Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana Shiga parlonshi ya zauna kan three seater tareda dialing number ta yana lumshe ido..har ya gama ringing bata dauka ba ya sake kira still no answer kawai sai ya ajiye wayar tareda mikewa ya shiga bedroom direct ya fada bathroom ya daura alwala ya fito ya shimfida carpet ya tayar da sallah don ya nuna godia wa ubangijinshi for such a blessing da yayi mashi na bashi auren Lamido…har azumi ya kamata yayi don nuna godiyarshi wa Allah…har dare ya tsala bai dena Kiran wayanta ba ita kuma bata dauka ba..ganin ba daga wa zatayi ba yayi sending mata”thank u..thanks for accepting me..I love you”..daga haka ya jiye wayar ya lumshe ido yana tuna duk moments da yayi spending da ita..kaman yayi tsuntsu yakai kanshi Gombe haka yakeji amma ba zaiyi wnn rashin kunyan ba matukar ba cewa akayi yazo ba..afterall saura baifi 4 days suyi resuming school ba so zai na samun daman ganinta duk time din da yaso..he prays Allah ya shirya mashi ita yasa bazata na aikata abubuwanda dole zaisa yayi mata masifa ba.
Gombe..
Tunda Lamido ta samu labarin yanda reshe ya juye da mujiya sai abun yazo mata a bazata sosai..wani irin sanyi taji jikinta yayi zuwa yanxun for sure tasan she does not hate him amma ya zatayi da Prof ne kam?..ba wai aurenta da Bobby ke 6ata mata rai ba..kawai yanda baby zai dauka kaman dama can yaudaranshi take shiyasa ta hanashi zuwa ga parents dinta da wuri..and shi kanshi proprietor nan ba sabawa tayi dashi ba..ita bata San ma ta ina zata fara zama da wnn mutumin as her hubby ba..tasan yana sonta da gaske amma har ga Allah itadai gani take kmr bayan auren zai sake rikidewa ya dawo asalin proprietor data sani a baya..gaba daya ranar yini tayi a daki tana faman kunchi ko abinci bataci ba kuma ba wanda yace mata don me…conference video call ta hada musu itada Billy da besty tana tuttura baki ta fada masu duk abunda ke faruwa ga mamakinta sai taga gaba daya sunyi farin ciki da mgnr don har lissafin biki suka fara kawai ta kashe wayarta tana huci..ita fa har yanxu bata ga ta inda ita da proprietor za’ace suyi aure ba..to ta inama za’a fara?..kawai gani take kmr abun ba mai yiwuwa bane..gashi tun jiya take kiran wayan Prof a kashe har zuwa yanxu kama a kashen yake ta rasa dalilinda yasashi kashe waya..so take ta sanar dashi an samu turn of events ya gwada turowa wai ko Lamido zai sauraresu amma bata samun wayan nashi..duk tabi ta zama wata iri ita ba mai lafia ba kuma ba mara lafia ba..tana gani tun daxun yake kiran wayanta taki dauka don batasan abunda zai fada mata ba kmr yanda itama batasan abunda zata fada mashi ba…kunayanshi ma taji tanaji wlh..tana nan kwance a daki har dare daddy ya turo Yusra ta kirata..ba musu ta mike tareda maida hulan kanta ta nufi parlon nashi..suna zaune tareda Ammi ta karasa ciki a nutse ta zauna a kasa..daddy yace”nasan kin samu labarin abunda ke faruwa wajen Amminki koh?..”ta daga kai alamar ta sani..daddy yacigaba”to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi mana biyayya a wnn auren..a yanda yaron ke sonki nasan kema bazaiyi taking naki long time kafin ki fara sonshi ba..kuma ban yadda ki mashi wani rashin kirki ba Aisha..inaso ki girmamashi kmr yanda kikeyi a baya snn kar in sakeji ance kin hadu da wnn mutumin ko waya ban amince kiyi dashi ba..idan Allah ya kaimu gobe zasuzo a tsaida ranar aurenku..Allah yasa haka shine alkhairi a tare daku Allah kuma ya maku albarka baki daya”..a hankali ta gyada kai idonta a kasa..saida ta tabbata ya gama snn tace”daddy dan Allah ina son zuwa Bauchi gidan aunty fiddausi”..daddy yace”ba wnn sunday zakuyi resuming school ba?..”a hankali tace”eh amma kafin sunday din zan dawo..ko kuma a daukemu daga can tareda Billy kawai mu wuce”..shiru daddy yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can yace mata”shknn saiki shirya gobe da safe a kaiki..Allah maki albarka”..ta amsa da”Ameen daddy”..snn ta mike ta fita daga parlon..Ammi ta bita da kallo bayan fitar nata tace”ikon Allah..wai Aysha ce tayi wnn nustuwa haka sbd mgnr aure ya 6ullo..wonders shall never end”..ta karasa mgn tana daria yayinda daddy ke girgiza kai shima yana murmushi..shi kanshi yaga wnn canjin tattare da ita fatanshi dai Allah yasa auren nasu shine alkhairi a tareda kowannensu.
Washegari da safe ta shirya kmr yanda daddy yace driver dinsu ya dauketa zuwa Bauchi..tana zuwa gidan ta fashewa small mom dinta da kuka wai za’a mata auren dole..Aunty Fiddausi nata aikin rarrashinta tace”ni banga abun tada hankali anan ba Aysha bayan kowa ya shaida irin son da akace yana maki”..tun kafin ta rufe baki tace”Aunty inyamuri ne fa..kuma wlh bashida mutunci masifaffe ne na bugawa a jarida..shknn ni sai a hadani dashi salon yayitama mutum masifa komai fa shi abun fada ne a wurinshi”…daria aunty fiddausi ta kunshe kafin tace”to kiyi hakuri ni da kaina zanyi masa fada ya dena maki masifa gaskia..kuma shi da yake jikan waziri ta ina ya zama inyamuri kuma?..”da sauri tace”babarshi inyamura ce kuma shima yanayin inyamurancin..kawai sai in haifi ‘ya’ya a dinga koya musu igbo..wlh an cuceni”..daria sosai small mom dinta ke mata don ita bataga abun daga hankali a nan ba…idan ta fahimceta ba ma rashin auren wancan saurayin ne damuwarta ba kawai damuwarta an hadata dashi kuma wai masifaffe ne..ta lura iskanci ne kawai yasa take wnn abun amma ba kiyayya ba don bisa ga dukkan alamu itama tana sonshi kilan ganewa ne kawai batayi ba.
Sha biyu da wani abu tayi sallama da aunty fiddausi ta wuce gidansu Billy..ta iske Ummansu a parlor tareda sauran siblings din Billy maza..ta karasa ciki a hankali kaman wata mara lafia ta shiga gaisawa da Umma..Umma dake dubanta with smile tace”ashe kuma proprietor dinku zaki aura?..dazu Bilkisu ke fadamun..to Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin Aysha Allah yasa albarka”…juyawa tayi tana kallon Billy kmr zata fashe da kuka kafin ta sake juyowa ga Umma tace”Umma masifaffe ne fa”..daria Umma da sauran brothers din Billy suka sa jin abunda tace…Umma tace”banda abunki Aysha ai ba’a cika son namiji ya zama mara fada ba sbd raini”..turo baki kawai tayi bata sake mgn ba..wani elder brother din Billy mai suna Mubarak yace”naji ance jikan wazirin Gombe ne koh?..”mikewa tayi still tana turo bakinta tace”kuma babarshi inyamura ce”..daria suka kara saki Billy ta mike da sauri zuwa inda take ta kama hannunta tana kokarin kunshe dariar dake cinta itama tace”ki kyale Yaya best friend tsokanarki yake..yanxu mu shiga ciki ki bani labari in detail”..kwace hannunta ta shiga kokarin yi Billy bata sakeshi ba saida suka shiga dakinta..tana sakin hannun nata ta sake fashewa da daria har tana clapping hands dinta tace”wlh ba karamin dacewa kikayi dashi ba..dama garinku daya”..kallonta Aysha take har ta gama iskancinta snn ta karasa ciki ta zauna gefen gado tana duban Billy da wani murmushin mugunta tace”dadin abun dai kema naki yana nan zuwa..kwanan nan na samu labarin wani yana sonki har turowa ma zaiyi gidanku ayi mgn”..tsaki Billy ta saki tareda zama nan kusada ita tace”matsala na dake karya..uban wa ya baki wnn labarin?..”Aysha tace”ba labari aka bani ba kan idona komai ya faru..da gaske kema very soon zakiji ance an fidda maki miji sai ki zama cikin shiri”..kallonta Billy take kmr mai son gano gaskia..sake matsawa jikinta tayi tana marairaicewa tace”bani labari dan Allah..da gaske kike ko da wasa?..”Aysha tace”da gaske nake wlh..Hammana ne yake sonki”..wani kwalo idanu waje Billy tayi kmr taga abun tsoro tace”Lamido kiji tsoron Allah”..Aysha tace”Allah kinji na ranste maki da gaske nake..a gabana ya fadama Lamido ke yakeso shi kuma Lamido yace zaiyi mgn da grandpa dinku”..dakatawa tayi tareda kamo hannayenta tace”Billy i cant believe this wlh..abun yayi mun dadi wai ace Hamma na zai aureki..dan Allah Billy kema ki soshi kinji and kada kije ki fada masa na sanar dake dan cewa yayi bai yadda in fada maki ba”…murmushi Billy ta saki tareda zame hannunta daga nata tace”banza ‘yar rainin hankali”..ta fashe da wani daria tana cewa”ni dake za’a ga dan rainin hankali a ciki..yarinya tanaso tana kaiwa kasuwa”..da sauri Billy tace”ai kema kina son proprietor kuma kina kaiwa kasuwa”…haka dai sukaita tsokanar junansu Aysha bata bar gidan ba sai dab da magrib tayi sallama dasu ta koma gidan aunt dinta.