Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan sun gama cin abincin ta dawo tareda Yusra data dage sai taje ta gaishesu…kanta a kasa har ta karaso ciki ta zauna..Bobby daketa kallon Yusra ganin kamar Ilham dinshi yace mata”hey cutie”..washe baki tayi tana gaisheshi yace”ya sunanki?..”tace”Yusra Lamido..kaine wanda zaka auri Addah?..”dan wara ido yayi yana kallonta da murmushi yace”yeah nine..waya fada maki ni zata aura?..”da sauri Yusra tace”Adda Husna ce tace wai kai proprietor dinsu ne kuma wai kai inya…”Aysha bata bari ta karasa ba ta toshe mata baki…Bobby sai yayi relaxing yana kallonsu..dukda bata bari ta karasa ba yasan inyamuri zata ce..girgiza kai kawai yayi yana murmushi..Aysha ta mike rikeda hannun Yusra suka fita daga parlon tace”ni zaki tonawa asiri Yusra?..”a hankali tace”kiyi hakuri Adda mantawa fa nayi”..Aysha tace”oya wuce ki koma wajen Ammi kar na sake ganin kafarki a nan”..ba musu ta wuce ta bar wurin ita kuma ta sauke ajiyar zucia tareda komawa ciki…bata samu Nur a parlon ba sai shi kadai…tana karasawa ta zauna yace mata”daddy baya gari ne?..”tace”eh yana Abuja”…gyada kai yayi kafin ya sake cewa”inyamuri kike cemin koh?..”wani irin zare idanu tayi hadda su dafa kirji tace”Nii????”..murmushi ya kara saki yana gyada kanshi yace”yes ba gashi zata fada kin hanata ba”..turo baki tayi tana kawar da idonta daga wnn kallon nashi tace”nidai ba haka nake cewa ba ba ruwana”…daria mgnr nata ya bashi aiko ya shiga yinta kmr me..saida ya gama don kanshi snn yace”ko haka kika fada ma ba wani abu ke bakaya laifi ai..and niba igbo bane..ni bafulatani ne just like you”..shiru tayi tana wasa da fingers dinta..shi kuma kallonta yakeyi yanajin tamkar ya janyota jikinshi yace”ko har yanxu baki yadda nima dan Gombe bane?..”sake turo baki tayi cikin gajiya da tambayoyin nan nashi tace”na yadda”..shiru ya sakeyi for some minutes kafin kuma yace”so yanxu dai ni zan aureki?..”sake sunne kai tayi tanajin wani irin faduwar gaba..shi kuma har yanxun ya kasa dena murmushi yacigaba da fadin”i just can’t wait for ranar da za’a daura mana aure..am eager in ganki cikin gidana as my wife”..wnn karon rufe fuskanta tayi da hands dinta don wani irin kunya taji ya rufeta..shiko murmushi kawai yake saki non stop murya can kasa ya kira sunanta”Aysher”..dagowa tayi a hankali tana kallonshi..shima kallon nata yakeyi kafin yace”i love you..to the moon and back..kuma nagode sosai for agreeing to marry me insha Allah bazakiyi regretting decision din nan ba”..kasa ta sakeyi da idonta tanajin wani baqon al’amari na zaga jikinta…banda yake ba abunda take yau duk uban surutunta nemanshi tayi ta rasa kuma ta rasa dalili..duk wnn rashin kunya data gama planning zata mishi saita kasa sbd kwarjini na musamman da taga ya mata uwa uba kuma wnn words da yake sake kashe mata jiki dasu…duk sai taga ya sauya kaman ba proprietor data sani mai dan karen masifa ba…shiko murmushi yaki yankewa a face dinshi sam sai wani jin dadi yake kmr anyi mashi bushara da aljannah…sake kasa da murya yayi kafin yayi mgn wayanshi dake ajiye kusa dashi ya fara ringing..dubawa yayi yaga wanda ke neman katse mashi wnn jin dadin sai yaga Mummy dan haka yayi picking da sauri yana cigaba da murmushi da igbo yace”Hello Mummy”..da igbo din itama ta amsa mashi da”tun daxu nake kiran wayoyinku bai shiga..ka bani ita mu gaisa idan kuna tare”..mika mata wayan yayi yana binta da wani kallo mai wuyar fassarawa yace”Mummy”..ba musu ta amsa wayan tareda kaiwa kunne..a daya banagaren Mummy tace”daughter”Aysha ta sake sinne kai tana murmushi tace”Mama ina yini”..Mummy tace”lafia lau ya hutu”..tace”Alhamdulillah”..Mummy tace”maasha Allah dama so nake in maki godia for accepting him..Allah maku albarka yasa haka ne alkhairi a tareda ku”..kasa tayi da kanta ta kasa amsawa..ita duk bata san yaushe kunya ya shigeta har haka ba wlh..bata taba zaton zataji wani abu wai shi kunya ba a rayuwarta amma yau gashi tanaji kuma batasan dalili ba…godia sosai Mummy ta sake kwararo mata snn tace ta gaida Mamanta..ta amsa mata da zataji snn ta mika mashi wayar…yana karba ya sake maidawa kunne yana sauraran abunda take fada yanata murmushi…baice komai ba har saida ta gama snn ya ajiye wayar…agogon hannunshi ya duba yaga time na wucewa gashi yau zasu koma Kano dan haka ya wani langabar da kai yana kallonta in a pleading tone yace”tafia zamuyi Aysher..amma dan Allah i beg of u ki bar fesa turare haka da yawa idan zaki fita kuma ki taimakamun ki dinga sa hijabi please”…dagowa tayi ta kalleshi ya sake narke mata idonshi aikuwa ta dauke nata da sauri jin wani abu ya fito daga cikin idon nashi ya shiga nata..itadai ta shiga uku da idanun nan nashi da ba dama ta kallesu ko ya kalleta dasu sai ya sata jin wani iri..ganin har yanxu batace komai ba ya sake kasa da murya yace”kinji?..”kai kawai ta iya daga mashi ba tareda ta kalleshi ba..shiko bai dauke idanunshi a kanta ba ya sake cewa”And dan Allah ki taimaka ki dinga daukan wayana..hankalina tashi yake idan ina kira baki dauka ba kinji?..”nan ma kai ta sake gyada mashi without saying a word..gaba daya yawun bakinta ma taji ya kafe mata all of a sudden..kallonta yake yana so ya samu eye contact da ita amma taki dagowa..yace”to kiyi mgn da Ammi zamu gaisheta kafin mu wuce”…ba musu ta mike ta fita daga parlon shi kuma ya bita da kallo yanajin sonta na sake zagaya duk wani system na jikinshi…after like 5 mins ta dawo tace Ammi tace su shiga dan haka ya kira Nur a waya ya dawo snn suka shiga main parlor gaba dayansu…Ammi na zaune kan one of kujerun parlon sanyeda hijab sai Yusra a gefenta…suka karasa ciki duk suka zauna a kasa Ammi nata cewa su koma kan kujera amma basuyi hakan ba suka fara gaisheta a haka…ta amsa da fara’a tareda tambayan iyayensu duk sukace suna lafia..nasiha sosai tayi musu kafin su mata sallama su fita Bobby na sakejin matar ta kwanta mashi a rai sbd kamalarta..wato ba daddy kadai ne dattijo a gidan ba ita kanta Ammi dattijuwa ce..sunada halin girma sosai ba kadan ba..ya kuma san yayi dace da Allah yasa zai auri diyarsu don mutanen kirki ne..shi sai yau ya samu ganin tsananin kamar da Aysha takeyi da Amminta..irin kama sosai wanda ko mgnrsu ma kusan iri daya ne likewise dimples dinsu…halayyan su ne kawai ya bambamta don yasan da kyar idan wnn fitinan na Aysha a wurin Ammi ta dauko..ita batayi kala da fitinannu ba sam amma ita indo a kallon farko da mutum yayi mata yana iya gane tsantsar rashin jin dake tattare daita dukda ma dai yanxu ta girma ta rage kiriniya…ita kadai ta rakosu har compound don Husna ta wuce islamiyya…suna gama sallama da Nur ya bude mota ya shiga yayinda shi kuma Bobby ya karasa inda take tsaye ya zaro kudi a aljihunshi ya mika mata yana cewa”sorry ban kawo maki komai ba..hankalina ne duk ba daidai ba lokacinda zamu taho amma ga wnn kisai duk abunda kikeso”..girgiza mishi kai tayi alaman bazata karba ba..ya wani langabar da kai yana kallonta yace”dan Allah accept it..bazanji dadi ba in kikamun haka”..shiru kawai tana kallonshi..ya kamo hannunta yasa kudin a ciki snn ya sake kasa da murya still bai bar kallonta ba yace”shknn zamu wuce..ai ranan sunday zakuyi resuming school koh?..”kai a kasa ta amsa da”eh..zamu tafi clinical posting”..gyada kanshi yayi yana murmushi don tuna zai samu damar ganinta son ranshi a asibiti yace”i can’t wait for sunday..i love u sosai”..kasa ta sakeyi da kanta batace komai ba..yace”Aysher look at me mana”..dan dagowa tayi ta kalleshi suna hada ido ta juya zuwa cikin gida da sauri har tana tuntu6e shi kuma ya shiga shafa kanshi yana sakin murmushi ba kakkautawa…shi kanshi baisan ya iya murmushi ba har haka..gaba daya 6acin ran daya kwaso tun daga kano yana zuwa gareta sai ya nemesu ya rasa sai farin ciki daya baibayeshi kuma..”oh Allah nagode maka..Allah Alhamdulillah bazan gaji da godia kan wnn kyauta da kayimun ba..i will be forever grateful”..abunda yake fada knn yayinda ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga snn driver ya tada ita suka fara tafia…ko a cikin motar relaxing yayi kan kujera yana shafa kai yana murmushi kamar sabon kamu..Nur dai na zaune gefe yana kallon ikon Allah..a fili yace”muma dai mun kusa isowa wurin nan…lokaci karami muke jira muma mu shigo sahun manya”…Bobby dai kala baice dashi ba yacigaba da murmushinshi..idan yace zai biyewa Nur yasan tsaf zai iya harxukashi suzo suna rigima gaban driver shiyasa bazai kulashi ba ko don ma farin cikin da yake ciki a yanxu haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button