Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau Friday da safe ta shigo asibitin ita kadai kasancewar Billy evening duty gareta..bata je office dinshi ba kai tsaye ta wuce maternity sbd ta danyi latti..tana shiga ta cire hijab dake jikinta ta bar iya na uniform dinta snn ta shiga cikin labour room bayan ta gaisa da sauran staff dake dakin..Nurses station ta shiga ta ajiye bag dinta snn ta shiga ciki..mutum biyu ta samu kwance a dakin..daya daga cikinsu nata fama don har anyi rupturing membrane..karasawa tayi tana dubata sai taga head ya fara tahowa dan haka tayi saurin daukan hand glove ta saka snn ta shiga assisting matar..cikin ikon Allah ta haifi yaronta lafi..bayan tayi musu duk wani necessary abu tace ma matar ta fadi sunanta wanda suka kawota aje a karbo kayan baby a wurinsu..ba musu matar ta fadi sunan mijinta ita kuma ta fita don sawa a karbo kayan sai bataga ko daya daga cikin messengers dinsu ba dole ta fita da kanta ta amsa kayan ta dawo..tana cikin shirya babyn ya shiga cikin labour room din sbd kiranshi da akayi ya duba daya matar dake cikin dakin..abunda ya bata mamaki shine yanda yayi kamar bai ganta ba ya wuce inda matar take fuskan nan nashi a daure kmr an aiko mashi da saqon mutuwa..dakatawa tayi da abunda take ta juya tana kallonshi still taga ko inda take baya kallo ya fara aikin gabanshi..ranta taji ya 6aci sosai..to uban me tayi kuma da zai wani dinga shareta dan rainin hankali kawai.

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
49
Kallonshi ta tsaya yi da mamaki bayan ta gama shirya yaron ya dorashi jikin mamanshi da aka wuce da ita post natal..yanxu laifin me tayi kuma?..ko dan sbd bataje office dinshi bane yau?..karasawa tayi inda yake bayan sauran Midwives din sun fita..murya can kasa tace mishi”ina kwana”..wani kallo daya sakar mata saura kiris ta fadi kasa sbd tsabar rudata da yayi..ta tabbata wnn fushin ba iya na rashin zuwa office dinshi bane dole da akwai wani abu to amma menene?..duk jikinta yayi sanyi taji bataji dadin wnn cold treatment dinba tunda ba haka ya saba mata ba..tafiso yacigaba da kulawa da ita yana nuna mata so kmr dai yanda yakeyi a baya..ganin har yanxu bai kalli inda take ba aikin gabanshi kawai yake sai ta juya ta fita daga labour room jiki a sanyaye..lumshe ido yayi bayan fitan nata yana sauke numfashi..jiya ko baccin kirki kasawa yayi sbd labarin da aka bashi wai tsohon saurayinta yaje har hostel wurinta kuma ta fito ta sameshi sbd batada hankali..abun yayi mashi ciwo sosai ta yanda har zata iya zuwa ta kula wani bayan alqawarin aure dake tsakaninsu..snn kuma da zai shigo nan ya hangeta tareda wani suna mgn kuma ko hijab babu a jikinta haka ta gama nuna mishi jikinta ta juya ta tafi yana ganin yanda mutumin yabita da kallo..a yanda yasan halinta da shegen rashin jin mgn tabbas idan ba zafi zafi yayi mata ba bazata shiga hankalinka ba shiyasa dole ya dake ya nuna mata abunda tayi ba daidai bane sbd ta kiyaye gaba amma shi kanshi bajin dadin fushin da yakeyi da ita yake ba..kawai dauriya yake amma Allah kadai yasan halinda yake ciki…a takaice har ya gama aikinshi ya bar ward din baibi ta kanta ba hakan kuma ya sake daga mata hankali fiyeda tunani..lokacin tashi nayi ya tura mata text saying tazo office dinshi idan ta tashi ya maidata hostel..ba bata lokaci ta nifi office din nashi bayan tasa katoton hijab dinta..tana shiga ko zama batayi ba ya dauki wayoyinshi dake kan desk dinshi ya bude kofa yana kallonta fuska daure yace”muje”..kai a kasa ta ra6a ta fita daga office din shima ya fita suka wuce parking space..amsan key yayi hannun drivernshi snn ya bude mata front seat ta shiga shima ya shiga snn ya tada motar suka wuce..ko a hanya sai satar kallonshi take taga fuskan nan a cunkushe kamar na shanu..sun danyi nisa da tafia wayanta ya fara ringing ta duba screen sai taga thesame number ne da baby ya kirata dashi jiya dan haka tayi daurin silencing wayar tareda turata cikin jaka tana rarraba ido..Bobby dake ankare da duk abunda take hannu yakai ya dauki bag din nata tareda zaro wayar daga ciki snn ya ajiye mata jakar ta..kallon wayar ya tsayayi kafin wani kiran ya sake shigowa bai tsaya wata wata ba kuwa yayi answering tareda sawa a speaker..on the other hand Prof na jin tayi picking call din ya fara cewa”baby girl listen to me plss..i will explain everything..lokacinda..”kitt Bobby ya katse kiran tareda kashe wayar gaba daya yasa a aljihunshi saura kiris kan motar ya kwace mashi Allah ya taimaka yayi saurin daidaitashi..Lamido kuwa banda kwalo ido ba abunda take shknn ya gama tona mata asiri..kodai ya samu labarin yazo hostel jiya?..tunanin hakan yasa taji kaman fever na neman rufeta..yanxu idan ya fadawa daddy ai ta shiga uku..shidai yana driving yana kokarin cooling temper dinshi don idan ta zuciyarshi zai bi yana iya gaura mata mari a wurin..kawai zafi yakeji na wnn tsohon mutumin da bazai bar mashi ita ya huta ba..idan ba iskanci bama baiga dalilinda zaisa yace yana son ‘yar cikinshi ba wlh..duk ranshi ya sake 6aci kafin su isa hostel ya cika yayi fam kiris yake jira ya fashema wanda keda rabon shan masifa..daurewa tayi ta tattaro duk karfin halin da take dashi ta kira sunanshi a hankali”Sir”..bai kulata ba kuma bai kalli inda take ba..ta sake juyawa taga yanda yake cin kuna sai kawai ta kauda kanta tana turo baki..tun asali fa wnn baqin halin nashi ne yasa bata wani so aurenshi ba..kan a very minor abu zaizo ya nemi daga mata hankali..har suka karasa hostel batace ba shima baice mata ba..bayan ya gama parking ta juya tana kallonshi kafin tayi mgn taji yace”sauka”..ko minti daya bata kara na cikin motar ba ta bude tayi ficewarta ko sallama bata yi dashi ba..da kallo ya bita zuciyarshi na tafasa yayi reverse ya bar hostel din..direct gida ya koma don yana bukatar mgn da Mummy a halin yanxu..ya fuskanci idan ba wani mataki ya dauka ba tsaf tsohon mutumin nan zaiyi snatching dan attention dinta daya fara samu yanxu..direct bedroom din Mummy ya shiga ya sameta zaune tana karatun Qur’ani ya karasa da sauri ya zauna kusada ita yana kallonta kmr wanda ke shirin fashewa da kuka..Alqur’anin hannunta ta ajiye bayan takai ayah snn ta shiga dubanshi tace”kai lafia kuwa?..why zaka shigomin daki a zabure haka?..”kama hannayenta yayi yanayi mata puppy eyes yace”Mummy akwai matsala wlh”..kallonshi Mummy keyi tace”matsalar me?..”yace”Mummy so nake ayi mgn da Lamido ya tsayar mun da rana nidai..bazan iya jira har saita gama karatu ba wlh”..zare idanu Mummy tayi tana kallonshi tace”rashin kunya Bobby?..”girgiza kai ya shiga yi yace”ba mgnr rashin kunya ba..wani mayen mutumi ne ya makale ma yarinyar nan yake kokarin rabani da ita ni kuma hankalina bazai kwanta ba tunda kinga ba wani sona takeyi ba har yanxu”..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace”sai kaje kayi mgn da Waziri sune masu nema maka aure bani ba”..da sauri yace”kunyarshi nakeji wlh..kiyi masa mgn da kanki”..girgiza kai Mummy ta shigayi tana murmushi..ya sake kama hannunta yace”Mummy please mana..ba tuntuni kikeso inyi aure ba?..”kai ta gyada alamar eh..yace”to yanxu nakeso nayi auren Mummy kiyi wani abu plss”..kai ta gyada mashi tareda fadin”zanyi mgn da wazirin”..da sauri ya rungumeta yana cewa”nagode sosai mother..Allah ya baki aljannah”..kai kawai ta iya gyadawa tana shafa kanshi..har yanxu bata dena mamakin wnn so da Bobby kema yarinyar ba…sallama yayi da ita ya sake komawa hospital don bai kammala aiyukanshi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button