Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Jama’a wa kuke ganin Lamido ya za6a a matsayin mijinda zata aura..Bobby ne?..ko kuma wani ne daban?..????

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
43
Kuka takeyi sosai cikin tsananin tashin hankali da rashin sanin tudun dafawa…yanxu wnn mgnr na Lamido na nufin auren dole za’ayi mata knn?..yanxu suna suna nufin ta rabu da baby knn?..innalillahi wa inna ilaihi rajiun…bude baki daddy ya sakeyi da nufin yayi mata masifa sai Lamido ya daga masa hannu alamar he shouldn’t say a word..ba musu yaja bakinshi ya rufe yana kallonta..Ammi dama tana zaune ko kai bata dago ba balle tayi mgn…kallonta Lamido yayi fuska a daure ya sake kiran sunanta…ta dago tana kallonshi hawaye nata sintiri kan cheeks dinta…murya a dake yace”anyi maki wani abun ne kikema mutane kuka?..”shiru tayi kai a kasa..a fusace Lamido yace”ba mgn nake maki bane?..”girgiza kai ra shigayi da sauri tana runtse idanunta…yace”to kan wane dalili zaki zauna kina mana kuka?..ko kinga abokin wasanki a nan wurin,?..”nan ma kai ta sake girgiza alamar babu..yace”then wipe off those tears tun kafin raina ya 6aci..kika bari na sakejin kukanki kuma zakiga matakin da zan dauka”..tsit tayi tana toshe baki da hannayenta…shi kuma ya zuba mata ido har saida ta goge hawayen tas snn ya juya yana duban daddy yace”Ina Najeeb yake?..”kai a kasa daddy yace”yaje wajen aiki”..Lamido baiyi mgn ba sai wayarshi daya dauka nan kusa dashi yayi dialing number Najeeb..yana fara ringing Hamma Najeeb ya dauka da fadin”barka da safiya”..Lamido yace”barka dai..kana ina yanxu?..”Najeeb yace”ban dade da shigowa office ba”..yace”to ka dauki excuse ka dawo gida inason ganinka yanxun nan”..da sauri yace”Baffa lafia kuwa?..”katse wayarshi Lamido yayi bayan yace”ka hanzarta ba zaman jiranka zamuyi a nan ba”..su daddy dai na zaune sunajin me yake cewa amma ba wanda yace uffan…zaman kurame suka shigayi a parlon har Najeeb ya karaso…waje Lamido ya nuna mashi kusada Aysha ya zauna snn ya sake daure fuska yanda zai dauki mgnr da zai fada da muhimmanci kafin ya nuna Aysha da hannunshi yace”fadamun ya kake da wnn yarinyar?..”kallonta Hamma ya juya yayi snn ya dawo da kallonshi ga Lamido cikeda mamakin tambayar…cikin tsawa Lamido yace”bada kai nake mgn bane?..”da sauri yayi kasa da kanshi kafin yace”qanwata ce ita”..Lamido ya sake cewa”qanwarka kawai?..”juyawa Hamma ya sakeyi ya kalli su daddy snn ya kuna juyowa ga Lamido yaga yanda ya tsareshi da ido sai yace”kuma tanada sunan Mamana”..duk yanda Lamido yakai da daurw fuska saida mgnr nan ya bashi daria..wai tana sunan mamanshi..amma wnn yaro Najeeb ba dan karamin soko bane…hatta su daddy saida mgnr ya basu daria kuma duk basu kawo komai a ransu ba saida Lamido yace”to itace wadda na za6a maka matsayin matar da zaka aura kamar yanda kaima kaine na za6a mata matsayin mijinda zata aura”..wani irin diff dakin yayi kmr anyi ruwan sama an dauke…daddy da Ammi syka shiga kallon kallo dan ba wanda tunaninshi yazo nan wurin…Aysha kuwa wani irin darammm taji gabanta ya fadi ta shiga zare ido kmr wata zakanya ta juya tana kallon Hamman da shima idanunshi ke kanta yana zare ido…relaxing Lamido yayi yana kallon yanda suke kallon kallo a tsakaninsu..daga reaction dinsu ya fahimci mgnr a bazata yazo musu…har yanxu kuma parlon tsit an rasa mai kwarin guiwar da zai fara mgn cikinsu…baki Aysha ta bude zata sake rushewa da kuka Lamido ya daka mata wani tsawan da batasan sanda ta kankame Najeeb dake zaune kusada ita ba…ba shiri ta hadiye kukan tsaf tana cigaba sauke numfashi gamida rarraba ido kmr shege a rabon gado…wani shiru dakin ya sake dauka kafin Lamido ya juya yana fuskantar su daddy yace”Ahmad ko baku fahimci mgnr dana fada bane?..”daddy ta hadiye wani yawu daga bakinshi kafin cikin karfin hali yace”mun fahimta Baffa..kuma munyi na’am da haka ubangiji ya sanya alkhairi a ciki”…kasaitaccen smile Lamido ya saki ya dubi Ammi ita yace”kema kin amince Maimuna?..”har yanxu kanta na kasa tace”na amince..Allah ya tabbatar da alkhairi”..wanu murmushin Lamido ya kara saki kafin yace”Allah ya maku albarka”..suka amsa da Ameen snn ya sake juyawa ga iyayen gayyar wato Lamido da Hammanta…idanunshi ya tsayar kan Najeeb da yake ganin komai dake faruwa kmr a faraki yace”daga yau inaso ka fara daukanta matsayin matar da zaka aura ba wai qanwa ko mai sunan Mamanka ba..kema kuma ki tabbata kin bashi wnn matsayin don ko mutuwa daya daga cikinku yayi sai an daura wnn auren..kuje na sallameku”…mikewa Hamma yayi da kyar ya juya zai fita daga parlon Lamido yace”dawo ka tafi da ita”..ba musu ya dawo tareda durkusawa ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye snn ya shiga janta kmr mara lafia suka fita daga parlon…juyawa yayi wajen su daddy yace”kuma kuna iya tafia Allah ya maku albarka”..bayan sun amsa da Ameen duk suka mike suka sake mishi sallama zasu fita Lamido yace”Ahmad ka tabbata ka fada masu suyi kokari su fahimci junansu kafin ta gama makaranta don wnn aure ko mutuwa nay banaso a fasa yinshi”…gyada kai daddy yayi before”zanyi kokari in Allah ya yarda..mun barka lafia”..daga haka ya juya yabi bayan Ammi suja fita daga parlon…basu samu su Aysha nan compound ba hakan ya nuna musu cewa kilan sun wuce gida dan haka shima ya bude nashi motar suka shiga wnn karon da kanshi ya jata suka bar gidan…a hanya Ammi tayi tsit ta kurawa waje daya ido tana tunani…gangarawa gefen titi yayi yai parking tareda jama hannunta ya rike cikin nashi…ta juyo da sauri tana kallonshi sai kuma ta sakar mashi smile dinta me kyau…kallonta yakeyi da damuwa yace”kiyi hakuri Maimunatu”..Ammi ta dan wara ido tana dubanshi tace”hakurin me kuma?..”yace”nasan bai zama lallai kiso wnn hadin nasu ba amma inaso kisan babu yanda zamuyi da Lamido tunda ya riga ya furta”..hannunshi itama ta rike tana sakin murmushi tace”ko kusa bana kin auren Aysha da Najeeb wlh..kawai mgnr ne yazomin a bazata kasan ban ta6a kawo a raina wai shine mijinda ya za6a mata ba…Najeeb yaron kirki ne mu muka raineshi sbd haka babu wanda ya dace da auren Aysha idan bashi ba..nasan zai riketa da kyau kuma zai iya bida ita a hankali sbd rashin jinta”…ajiyar zuciya daddy ya sauke yana kallonta da murmushi..gaskia Maimunatu matar arziki ce…da wnn maganganun nata sai yaji duk kokwanton da yake akan batun ya gushe..tabbas shi kanshi yasan Najeeb yaro ne mai hankali kuma bayada wani mugun hali da za’a hanashi aure sbd shi..dadin dadawa kuma danshi ne domin shi ya rikesh tun yana dan karami kuma kmr yanda ta fada zai iya da Aysha sosai sbd ya riga dama yasan halinta ciki da bai so basu da damuwar komai…tayar da motar yayi suka karasa gida kowa ranshi fess dan Allah ya gani sunyi na’am da wnn za6in na Lamido…a parlor suka iske Najeeb din zaune ya buga uban tagumi ga kukan Aysha daya karade dakin gaba daya…yana jin shigowarsu ya mike da sauri ya isa garesu yana cewa”dan Allah daddy babu yanda za’ayima Lamido ya janye mgnr auren nan?..”kallonsh duk su biyun sukeyi kafin su hada baki wajen cewa”baka sonta ne?..”wani irin kunya yaji ya rufeshi dajin tambayan nasu…shaf ya manta fa iyayenta ne and suna iya jin babu dadi idan ya nuna bai sonta..amma shi harga Allah ba kinta yake ba kawai abun ne yazo mishi unexpected sai kuma wnn uban kukan da take sai kace ance za’a aura mata dodo…girgiza kai ya shiga yi da sauri yana nuna kofar dakinsu yace”kawai..banaso ayi mata dole ne..rufe kanta tayi fa a daki taketa kuka daddy kada wani abun ya sameta”..kama hannunshi daddy yayi suka karasa cikin parlor suka zauna snn yace mishi”indai don wnn ne ka kwantar da hankalinka ai ka riga kasan yanda take dama..wnn kukan koma waye akace zan za6a mata sai tayishi so wnn kar ya dameka ko kadan..kawai kacigaba da addu’a”..kai kawai ya iya gyadawa cikin ranshi yana jinjina kalar darun da za’ay da ita don yasan dole ne sai tayishi wlh…mikewa yayi bayan yayi musu sallama ya koma wurin aikinshi yayinda Ammi ma ta shiga kitchen shi kuma daddy yai zaune a parlon yana sakawa da kwancewa..fatanshi kawai Allah ya daidata al’amura kada azo ana samun matsala…Aysha kuwa tana daki tanata rizgar kuka ba wanda yabi ta kanta don a cewarsu idan ta gaji dan kanta zata dena kuma zata bude kofa ta fito ko don yunwar cikinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button