Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

A daidai lokacinda Waziri ya kira wayar Lamido shi kuma yana tareda daddy da bai jima da dawowa ba yana sanar dashi mgnr da Aysha sukayi da Amminta daxu na cewa wani wanda yake son aurenta yanaso yazo ya gana dasu…tunda daddy ya fara mgn Lamido yayi shiru yana sauraronshi har saida yakai aya snn ya numfasa yace”ka gama?..”a hankali daddy dake zaune nan kasa yace”na gama Baffah”..Lamido yace”to koma waye kace mata ta sanar dashi ba sai yazo ba”..da mamaki sosai daddy ke duban mahaifin nashi saidai baice komai ba…Lamido daya daure fuskanshi yace”saboda nayi mata miji”…sake dukar da kai daddy yace”Allah yasa hakane yafi alkhairi”..Lamido yace”Ameen..gobe idan Allah ya kaimu inaso ka kawomin ita Aishan da Maimuna inason mgn dasu”..cikeda ladabi ya sake fadin”InshaAllah za’a kawosu..Allah ya kara girma”..Lamido ya sake cewa”Ameen..kana iya tafia”..ba musu daddy yayi sallama dashi snn ya tashi ya fita…har ya isa gida bai dena tunanin mgnr da Lamido ya fada ba..ko waye mijin da yayi mata oho?..abu daya dai ya sani shine Lamido bazai ta6a yi mata za6en tumun dare ba don haka tun ma kafin yasan waye yayi na’am dashi domin sanin halin Lamido da kalamu waheed..zaiyi wahala ya fadi mgn kuma daga baya ya dawo ya canza ta..fatanshi dai bai wuce Allah ya daidaita kansu da Aysha ba don yasan muddin aka ce za’a aura mata mutuminda bataso za’aga tashin hankali..Aysha da kan abunda baikai ya kawo bama take kuka balle kuma wnn daya shafi rayuwarta na gaba..ai saidai Allah ya dorashi kanta kawai idan bahaka ba kam za’a ga rashin hankali.
Koda ya koma gida sai ya kasa sanar da Ammi yanda sukayi da Lamido..kawai yana tunanin itama bai zama lallai taji dadin hukuncin na Lamido ba amma ya zaiyi?..bashida yanda zaiyi ne kmr yanda suma basuda yanda zasuyi dan haka ya zama musu dole su kar6i koma waye Lamido ya za6a mata da hannu bibbiyu…Ammi ta lura yana tareda damuwa kuma jikinta ya bata akan mgnr da yajema Lamido dashi ne..bata tambayeshi ba’asi ba saida dare yayi ta shigo dakin nashi cikin shirin bacci kmr yanda ta saba…daddy najin shigowarta yayi saurin rufe ido sbd tayi zaton yayi bacci amma abunda bai saniba shine duk wani 6oye 6oyenshi Ammi ta riga ta fahimci akwai damuwa a taredashi damuwan kuma baya rasa nasaba da batun auren Aysha da sukayi da Lamido…saida ta bari ya gama gyara kwanciyarshi shi bai yadda ba bacci yake snn a hankali tace”daddy..”daddy ya runtse ido yana addu’ar Allah yasa bata gano me yake 6oyewa ba kuma bai amsa mata ba…sake kiran sunanshi tayi still ba amsa dan haka takai hannu ta yaye duvet daya rufe dashi cikin raunin murya tace”wace mgn ce wnn da bazaka iya fadamun ba har kake baccin karya daddy?..”sake runtse ido yayi yana salati..Maimunatu badai fahimta ba..yanxun duk wnn 6oyewan da yake saida ta fahimci akwai wani abu a tattare dashi?..kasa cewa komai yayi sai mikewa da yayi zaune yana kallonta…kallon nashi itama take cikin sanyin murya tace”ka sanar dani abunda kw faruwa dan Allah..me Baffa yace?..”kallonta kawai daddy yake yana mamakin kwakwalwa irin nata..no wonder gaba daya yaransu sukeda brain especially Aysha data dauko komai da komai irin nata..itama bala’in kwanya gareta…kama hannunta yayi yana kallon cikin idonta yace”ki kwantar da hankalinki Maimunatu..ba wani babban abu bane”..tun kafin ya rufe baki tace”da wnn abun da kake yana sawa inyi tunanin babban abu ne daddy..kawai ka sanar dani ya kukayi da Baffa?..”ajiyar zucia ya sauke kafin yace”naje mishi da mgnr Aysha kmr yanda kika fadamin saidai tun ban karasa ba yace ace mata ta fada mashi ba sai yazo ba don yayi mata miji”..ya karasa mgnr cikin sanyin murya…dan murmushi Ammi ta saki tana kokarin 6oye dan rudanin data shiga tace”yanxu akan wnn mgnr kaketa 6oye 6oye bakaso ka sanar dani daddy?..”sake kama hannunta yayi yana dubanta da kyau yace”nasan Lamido bazai taba zaba mata mijin da bai dace da itaba saidai ina tsoron yanda ita Aishan zata dauki mgnr..kinsan halinta”..murmushi Ammi ta kara saki a kokarinta na ganin ta kwantarwa da mijinta hankali tace”wnn baikai dalilinda zai saka damuwa ba daddy..Ayshan nan fa ‘yarka ce..da kai da ita kuma duk kuna karkashin Lamido ne so ya zama mata dole tayi mashi biyayya kmr yanda kaima ya zama maka dole”..kallonta daddy keyi yanajin wani irin sanyi a cikin ranshi…yaji almost 70%na damuwar da yake ciki ya gushe sbd maganganun nan nata..shiyasa dai ake cewa mace ta gari jin dadin rayuwa domin komai arziki da mulkin mutum matukar bashida mace ta gari bashida jin dadin rayuwa..duk wnn abunda take yasan itama baza’a rasa ko yayane dan damuwa a tareda ita ba amma ko kusa bata nuna mashi ba..yasan kuma koda za’a aura mata wanda bataso bazata ta6a bude baki tace mishi bataso ba ko kuma ta nuna wani alama da zai tabbatar da hakan…mace ce ita mai tsananin kara musamman akan Aysha data kasance ‘yar fari..wnn dabi’un nata yasa a kullum sonta ke zama sabo fil a cikin zuciyarshi..bashida burinda ya wuce yaga ya faranta mata kmr yanda itama bata gajia da faranta mishi…(ubangiji ka azurta duk wani miji na gari da samun mata ta gari????????sisters kuce Ameen????).

The following morning tare sukay breakfast gaba daya a dinning dake nan parlor which is so unlike them..zaiyi wahala daddy da Ammi suyi breakfast tare dasu mostly su biyu sukeyin abunsu a can parlon daddyn…Aysha dai sai baza ido da kunne take tana jira taji yanda Ammi sukayi da daddy amma bataji komai ba..so take taji shin Ammi tayi masa mgnr ne kuma ya sukayi da Lamido?..baby gaba daya ya daga mata hankali sai rigima yakey mata wanda batasan sanda ya koya ba..kawai duk yabi ya sata cikin rudani itada takeso ta gama FCNM snn ta tafi abroad tayi furthering karatunta kmr yanda sukayi da daddy shine yanzun yake 6ullo mata da mgnr aure…Allah ya gani itadai ba shiryama auren nan tayi ba kawai ta yadda ne don batada yanda zatayi dashi…har suka gama breakfast dinsu ba wanda yace mata uffan hakan kuma yasa tasha jinin jikinta…Najeeb ne ya mike yayi sallama dasu snn ya fita tareda Husna da Yusra da zaiyi dropping nasu a islamiyya da sukayi resuming yau shima kuma ya wuce wajen aikinshi…itama Aysha mikewa tayi zata bar dinning din daddy ya kira sunanta…gabanta yayi wani irin faduwa na ba gaira babu dalili kafin ta juyo a hankali tana kallonshi tace”na’am”..ba tareda ya kalli inda take ba yace”kije ki sako hijab dinki yanxun nan kizo zamuje wajen Lamido”…wara idanu tayi gabanta na sake faduwa jin abunda ya fada..tabbas tasan akwai wata a kasa..babu yanda za’ayi ace ta shirya aje wajen Lamido a irin wnn lokacin..Innalillahi kawai take furatawa a ranta ta kasa ko mosti..Ammi da taga tayi wani tsaye kmr bada ita ake mgn ba tace”wai badake ake mgn bane?..wane irin iskanci ne wnn?..”juyawa tayi da sauri tana fadin”sorry Ammi”snn ta shige dakinsu…daddy ya mike daga dinning din yana duban Ammi cikin sigar wasa yace”fadanki ya fara yawa fa Maimunatu..inajin yanda kullum kike samun yara a gaba kina musu fada kawaici nakeyi maki”..mikewa tayi itama tana murmushi tace”yaran naka ne ai basajin mgn musamman ita wnn da har yanxu ta kasa fahimtan cewa itace babba”…murmushi kawai ya sakeyi ya wuce zuwa parlonshi tana mara mishi baya…car keys dinshi ya dauka itama Ammi ta zura hijab snn suka fito tare…daidai lokacin itama Aysha ta fito sanyeda katon hijab dinta har kasa…ficewa sukayi daga gidan daddy ya mikama Ammi makullin motar ba musu ta kar6a ta bude musu ya shiga front seat Aysha kuma ta shiga baya sai ita Ammin ta shiga driver seat..dama haka yake bai cika daukan driver zuwa gidan Lamido ha sai dai idan daga can zai wuce aiki bazai dawo ta gidan ba..itama Ammi duj zataje da kanta take driving kanta tareda yaran…motar shiru har suka isa gidan Lamido ba wanda yayi mgn cikinsu…a tare suka bude mota suja fito snn suka nufi entrance din gidan…daddy ne yayi sallama Lamido ya bashi izinin shiga snn suka shiga makeken parlon nashi…as usual yana zaune kan kujera yana kallonsu har suka karaso duk suka zauna a kasa snn suka fara gaisheshi..amsawa yayi cikin dattako da kamala irin nashi kafin yayi shiru yana kallonsu kmr bazaiyi mgn ba sai can kuma yace”Maimuna mgn ce nakesonyi dake”..kai a kasa Ammi tace”ina sauraronka Baffah”..yace”ina fatan Ahmad ya sanar dake yanda mukay dashi jiya”..kai ta daga tareda fadin”ya sanar dani”..Lamido yace”MashaAllahu…yanxu meye shawaranki akai?..”da sauri tace”ai ni banida wani shawara face bin umarninka Baffah..duk hukuncin daka yanke daidai ne Allah yasa haka shi yafi alkhairi”..cikin murmushin jin dadin kalamanta yace”to Madallah Maimuna Allah ya maki albarka”..ta amsa da”Ameen Ameen”..shiru dakin ya sakeyi kafin Lamido ya tsayar da idonshi kan Aysha da taji wani hadadden tashin hankali ya risketa yanxun nan..haka nan jikinta ya bata wnn kiran na Lamido bana lafia bane..gashi sai wani mgn sukeyi a kunshe ta kasa gane me suke cewa…ganin yanda duk tabi tayi tsuru tsuru tana rarraba ido Lamido ya saki murmushi wai tunma kafin taji mgnr da zai fada nata knn..dama yasan zaisha rikici ba dan karami ba da yarinyar nan amma saidai ko mutuwa zatayi bazai canxa mgnrshi ba..cikin muryar daya kusa sata fitsari yace”Aisha”..a firgice ta dago kai tana kallonshi har hawaye sun fara ciko idanunta..Lamido bai damu da hawayen nata ba yacigaba da mgn”kin turo mahaifinki jiya akan mgnr wanda kikeso koh?..”da sauri ta gyada mishi kai kmr mara hankali..Lamido yace”Alhamdulillah to inaso ki sanar dashi cewa ni Lamido na dade dayi maki miji”..wani irin zare idanu tayi tana kallonshi kmr bata gane me yace ba…ganin haka Lamido ya sake daure fuska yanda bata isa ta kawo mashi wargi ba yace”kinji abunda na fada ko in sake maimaitawa?..”nan take ta dawo daga suman zaunen da tayi hawaye suka shiga sauko kan fuskanta tace”na..ji”..yace”MashaAllah saiki kirashi ki fada mashi”..sake gyada mashi kai tayi hawaye na sake tururuwar zubowa fuskanta…har wani sarawa taji kanta nayi sbd tsabar tashin hankali..tunda take zata iya ranstuwa bata ta6a tsintar kanta cikin tsananin tashin hankali irin wnn ba..me Lamido yake nufi da yayi mata miji ne wai?..yanxu yana nufin bazata auri baby ba?..kuma waye shi wnn mijin da yayi mata?..lokaci daya ta kasa daurewa ta saki wani irin kuka tareda dora hannunta a kai kmr wanda uwa da ubanta suka mutu..shknn tasan ta riga ta gama yawo domin Lamido bazai ta6a canxa mgnrshi ba..abune wanda tasan ya zamar mata dole ta auri za6in da yayi mata amma shin waye wnn za6in nashi?..meyasa tun tuni bai ta6a furta yayi mata miji ba sai yanxu?..meyasa saida ta kawo wanda takeso Lamido zaiyi mata haka?..kuka takeyi wiwi tamkar wanda ta rasa iyayenta..Lamido sai yayi relaxing kan kujeran da yake yana kallon yanda take kuka kmr ranta zai fita..ganin haka daddy ya daka mata tsawa yana cewa”Aysha bakida hankali ne zaki tasa mu gaba kina mana kuka haka?..so kike ki nuna ba’a isa dake bane ko yaya?..”da sauri ta hau girgiza kai har yanxu hawaye basu dena ambaliya kan fuskanta ba ko mgn ta kasayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button