Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Karfe biyu daidai suka baro masallaci…Bobby ba tareda ya dubi Nur dake zaune gefenshi ba yace”a ina zamuyi dropping dinka kasan ba komawa college zanyi ba ni..am going home”..da fara’a Nuru yace”don’t worry muje gidan..dama mun kwana biyu bamu gaisa da Mummy ba”..Bobby bai sake yi mishi mgn ba har suka karasa gida…driver na gama parking ko jira ya fito ya bude mishi motan baiyi ba ya bude ya fita abunshi..shi kuma ya dauko briefcase dinshi yabishi a baya…shima Nur fitowa yayi zuwa cikin gidan yana daria kasa kasa gamida girgiza kai dan masifar Bobby daria yake bashi wlh…babu kowa central palor as usual suka wuce parlon Mummy…tana zaune da wasu yammata guda biyu da kallo daya Bobby yayi musu ya wani sake tamke fuska…a hankali ya karasa kusada Mummy ya zauna yanata wani basarwa cikin igbo yace”mummy sannu da gida”…tana murmushi tace”sannu Bobby ya aiki?..”can kasa kasa yace”fine..”Mummy ta maida dubanta ga Nuruddeen daya karaso shima ya zauna kusada Bobby tace”yau an tuna damu knn Nuru”..murmushi yake ya shiga shafa kanshi yace”wlh aiki ne kemin yawa Mummy…duk Bobby ya gama sakar min komai ko taimaka min bayayi”..girgiza kai kawai Mummy tayi tace”to ya aikin?..yasu Mom dinka?..”yace”duk suna lafia Mummy..ina auta?..”tace”auta bai dade da fita ba wai zasuje dubiyan wani abokinsu”..gyada kai Nur yayi alaman gamsuwa…sai yanxu yammatan dake zaune suka samu daman gaishesu…Nur kadai ne ya amsa Bobby kam saima sake tamke fuska da yayi…kallonshi Mummy tayi tace”Bobby bakaga Rayhan bane?..”fuskan nan ba sarari yace”na ganta Mummy”..tace”kuma baka iya amsa gaisuwa ba koh?..”a karkace ya juya yana kallon inda suke murya a dakile yace”lafia lau”..daga haka ya mike ya kama hanyar flat dinshi Mummy ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai..cikin ranta take cewa”Ya Allah ka shiryamin Bobby”…shima Nur mikewa yayi yana duban Mummy yace”Mummy bari in shiga ciki”..kai kawai ta iya daga mishi dan Bobby ba karamin sanyayar mata da jiki yayi ba..ya juya kenan zai tafi aunty sumy da Miemie suka shigo parlon suma…dakatawa yayi da tafiyar tareda wara idanu sosai akan Miemie yace”hey pretty!..”murmushi ta saki itama ta karasa kusa dashi tace”Uncle Nur good evening”yace”evening pretty how are you..how was school?..”tace”Alhamdulillah”…juyawa yayi ga aunty sumy da har ta karasa kusa dasu Mummy ya wani daga hannunshi alamar salute yace”Allah ya taimaki babbar yaya..barka da rana”..aunty sumy na daria tace”barka dai Nur kwana biyu..ya aiki”..yace”normal normal aunty ya naki aikin?..”dan tabe baki tayi kafin tace” babu dadi wlh..duk Bobby ya sakar min komai ni kadai”..daria ya saki yace”nima haka nake fama dashi aunty..saidai hakuri kawai”..yana rufe baki Mummy tace”to ka wuce ka tafi Miemie zata kawo maku abinci yanxun nan”..bai sake mgn ba kuwa ya kama hanyar flat din Bobby…itama aunty sumy mikewa tayi bayan sun gaisa da baqin Mummy ta kama hanyar nata flat din itama…Miemie kuma Mummy tace taje ta cire uniform sai ta kai musu abinci…ba musu ta juya itama zuwa flat din mamanta.

Yana shiga ya fada bathroom ko kayan jikinshi ma sai a bathroom din ya ciresu…ruwan sanyi sosai ya sakar ma kanshi wai ko zai samu yaje inda yake son yaje wala’alla ya samu saukin abunda yakeji amma inaa…shi abubuwan ma sun mishi yawa baisan da wanne ya kamata yaji ba..na farko waccan bafulatanar yarinyar da yakejin ya tsaneta sama da komai a dunia…sai kuma Nur da kalan iskancin da yayi koma yake kan yi mishi..yanxu kuma ga wnn jarababbiyar yarinyar itama tazo zata kara mashi akan wanda yake ciki already…shi ya rasa wnn masifa da bazata hakura ta kyaleshi ba tunda tasan ba sonta yakeyi ba..wlh ko yanada niyyar yin soyayya baiga dalilinda zai sashi kula mace marar class irin wnn ba..ace mace kaman chewing gum sai nanikewa kike ana koranki amma bazaki hakura ba..wnn wace irin rayuwa ce?.

Koda Nuru ya shigo yanajin alaman yana bathroom sai ya nemi kan sofa ya zauna yana pressing wayarshi…after like 7 minutes Bobby ya fito daure da towel a waist dinshi…dagowa Nur yayi yana kallon pure white skin dinshi da ruwa ke tsere akai as result of wankan da yayi snn ya saki wani murmushi…murya can kasa ya furta”what a hottie!..”sarai Bobby yaji abunda ya fada amma bai kulashi ba ya karasa gaban mirror ya fara shafa cream dinshi…shima Nur sake juyawa yayi yana facing inda yake hadda su yin tagumi yana cigaba da kallonshi…kawai ayyana baiwar kyau da Allah yayi mishi yake…gani yake kaman Bobby is the most cutest and hottest guy alive…baisan why ba amma shi kam kyawunshi na burgeshi sosai…cikin ranshi yake ayyana idan shi da yake namiji yana admiring kyawun Bobby yammata kuwa ai kilan sai sunyi hauka akanshi cox yanada wani irin kyau da a kallon farko zaka fahimci hakan…ko dan kasancewarshi ruwa biyu ne oho?..dama ai ance duk dunia babu wanda yakai halfcast kyau so maybe shiyasa duk yan gidansu Bobby keda kyau tunda Mom dinsu igbo ce Daddy kuma Fulani…ta cikin mirror Bobby yaga yanda Nur ya sake juyowa yana zuba mishi ido kaman wanda bai sanshi ba dan haka ya dan saki tsaki tareda juyawa yana dubanshi yace”malam what is the look for?..haka nan ka kafa min ido kana starring..are you sick?..”numfashi Nur ya saki tareda sauke hannunshi daga tagumin da yayi before saying”kawai ina kallon hottie ne…the only cute and sexy man around..guy ba dole yammata suyita hauka kanka ba..ga Rayhan can ma tunda na ganta nasan zuwa tayi kuyi zance”…wani kululun baqin ciki yaji ya sake tokareshi just by mentioning Rayhan’s name…Goodness he hates that girl with passion…he hates her like hell and not only Rayhan he hates duk matan dake kawo mishi kansu…he hates classless women…sbd tsabar baqin ciki ma kasa cewa komai yayi kawai ya juya zuwa closet dinshi ya shiga ciki ya sako white crazy jean da wata black polo snn ya fito fuskan nan ba fus…gefen bed dinshi ya zauna ya dauki wayanshi knn Miemie ta shigo dakin rikeda tray da aka dora transparent glass jug mai daukeda pineapple juice a ciki…kan dan table dake tsakiyan sofas din ta ajiye snn ta mike…tun kafin ta juya Bobby ya daka mata wani tsawa”Miemie bakida hankali koh?..kina hauka zaki shigomin bedroom without my permission?.. “jikinta har ya dauki rawa tace” Uncle Bobby nayi sallama f..”bai bari ta karasa ba ya shiga nuna mata kofa yace”leave immediately”…ba musu ta juya tana turo baki ta fita daga dakin…Nur ya juya yana dubanshi yace”kaidai bakayi ba wlh…baka ajiye komai ba sai shegen masifa mara amfani”…ya bude baki zaiyi mgn aka sake turo kofan dakin wnn karon Rayhan ce ta shigo daukeda tray din abinci…wani azababben zafi yaji ya faraji all over his body kaman ba yanxun ya fito daga wanka ba…like how dare this girl enter his bedroom like this…how dare she…Nur na ganin yanda yanayinshi ya sauya ya saki murmushi cikin ranshi yace”Allah ya kara”..a fili kuma kallon Rayhan data ajiye trayn hannunta yayi yace”sannu da aiki fa”..tana murmushi ta daga mishi kai…shi kuma ya mike yayi pouring juice da Miemie ta shigo dashi a cup snn ya fita palor yana sipping juice din yace”bari in baku space”…Bobby ya bishi da wani uban harara kaman idanunshi zasu fado kasa…idanuwan Rayhan a kanshi kaman zata cinyeshi itama…bata taba ganin wanda harara yayi mishi kyau kaman shi ba…rai a bace ya juyo da idanunshi gareta voice dinshi har bai fita sosai sbd bacin ran da yake ciki yace”how dare you?..how dare you enter my bedroom without my permission?..”a hankali tace”am sorry..Mummy tace in kawo maka abinci”..tun kafin ta karasa yace”Mummy tace ki kawo ko kuma kikace zaki kawo..wato bazaki fita harkana ba koh?..”a hankali tace”bazan iya fita harkanka ba because i love you”…daga mata hannunshi yayi yana fadin”hold it there…wai how many times do i have to push you away ne?..don’t you get tired?..”nan da nan hawaye ya kawo idanunta tace”Uncle Bobby please!..wlh i love y..”still bai bari takai karshe ba yace”who’s ur uncle anan?..stop calling me that am not ur Uncle”..ya karasa mgn yana kawar da kanshi daga gareta kaman wanda yaga poopoo…baisan why duk ta ce mishi Uncle Bobby yakejin wani iri ba…duk Miemie ce ta cuceshi tasa mishi wnn sunan shknn yanxu kowa ke kiranshi haka…hatta Sab da yake brother dinshi shima ta koya mishi kiranshi da Uncle Bobby and now wnn super glue din ma ta kama…hannu Rayhan takai ta goge tears dinta…wlh da tanada yanda zatayi ta cireshi daga ranta da tayi ko don sbd wulakancin da yake mata amma bazata iyaba ita kanta ta sani…mikewa tayi bayan ta gama wiping tears din nata tace”zan tafi..amma dan Allah Uncle Bobby ka dinga picking call dina ko sau daya ne a rana please”…baice mata komai ba sai kanshi daya daga ita kuma ta juya a hankali ta fita tana cigaba da share hawaye…Nuru na ganin ta fita ya dawo dakin rikeda empty cup daya shanye juice din ciki…kai tsaye warmers data shigo dasu ya shiga budewa kobi takan Oga Bobby baiyi ba…ya wani lumshe ido yana smelling aroma din abincin hadda su girgiza kai…serving kanshi yayi ya fara cin abincin…su Uncle Bobby dai har yanxun ana zaune dafe da kai feeling extra hot inside.
Saida Dr Nuru ya gama cinye abincinshi tas ya kora da juice snn ya dawo da hankalinshi kan Bobby da har yanxun ke zaune kaman statue yace”Man if bakaci abincin nan ba kayi missing wlh..na tabbata wnn handwork din Mummy ne for the food taste good”…banza Bobby yayi dashi dan abunda ya dameshi ma ya isheshi…shi kuwa Nur ya sake zuba juice dinshi a cup snn ya mike yana sipping abunshi ya fita daga dakin…parlon Mummy ya koma ya samu tana sallama dasu Rayhan zasu tafi sai Miemie dake zaune dinning tana cin abinci…karasawa yayi ciki shima ya zauna idanunshi kan Miemie kafin Mummy ta dawo cikin parlon itama…Nur ya gyara zama yana fuskantarta yace”Mummy karan abokina na kawo fa”…juyawa itama tayi gareshi tace”wai Bobby?..meya hadaku kuma?..”saida ya sauke ajiyar zuciya snn yace”akan college ne wlh…malamar da take daukan reproductive health ne ta tafi maternity leave and su biyu dama mukeda a wnn bangaren shi kuma Umar yanada classes da yawa da yake attending shine nace Bobby ya taimaka ya danyi covering yaran ko na 1 week ne before we employ new staff amma sam yace bazaiyi ba..that shi ba lecturer bane kuma Mummy na tabbata ba wanda zai iya koyar dasu kamanshi tunda field dinshi ne amma yaki amincewa and in the next 3 to 4 weeks students zasu fara exam bansan me yakeso su rubuta a course dinba tunda duk wnn semester baifi lectures din 1 month suka samu ba shine naga i have to talk to you ko zakiyi mishi mgn ya taimaka musu plss”…if you see yanda ya karashe mgnr da wani puppy eyes zakayi tunanin mutumin kwarai ne????Mummy na gama sauraranshi tace”amma Bobby bai kyauta ba gaskia..don’t worry zanyi mgn dashi ai bai kamata a bar students a haka sunata wasting time dinsu a banza ba..i’ll speak to him”…Mummy na fadin haka ya saki wani murmushi yana shafa kanshi yace”yauwa Mummy thank you…thank you sosai”…murmushi itama tayi tareda gyada mishi kai…Aunty Sumy ta shigo parlon sanyeda dogon riga mara nauyi da alama tayi wanka ne…ta karaso ciki ta zauna tareda umartan Miemie data kawo mata abinci…ba musu ta mike zuwa kitchen tunda ta gama cin nata already…zubowa tayi ta kawo mata snn ta nemi wuri ta zaune kusada Mummy…Aunty Sumy data fara cin abincin tace”Mummy yanxu mukai waya da Hafsa tace zasu dawoda Ilham gobe”…Mummy na gyada kai tace”to Allah ya kaimu goben..nasan da kyar idan ba halin nata tayi musu ba tunda zasu dawo da ita da wuri”…Aunty Sumy tace”nima nayi tunanin haka..ai tama dade wnn karon yau satinta daya fa”…sauke ajiyar zuciya Mummy tayi kafin ta sake fadin”Allah ya kaimu goben toh”..Aunty Sumy tace”Ameen”…Miemie da har yanxun ke zaune kusada Mummy tace”Allah ya kaimu dama na matsu ta dawo wlh..duk gidan ba dadi idan bata nan”..murmushi Nur yayi yana kallonta yace”to mai ‘yar uwa”..murmushin itama kawai tayi mishi..shi kuma ya sake kafa idanu a kanta..yarinyar na burgeshi sosai…ana haka Sabeer ma ya shigo parlon sanyeda yadi milk…dogo ne sosai shima dan kusan tsayinsu iri daya dana Bobby saidai Bobby yafishi da kadan…kai tsaye jikin Mummy yayi masauki yana wani kwabe fuskanshi kaman dan yaye yace”Mummy yunwa”..shafa cikinshi Mummy tayi tace”shiyasa nace ka tsayi kaci abinci kafin ka fita amma kaki…nasan ba abincin waje kake iya ci ba..Miemie tashi ki kawo mai abinci”..ta karasa mgnr referring to Miemie dake zaune…batayi musu ba ta mike zuwa kitchen tana kunkuni…itafa ta dena kula Uncle Sab a gidan nan sun kasa fahimta…Nur da yaga yanda Sabeer ke sake lafewa jikin Mummy sai ya saki daria yana fadin”haba Oga ASP da girmanka?..irin wnn shagwaba ai na civilians ne irinmu mu bana officers ba”…cikeda yar kunya ya dago daga jikin Mummyn yana wani shafa kanshi yace”Uncle Nur barka da zuwa..ashe kana nan wlh ban lura da kai ba”…Nuru na girgiza kanshi yace”dama ya zaayi ka lura dani Sab kana irin wnn shagwaba haka..wai kai auta koh?..”daria kawai Sab yayi yana sunkuyar da kai…Miemie ta dawo da abincin nashi ta ajiye tana kokarin zaunawa yace”Mummy kinga bata kawomun spoon ba kuma idan na gama ci wane ruwa takeso nasha?..”kafin ma Mummy tayi mgn Aunty Sumy tabi Miemie da wani kallo tace”haka ake kawo abinci?..”dan turo baki tayi tace”shine fa dazu da safe hadda cemin skeleton”…a fusace Aunty ta sake cewa”sbd ya fada maki haka shine zaki rama yanxu koh?..wai yaushe kika raina Sab ne haka a gidan nan?..abokin wasanki ne shi?..”bata ce mata komai ba sai mikewa da tayi zuwa kitchen da dauko spoon din hade da ruwa ta kawo mishi..ya faki idon su Mummy yayi mata gwalo ita kuma ta kwabe fuska tana duban Mamanta tace”Aunty kinga yanamin daria koh?..”tsaki Aunty Sumy ta saki tareda tura mata plate data gama cin abinci dashi tace”C’mon dauka ki kai kitchen”…da gudu ta mike ta dauki plate din tayi kitchen…tana ajiyewa ta sake fitowa a guje tayi dakinta rai duk a bace kaman zatasa kuka…Mummy ta bita da kallo tana girgiza kai…ta fuskanci wnn rigiman nasu hali ne a kokon rai dole sai sunyi shi…hakan kuma baya hana duk daya baya nan dayan yayita kewar dayan ba…dan ma akwai Bobby da suke tsoro ai da kilan rikicin nasu sai yafi haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button