Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwananta biyu da komawa small mom dinta tazo ta dauketa suka wuce Bauchi wai za’a fara mata gyaran jiki and stuffs dai da akeyi na gyaran amarya..dukda Ammi bataso haka ba sbd zaman Fiddausi da Aysha a cewarta ba abunda yake karawa sai lalata Ayshan sbd ba wani fada take iya mata ba..amma da daddy yasa baki haka nan ta hakura suka tafi Bauchin bada son ranta ba..ita fa so tayi a dan zaman nn da zatayi ta gyara mata zama sosai ta yanda bazata je gidan miji tana basu kunya ba don tasan halin kayarta tsaf har yanxu ba cikakken hankali ne da ita ba.
Tunda ranan da suka isa Bauchi ko kofar gida bata sake fitowa ba wai idan ana gyara ba’a son shiga rana…mai gyaran jiki sosai auntyn nata ta dauko takanas take gyara mata ita ciki da waje don komai daya danganci gyaran amarya ana mata and ita da kanta ta fara ji da kuma ganin canji a jikinta..biki ya rage saura 3 weeks Billy ta dawo gidan aunty Fiddausi da zama sbd shirye shiryen biki da suka fara ka’in da na’in…events sosai Billy suke shiryawa ita da Provost don sune Organizers na komai da zasuyi a bikin..dama Kuma halinsu ya kusa zuwa daya dan haka suketa planning events kala kala hadda na shirme dan kusan week guda za’a kwashe ana bikin..ko Lamido da take mayyar biki Saida tace ma Billy events din sunyi yawa da taga uban abubuwan da suka rubuta za’ayi amma sai Billy tace mata babu ruwanta nata kawai zuwa ne amma ko event guda baza suyi cancelling ba.

Shirye shirye sosai akeyi ta kowane 6angare..baga ahalin Lamido da Waziri ba..ba Kuma ga ahalin hajia Mummy da aunty Sumayya ba…bride and groom dai nasu Ido ne kawai almost komai na bikin shirya musu akeyi so nasu kawai suyi attending ne..lokacinda aunty sumy ta fada mishi events da zasuyi cewa yayi a rage that shi bayason big wedding wai gajia zaiyi ma da attending events din..amma aunty sumy tace ko event daya bazasuyi cancelling ba idan yaga dama kar yazo su zasuyi abunsu tareda amarya…murmushi kawai ya iya sakar mata ya wuce flat dinshi yana dialing number amaryarshi da rabonshi da sanyata a ido tun ranar da tabar Kano..kiri kiri yanason zuwa ya ganta yarinyar nan ta hanashi wani wai aunty Fiddausi bazata bari ba which he knows she’s lying of course..kawai shima sai ya rabu da ita cikin ranshi yace zaiyi maganinta ne idan ta shigo hannunshi..ganin har Kiran ta katse bata dauka ba ya ajiye wayar ya shiga wanka don dawowarshi knn daga clinic.

Aunty Fiddausi ta shigo dakin da take kwance hannunta rikeda bottled water mai sanyi sai sachet na inflanil a hannunta ta karaso ciki ta zauna gefen Aysha dake kudundune cikin bargo tace”oya mike ki samu Kisha maganin nn yanxu zaki samu sauki inshaAllah”..dan bude Ido Aysha tayi tana ganin magani a hannunta ta wani yatsine fuska tana marairaicewa tace”aunty dan Allah kiyi hakuri da kanshi zai dena wlh”..a fusace aunty Fiddausi tace”kinsan Allah zan kira Adda in fada mata wnn iskancin da kikeyi..Shan magani kawai ya gagareki kuma don walakanci har likita na kira tazo ta dubaki kememe kina hana ta maki allura yanxu maganin ma Kuma bazaki Sha ba sbd kin maidani yar iska”..sake marairaicewa tayi tana duban small mom din tata tace”aunty na rantse da Allah idan nasha bakina sai yayi sati yanamin daci..shi Kuma allura fa kinsan dai yanda yakemun ba saina fada maki ba”..a fusace aunty Fiddausi ta ajiye drug da ruwa dake hannunta tace”sai kiyita zama da ciwonki har bikin naki yazo ni ba ruwana”..daga haka ta mike tayi ficewarta daga dakin..a waje suka kusa karo da Billy zata Kai mata tea tasha..ganin yanda ta fito rai a 6ace Billy tace”bata Sha maganinba Koh?..”aunty Fiddausi tace”inafa tasha..yarinya dai shege taurin kai kmr mutanen farko”..girgiza kai Billy tayi tace”bari in kai mata tea din nan inzo aunty nasan wanda ko bataso zai iya mata allura”..daga haka ta wuce dakin ta dire mata tea din gabanta ko kallonta batayi ba ta juya ta fita Aysha ta bita da harara kmr Idonta zasu Fadi kasa..kawai batada lafia ma bazasu daga mata kafa ba kowa sai yayita nata masifa kmr an gaji da ita…Billy na fita ta iske aunty Fiddausi zaune a parlor samun wuri tayi itama ta zauna snn ta dauko wayanta tana searching contact dinshi tace”aunty proprietor ne kadai zai iya mata allura komai isakancin da zatayi”..kallonta aunty Fiddausi tayi kafin tace”sai Kuma mu tasoshi tun daga Kano sbd yazo ya mata allura Bilkisu”..Billy tace”zaizo wlh aunty shima nasan da kyar idan ba son ganinta yake ba yanxu..rabonshi da ita fa tun da mukayi graduation”..ajiyar zucia aunty Fiddausi ta sauke tana cewa”to kirashi ki fada mishi yazo yasan yanda zaiyi da ita nidai..dan wlh idan ta kaini bango ubanta zanci babu ruwana da ita amarya ce tunda batada mutunci”..Billy na murmushi tayi dialing number dinshi tana fadin”bama za’a Kai ga hakaba zaizo yayi maganin kayarshi”..yana daukan waya bayan ta gaisheshi tace mishi aunty Fiddausi tace idan zai iya zuwa Bauchi yazo ya duba musu ita batada lafia as usual Kuma taki yadda ayi mata allura snn taki tasha magani..Bobby da yaji abun kmr gaba ta kaishi nan take yace zai taho yanxun nn don shima son ganinta yakeyi musamman yanxu da akace batada lafia yasan ko yace sai gobe ma ba iya baccin kirki zaiyi ba so gwara ya taho yanxun..suna gama waya ta sanar da aunty Fiddausi yanda sukayi dashi dan haka tasa aka fara shirya mishi abinci kala kala yayinda hajia Ai ke kwance daki tana bacci bata ma San abunda ke faruwa ba.
Bobby na gama waya da Billy ya shirya kanshi sharp sharp ya dauki duk wani abu da yasan zai bukata tareda key din mota ya fita ka tsaye ya shiga flat din Mummy ya mata sallama kan zaije Bauchi wai Aysha batada lafia..Mummy batayi yunkurin hanashi ba ta bishi da addu’an dawowa lafia don tasan yanda duk ya rikice din nn idan ma ba’a barshi ya tafi ba hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba…yana fita ya fada mota direct ya wuce gidan su Nur haka ya azalzaleshi ya shirya sharp sharp snn suka shiga motanshi suka kama hanyan Bauchi..Nur sai mita yake mishi wai daga dawowa gida ko hutawa bai barshi yayi ba yazo ya wani jajibeshi zuwa Bauchi sbd rashin hakuri ba yanda baiyi dashi akan ya bari sai gobe ba amma ya dage sai yau sai kace dai a kanshi aka fara soyayya.

Karfe hudu da wani abu suka shigo cikin Bauchi..driver aunty Fiddausi ta tura ya taho dasu daga inda suke har zuwa gidanta..shi ya fara shiga ciki kafin suma su shiga da nasu motan..parking Bobby ya karasa ciki yayi yayinda driver daya rakosu ta shiga cikin gidan ya sanar da aunty Fiddausi karasowarsu..Jim kadan ya dawo yace musu tace su shiga ciki..basuyi musu ba suka fita daga mota dukabi bayanshi har zuwa cikin gidan..a main parlor suka zauna shi Kuma driver ya fita..bayan few minutes Billy ta shigo parlon rikeda tray din su juice a hannunta..ta karaso ciki ta ajiye tray akan table snn ta zauna kan one seater tana dan sunkuyar da kanta tace”barkanku da zuwa”..Nur ya fara cewa”barka Bilkisu..ya jikin Lamidon?..”tace”da sauki sosai”..juyawa tayi tana kallon Bobby ya sakar mata murmushi..murmushin itama ta saki snn ta shiga gaishesu..bayan sun gaisa ta mike ta bar parlon can sai gata ta sake dawowa da wasu dirka dirkan warmers ta ajiye snn ta sake komawa ta kawo wasu ta kuma ajiyewa snn ta wuce don kiran aunty Fiddausi..tare suka dawo da ita parlon ta karaso ciki ta zauna opposite to them tana dubansu da murmushi sosai fuskanta tace”sannunku da hanya”..durkusawa sukayi har kasa suka gaisheta dukda ko zata girmesu ba irin sosai din nan ba..aunty Fiddausi ta amsa gaisuwarsu tana murmushi bayan sun zauna tace”ku fara cin abinci sai raka ku inda take..bacci ma takeyi don batasan da zuwanku ba”..tana rufe baki Bobby da ya matsu ya sanyata Idonshi yace”am..ni bana tareda yunwa aunty”..dan murmushi aunty Fiddausi ta saki kafin tace ma Billy”ki rakashi dakinda take”..ba musu Billy ta amsa da toh ta juya ta kama hanyar dakin Bobby yabi bayanta yayinda oga Nuruddeen ya baje ya shiga bama cikinshi haqqinshi don a cewarshi soyayyar Bobby bazai hanashi cin abinci ba shikam…Billy na nuna mashi dakin ta juya ta bar wurin yayinda shi Kuma ya tura kofar dakin a hankali ya shiga da sallama…wani irin sanyi dakin ya dauka sosai sbd ac dake kure ita Kuma tana kwance can karshen gado ta kudundune kanta cikin blanket tana bacci peacefully kmr ba mara lafia ba..a hankali ta shiga takawa har zuwa bakin gadon ya tsaya yana kallon yanda tayi coiling kanta a kan gadon kmr ba mutum ba..stool ya janyo ya zauna dab da gadon yana facing dinta kafin yakai hannunshi a hankali ya janye blanket din..da uban gashin kanta dake tsefe ya fara cin karo sai kuma cute and beautiful face dinta da yaga har wani glowing yakeyi a Idonshi..baisan ko sbd ya jima bai ganta bane amma yaga ta Kara kyau sosai ba kadan ba…janye blanket din yayi daidai stomach dinta sai yaga tayi motsi tareda jan blanket din zata sake rufewa dashi yayi saurin janyeshi tareda daukan remote ya kashe air condition din dakin gaba daya…kallonta yacigaba dayi yanajin wani abu mai matukar karfi yana kokarin fizgarshi zuwa gareta baisan lokacinda ya lumshe ido tareda sunkuyawa yayi pecking forehead dinta ba..hannunta ya kama ya rike yana cigaba da kallonta kmr Wanda keson gano wani abun..left hand dinshi da yake free ya mika yayi feeling temperature dinta yaji jikinta normal babu wani zafi kawai sai ya saki wani hadadden murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi Kuma still hannunshi na cikin nata..a hankali ta fara motsawa sbd zafi data faraji as a result of kashe ac da yayi..lokaci daya Kuma ta bude Idonta tar tana kallonshi shima sai ya tsayar da nashi idon a kanta yana kallonta…mikewa tayi zaune da sauri tana Mirza idonta to make sure ba dreaming take ba Kuma sai taga its real ba mafarki bane..wara idon tayi da kyau tana kallonshi kallo irin na mamaki kafin tace wani abu ya rigata da fadin”ya jikinki?..”hadiye yawu tayi da sauri tana gyada kanta tace”naji..sauqi..amma ya akayi kazo nan?..”murmushi ya saki yana kallonta yace”kirana sukayi wai bakida lafia kuma kinqi yadda ayi allura and kinqi shan magani”..turo baki tayi tana hade rai lokaci guda tace”to nidai bazaka mun allura ba wlh”..murmushi yakeyi har yanxu yace”baby bakida lafia fa?..”rau rau tayi da Ido kmr zata fara kuka tace”Allah kamun allura fasawa zanyi”..daria ta bashi sosai jin abunda ta fada..ya fuskanci these days rigima takeji dashi dan abu kadan zata ce mishi fasawa zatayi..Saida ya gaji da dariarshi kafin yaja dogon hancinta yana cigaba smiling yace”da yake fasawan a hannunki yake Koh?..”turo baki tayi tace”nidai kada kamin allura dan Allah”..gyada mata kai yayi alamar bazaiyi ba..dan kura mata ido yayi for like 3 mins sai Kuma ya saki murmushi yana kallon eyeballs dinta yace”meke damunki?..”a hankali tace”fever”..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai yana cigaba da kallonta yace”ba fever ba dai..ki fadi gaskia”..daure fuska tayi tana harare harare tace”nidai fever ne ke damuna”..shiru yayi yana kallonta kawai sai ya girgiza kai..Aysha da gaba daya ta gama tsarguwa da wnn abun nashi tace”and what does that mean?..”shoulder ya daga mata alamar nothing..da sauri tace”ban yadda ba wlh..da akwai wani abu cikin ranka”..girgiza mata kai yayi alamar ba komai ita kuma ta wani hade rai zata kwanta baisan lokacinda ya janyota jikinshi yana danne dariarshi ba..murya can kasa yace”kawai ki fadamun period kike ba sai kina wani 6oye 6oye ba mana..am ur soon to be husband”..tun kafin ya rufe baki ta daddage ta tureshi daga jikinta ta sake juyawa zata kwanta yayi saurin dawo da ita jikinshi yana cigaba da dariarshi yace”nifa bada wani abu na fada ba..am sorry”..banza tayi dashi ta shiga kokarin kwace kanta..ya dagota tareda cupping fuskanta still yana murmushi yace”bafa laifi kukayi ba ni kyautamun ma kukayi keda period din naki da kukeyin abunku tun yanxu ba sai…”bata bari ya karasa ba ta toshe mishi bakin da hannu daya tana dukan chest dinshi da dayan hannun tace”banaso..banasoo”..sake rungumeta yayi yana sakin daria sosai yace”to kuyi hakuri na dena”..sake dukan chest din nashi tayi yace”to kiyi hakuri love..am sorry ba period kike ba”..daga haka ya dagota daga jikin nahi yana kallonta da kyau yace”yanxu kici abinci sai muyi allura”..girgiza kai ta shigayi tana cewa”No pls”..da sauri yace”ohk to ki samu kici wani abu sai kisha magani”..gyada mishi Kai tayi alamar toh..shi Kuma ya mike daga inda yake zaune ya mika mata hannunshi yace”tashi muje parlor kici abinci”..girgiza kai ta sakeyi tace”rigana baida tsayi kaje zan fito”..yace”U sure?..”Kai ta gyada mishi meaning she’s sure..bai sake cewa komai ba ya fita daga dakin ita Kuma ta mike da kyar ta janyo hijab ta zura snn ta shiga takawa a hankali ta fita zuwa parlon..itadai tsoronta Allah tsoronta kada yace zaiyi mata allura dan bataso wlh..haka kawai salon azo bikinta allura nayi mata ciwo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128Next page

Leave a Reply

Back to top button