Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

To habibties ina ganin zamu dakata a nan sai Allah ya kaimu bayan sallah.

Ina ma kowa barka da sallah in advance Allah ya maimaita mana..Allah kuma yasa muyi azumin arfah lafia mu gama lafia.❤️????

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan diya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
52
Driver na gama parking a gida ya bude motar ya fita yana takawa a hankali zuwa cikin gidan..bai ko lura da Mummy da aunty sumy dake parlor ba yayi wucewarshi flat dinshi..yana shiga ya fada kan gado ba tareda ko takalman kafanshi ya cire ba..haushin kanshi yakeji sosai na abun da yayi..Sam bai kamata yayi hakan ba yanxun gashi baisan ta Ina ya kamata ya fara bata hakuri ba…yana cikin wnn tunani kiran Nur ya shigo wayanshi..ya dauka tareda sashi a speaker ya ajiye daidai face dinshi kafin yace”what?..”tsaki Nur yaja before yace”kaidai kanada matsala wlh banza..are u at home?..”Kai ya gyada tareda cewa”yes”..katse wayar Nur yayi ba tareda yace komai ba shi Kuma ya sake gyara kwanciya tana tunanin abunyi..yasan da kyar idan Nur ba zuwa zaiyi ba tunda ya tambayi ko yana gida amma yasan idan ya fada masa abunda ya faru shknn ya shiga uku da walakancinsa dan tsona ne zaisha a wajenshi tunda yasan halin kayanshi.

Lokacinda Nur ya shigo dakin ya fito daga wanka knn ya shiga closet zai canxa kaya..yana jinshi baice mishi kala ba har ya gama shiryawa ya fito..Nur ya juya yana kallonshi da wani murmushi yace”na Lamido bada kanka a sare idan kaje gida kacewa Mummy ya Fadi”..murmushi Bobby ya saki tareda zama nan kusa dashi yana dubanshi yace”bansan a inda kaji Hausa ba Nur.. duk wani mgn na hausawa ka iya sai kace dai ba inyamuri bane Kai”..daria shima Nur din ya saki yana shafa Kai yace”sai kace dai ba inyamurai bane mu..kaima ba kace kai ba bahaushe bane?..”harara Bobby ya watsa mashi yace”to yanxu nace bahaushe ne ni.. bafulatani ma kuwa”..tun kafin ya rufe baki Nur ya kwashe da daria kmr ta6a66e.. Bobby na jinshi bai kulashi ba Saida ya gaji don kanshi ya bari snn ya sake dubanshi yana cewa”wai Dr Bobby ne yau yake kiran kanshi bafulatani..wonders shall never end”..banza Bobby ya sake yi dashi yanata danna wayarshi..Saida Nur ya gaji da iskancinshi don kanshi snn ya dan rage murya yace”sorry abokina wasa nake Maka”..shidai baice dashi komai ba..shi Kuma Nur dan nustuwa yayi tareda maida hankali gareshi yace”wata yarinya ce nake tsananin sonta wlh Kuma na kasa fada mata”..kallonshi Bobby ya danyi for like 3 secs kafin ya maida duba ga wayarshi dake hannunshi yace”Ina jinka”..dan shiru Nur yayi kmr bazai ce komai ba sai can yace”Bobby pretty nakeso”..dagowa Bobby yayi da sauri yana dubanshi cikeda mamaki sosai yace”are u even listening to ur self?..kaji abunda kace kuwa?..”Nur yace”na sani mana..ce Maka nayi Ina son pretty and I want to marry her”..girgiza Kai Bobby ya shigayi har yanxun yana binshi da kallo irin na mamaki yace”yanxun of all mata dake garin nan ka rasa wadda zakace kanaso sai Miemie da ko secondary school bata gama ba?..”dan daure fuska Nur yayi yace”kasan I don’t tell my heart whom to love..kawai idan bazaka taimakamin ba its ok ba sai ka biyo ta wnn hanyan ba”..murmushi Bobby ya saki ya sake duban Nur da mamaki yace”ikon Allah..when did i say that?..”Nur yace”gashi nan ka fara cewa bata gama secondary school ba..ai ba cewa nayi zan fada mata Ina sonta tun yanxu ba..I just want u to know sbd kada a samu matsala nan gaba amma its ok”.. daria sosai Bobby ya fashe dashi Wanda rabon da yayi irinshi har ya manta…he can’t believe Nur da gaske yake..yanxu of all yammatan Kano ya rasa warce zaiso sai yar karamar yarinyar da batafi 17 years ba..abun ba karamin daria bane..shi Kuma Nur ya cika yayi fal kiris yake jira ya fashe ganin sbd rainin hankali daria ma yake mashi…Saida ya gaji da daria dan kanshi snn ya dan dakata ya kama hannun Nur kafin yace wani abu Nur ya fizge hannunshi yana zabga mashi harara..daria Bobby ya sake yi kafin yace”C’mon sorry mana abokina..sorry sirikin aunty sumy”..yana gama fadan haka ya sake kwashewa da daria..Nur dai na zaune yana kallon tsabar walakanci kawai sai ya mike ya kama hanyar fita daga dakin Bobby yayi saurin mikewa ya isa inda yake suka fita dakin a tare yana cigaba da murmushi yace”to ka tsaya mu karasa mgn mana”..girgiza Kai Nur yayi ba tareda ya tsaya da tafiyar da yakeyi ba yace”don’t bother”..kama hannunshi Bobby yayi ya dawo dashi cikin parlor suka zauna snn ya dan daidaita dariar da yakeyi yace”to yanxu ya kakeso ayi?..”marairaicewa Nur yayi yana dubanshi yace”kawai nidai kayimin kokari akan mgnr..ba sai ka fadama kowa Ina sonta ba amma daga nan zuwa ta gama secondary school kada a bari ta kula kowa dan Allah sbd banaso wani yazo ya rigani”..murmushi Bobby keyi yana gyada kai yace”baka da matsala da wnn..dama bata kula kowa and bazata fara ba har ta kammala secondary school din”..ajiyar zucia Nur ya sauke tareda fadin”thank u..wnn year din zata gama Koh?..”Bobby yace”mene?..”Nur yace”secondary school din mana?..”murmushi ya Kara saki yace”yeah this year zata gama”..Nur ya sake cewa”ohk Allah ya kaimu..and thanks for ur understanding”..murmushi kawai Bobby keyi yana shafa kanshi..har yanxun mamakin abun yakeyi ne..saidai Kuma ba abun mamaki bane idan akayi duba da how love is..kwata kwata baisan wani dacewa ko cancanta ba..snn Kuma baya duba kan abunda ke iya zuwa ya dawo duk kan wanda yaga dama kawai fadawa yake..yasan Nur husband material ne sosai and tunda har ya furta yana son to lallai fa gaske son nata yake..shi Kuma zaiyi bakin kokarinshi wajen ganin itama Miemien ta soshi ko don sbd abotar dake tsakaninshi dashi.

Da dare yayi dialing number dinta praying Allah yasa ta dauka sai Kuma gashi ta dauka din..ya lankwasa muryanshi in a pleading tone yace mata”Love am sorry”..shiru tayi bata amsa mashi ba shi Kuma ya sake cewa”Aysher”..a hankali tace”umhum”..yace”am sorry for kissing u..nasan I shouldn’t have done that amma ba laifina bane..u couldn’t control my self am sorry”..ajiyar zucia yaji ta sauke ita bama wnn ne damuwarta ba..Kai tsaye tace”wacece ita?..”yace”Mom dinta friend din Mummy ne..and..”kasa karasawa yayi yai shiru tana tunanin yanda zaiyi mata bayani…jin yayi shiru tace”and?..”a hankali yacigaba”tana Sona sosai amma believe me I never loved her..infact na tsaneta”..dan daure fuska tayi kmr yana ganinta tace”i don’t believe that..baka sonta shine kake bata daman binka har flat dinka?..”tana rufe baki yace”wlh da gaske nake maki Aysher bana sonta..koda ta shiga flat din nawa explaining mata nayi cewa ni ke nakeso Kuma kece zan aura..dan Allah kiyi hakuri mana plss..u are the only person that matters to me and i love only u”..shiru tayi batace komai ba..shi Kuma ya sake marairace mata yace”love please!..”ajiyar zucia ta Kara saki before saying”nidai wlh ta sake zuwa inda kake ban yafe ba..and I mean it”..ya saki wani murmushi yana cewa”baza ma ta sake zuwa ba believe me..I Love u”..shiru ta sakeyi kafin yace”Love say u love me too mana plss..i want to hear that”..dan turo bakinta tayi kafin tace”I love u too”.. tun kafin ta rufe baki ya shiga blowing mata kisses ta cikin wayar yana cewa”thank u..thank u..thank u so very much baby..thank u”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button