa…da sauri suka yi kanshi gaba dayansu kowa na kiran sunanshi amma sai sukaga ya sake komawa yacigaba da baccin..bakinshi ne ya fara mosti alaman yana cewa wani abu dan haka Aunty Munubiya ta kai kunnenta daidai bakin nashi amma bata fahinci abunda yake cewa ba..ganin hawaye ya faro zubowa daga cikin idanunshi dake rufe waziri yace Mummy takai kunnenta ita ko zata fahimci me yake fada…ba musu kuwa ta kara kunnenta a bakin nashi still itama bata ji me yake cewa ba..ga kuma idanuwanshi a rufe suna fidda hawaye sai kuma legs dinshi da suka fara mosti suma yanzu…hannunshi ta kama tareda zaunawa nan gefenshi ta shiga murza hannun nashi tace”Bobby..”da sauri ya bude idanuwanshi tamkar abunda yake jira knn..sake matsawa tayi kusada fuskanshi tana dubanshi tace”meya sameka?..me kakeso kace?..”lumshe idonshi yayi yayi kokarin dakatar da hawayen dake cikowa idonshi snn ya damke hannunta dake cikin nashi muryanshi na fita da kyar yace”bata sona Mummy”..dakatawa yayi hawaye na sake antayowa fuskanshi kafin yacigaba da cewa”mutuwa zanyi Mummy..wlh duk ranan da ta auri wani mutuwa za…”kasa karasawa yay sbd kukan Mummy daya cika dakin..mikewa yayi zaune da sauri yana kokarin goge mata hawayen yace”Mummy am sorry plss..ki bar kuka dan All..”still ya kasa karasawa sbd ganin sauran jama’an dake dakin..wara ido yayi yana kallonsu sosai..idonshi na tsayawa kan waziri yayi kasa da kanshi da sauri yana sauke numfashi da sauri da sauri…karasowa waziri yayi Mummy ta bashi wuri ya zauna nan kusada dashi shima ya kama hannunshi snn ya dubeshi fuska ba yabo ba fallasa yace”wacece ita Attahir?..wace yarinya ce kake neman kashe kanka sbd ita?..”runtse ido Bobby yayi yana salati shknn asirinshi ya gama tonuwa..baiso waziri yaji mgnr nan ta haka ba..so yayi ya sameshi yayi mishi bayani in person bayan sun daidaita da ita amma she ruined everything..tun jiya daya fahimci da gaske bata sonshi bai sake samun kwanciyar hankali ba..gani yake shknn ya rasata wanda damuwar hakan ya sanya mashi zazza6i da ciwon kai wanda baya ko tantama blood pressure dinshi ne ya hau..ganin yayi tsit baida niyyar mgn Waziri ya janyoshi jikinshi ya rungume ya shiga shafa bayanshi a hankali yace”ka fadamin ‘yar gidan waye kuma a wane gari take?..nayi maka alkawarin duk inda take a fadin dunia ni da kaina zanje in nema maka aurenta”..lumshe ido yayi ya bude yanajin yanda zuciyarshi ke tsananta bugu still ya kasa cewa komai saida waziri ya sake cewa”Attahiru”..snn ya hadiye wani yawu daya cika mashi baki from no where yace”a..nan..Gombe take”..dagoshi waziri yayi daga jikinshi yana mishi duba irin na mamaki yace”Gombe?..wnn Gomben da muke ciki?..”gyada kai Bobby yayi idanunshi na kallon kasa yace”eh..”waziri ya sauke wani ajiyar zucia kafin yace”kaga faduwa yazo daidai da zama knn..fadamun ‘yar gidan waye a Gombe take neman zautar min da abokina haka?..”ya karasa mgnr cikin sigar wasa sbd yayi cheering dinshi up..su Mummy dai suna daga gefe sun zama yan kallo a tsakaninsu…waziri ya sake kama hannunshi yace”ka fadamun waye mahaifinta a Gombe?..”saida ya runste ido snn ya iya bude baki yace”Col Ahmad Lamido”..wani irin tsit dakin yayi kmr babu masu rai a ciki…waziri da yayi dif shima yana kallonshi kallonda ya kusan sa zuciyar Bobby ya buga sbd wasu abubuwa da zuciyarshi ke saka mishi gameda kallon..lumshe idonshi yayi kmr daga sama yaji waziri yace”Ahmad Lamido fa kace”..a hankali Bobby ya gyada mishi kai..cikeda wani mamakin waziri ya kuma cewa”Lamido dai wnn Adnan Lamido nawa?”..nan ma kai ya sake gyada mashi…lokaci daya wani annuri da farin ciki suka mamaye fuskan waziri…hannu ya budawa Bobbyn shi kuma ya shige jikinshi ya rungumeshi yana sakin murmushi yace”yanzu akan jinin Lamido kake wahalar da kanka haka?..kasan alaqar dake tsakanina da Lamido kuwa?..shi kanshi Ahmad din mutumin mahaifinka ne sosai kafin Allah ya kar6i rayuwarshi”..dagowa Bobby yayi yana dubanshi da murmushi ya gyada mishi kai alaman ya sani..waziri daya kasa dena murmusawa yace”baka saniba Attahiru..daka sani da baka tsaya kana wahalar da kanka kan jinin Lamido ba domin kaima ahalin Lamido tamkar ahali yake a wurinka”…wani irin hamshakin dadi Bobby yaji yana saukan mishi from no where…ya kama duk hannayen waziri ya rikesu gam cikin nashi voice dinshi na rawa yace”yanxu..zan iya..samun..aurenta?..”tun kafin ya rufe baki Waziri yace”da izinin Allah zaka samu..nasan Lamido bazai taba hana jinin Waziri jininshi ba”..wani irin runguma Bobby yayi mashi yana fadin”nagode sosai Baffa Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara girma”..waziri na shafa bayanshi yana cigaba da smiling yace”Ameen Ameen Attahiru..Allah ya jikan mahaifinka”..duk suka amsa da Ameen kafin ya dago yana sake duban waziri murmushin fuskanshi na raguwa yace”amma fa bata sona Baffa..da bakinta ta fadamin hak..”bai karasa ba waziri ya rufe mashi baki yana fadin”karka damu wnn a wurin Allah yake..nidai zanyi magana da Lamido da zarar mun koma gida”..gyada kai ya shigayi new tears na cikowa idonshi na farin ciki yace”Allah ya baka aljannah”…waziri ya amsa da Ameen snn yace khalid yaje ya kira doctor..ba musu ya juya ya fita su Mummy kuma har yanxun suna tsaye kowa tana goge hawaye tana kuma sakin murmurshi at the same time..musamman Mummy da take ganin Allah ne ya amsa addu’anta.
Doctor na zuwa ya danyi gwaje gwajenshi kafin yace”da akwai stress a tareda kai so ina ganin zamu ajiyeka a nan for 1 or 2 days sbd ka samu enough rest”..yana rufe baki Bobby yace”don’t worry i will take care of myself amma ayi discharging dina dan Allah”..kallonshi likitan keyi kafin yayi mgn Aunty Munubiya tace”he is a medical doctor”..tana rufe baki waziri yace indai yana ganin bai isa ayi discharging dinshi ba kada ya sallemshi har sai ya samu lafia…doctor yace ba damuwa zaiyi discharging din nashi sai ya dinga zuwa gida yana dubashi..yayi prescribing drugs da zaiyi amfani dasu ya bashi snn yayi discharging nashi yace zasu iya tafiya…a hankali yake takawa sbd jikinshi da baijin karfinshi kwata kwata…motan waziri ya shiga suma su Mummy suka shiga wanda aka kawosu snn suka bar asibitin…suna zuwa gida Aunty Munubiya ta hada mashi ruwa ya shiga yayi taking shower ya fito yasa kaya snn aka kawo mashi abinci…kasa cin komai yayi sbd shifa har yanzun hankalinshi ba kwantawa yayi ba sbd rashin sanin takamaimai halinda ake ciki…shin zai samu auren nata ne ko bazai samu ba?..shin zata hakura ta aureshi dukda bata sonshi ko bazata hakura ba..a soyayyan da yake mata shi gani yake ko bata sonshi matukar zata yadda ta aureshi he’s ok..kawai yayi feeling kanshi cikin gida daya da ita ma ba karamin abu bane a wurinshi so muddin zata zauna dashi ko bata sonshi he won’t complain…haka ya kasa taba komai cikin tarin abincin da aka jere a gabanshi saida waziri ya shigo da waya a hannunshi yace yayi sauri ya gama cin abincin sai ya kira Lamido ya fara sanar dashi abunda ke da akwai kafin yaje har gida ya sameshi…nan da nan kuwa ya shiga tunkuda abincin Aunty Munubiya na kallonshi tana mishi daria…yana gamawa waziri ya kira Lamido a waya as he promised saidai har wayan ya gama ringin baa daga ba..ya sake Kira nan ma no answer dan haka ya jiye wayar yace zuwa anjma zai sake kira kilan yana wani uzuri ne don dai yasan matukar babu babban uzuri ba yanda za’ayi ya kira wayar Lamido har sau biyu ba tareda ya dauka ba.