Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Bai baro hospital din ba sai after magrib..yaso ya wuce gida amma yaji bazai iyaba sai yaje yayi mgn da ita..so yake fushin nashi ya dore amma yasan bazai iyaba don wahalar da kanshi zaiyi..gashi ita ko text message batayi masa irin na bada hakuri ba balle yasa ran kira..jikinshi duk yayi sanyi yasan dama shi kadai yake sonta ita ba sonshi take ba..bayan driver ya gama parking ya bude motar ya fita shi kuma ya kira wayarta tana dauka yace ta fito waje yana jiranta…hijab ta dora akan dogon rigan dake jikinta ta fita..kafin ta karaso ya bude mata kofa dan haka tana zuwa ta shiga tareda maida kofar ta rufe..kamshinshi duk ya cika motar ga kuma sanyin ac da driver ya bari a kunne..kallonta Bobby yake yanajin ciwon tsayawa da tayi kula tsohon saurayinta..kmr tasan tunanin da yake knn tayi kasa da murya tana dan kallonshi a hankali tace”sir nidai dan Allah kayi hakuri”..kallonta yacigaba dayi kafin yace”why are u doing this?..”a hankali ta sake cewa”am sorry”…lumshe ido yayi tareda jingina kanshi jikin seat din da yake yana sauke numfashi..dama yasan wnn fushin ba wani wurin zaije ba tunda ba iya fushi zaiyi da ita na lokaci mai tsaho ba..bude idon yayi yana kallonta ita kuma ta sake narkewa cikin shagwa6an da ta manta yaushe rabonta dashi tace”nidai kayi hakuri bazan kara ba”..kallonta kawai Bobby yake gabanshi har wani faduwa yake..yau dai itama ta tsayar da idonta a kanshi tana kallonshi da puppy eyes don da gaske bata son yana fushi da ita..wani irin sanyi da kasala Bobby yaji sun dirar mashi at once..gaba daya joints din jikinshi sukayi wani irin weak kaman wanda yayi shekara da shekaru ba lafia..lumshe ido yayi ya bude yana sake kallon yanda har yanxu bata dauke idanu akanshi ba..baisan wane force of attraction ne ya matsar dashi kusada ita ba kawai shidai yaji yana iya zaucewa yau idan baiji yarinyar nan a jikinshi ba..Allah kadai yasan yanda yake kokarin fighting wnn feeling dake bijiro mishi duk yake tareda ita amma wnn is different and beyond his control..a hankali yakai hands dinshi yayi cupping fuskanta dasu yana sauke numfashi da sauri kmr wanda yayi aikin karfi..da sauri ta lumshe eyes dinta gabanta na faduwa..fuskanshi ya dora kan nata yana kallon the most cutest and attractive lips daya taba coming across duk rayuwarshi..a hankali ya bude bakinshi yace”i..i..want”..kasa karasawa yayi kawai saiya rungumeta a jikinshi yana sauke ajiyar zucia..wani irin azababben so da qaunarta suna sake zaga kowane kafa na jikinshi..shidai yasan yarinyar nan idan bata soshi ba mutuwa zaiyi for sure..wnn son da yake mata bana lafia bane ya sani..wani irin dif Lamido tayi tanajin yanda heart dinshi ke beating da karfi..ga wani irin force da yayi applying a hug din kaman zai maidata jikinshi…batayi mosti ba kmr yanda batayi kokarin kwace kanta ba..heart beat dinshi da taji kadai ya isa ya tabbatar mata da ba karamin so yake mata ba..wani tausayinshi taji ya kamata…shiko Bobby har yanxun eyes dinshi lumshe yanajin wani extra hot feeling na sake rushing into him..gashi duk kokarinshi na yaga ya rabata da jikinshi ya kasa sbd ko energy baidashi..saida ya daddage snn ya iya raba jikin nata da nashi idanunshi kumshe ya jingina kanshi da kujera..kallonshi Aysha keyi ba tareda tace komai ba har ya dan samu nutsuwarshi snn ya bude idonshi da sukayi jaa sbd abunda yakeji voice dinshi na fita da kyar yace mata”i will die without u..i love u”..kallonshi kawai Aysha keyi batace komai ba..shi kuma yana dubanta ya gyada mata kai yace”yes..i love u to the core..duk wnn abunda kike ba karamin daga hankalina yake ba..am sure yanxu if za’ayi diagnosing dina baza’a rasani da high blood pressure ko kuma cardiac problems ba and it’s all because of u”..kallonshi har yanxu takeyi fana langabar da kai kmr zata sa kuka..hannunta ya kama ya dora saitin heart dinshi yace”zafi nakeji a ciki duk lokacinda namiji ya ra6eki..inajin kmr zata fasa kirjina ta fito idan kika fita ba tareda covering jikinki completely ba..snn inajin ciwo idan kika nuna baki damu dani ba”..shiru ya sakeyi yana sauke numfashi..itama tayi tsit tana sauraran heart beat din nashi..hannun nata ya cire daga chest dinshi ya rikeshi gam da nashi hannun yana yi mata kallon da ya kusa tafia da imaninta in a pleading tone yace”i beg u in the name of almighty ki bar wahalar dani haka..all i want from u is love and care..ko baki soni yanda nake sonki ba i will manage and i will live a happy life for as long as ina tareda ke..i love u so so very much Aysher..i love u to the moon”..kai kawai ta shiga gyada mashi hawaye har ya ciko idonta tace”kayi hakuri ban karawa”..dan murmushi ya saki tareda matsawa ya manna mata peck a forehead dinta yace”thanks love..i love u”..lumshe ido tayi hawayen dake cikeda idon suka zubo kan fuskanta..kmr an fizgi mgnr daga bakinta tace”and i..i..i..”kasa karasawa tayi ta sake lumshe ido..da sauri Bobby ya sake kama hannayenta yana kallonta cikeda son yaji abunda zata fada”say it..say it plss it’s what i have been longing to hear from u..please say it in samu saukin zuciata”..sake runtse idanu tayi voice dinta na rawa tace”i..love..u”..tun kafin ta karasa ya cike gap din dake tsakaninsu ta hanyar yi mata kyakykyawar runguma…wani irin bright smile ne kwance kan fuskanshi yaji kalmar i love u din nan tafi diamond da gold a wurinshi..wani irin sanyin dadi yaji yana kamashi ashe haka akeji idan masoyi ya furta kalmar so?..ashe haka feeling din yake?..”oh Allah thank u..Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah yaa rabb”..sun dauki lokaci mai tsaho a haka kafin yayi breaking hug din ya dagota sai yaga hawaye take wani nabin wani..hannu yakai yana share mata hawayen yace”don’t cry okay?..stop crying i love u”..kai ta gyada mashi tana wani turo baki..ita kanta batasan wai ita zata iya bude baki tacema proprietor she loves him ba amma gashi tayi..it happened all of a sudden..kawai batasan yaushe ta fara sonshi ba amma for sure yau ta tabbata she loves him too and she doesn’t want to share him with any other woman..ido ya kuma lumshewa tareda pecking forehead dinta yana dubanta da bright smile nasa yace”thank u so much love..thanks for loving me”..murmushi kawai ta saki dimples dinta suka fito..Bobby dake kallonta yau dai yakai fingers dinshi ya aza bisa dimples din nata..hannunta tasa ta dafe nashi hannayen snn ta dan bude ido kadan ta kalleshi sai kuma ta sake maidawa ta rufe..sunkuyawa yayi ya hade fuskanshi da nata yace”open ur eyes mana ki sake maimaitawa inji”..shoulder ta makale tana wani turo baki tace”oh oh”..daria sosai Bobby ya saki har yanxu fuskanshi hade da nata..wani irin mashahurin nishadi yaji yana saukan mishi ta ko ina kmr bashine dazu kunci suka mai zucia ba..wato Allah dai shine mai yanda yaso kuma a lokacinda yaso..bayan ya gama dariarshi ya raba jikinshi da nata tareda duba agogon hannunshi nan take ya wara ido cikeda mamaki ganin time ya wuce har haka..juyawa ya sakeyi yana kallonta har yanxu bata bude eyes dinta ba..shi duk bai gaji da ganinta ba wlh..ya zama dole ma yaje ya hura wuta shidai asa rana ayi ayi a daura a kawo mashi ita gidanshi don bazai iya jurewa ba anymore..hakurinshi ya kare don haka kawai asan yanda za’ayi dashi shidai..hannunta ya kama yana kallon yanda har yanxu eyes dinta ke rufe yace”love to ki bude idon naki muyi sallama mana”..shoulder ta sake makalewa tana girgiza kai..hands dinshi ya hada wuri daya alaman begging yace”Aysher please mana..ki tausaya min please”..bude idanun tayi a hankali tana kallonshi sai kuma ta bude kofar da sauri ta fita daga motar har tana hada hanya..wani kunyanshi taji ya rufeta wlh..sam bazata iya hada idanuwa dashi ba ita dai..Bobby kam relaxing yayi nan cikin motar yana binta da kallo har ta shige gate dinsu…ajiyar zucia mai karfi ya sauke yana sake godia wa Allah daya nuna mashi wnn rana..shikam babu abunda zaima Allah sai godia..hakika an gama mashi komai na dunia saidai fatan cikawa da imani kuma..driver na ganin fitarta ya koma ciki ya tada motar suka tafi yayinda Bobby ke jingine da seat yana ayyana yanda zaije ya takurama kowa har ansa mashi ranarshi..kuma bada nisa yakeso asa ba shi in ta nashi ne ma nan da two months yakeso ayi komai a kawo mashi matarshi.