Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Wnn dai page din gobe ne na dawo muku dashi yau so koda kun jini shiru gobe ga abunku nan na baku.????
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
48
Ranar sunday around 11 suka baro Gombe zuwa Kano sbd posting da zasu fara..saida suka fara tsayawa Bauchi sukayi picking Billy da duk ta kasa sakin jikinta da Hamma sbd mgnr so daya 6ullo tsakaninsu..yana ankare da ita shiyasa tun farko baiso tasan yana sonta ba sai sun kammala school amma mgnr da Lamido yayi shi ya hargitsa komai..tana zaune back seat sai sunkuyar da kanta take kmr munafuka..ita kuma Aysha banda daria ba abunda take mata..shidai yana jinsu baice komai ba sai kallonta da yakeyi ta mirror time to time…karfe biyu da wani abu suka shigo Kanon Dabo kai tsaye kuma suka wuce FCNM kmr ko yaushe dai…sai yanxu hankalin Aysha ya dawo jikinta ta shiga tunanin rayuwar da zatayi da proprietor yanxu kuma..a dan wnn lokacin ta fahimci ba karamin mara kunya bane shi..yanda yake nuna yana sonta gaban uban kowa abun har tsoro yake bata kada yaje yayita nunawa har kowa ya fahimci abunda ke tsakaninta dashi…a 6angarenta dai har yanxu tasan ba sonshi take ba kawai dai taji zata iya aurenshi ne sbd son da yake mata da kuma kasancewarshi za6in iyayenta…ga mamakinta suna shiga premises na makarantan sukaci karo da motarshi parke wajen parking space alaman yana cikin makarantan knn..tuj daxu yazo yana so ya ganta shiyasa ko office dinshi bai shiga ba yayi zaune nan cikin mota tunda yanafa tint so ba wanda zai ganshi…kmr ance ya dago suna shigowa kuwa ya juya yana kallonsu..ranshi yaji ya 6aci da ganin wanda ya dawo dasu..to meye hadinta da wnn kuma yanxu?..har abada bazai manta shine wanda akaso bashi aurenta ba kawai Allah ya rubuta bashine mijinta ba amma da yanxu wani mgn akeyi ba wnn ba…yana kallon lokacin da ya fito ya rakasu zuwa inda zasu duba posting..da kanshi ya duba masu gaba daya ya kuma ce Freedom aka sake posting nasu again wnn karon Aysha ko kadan batayi mamaki ba don dama tasan abunda zai faru knn kuma da bakinshi ya fada mata bazai bari tayi nesa dashi ba wai kada taje inda doctors da sauran health workers zasuyi caa akanta da sunan suna sonta..ita bata ta6a ganin mutum mai kishi ba irinshi..kishinshi har tsoro yake bata wataran don akan kowa da komai ma kishi yake shi kam..bayan sun gama duba posting din suka koma jikin motarshi nan kuma Aysha ta shiga tsokanar Billy wai kunyanshi takeji sai faman kyalkyala mata daria take ganin yanda duk ta wani nustu kmr ba Billynta mai masifa ba..Hamma dai sauraronta yake yana kuma tare mata don yasan iskancin Aysha ba dan karami bane tsaf zata saka mishi ita a gaba da tsokana har saita tunzurata…tsabar takaici Bobby kiran driver dinshi yayi yace yazo su wuce don idan yacigaba da zama nan kilan yana iya jin abunda yafi wanda yakeji yanxu..yasan dole bai isa ya rabata dashi ba tunda cousin dinta ne cousin dinma kuma wanda suka tashi a gida daya dan haka dole yayi hakuri dashi tunda yasan dai bai isa ya rabata dashi ba..shiyasa dai maza da yawa suke tsoron cousins sbd ba karamin ruining relationships sukeyi ba..lokaci guda sai besty ya fado ranshi har ya tambayi kanshi ko suna tare dashi har yanxu ko kuma sun dena friendship din oho..ya tuna ma tare dashi ya gansu a Gombe ranar birthday dinta kuma hakan na nufin yana nan matsayin bestynta ba abunda ya sauya…driver na shiga tayar da motar suka fita bayan an bude musu gate…da kallo Lamido tabi motar kmr idanunta zasu fado kasa..knn dama tun daxu yana cikin motar tunda dai ita bataga lokacinda ya shiga sai kawai gani tayi anja motar an tafi…ta6e baki tayi data tuna bama abunda ya shafeta bane…saida Hamma ya shiga dasu har hostel snn ya juya zai koma Gombe su kuma suka shiga daukan kayansu zuwa cikin apartment dinsu.
Karfe takwas da wani abu ya iso hostel dinsu cikin motan aunty sumy don yasan idan yazo da motarshi masu gadi suna iya ganewa shi kuma baiso su ganshi sbd dare yayi shiyasa yayi disguising kanshi da motarta..so yayi ma ya hakura da ganin nata sai gobe sai kuma yaji bazai iya ba at leat ko ganinta ya samu yayi ya danyi mgn da ita yasan zai samu bacci mai kyau shiyasa baiyi ka sa a guiwa ba..yana gama parking yayi dialing number dinta..lokacin suna zaune sun hadu a room 1a gaba dayansu sai labari suke suna daria kowa tana bada labarin hutunda tayi a gida…Lamido na zaune daga gefe tana sauraronsu tana sakin smile ita nata holidays din dai la ba’asa zatace don kwata kwata ba wani enjoying dinshi tayi sosai ba..suna tsaka da wnn hira wayanta ya fara ringing ta dauka da sauri tana zare ido ganin Proprietor akan screen..mikewa tayi ta fita daga dakin sbd hayaniyarsu bazai bari taji ba..kiran na katsewa wani ya sake shigowa dan tayi picking tareda cewa”sir ina yini”..bai amsa gaisuwar ba sai yace mata”ki fito in ganki ina bakin gate dinku plss”..dan tura baki tayi kmr yana ganinta tace”sir dare fa yayi”..a hankali yace”i know..bazan iya bacci bane tunda nasama taina saina ganki nasan matsala zan samu idan ba ganin naki nayi ba..ki daure kizo kinji”…bata sake mgn ba ta kashe wayarta tareda dora babban hijab akan three quarter da rigan dake jikinta..wayanta na rike hannunta ta fita daga hostel din..idanunshi na kanta yana kallo kmr bai taba ganinta ba har ta karaso inda yake..da sauri ya bude mata kofa ta shiga snn ta rufe kofar..kanta a kasa tana wasa da fingers dinta tace”ina yini”..maimakon ya amsa sai ji tayi yace”i missed u”..sake sinne kanta kasa tayi tanajin wani irin yanayi tattare da ita..shi kuma kallonta yakeyi kmr an aikoshi..wani abu yakeji mai kamada magnet ko kuma ince maganadisu yana kokarin janshi gareta amma bai bari yayi tasiri ba ya dan janye jikinshi kadan ya sauke wani ajiyar zuciya mai karfi tareda relaxing jikin kujera yana cigaba da kallonta..shi baiqi su kwana a haka yana kallonta ba wlh..he can’t get enough of her..komai nata abun kallo ne a wurinshi shiyasa wani lokaci shi kanshi yakan ba kanshi mamaki…ganin yanda suke zaman kurame yayi breaking silence ta hanyar kiran sunanta”Aysher”..amsawa tayi da”na’am”..ba tareda ta yadda ta dago idonta ba..shikuma yana cigaba da kallonta murya kasa kasa yace”i missed u so much..can i hug u plss”..da sauri ta shiga girgiza kai tace”Noo”..hannunshi ya daga alaman surrender yace mata”shknn i wont touch u tunda bakiso..amma da gaske am missing u sosai..ko bacci bana iyayi”..lumshe idanunta tayi tanajin wnn baqon yanayin daya tsiri bijiro mata a duk sanda take tare dashi..gabanta har wani faduwa yake na rashin dalili…sake matsowa yayi yana kallon cute face dinta da kyau har breathe dinshi na sauka direct akan fuskan nata sbd kusancinsu yayi mata wispering”i love u”..sake runtse idanun tayi tanajin faduwar gabanta na sake tsananta..wai wane irin mutum ne shi kam?..yana gama fadin haka ya sake komawa ya kafe jikin seat din da yake har yanxun yana kallonta yace”bari in barki ki tafi saida safe..dama kawai nace izo in ganki sbd in samu bacci sosai”..kai kawai ta iya gyada mashi ta kasa cewa komai..dan marairaicewa yayi yana dubanta yace”Aysher this is not fair mana..kin kulle idanunki kin hanani ganinsu snn mgn ma bazan samu ayimun ba?..”da kyar ta iya bude bakinta tace”saida..safe”..kallon bakinta kawai ya tsaya yi and he couldn’t help it but closed his eyes sbd yanda yakejin kmr ya kama dan bakin yayita sha..hannunshi ya mika baya ya dauko wani shopping bag mai kyau ya mika mata ganin idanunta a kulle ne yace mata”take mana”..sai yanxu ta bude idanun tana kallon bag da yake miko mata..sbd tsabar bazata iya masa musu ba don ko bude baki bata sonyi ta amsa bag din kawai batareda tace komai ba..bayan ta amsa yace”Mummy tace in kawo maki”..gyada kai ta shigayi kafin a hankali ta sake cewa”nagode”..yayi murmushi tareda daga mata kai kawai duk mood dinshi ya sauya wanda har yayi affecting idanunshi…cire mata lock yayi ta bude motar ta fita snn ta sake sukuyowa ba tareda ta yadda sun hada ido dashi ba tace”thank u..saida safe”..yana kallonta kasa kasa shima yace”saida safe..love u”..bata sake gigin cewa wani abu ba ta bar wurin da sauri rikeda bag din daya bata..shiko lumshe ido yua sakeyi kafin ya bude ya tayar da motar snn yayi reverse ya fita daga hostel din.