Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari Waziri da Uncles din Bobby biyu suka je nema mashi aurenta wajen Lamido…Waziri da kanshi ya bada kudin aure inda Lamido,daddy da uncles dinta suka karba tareda tabbatar musu da cewa an bashi ita halak malak..Lamido yasha godia wajen waziri kaman wani gagarumin abun yayi mashi..an tsayar da mgn kan baza’ayi biki ba sai ta gama makaranta amma zai iya zuwa duk time da yakeso yayi mgn da ita wnn kam an bashi izini batun aure ne dai akace sai ta kammala.
Washegarin ranar suma sukaje Bauchi nemawa Hamma auren Billy a hannun kakanta babu wasting of time suma suka amince suka kuma ce an bashi aurenta lokaci kadai ya rage a shafa fatiha.

Lokacinda labari ya iske Bobby ji yayi kaman yayi tsuntsu ya tafi Gombe sbd farin ciki..bai taba tunanin komai zai faru cikin sauki haka ba..matsala daya da yake fuskanta yanxu shine rashin samunta a waya..ba wai bai samun wayan nata bane aah yana shiga dauka ne kawai batayi wanda baisan dalilin haka ba..duk iya dauriyarshi kasa cigaba yayi sbd yanda take neman ta tarwatsa mashi dan farin cikin daya samu yanxu a dalilin aurenta da yasan an bashi…daukan wayanshi yayi ya kira waziri sukayi mgn dashi yace shidai yanaso yazo Gombe a gobe sbd ya samu ya ganta..Waziri bai hanashi ba yace babu damuwa yazo ya ganta ko don su fara fahimtar junansu.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba… masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
47
Da wuri ya gama shirinshi don ko breakfast bai fitoyi ba saida ya gama..flat din Mummy ya fara shiga ya sameta zaune tana mgn da waziri a waya..karasawa yayi ciki ya zauna kusada ita yana jira ta gama..sun dauki lokaci mai tsayi suna discussing kan mgnr da bai fahimci inda ya dosa ba kafin su gama..Mummy na ajiye wayanta ta jiya tana dubanshi tace”so ka gama shiryawa?..”yace”na gama Mummy..Nur kadai nake jira”…Mummy ta mike tace”to muje kayi breakfast kafin Nur din ya karaso”..mikewa yayi ya matairaice yace”Mummy am not hungry plss..kinsan idan zanyi tafia ba son cin abinci nake ba”..hannunshi ta kama zasu fita daga dakin tace”ko tea ne sai kasha in ba haka ba kuma u will not step out if this house”..bai sake yi mata musu ba yabita har dinning..aunty sumy itama daidai lokacin ta fito don da wuri zata fita aiki…su Miemie ne bai gani ba ya tambaya Mummy ta wani hade rai tace sun tafi gidan kakarsu..baice komai ba sbd yanda yaga ta hade rai..batasan ko bata hade rai ba ba mgn zaiyi ba sbd shima yanxu na gabanshi ya isheshi..Allah Allah yake ya ganshi a gaban yarinyar nan yaji dalilinta na ignoring calls dinshi..koma me zatayi dai daga baya ne tunda an rigada an bashi aurenta so duk ihu bayan hari takeyi ya sani..tea Mummy ta hada mashi ya dauka ya shiga sha cikin ranshi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita…kafin ya gama sha Nur ya iso gidan dan haka ya mike da sauri bayan ya ajiye mug dake hannunshi yana duban Mummy yace”zamu wuce Mummy..tafiyan akwai nisa”..murmushi kawai Mummy tace”Allah ya kiyaye hanya..ina gaida ‘yar tawa”..murmushi yayi tareda fadin”zataji”..snn ya koma zuwa flat dinshi don daukan keys..Nur kuma ya karasa yana gaisawa dasu Mummy..aunty sumy dake cin abincinta tace”wnn abokin naka zalamamme ne wlh..haka ake zuwa zance tun sassafe sbd rashin hakuri”..daria Nur yasa kafin yace”ai aunty kinsan qanin naki halinshi sai shi..ita kanta Lamidon fa wai haushinta yakeji bata daukan mishi waya..so nake muje dai inga iya inda fushin nashi zai kare”..daria itama aunty sumy tayi tana cewa”ai matar Bobby ta shiga uku da masifa..koda yake ita wnn yana sonta bazai iya mata masifan ba kila”..Nur yace”ina ya isa ya mata?..daidai dashi ya samu ai”..daria suka kara saki Mummy dai na jinsu tana murmushi..ita kanta wani lokaci takanyi tunanin yanda Bobby zai kare da matarshi da wnn temper din nashi..saurin hawa gareshi kmr farashi gashi kuma da wuyar sakkowa..amma ta bakin na Nur ta lura yarinyar daidai dashi ce snn kuma uwa uba soyayyan da yake mata wanda bazai barshi yanayi mata anyhow ba..sbd wnn fadan nashi yasa a kullum addu’arta Allah ya bashi macen da yake mutuwar so ba wadda ke mutuwar sonshi ba don idan ya auri macen da baiso matsala za’a samu gagaruma..Allah almusawwir kuma sai ya amsa addu’anta ya bashi wadda sonshi yafi nata..fitowa yayi daga dakinshi yanata baza kamshi..Nur ya kalleshi yana wani kashe ido yace”bakaga kyan da kayi ba wlh..manyan kaya na suiting dinka and da wnn wankan nasan dole Lamido ta ajiye ego dinta ta bada kai don zata fahimci kai din fa ba kmr kowa bane”..harara Bobby ya watsa mashi baice komai ba..yana karasowa yayima Mummy da aunty sumy sallama snn ya juya ya fita Nur yabi bayanshi yana kunshe daria…driver na ganin su ya karaso suka gaisa Bobby ya bashi key din motar da zasu fita yana sake trying number dinta bata dauka ba..driver ya kawo motar inda suke snn suka bude suka shiga shi kuma ya tayar da ita suka fita already dama ya sanar dashi cewa Gombe zai kaisu…ko a hanya saida ya sake trying number still no answer sbd tsabar haushi baisan sanda ya wurga wayan nan gefenshi yana fadin”to hell with you”..juyawa Nur yayi yana kallonshi then back to wayarshi dake yashe a tsakiyarsu…hannu yakai zai dauki wayan Bobby yayi saurin daukan kayarshi shima yace mishi”fuck you”..Nur ya kwashe da daria hadda kyakyatawa…Bobby ya kulu iya kuluwa amma baice komai ba..gaban driver dinshi zai dinga mashi irin wnn iskancin?..zaiyi maganin Nur wlh…bai sake ce mishi komai ba har shima ya gaji da daria don kanshi ya bari daga karshe ma baccinshi yayi hankali kwance..a kufule Bobby ke kallon yanda ya wani yi bacci a mota kmr karamin yaro..shiko tunanin dake ranshi ma bazai iya barinshi baccin ba..gani yake kaman ba tafia suke ba don Gomben yaga tayi nisa sosai baisan ko don sbd matsuwar da yayi ya hadu da ita bane…haka yayita sake sake har suka shigo Gombe around 11:45..saida ya fara zuwa suka gaisa da waziri snn suka wuce estate dinsu…suna zuwa bakin gate gabanshi ya fara faduwa da baisan dalilinshi ba…gidan Lamido suka sauka kmr yanda waziri yace daga nan kuma Lamido yasa aka rakasu har kofar gidansu..tun jiya da waziri ya sanar dashi zaizo dama yasa da sassafe akaje aka daukota daga Bauchi don daddy baya gari ya koma wurin aiki…a bakin gate sukayi parking Bobby sai kallon gidan yake cikin ranshi yace”so this is their house?..”ya karasa da wani murmushi kan face dinshi…yaron da ya rakosu ne ya shiga ciki yace ma Ammi sun iso ita kuma ta tura Husna tace ta shiga dasu parlon daddy..babu wasting of time kuwa Husna ta fito tana hangosu ta karasa kusa dasu ta washe musu baki tace”sannunku da zuwa”..Nur ne ya fara cewa”yauwa sannu yanmata..ke qanwar Lamido ce koh?..”gyada mishi kai tayi still smiling tace”nike binta ai..sunana Husna Lamido”..Nur dake gyada kai yace”MashaAllah Husna Lamido”..juyawa tayi tana kallon Bobby daya rungume hands dinshi yana kallonsu..suna hada ido ya sakar mata smile tareda cewa”Sannu Husna Lamido”..murmushinta ta kara fadadawa kafin tace”Ammi tace ku shigo ciki”..daga haka tayi gaba sukabi bayanta har cikin gidan..parlon daddy ta shiga dasu as instructed by Ammi snn ta gaidasu ta fita…Nur ya shiga kallon parlon yana yaba kyau da yayi mashi…shiko Bobby idonshi bai sauka ko inaba sai kan wani picture dinsu gaba daya lokacin suna kanana..ita da Ammi ne a pic din daddy ya dauki Husna Ammi kuma ta dauki Yusra aysha kuma tana tsakiyarsu…tayi murmushi a picture din har dimples dinta sun fito..murmushi da bai shiryaba ya saki yanajin wani weird feeling tattare dashi..sake maida dubanshi yayi ga dayan picture din shima gaba dayansu ne amma wnn sun girma gaba daya snn akwai Hamma Najeeb a jiki..dan hade rai yayi ganin yanda take zaune kusa dashi gaba daya suna daria kawai sai yaji baiji dadin zama kusa dashi da tayi ba..da sauri ya dauke idonshi daga hoton don gudun kada ya karasa spoiling mood dinshi da dama ba daidai yake ba…wani fitinannen kamshi ne ya bugi hancinshi kafin ta shigo parlon a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki…kallonta kawai Bobby yake yanajin zafin a yanayin da ta fito..is she mad zata sanya turare haka ta fito kuma ba tareda hijab ba?..juyawa ga Nur yaga sai wani kallonta yake yana murmushi nan take yaji 6acin ranshi ya karu akan wanda yake ciki..shi baima san kaddarar data kaishi daukan Nur ya taho dashi ba gashi nan sai kalle mashi ita yake a banza kmr yaga matarshi…karasowa ciki tayi ta zauna hankalinta gaba daya kan Nur fuskanta ba yabo ba fallasa tace”sir good afternoon”..Nur da har yanxu ke murmushi yace”good afternoon amarya Lamido ya hutu?..”dan murmushi kawai tayi tareda cewa”Alhamdulillah”…Bobby daya cika yayi fam ya shiga dubanta da angry eyes dinshi yace”bakida hijabi ne?..”daure fuska tayi ba tareda ta kalleshi ba tace”bani dashi”..yace”then tashi muje a siyo”..banza tayi dashi tana sake dinke fuska..shi wnn irin masifaffe ne wai?..a nan dinma sai ya mata bala’i bazai bari su rabu lafia ba?..mikewa yayi hands dinshi a aljihun wandonshi yace”ki tashi muje a siyo nace”..ko motsawa batayi ba Nur dai da yaga abun na Bobby azimun ne sai ya mike ba tareda ya kalli inda yake ba yace”i will wait for u in the car”..daga haka ya fita daga parlon shi kuma ya shiga takawa a nuste zuwa inda take yayi kata wani tsaye yana kallonta kmr soldier…dan dagowa tayi a hankali ta kalleshi taga kallonta shima yake kmr an aikoshi nan da nan ta sauke nata idon tana kunkuni…zama yayi nan kusa da ita still yana dubanta yace”and wa ya fada maki ana sa turare haka a shiga cikin mutane?..”kallonshi ta juyo tanayi kmr zata sanya kuka..ya lumshe ido tareda jingina da jikin kujerar yana maimaita innalillahi a cikin zuciyarshi..kada kuma ta fara tunanin yana overacting amma Allah ya san ba karamin kishi yake dashi a kanta ba..ganinta a haka shi kanshi saida yaji wani abu balle kuma Nur da bai hada komai da ita ba..shi bayason ana ganin beauty dinta ne and fesa turare ko Allah ya haramtawa mata su fesa su fita sbd kamshi ba karamin fitina yake haddasawa ba..a hankali ya bude idon nashi tareda gyara zama yana dubanta yace”why are you ignoring my calls?..”tace”ba komai”..girgiza kai ya shigayi yana dubanta cikin ido yace”karya kikeyi”..ta wani zaro ido tana kallonshi saura kiris daria ya subuce mata tace”sir karya kuma?..”kai ya sake gyadawa alamar haka yake nufi…ta dan turo baki tace”nidai ba karya nake ba”..kallonta ya tsaya yi kawai kmr baiji abunda ta fada ba…riga da skirt ne a jikinta na lace da yayi matukar amsarta..ta daura dankwalinta as usual saidai wnn karon bata fito da gashi ba don tasan sai yayi mgn sai kuma veil dinta data yafa a kafada…gani yake duk dunia babu macen da zata kaita kyau a idanunshi..ita komai ta sa kyau yake mata shiyasa a kullum kishinshi karuwa yakeyi a kanta…lumshe ido yayi tareda sauke ajiyar zucia cikin voice dinshi da yaji ya dashe all of a sudden yace mata”i love u so much Aysher..plss i beg of u ki bar kin answering calls dina..am about going crazy.i..i am…”kasa karasawa yayi kawai yayi shiru yana sauraran heart beat dinshi…kallonta yacigaba dayi voice dinshi na rawa sosai yace”have mercy on me plss..i promise to love u till my very last breathe..I promise to be a good husband..i will never rufuse u anything in the world just wanted u to love me nor matter how little i wont complain..kawai ki soni ki zauna dani for i dont think i can live without u..i love you dearly”..lumshe idanu Aysha tayi tana sauraran words din nan nashi..bata san why ba amma words din really galddens her heart..sunyi mata dadi sosai ba kadan ba..kawai mamaki take yanda the whole Dr Bobby ke pouring mata love words haka..bata san ita ko tana sonshi ba amma this very moment taji ya burgeta matuka..da dadewa dama tasan son da yake mata ba gama garin so da ake iya samu a ko ina bane sai wanda Allah ya zaba yake bama masoyi mai matukar sonka kamarshi..kawai gani take Allah knows best shiyasa ya hada aurenta da nashi..idan kuwa haka ne ita bazata ja da ikon Allah ba saidai tayi fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya…ganin yana mata wnn kallon nashi mai sawa taji wani iri ta mike da sauri har veil dinta yana faduwa ta dauka da sauri ta fita daga parlon ta bar Bobby da lumshe ido yana saqan kamshin da ta tafi ta bar mashi…yana nan zaune after few minutes ta dawo dauke da tray a hannunta ya mike da sauri ya amsa tray din ya ajiye kan table ita kuma ta sake fita ta dawo da wani..a takaice saida ta cika musu gaba da kayan ci dana sha snn ta kama haya zata fita yayi saurin cewa”where are u going to?..”tace”zan kira provost ne yazo kuci abinci”..girgiza mata kai ya shiga yi yana zaro wayanshi yace”don’t worry i will call him..amma haka kike fita Aysher duk mazan dake gidan nan suna kallonki?..”juyawa tayi ta koma ciki ba tareda tace komai ha don bata ma san abunda ya kamata ta fada ba..shi kuma yayi dialing number din Nur yana dagawa yace ya shigo suci abinci..ba musu Nur ta dawo parlon ita kuma ta mike tana fadin”bari inyi excusing naku idan kun gama sai in dawo”..kai kawai Bobby ya iya daga mata yabi bayanta da kallo har ta fita snn ya sauke ajiyar zuciya ya fara cin abincin…sai yanxu ya samu kwanciyar hankalin cin abinci amma daxu ji yake gaba daya tension din dunia kanshi ya kare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button