Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Kmr yanda Waziri ya fada Baffanin Bobby su hudu tareda shi wazirin na biyar sukaje suka kai lefe wa Lamido inda shima ya kar6a tareda saura uncles dinta..farin ciki sosai sukayi da ganin uban kayan kowa yana Allah sambarka..daga nan Kuma suka tsaida biki bayan sati hudu da gama council exam dinsu..sosai su waziri sukayi na’am da da ranar sbd ita kanta amaryar tabada buqatar hutawa kafin lokacin bikin nata…dukda Lamido yaso hada bikin dana Hamma Najeeb amma hakan bai yiwu ba sbd wani special assignment da aka turashi yi a Cameroon and bazai gama ba sai bayan shekara daya..wnn dalilin yasa dole suka bar nashi bikin har zuwa lokacinda zai dawo shi kuma Bobby tunda ya matsa lallai so yake ayi nashi sai a fara yinshi kafin zuwan na Najeeb din..lokacin da labarin sa ranar ya iske Bobby Saida yaji ba dadi..yanxu bayan duk wnn jiran da yayi so suke ya kara cinye wani month bayan exams dinsu snn ayi biki?..Sam baiji dadin wnn four weeks din ba..shi da zasu gane ma da dawo da bikin sukayi ya dawo one month din amma ba su sake Kara mishi another month akai ba…yana zaune office dinshi tun daxu sai jujjuya mgnr yake yanajin haushi kmr tasan halinda yake ciki saiga kiranta ya shigo wayarshi..daukan wayan yayi tareda relaxing kan kujera yayi answering call din ba tareda yace komai ba..a daya 6angaren Lamido najin yayi picking ta wani kashe murya tace”partner nah”..dan turo baki yayi exactly yanda take tura mishi nata bakin yace”stop calling me that”..wara ido tayi da mamaki tace”why?..what happened?..”sake marairaicewa yayi kmr zaisa mata kuka yace”wai bakiji ma abunda ke faruwa ba?..”dan rausayar da Kai tayi itama kmr yana ganinta tace”meya faru?..”tun bata rufe baki ba yace”two months..sbd Allah wane hutawa akeso kiyi har na tsahon one month bayan kammala exams..ya kamata aji tausayina mana”..Saida ta bari ya gama haqilonshi snn ta saki wani murmushi tana cewa”Partner its just four weeks fa..before u know it zakaga har lokacin yazo”..girgiza kai kawai yake yana dafa head dinshi alaman she won’t understand..ita Kuma jin baice komai ba ta sake lankwasa murya tace”sati hudu ai kaman yau n…”bata karasa ba katseta da fadin”idan kika sake kiramin four weeks din nan zakiga other side of me wlh..a tunaninki four weeks din kmr four days yake?..”dan daure fuskanta tayi tana turo baki tace”nidai kayi hakuri..ai bani nasa maka biki ba zaka wuce a kaina”..shiru yayi kmr bazai sake mgn ba yace”haka kikace?..”with full confidence dinta tace”yes”..yace”ohk then”..sai kuma ya dakata ya shiga sakin murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi murya can kasa yace”don’t worry my turn will soon come..and yes ya kamata ki samu enough hutu sosai for what u are about to face”..dan daure fuska tayi tana muzurai tace”what are u insinuating?..”yana cigaba da shafa uban gashin kanshi yace”nothing oo..it’s nothing”..shiru tayi tana ture turen baki sai kace ganinta yake..shi kuma har yanxu bai dena smiling ba ya sake cewa”kullum Ina cewa zakiga other side of me baki ta6a gani ba koh?..to a wnn ranan zakiga the real definition of my other side”..tun kafin ya rufe baki tace”banaso”..yace”badai ni kike cema its just four weeks ba?..zakiga it’s just four weeks duk ranan da kika shigo hannuna..a ranan zaki gane Attahir nake ba proprietor ko Dr Bobby ba”..ya karasa mgnr da wani killer smile a fuskanshi..yanda yake mgn kadai says it all domin duk wanda yaga how he’s talking yana lumshe ido zai gane da mace ne yake waya..kawai baqin cikin da yake na Kara mishi one month duk yayi disappearing sbd tunawa da wani abu da yayi..hakan kuma yasa yaketa sakin murmushi yana shafa kai kmr wani sabon kamu…Alhajia indo kuwa jikinta ba karamin sanyi yayi da wnn kalaman nashi ba..ta lura fa dama these days wani sabon iskanci yakeji dashi haka zaiyita 6aro mata mgn yana sata jin kunya shi kuma ko a jikinshi..ita bata ta6a sanin there is this side of him ba sai yanxu..duk ya wani dawo mai dabi’un ‘yan iska shiyasa yake bata tsoro ma…jin yanda tayi dif kmr bata jinshi ya sake relaxing yana lumshe ido kafin yace”baby”..banza tayi mishi tana turo baki kmr yana gabanta..ya sake cewa”partner”..still taki tankashi kawai sai ya saki murmushi yana girgiza kai yace mata”duk wnn abun fa love wasa nake maki..ke bakisan wasa bane?..”murguda baki tayi tana sake dinke fuska tace”ba wani wasa..Allah idan kacigaba da tsokana na fasawa zanyi”..Bobby ya dan wara ido yana sake murmusawa yace”baby idan kika fasa kuma ai mutuwa zanyi”..tace”to ka dena tsokana na nidai”..tun kafin ta rufe baki yace”na bari..ban karawa believe me”..ajiyar zucia ta sauke kafin tace”shknn”..ajiyar zuciyar shima ya sauke tareda lumshe ido yana sake relaxing kan seat dinshi yace”I..love..you..and i can’t wait to..marry you”.

Bayan sati hudu…

Rano✨

Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
53
Bayan sati hudu…
Yau Friday sukayi final laper dinsu and tun da suka fito daga exam hall around 11 kowa yaje ya sake shiri cikin sign out shirts da sukayi iri daya kowa nashi dauke da sunanshi a jiki..hall da suka saba gabatar da celebrations aka bude musu suka shiga nan sukaita celebrating kammala exams dinsu saura fitowa results kuma..har dj suka kira yaketa playing musu waqoqi iri iri masu rawa nayi masu daukan pictures ma sunayi…a extreme end of the hall Lamido zaune tana kallon su Billy daketa dirkan rawa kan stage da sunga wani da bai musu signing jikin shirts dinsu ba zasu bar rawan suje ayi musu signing din suma suyima wanda basuma ba snn su sake komawa dance floor..haka suketa yi tun daxun ita tana nan zaune tana kallonsu..kawai tunanin yanda zasu kwashe da Bobby takeyi idan yaga shirt dinta da signing musamman ma signing na namiji sai kuma rawa Kiri kiri da takeso tayi amma sbd tsoron kishi irin nashi ta kasayi..har sha’awan Billy da sauran colleagues dinta dake wurin takeyi sai taji inama ba’a college din nan yake ba itama da ba abunda zai hana mata enjoying wnn ranan amma yanxu bata isa ba…Billy ce ta nufo inda take zaune da sauri tana zuwa ta Mika mata wayanta dake hannunta tana cewa”Ur Hamma wants to speak to u”..ba musu Aysha ta karbi waya suka fara mgn dashi ita Kuma Billy ta dauki bottled water dake ajiye nan kusa da ita ta zauna tana sipping ruwan tana sauke numfashi…after like 4 mins suka gama mgn da Hamma Aysha ta shiga mikawa Billy wayanta kafin tace”Billy dan Allah zan danyi rawa ko kadan ne kinga fa ba zuwa zaiyi ba nasan yana hospital wlh”..girgiza kai Billy ta shigayi tace”aah fa ba ruwana Lamido bazaki hadani da wnn rigimammen mijin naki ba..haka nan kisa yazo yana tsareni da idon nan nashi da dadine dasu ba”..langa6ewa tayi tana kallonta kmr zata sa kuka tace”yanxu knn kinfi sonshi akaina Billy?..dan girman Allah in dan shiga inyi Allah ba dadewa zanyi ba”..girgiza Kai Billy ta sakeyi saidai kafin tace wani abu Aysha da ta riga tazo wuya sbd haushi tace”ko baki yadda ba sai nayi wlh saidai kije kiyita fada masa din i don’t care”..daga haka ta mike zata bar wurin Billy ta dawo da ita da sauri tareda mikewa itama tana kallonta tace”amma banda signing kou?..kinsan fa halin mutumin nan Lamido banson kuxo kuna samun matsala akan haka”..kwace hannunta Aysha tayi ta bude bag dinta ta fito da wani shirt din sabuwa sak irin na jikinta tana nunawa Billy rigan tace”indai ba kece munafukar da zaki fada masa ba ba yanda za’ayi ya sani..ana gama min signing kafin mu fita hall din nan ma zan cire in saka wnn”..kallonta kawai Billy keyi ita wnn abun bai gamsheta ba..a yanda taga yake mgn jiya tasan wlh da kyar idan basu samu matsala kan haka ba tunda he made it clear cewar bayason wnn abun…ganin har ta kama hanyan dance floor ta daga shoulder alaman ba ruwanta snn itama ta bita a baya…tana hawa kan stage din sai kuma ta juya zata sauka da sauri colleagues dinta suka kamata suka maidata wurin..daya daga cikinsu taje ta samu dj tace mishi class rep dinsu ta shigo don haka ya samu Waqar favorite dinta mai azabar dadi yayi playing musu zasu cashe yanxun nan..dj kuwa ba musu ya sakar musu waqa mai dadi nan suka shiga rawa suna janta wai itama dole sai tayi..tun tana nokewa tanajin tsoro har dai daga baya ta saki jiki ta dilliqi rawar ta son ranta..at that moment gaba daya mantawa ma tayi da wani warning dinshi na jiya kan baiso tayi rawa and bai yadda wani ya taba rigarta da sunan signing ba..enjoying dinta takeyi kawai tana cashiya kmr ba Lamido ba…saida tayi me isarta snn ta fara zuwa ana mata signing jikin shirt dinta duk wanda ta gani da sauri take zuwa wurinshi yanayi mata zatayi sauri ta rufe wurin da kimono din jikinta wai duk sbd kada ya samu labari idan yazo…a takaice har after five suna cikin hall din nan suna abu daya..ganin yamma ya farayi hankalinta ya dawo jikinta tasan yanxu duk inda yake ya kusa shigowa college din don haka baki alekum ta fita daga cikin hall din zuwa wani dan small room dake kusada wurin ta shiga ciki da sauri ta zare kimono dinta tana kokarin cire sign out shirt din kawai taga mutum a gabanta..batasan sanda gabanta yayi wani irin yankewa ya fadi ba..lokaci daya ta saki rigar tana yarfa hannayenta hawaye har ya ciko eyes dinta tace”wayyo Allah na”..kala bai ce mata ba sai kimono daya dauka ya mika mata..da sauri ta kar6a ta maidata jikinta tana kallonshi..tana gamawa ya kama hannunta a fusace suka fita daga room din..direct office dinshi ya nufa da ita mutane nata kallon yanda ya riko hannunta amma kobi ta kansu baiyi ba don abunda ya dameshi kadai ma ya isheshi..yana bude office din ya turata ciki snn shima ya shiga ya maida kofar ya rufe ya shiga kallonta da eyes dinshi da sukayi jaa sbd bacin rai…kuka sosai ta fara tana yarfe hannayenta shi Kuma baice mata komai ba sai tsareta da yayi da eyes dinshi da taji sun dawo mata eyes dinshi data sani a baya masu sanya mata firgici da nutsuwa ba tareda ta shirya ba..da sauri ta matsa zuwa kusa dashi ta dan daga Kai tana kallonshi sbd yafita tsayi sosai kawai sai ya lumshe eyes dinshi don bazai iya juran kallonta a haka ba karyar mishi da zucia zatayi…ba zato ba tsammani kawai yajita fada jikinshi ta kankameshi tana sakin wani kukan da koshi yasan na shagwa6a ne kawai muryanta na rawa tace”am so..rry”..lumshe idanu ya sakeyi yana sauke ajiyar zucia..baisan ya zaiyi da rashin jin Aysha ba amma ko Allah yasan ba karamin wahalar dashi take ba..bude idanunshi yayi tareda dagota daga jikinshi ba tareda ya kalleta ba yakai hannu ya bude kimono dake jikinta nan take uban signings din dake jikin riganta suka bayyana..kallonsu kawai Bobby keyi ranshi na sake 6aci..duk Wanda yayi signing din nn yasan ya ta6a masa jikinta Kuma shidai Allah ya isanshi wlh..da iya class mates dinta ne ma da sauki tunda mata ne amma yasan baza’a rasa ‘yan nursing a cikin Wanda sukayi mata signing din ba…runtse Ido yayi da karfi da yaga har wurin chest dinta saida akayi signing..ya juya bayanta nan ma yaga har waist dinta signing ne kaca kace kawai sai ya juya tareda zaunawa kan sofa yana date head dinshi da yaji kaman zai 6alle sbd ciwo..karasawa tayi ta zauna kusa dashi tareda dora kanta a shoulder dinshi tana hawaye sosai tace mishi”dan Allah kayi hakuri partner..zaka iya punishing dina da any kind of punishment amma don’t be mad at me plss..am sorry”..hannunshi yakai a hankali yana shafa kanta sbd yanda kukan ke ta6a zuciarshi kwarai…sake langabewa tayi tana sauke numfashi..shi Kuma murya can kasa yace mata”you danced right?..”shiru tayi tana rarraba ido kmr munafuka shi Kuma ya saki murmushi mai ciwo dama ya tambaya ne wai ko hasashenshi zai zama ba gaskia ba amma shirun da tayi ya tabbatar mishi da cewa tayi rawa..zafi sosai yakeji cikin ranshi Wanda inda zai fito dashi ya nuna mata yanda yakeji kilan tsorata zatayi ta gudu shiyasa yake kokarin dannewa kawai..zuwa yanxu ya fuskanci zafi da takura babu abunda zai kara mata sai kangarewa so it’s better ya fara binta da lallami da nasiha kilan Allah yasa ya dace..sake Kai hannayenta tayi ta zagaya bayanshi zuwa stomach dinshi dasu dukda ba gama zagayawa sukayi ba tace”partner am sorry please”..Kai kawai ya iya gyadawa yana shafa kanta a hankali yana karanta duk addu’an da yazo bakinshi..inshort sun duki lokaci mai tsaho a haka tana bashi hakuri kafin ya samu saukin abunda yakeji..Saida ya dan nustu snn ya shiga nata nasiha sosai Wanda har kusan kuka yasata sbd yanda yake mgnr shows ba karamin zafin abun da tayi yakeji ba..bata bar office din ba saida ta tabbata he is no longer upset with her snn yayi dropping nasu a hostel da kanshi bayan sun sha love dinsu.
Washegari da safe bayan sun gama ‘yan koke kokensu na rabuwa da juna Hamma Najeeb yazo ya kwashesu dasu da komai nasu sai jihar Gombawa diban fari..ba’a kwana daku ba wai sai a tashi daku.
Wnn knn..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button