Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana shiga gida ko flat dinshi bai shiga ba ya fara shiga flat din Mummy..har ta fara bacci shigowan nashi ta farka ta shiga dubanshi da mamaki tace”lafia dai koh?..”zama yayi a gefenta yace”ba lafia ba Mummy..mgnr sa ranar nan ne dai”..da mamaki Mummy take kallonshi tace”Bobby yaushe ka zama mara kunya ne wai?..”turo baki yayi yace”Mummy ba rashin kunya bane kawai nidai na gaji da jira ne..nidai dan Allah kiyi mgn dasu in two months time nakeso ayi komai plss”..tace”shi kuma ginin gidanka daka ajiye ka denayi fa?..kana ganin zaka iya karasa shi in two months time?..”da sauri yace”Mummy ai finishing ne kadai ya rage and in 4 weeks time nasan za’a gama kawai kice musu nidai banaso ya wuce two weeks”..ha6a Mummy ta kama tace”innalillahi wainna ilaihi rajiun”..sake marairaice mata yayi yace”Mummy please”..kallonshi kawai Mummy keyi tace”ikon Allah”..ya sake bude baki zaiyi mgn tace”tashi ka barmin daki kafin ranka ya 6aci wlh..yaushe ka zama mara kunya haka ne”..mikewa yayi yana turo baki yace”Mummy ni ba rashin kunya nake ba”..tace”to wuce ka barmin daki idan ba haka ba ince shekara guda za’a sa ba wata biyu ba”..ya sake bude baki zaiyi mgn tace”nace ka fita daga dakina Bobby”..sum sum ya juya ya fita daga dakin yana kunkuni..shifa duk basu san halinda yake ciki bane..da sun san abunda yake going through da basu tsaya yi masa kwane kwane ba wlh..he’s kind of desperate..he’s eager..shi gane yakeyi idan ba’ayi komai da wuri ba tana iya dawowa nan gaba tace bata sonshi kuma..har yanxun there is this insecurity a tare dashi amma sun kasa ganewa.
Lamido kuwa da gudu gudu ta koma hostel kai tsaye ta shige room dinsu tareda fadawa gado tanata doka murmushi kai kace mahaukaciya ce sabon kamu..wani irin excitement taji ta tsinci kanta a ciki all of a sudden..wato Allah yayi ma Proprietor baiwar iya kalamai sai kace abunda ya karanta knn..yanda yake tsara mata love words abun har mamaki yake bata yanda baya taba running out of them..gashi da kirki da iya kula da mace snn kuma uwa uba yana yi mata sonda tasan duk dunia babu maiyi mata irinshi idan aka dauke parents dinta..bata san how and when ta fara sonshi ba kawai lokaci daya taji tana sonshi itama kuma zata iya auranshi ko don sbd wnn son da yake mata..ta lura he is super romantic dan yanda yayi wrapping dinta a chest dinshi daxun kadai ma abun tsayawa a rai ne balle kuma wnn maganganun da yayita fada mata wanda sune suka bijiro da nata son itama har ta kasa rikewa ta sanar dashi..she remember the smile on his face lokcinda ta furta tana sonshi..she remember how he pecked her kawai saita saki murmushi mai sauti..gaskia Dr Bobby is amazing..he is one in a billion and duk macen data aureshi will be considered as a lucky girl..tayi zurfi sosai cikin tunaninta har bata san yaushe Billy ta shigo dakin tana mata mgn ba..saida ta daddage ta daka mata duka snn ta dawo hayyacinta..ta mike zaune tana waji daure fuska tace”meye haka?..”zama Billy tayi nan kusa da ita tana kallonta with smile tace”bestie bani labari dan Allah..what’s the good news?..”murmushi Aysha ta saki tana wani kallonta ta gefen ido tace”who is ur bestie?..”Billy tace”to yi hakuri bestyn Sa’eed..bani labari inji what’s the secret behind wnn beautiful smile din naki?..”gyara zama Lamido tayi tana dubanta still face dinta da murmushi tace”hmm Billy u wont believe this..wai nice yau da kaina na bude baki nace ma proprietor ina sonshi..can u believe this?..”tagumi Billy tayi tana dubanta da murmushi tace”ai dama kin dade da fara sonshi ganewa ne bakiyi ba..bani labari in de tadail plss”..Lamido tace”aikam dai daxu bansan ya akai ba kawai sai jin bakina nayi yana furta i love u..kuma wlh Billy da gaske sonshi nake..ya samar ma kanshi special wuri a cikin zuciyata har mamakin abun nake..it happen so fast”..murmushi Billy ke saki kai kace itace Proprietor tace”ai dama na fada maki mutumin nan karshe ne..ni tun daga yanda naga yana miki a hospital nasan ba karamin sonki yake ba sbd bai iya 6oyewa a ko ina”..zama Lamido ta gyara ta shiga bata labarin komai daya faru in detail..Billy tayi tsit tana sauraronta banda murmushi ba abunda take saki..Allah ya sani ita dama ta dade tanama qawat tata sha’awar auren proprietor sbd mutum neshi na kwarai..yanada duk wasu qualities da mace take nema a wurin namiji and above all yana sonta fiyeda yanda yake son kanshi..labari sosai Aysha ke bata tana yi tana blushing ita kanta mamakin yanda farat daya ya mamaye ilahirin zuciyarta take..ko daxu da safe bataji wnn feeling din game dashi ba amma yanxu gasu nan sai rushing sukeyi zuwa heart dinta kmr zasu fasa ta..so sosai taji tana mashi kusan fiyeda wanda tayi ma Professor Ahmad…saida ta gama labarinta tsaf Billy ta dauki waya tana searching contact din Sa’eed tace”Sa’eed needs to hear this..i cant believe Lamido is in love with Proprietor..what a miracle!..”
Jama’a biki dai ya kusa sbd haka kowa ya fara shiri zamuje har Gombe mu gwangwaje????????????????????????
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
50
Soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu tun daga wnn ranan..Lamido har mamakin yanda take mugun sonshi take..she loves him to the moon and back kmr yanda yake fada mata..kawai gani take babu macen da ta kaita sa’a data sameshi..yana sonta sosai and ya iya kula da mace sosai ba kadan ba..yanda yake treating nata yasa ko kusa bataso taga wata ta ra6eshi don yanxun zasu samu matsala..kulawa takeyi da abunta yanda ya kamata don da gaske bazata so ta rasashi ko tayi sharing dinshi da wata ba..duk wani abu da tasan bayaso ta bar yinshi wanda yakeso kuma tanayi don ta faranta mishi..sbd tsabar nutsuwa yanxu su Lamido kullum hijab ake sawa babba idan an shigo school ta cire..tana sonshi sosai kusan duk wanda ke tareda ita sun san da haka ga kuma kishi da take dashi don akwai ranar da kiri kiri tace bazai duba wata mata ba wai tunda ta shigo sai kallonshi takeyi..haka nan ya hakura bai dubatan ba saida ta bar office yasa aka sake kiranta..farin ciki sosai yake ciki na samun soyayyarta da yayi shiyasa har kullum bazai gaji da yima Allah godia ba…before su gaka Clinical Posting kusan yan asibitin kadan ne basu san Dr Bobby zai auri Lamido ba sbd yanda suke nuna tsantsar caring wa junansu is something else..wani lokaci kota rigashi tashi bata tafia har saiya gama da patients dinshi snn ya maidata hostel..abun nasu is so so interesting sai ma wanda ya gani..a haka har suka kammala posting suka koma makaranta.
A hankali ta turo office dinshi ta shiga fuskan nan ba fus ganin yana tareda secretary dinshi da kuma wata da bata san wacece ba a office din..sake tamke fuska tayi ta karasa ciki rungume da hannayenta ta karasa ciki..tunda ya dago idonshi ya kalleta yasan akwai daru yau..yanda ta hade ran nan yasan drama ne zasuyi shi ba karami ba..File dake hannunshi ya mikawa matar dake gabanshi tareda sallamarta yace suje zai sake namants..ba musu suka bar office din Lamido ta shiga karasowa ciki har yanxun fuskan nan ba sarari..tsayawa tayi gaban desk dinshi tana mishi kallon tuhuma tace”who are they?..”dan wara ido yayi yana kokarin danne daria yace”secretary dina ce baki gane ba kuma?..”yana rufe baki tace”to na meye zasu wani shigo office dinka su zauna?..”kallonta kawai yake yana kunshe daria yace”to yi hakuri”..harara ta watsa mashi mai kyau tana sake dinke fuska tace”Kuma dayar hadda wani zuwa da dingilallen skirt..nidai bana so kana tara irin wayan nan mutanen a office dinka bakasan ‘yan iska bane koh?..”yana kallonta yace”baby ba tarasu nakeyi bafa..bakiga aiki ne ya kawosu ba?..”sake rungume hannu tayi ta zauna tana turo baki tace”nidai banaso..dama da aiki suke fakewa suzo suyita kallonka mana”..daria sosai ya saki jin kalamanta..har gobe wani extraordinary farin ciki yakeji idan yaga tana kishinshi haka..abun na qayatar dashi sosai..yanxu matsalanshi daya shine bikinsu da akace dole saita gama makaranta za’ayi..waziri da kanshi yace bazai ma jema da Lamido mgnr ba sbd yasan amincewa zaiyi bayan kuma ba haka sukaso ba..kokarin dakatar da dariyarshi yayi yana kallon yanda saura kiris ta fashe ya kama hannunta yace”to kiyi hakuri baby insha Allah bazasu sake zuwa ba..babu mai sake kallon miki ni kinji”..baki ta murguda tana hararanshi shi kuma yacigaba da kallonta full of affection yace mata”C’mon smile mana..da gaske sun dena zuwa daga yau and ko suna zuwa ma babu ruwana dasu you’ll always be my one and only woman..baby I love u so so very much..i love u alot”..murmushi itama ta saki dimples dinta suka fito sai wani blushing take tace”nima da gaske Ina sonka..ban ta6a son wani namiji kaman yanda nake sonka ba Allah..i love u sosai”..gyara zama yayi yana marairaice mata yace”yanxu ya mgnr mu na daxu?..”itama marairaicewa tayi kafin tace”Sir ni bazan iyaba”..tun kafin ta karasa ta katseta da fadin”i told u ki bar kirana da sir din nan bakiji koh..am not ur sir for God’s sake am ur partner..ur life partner so please ki bar kirana da wnn sir din is so irritating”..murmushi ta saki tana kallonshi ta wani kashe murya tana karkata kai tace”can i call u partner then?..”murmushi ya saki shima yana kallon eyeballs dinta yace”U can call me anything amma banda sir”..yana rufe baki tace”alright then daga yau ka zama partner kuma kaima dole kace mun partner”..makale mata shoulder dinshi yayi yace”No u are my baby..yanxun enough talking about that..ya mgnr mu na daxu?..”sake langabewa tayi tace”partner bazan iya bafa..kawai sai inje incema Lamido ayimun aure kafin na gama school”..tasowa yayi daga inda yake ya dawo kusada ita ya zauna suna facing din juna yace mata”partner yanxu bazaki tausaymin ba?..for how many months kikeso muyita zama a haka for God’s sake..if ke zaki iya jurewa ni bazan iya ba pls..na gaji da zama wothout u i want to get married”..baki ta rufe tana daria tace”partner rashin kunya fa”..yace”ba wani rashin kunya am saying the truth..ke baki ganin kokarina ma?..”..kama hannunshi tayi tana kallonshi in a pleading tone tace”nidai kayi hakuri dan Allah..bazan iya ba”..hannunshi ya zame daga nata tareda mikewa ya koma seat dinshi..kawai bazata gane bane shi kadai yasan halinda yake ciki..idan saita gama makaranta nan da almost four months fa ake mgn..dole ma yasan matakinda zai dauka gaskia..ita Mummy da anyi mgn kullum sai tace bai gama gidanshi ba amma yanxu ai ya gama gidan nashi tunda dama fininshing kadai ya rage to me ake jira kuma idan dai baso suke another sugar daddy yazo ya sake mishi gaba da ita ba..marairaicewa ta sakeyi itama kafin tayi mgn Nur ya shigo office din da files a hannunshi..yana ganinta nan zaune yayi wani saurin juya baya kmr wanda yaga abun kunya yace”A’uzubillahi Subhanallahi na shigo at the wrong time”..wani kallo Bobby ya bishi dashi yanajin kmr yaje ya rufeshi da duka..Lamido dai na zaune tana daria dan da gaske draman dake tsakaninshi da abokin nashi ba karamin daria yake bata ba..sake juyowa Nur yayi yana kallon Bobby da wani shegen smile yace”sorry for the interruption guys..will come back some later”..har ya juya zai fita Aysha tace”Sir ka dawo plss..dama ni tafia zanyi”..tana rufe baki Bobby yace”you won’t go anywhere until we finished our discussion”..kallonshi tayi taga ya hade giran sama dana kasa dan haka bata sake mgn ba ta gyara zama tana kallonsu..ta fuskanci shima ba karamin rigimamme bane wlh..at times ma sai taga kmr yafita rigima..juyawa yayi ga Nur da har yanxun yake tsaye rikeda files a hannu shi bai shigo ciki ba kuma bai koma waje ba..saida ya sakar mashi wani harara kafin yace”if u like ka karaso muyi abunda zamuyi as u can see ba zaman banza nakeyi ba”..da sauri Nur yace”ni din banza ince kana zaman banza bayan da idona naga babban aikin da kakeyi..ai ka wuce a kiraka da mai zaman banxa mr romeo”..sake daure fuska Bobby yayi baice mishi komai ba har ya karaso seat dake opposite to her ya zauna ita dai kanta na kasa sai ji tayi gogan nata yace ta koma kan sofa ta jirasu..dan dagowa tayi ta kalleshi tace”sir please..sorry i mean partner please inje anjima sai in dawo”..kallonta yayi yana jajjada mata ki dawo fa da idanunshi..murmushi ta saki tareda gyada kai hadi da lumshe ido meaning she will definitely come back..daga haka tayi sallama da Nur ta bar office din..tana fita Nur ya sauke wani ajiyar zucia yana shafa gemunshi yace”muma dai muzo mu fara love din nan..very soon zakaji nima na hau network wlh..bazanyita zama kuna kasheni da salon love dinku ba kaida Lamido”..harara Bobby ya watsa mashi kafin yace”abunda ya kawoka knn dama?..”girgiza kai Nur yayi tareda daukan files daya shigo dasu ya mika masa ya fara dubawa..shi Kuma Nur banda kallonshi yana murmushi ba abunda yakeyi..mamaki sosai yake na yanda abokinshi ya zama mastern soyayya kmr dai ba shine da yake cewa bazai iya soyayya da diyar kowa ba wai it’s a waste of time and resources..yanxun sai gashi tsumu tsumu yana soyayya da Lamido kmr ba Dr Bobby ba shiyasa har kullum bazai dena mamakin yanda ta shigo rayuwarshi farat daya kuma ta canxa mishi ita ba.