Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaune suke cikin parlon Lamido gaba dayansu kmr yanda ya bukata…Ammi,daddy sai Aysha da Najeeb..gaba daya suna zaune a kasa while Lamido da tun shigowarsu ya kasa cewa uffan yana zaune a usual seat dinshi…kawai tunanin ta inda ya kamata ya fara yake..kmr bazaiyi mgn ba sai can yace”Najeeb”..a hankali Najeeb da har yanxun kanshi ke kasa ya amsa mashi…Lamido ya gyara zama before saying”tambaya nake son maka kuma inaso ka bani amsa iyakar gaskiayarka”..a hankali ya daga kai tareda fadin”InshaAllah”…Lamido yace”shin akwai wadda kakeso kafin wnn mgnr ya 6ullo?..”shiru dakin ya dauka kowa na jiran yaji amsar da zai bada…ganin yanda yayi shiru kai a duke Lamido yace”ko bakaji abunda na fada bane?..”da kyar ya bude bakinshi yace”ina dashi”..Lamido yace”a ina take?..”shiru ya sakeyi ba mgn a fusace Lamido yace”idan ina maka mgn kanamun shiru zakasa in canxa ra’ayina wlh”..tun kafin ya rufe baki yace”kayi hakuri..a nan Bauchi take”..kallonshi duk sukeyi before Lamido ya sake cewa”Bauchi a ina?..bude baki fa zakayi kayi bayani don idan ba gamsuwa nayi da yarinyar ba bazaka aureta bane”..har yanxun shidai kanshi na kasa yace”sunanta Bilkisu Ibrahim Muqaddas..tare suke makaranta da Maama”…wani irin zare ido Lamido tayi kai kace wani mugun abu ya fada..lokaci guda fuskanta ya washe da murmushi cikin tsantsan farin cikin da taji ya diro mata all of a sudden tace”Hamma are u for real?..da gaske Billyna kakeso?..”dakatawa tayi da mgnr tareda matsawa kusa dashi sosai hadda su kama hannunshi tace”bani labari Hamma yaushe ka fara sonta?..ya akayi ma kana son Billy amma ban sani ba..Hamma dan Allah ka…”bata karasa ba Lamido ya daka mata wani tsawan da batasan sanda ta koma inda take ba da sauri tana rarraba ido..sam ta manta wai a gabanshi suke..farin ciki yasa ta manta da hakan jin wai Hamma da kanshi ne yakeson Billynta..knn hakan yana nufin tun tale tale yana son Billy basu sani ba..shin Billyn tasan yana sonta ta 6oye mata kmr yanda itama bata fada mata Proprietor na sonta ba ko kuwa itama bata san yana son nata ba..duk zaman wurin sai taji ya gundureta Allah Allah take su bar wurin ta samu ta kira Billy taji ya wnn batu yake…Lamido dai maida dubanshi ga Hamman yayi yana cewa”kace mene sunanta?..”a hankali ya sake cewa”Bilkisu Muqaddas”..Lamido yace”jikar Inuwa Muqaddas ce knn?..”kai ya gyada mishi..Lamido yace”to Alhamdulillah ‘yar manyan Mutane ce ai..shi Alhaji Muqaddas din was a very goon friend of mine and zan tuntu6eshi da mgnr”..da sauri yace”ai bamu gama daidaitawa da ita ba”..yace”wnn duk ba matsala bane zanyi mgn dashi dai..Allah yasa albarka”..duk suka amsa da”Ameen”..daga nan kuma ya maida hankalinshi kan Hajia Indo mai gayya mai aiki..ta sake sinne kai tamkar tana gaban surkai dukda cikin ranta murna ce fal na jin wnn labarin na Hamma da kuma warware wnn auren da Lamido keson hadawa da akayi..she’s super excited kawai sai murmusawa takeyi ita kadai kmr munafuka…ganin bata ma san kallonta yakeyi ba yace”Aisha..”da sauri ta dago tana kallonshi kmr mutumiyar kwarai..kofa ya nuna mata tareda fadin”kina iya tafia”..da sauri ta mike ta kama hanya zata fita tace”Nagode Allah ya saka da alkhairi”..Lamido baice mata komai ba har ta fita snn ya dawo da dubanshi ga Hamma yace”kaima kana iya tafia duk yanda mukayi da Muqaddas din zakaji”..kai a kasa shima ya mike tareda yi masa godia ya fita…ya rage daga daddy sai Ammi a parlon..Lamido na duban Ammi yace”Maimuna kin amince da mgnr dan wajen Attahir?..”kai a kasa tace”na amince..Allah yasa haka shi yafi alkhairi”..yace”to madallah zanyi mgn da wazirin anjima..ita kuma Aisha ina sane naki fada mata sbd nasan hauka zataimn..idan kunje sai ku mata bayani”..daria sosai mgnrshi ya basu haka suka mishi sallama suka fita suna sake darian mgnr daya fada…suna fita Lamido ya dauki wayanshi ya kira Waziri suka fara mgn.

dadi sosai daddy yaji da Allah ya sauya al’amura haka?..ya tabbata Attahir zai kasance miji na gari a gareta ko don son da akace yana mata.
Aysha na fitowa daga parlon ta shiga kiran number Billy bata dauka ba..sake dialing tayi tana tafiya tana fadin”Billy pick up the call mana..pick up pls”..har ya gama ringing dinshi Billy bata dauka ba ita kuma bata gaji da jera mata missed calls ba…Hamma Najeeb daya biyo bayanta da sauri ya karasa inda take kawai sai ji tayi ya fizge wayar daga hannunta yana kallonta…juyawa tayi tana dubanshi itama sai kuma ta saki murmushi tace”Hamma dan Allah mgnr daka fadama Lamido gaske ne?..da gaske Billyna kakeso?..”harara ya watsa mata mai kyau kafin yace”ban saniba..kiranta kikayi zaki fada mata kou?..”murmushi ta Kara saki tace”of course mana..so nake inji labarin komai in detail amma batayi picking call dina ba”..ta karasa mgn tana turo baki…hannu ya kai ya dan bugi bakin nata before saying”to ban aikeki kije ki fada mata ba dan itama ba sani tayi ba..idan kika barni da kaina zanje in sanar da ita when the right time comes”..kallonshi take tana murmushi sosai tace”to bazan fada mata ba Hamma..amma dan yaushe ka fara sonta?..does she loves u too?..”girgiza kai kawai yayi yana murmushi jin wai tambaya take if tana sonshi..sai kace ba yanxu yace mata bata ma san yana son nata ba shine take mishi wnn tambayan kmr ba itane ta dauke mishi wuta sbd ance zai aureta ba.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
46
Zaune suke office din Nur tun safe ya baro nashi office din yazo ya tasa shi a gaba shi baije yayi aikinshi ba kuma shima bai barshi yayi nashi aikin ba…kawai yazo ya mishi kwance a office kaman wani mara lafia…for the fifth time Nur ya sake cewa”kaga malam if zaman office din nawa ke maka dadi tell me insan inda dare yayi mun..haka nan kazo Kamin wani kwance office sai kace mara lafia”..banza Bobby yayi dashi kmr baiji abunda yace ba..Nur ya tsaya kallonshi cikeda takaicin wnn iskancin da yake mai…murmushin iskanci ya saki tareda fadin”dont worry nasan maganinka ai..da Lamido zanje in hadaka tunda yanxu naga duk dunia ba wanda kake jin mgnrshi kmr nata”..still Bobby banza yayi dashi idanunshi lumshe sai karkada legs dinshi yake..Nur ya mike tareda tattara papers daya baza kan desk dinshi ya dauki makulli da wayanshi snn ya kama hanya fita yana cewa”to in ka gama saika rufe office din..naga kaman kwana zakayi a ciki”..sai yanxu ya bude ido yana kallon Nur dake neman barin office din yace”wai meyasa bakada mutunci ne Nur..baka ga halinda nake ciki ba da zaka dameni da surutu?..”juyawa Nur yayi yana kada kanshi yace”nine ma Lamido da naki accepting soyayyarka zakazo har office dina ka faramun hayaniya..na tabbata ko ita da tayi turning dinka down bakayi mata irin wnn wulakancin ba sai ni daka gama rainama wayo..don’t worry nasan maganinka”..dafe head dinshi yayi yanajin yanda wnn iskancin na Nur ke neman kara mashi tension kan wanda already yake ciki..wayanshi ne ya fara ringing ya dauka da sauri ganin Mummy ce yayi picking tareda kaiwa ears dinshi before yace”Mummy”..a daya 6angaren full of excitement Mummy tace”Bobby guess what?..”dan shiru yayi kmr me tunani kafin yace”Mummy kinsan am not a good guesser kawai ki fadamin”..murmushi ta kara saki before tace wani abu another kira ya sake shigowa wayanshi..dubawa yayi sai yaga Waziri dan haka da sauri yace”Mummy hang on for a minute plss..Waziri ke kira”..Mummy bata ce komai ba tayi hanging call dinta shi kuma yayi picking na waziri tareda fadin”Baffa barka da rana”…Nur da yaji ya ambaci waziri yayi saurin komawa cikin office din ya zauna nan kusa dashi ya tattara duk attension dinshi a kanshi yana son yaji me wazirin zaice?..cikeda farin ciki shima wazirin yace”barka dai Attahiru ya jiki ka?..”yace”na samu sauki”..waziri yace”to Alhamdulillahi haka akeso..Allah ya kara lafia”..Bobby ya amsa da”Ameen”..suka yi shiru na dan lokacin kafin waziri yace”wani albishir ne zanyi maka mai dadi wane tukuici zaka bani?..”dan murmushi Bobby ya saki jin abunda ya fada..to wane albishir ne wnn?..shifa gani yake a halin nan da yake ciki matukar ba cewa za’ayi an bashi auren Lamido ba ba wani albishir da za’ayi ya faranta mashi rai..kawai gani yake ba wani albishir ne da zai sashi farin ciki ba amma dukda haka bai gwale Kakanshi ba yace”duk abunda kakeso Baffah”..waziri yace”to an baka auren Aisha…yanxun nan muka yi Waya da Lamido yake sanar dani yanda akayi”…wani irin diff Bobby yayi kaman baiji abunda yace ba…meyasa waziri zaiyi playing mashi such an expensive joke?..why zaiyi wasa da zuciarshi akan lamari irin wnn..duk sai yaji ranshi ya 6aci yama rasa abunda zaice…jin yanda yayi shiru waziri yace”ko bakaji abunda na fada bane?..”a hankali ya kakalo murmushi tareda fadin”nasan da wasa kake Baffah”..da sauri Waziri yace”na ta6a maka wasa da irin wnn mgnr dama?..”shiru ya sake yi yana tunani lokacin daya wani bright smile yazo kan fuskanshi yana cewa”da..Allah da gaske kake Baffah?..”cikeda assurance Lamido ya sake fadin”da gaske nake wlh..yanxun Lamidon ya kirani muka yi mgn”…lumshe ido Bobby yayi ya bude yana jin wani irin sanyin dadi na cika zuciyarshi kawai sai ya shiga karanta duk abunda yazo bakinshi kmr wanda ya zauce…addu’a kawai yakeyi ba tareda ya bude ido ba kuma ba tareda ya ajiye wayan dake makale kunnenshi ba..banda murmushi ba abunda yake saki sai kuma bakinshi dake motsawa a hankali sbd addu’a da yake…Nur dake zaune yana kallonshi wnn smile da yake saki kadai ya isa ya fahimci dalilin hakan…lokacin daya ya bude idon nashi sbd mgnr waziri da yaji ya mike tsaye yana shafa gashin kanshi still bai dena murmushi ba yace ” yanxu Baffa u mean ni zan aureta knn?..i can’t believe this?..”murmushi waziri ya kara saki before saying”kai zaka aureta insha Allah sbd haka rashin lafia ya kare”..murmushi kawai yake saki yana gyada kai yama kasa bude baki yayi mgn…kawai mamakin yanda al’amari ya canxa yake..is this really happening ko kuma day dreaming yake?..a hankali ya zauna kan sofa dake nan kusa dashi bayan sunyi sallama da waziri ya sake lumshe ido yayi relaxing kan sofa din murya can kasa yace”i can’t believe this?..Allah kasa ba mafarki nake ba”..Nur dake zaune yana kallonshi tasowa yayi daga inda yake ya karaso nan kusa dashi ya zauna yana dubanshi da murmushi shima yace”ba mafarki kake ba Dr Bobby..it’s reality..Lamido dai ta kusa ta zama matarka congratulations to u”..tun kafin ya rufe baki Bobby yayi mishi wani runguma cikin excitement yace”i still can’t believe this Nur..Anya ba mafarki nakeba?..”Nur yace”i told u ba mafarki kake ba da gaske ne..Allah ne ya amsa addu’anka”..dagowa yayi yana kallonshi har yanxu bakinshi kaman go at auduga yace”Allah Alhamdulillah..Alhamdulillah Rabbi am forever grateful”..yana gama fadan haka kuma ya mike tareda zura wayanshi a aljihunshi yace”lets get going I need to talk to Mummy about this”..Nur baice komai ya mike bayan ya day car key dinshi suka fita daga office din…Motan Nur suka shiga don dama da ita suka zo..kai tsaye ya kama hanyan gidansu kmr yanda Bobby yace..ko a hanya Bobby bai dena hamdala ba..kawai gani yake Allah yana matukar sonshi daya canxa mgnr aurenta a lokacin da ya gama giving up..gaskia ne da masu iya mgn suka ce duk wani tsananin yana tareda sauki kmr yanda duk mai hakuri yana tareda nasara…shidai yayi hakuri ya kuma fawwala Allah lamuranshi dai gashi ya kawo mashi canji a lokacin da bai ta6a tsammani ba..Lallai Allah abun godia…har suka isa gidansu bai dena godia wa wnn ni’ima ta ubangiji ba..gani yake an gama mashi komai a dunia saidai kuma yayi fatan gama wa lafia…ko parking Nur bai gama ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin gidan…Nur ya bishi da kallo yana girgiza kai yace”wa yaga ba sabon ba”..karasawa yayi ya gyara parking dinshi snn ya bude motar shima ya fita zuwa ciki…yana shiga yaci Karo da Mummy dake kokarin Shiga parlonta kawai sai ya rungumota ta baya yana cewa”Mummy I can’t believe this..waziri yace wai ni zan aureta yanxu..am super excited Mummy Allah yasa ba mafarki nake ba”..juyawa Mummy tayi ta dagoshi daga jikinta tana kallonshi da murmushi a fuskanta itama tace”ba mafarki bane..duk wani da kaji a gaske yake faruwa ba mafarki ba..dama ba nace maka jikina na bani kai zaka aureta ba?..”da sauri ya shiga gyada kai kafin ya lumshe idanunshi ya sake rungume Mummy yace”Mummy nagode sosai..nagode da addu’arki gareni Allah ya saka da aljannah”…hannunshi Mummy ta kama suka karasa parlorn suka zauna tana dubanshi tace”Ameen..kaima Allah ya maka albarka..waziri yace mun gobe zasuje su samu Lamido tareda uncles dinka akan mgnr auren naku”..sake rungumeta Bobby yayi yama kasa cewa komai…Nur dake tsaye tun daxun yana kallonsu sai yanxu Mummy ta lura dashi tace”Nuru karaso ciki mana”..yana murmushi ya karasa cikin parlorn ya zauna yana gaishe da Mummy…kmr wanda ya tunada wani abu sukaga ya mike da sauri ya kama hanyar flat dinshi duk suka bishi da kallo suna daria..daidai lokacin Aunty Sumy ta shigo wayanta rike a hannunta tace”yanxun muka gama mgn da Aunty Munubiya tace tana nan zuwa gobe inshaAllah”..Mummy tace”to Allah kawota lafia”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button