Dr. BOBBY COMPLETE HAUSA NOVEL

Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba…masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank…sai a tura evidence of payment via 07063800556.
55
Cocktail Party…
Karfe shidda da wani abu aka gama wa amarya make up dinta..tana sanye cikin gown na wani sky blue material..head dinta ma da akayi mata turban style blue sai su earrings da rings silver likewise takalmi da purse dinta..light simple make up da akayi mata ba karamin amsanta yayi ba dama ga lalle tasha red and black da suka sake haska pure white skin dinta…Billy ce ta shigo dakinda take cikin ankon da sukayi na dark blue material itama tayi kyau har ta gaji da haduwa..wayanta ne ya fara ringing ta koma gefen gado ta zauna ganin besty ke kira..daukan wayan tayi tana wani daure fuska kmr yana gabanta tace”besty what is it again?..why are u disturbing me?..”daga daya 6angaren Sa’eed ya saki murmushi yana shafa kanshi yace mata”wai yanxu besty har yanxun mgn bai wuce bane?..nace maki fa gobe zan taho inshaAllah”..sake 6ata rai tayi tana turo baki tace”amma ai ba gobe mukayi dakai zakazo ba yau kacemun zakazo”..yace”to nidai dan Allah kiyi hakuri..i promise idan nazo gobe bazan dawo kd ba har sai an kaiki gidan Proprietor”.. murguda baki tayi tana cewa”dole kace haka dama ai..kuma idan bakazo gobe ba dena kulaka zanyi wlh”tana rufe baki yace”bazai ma kaimu ga haka ba Hajia besty amaryar Proprietor”..dan murmushi ta saki kafin suyi sallama abd jiranta da aka fara yi..tana gamawa ta mike make up artist ta sake gyara mata face dinta snn ta fito daga dakin hannunta rikeda purse dinta..qawayen ta dake zazzaune parlor suna ganin fitowarta suka saki ihu suna yaba irin kyawun da tayi..banda murmushi ba abunda take musu ganin kusan kowaccensu ta fito da waya tana daukan pictures..suna cikin daukan pics din Husna ta shigo parlon itama taci ado har ta gaji da haduwa..kallo daya zakayi mata ka gane sister din amarya ce sbd tsabar kyau da tayi..ta karaso ciki tana duban yanda suka wani baibayeta suna hotuna tace”Adda jiranku akeyi fa tun daxu..ga motoci can a waje duk ku suke jira”..da sauri suka karasa pictures dinsu suka fita..ko a wajen ma duk wanda ya kalli amarya saiya furta MashaAllah sbd tsabar haduwan da tayi..mota aka bude mata ta shiga sauran friends dinta ma suka shiga aka kwashesu zuwa hall da za’ayi event din..tun suna hanya Bobby ke kiranta tana gani bata dauka ba dan da gaske ita dai tsoro yake bata yanxun..haka nan ta dauki wayanshi yazo yana kunyatata a gaban qawayenta.
Yau ma dai kamar jiya event yayi kyau sosai Kuma ya qayatar da mutane..idan kaga yanda Aysha ta dirki rawa bazakayi zaton she’s the bride ba..da yake babu manya Kuma ba maza daga ita sai qawayenta sukasha sha’aninsu..pictures da video coverage yau ma sunyi su kmr ba gobe..inda Billy tana gama daukan nata ta turama Bobby da tun daxun yake sake jaddada mata ta turo mishi hoton amaryarshi ya gani…event yayi dadi sosai sunci sunsha Kuma sunyi rawa kmr yanda sukeso..Lamido ji take ko event din jiya bai Kai na yau yi mata dadi ba..sunsha sha’aninsu ne itada friends dinta abun ba’a cewa komai…a takaice basu bar wurin ba sai around 9 o’clock..kai tsaye ana daukansu gida aka wuce dasu kowacce jiki yayi laushi sbd rawan da sukayi.
Yauma kmr jiya suna komawa gida ta sake yin wanka ta saka sleeping dress suma su Billy duk sun sauya kaya zuwa na bacci Wanda zasuyi wanka sunyi wanda baza suyi ba kuma sun wanke make up dinsu bayan sun rama sallolin da ake binsu..ta jona wayarta caji snn ta fita parlor inda sauran suke nan sukaita maida yanda akayi suna darawa abunsu…kusan raba dare sukayi suna labari a parlor sai wajen 1 suka mike kowa ta nemi makwancinta…tana daukan wayanta ta zare Ido ganin missed calls dinshi kusan 20 a wayar..komawa kan gado tayi da sauri ta zauna tana dialing number nashi..har ya kaste bai dauka ba tana shirin sake dialing kuma sai gashi ya kira..tana dauka tun ma tayi mgn ya shiga tambayarta inda taje ta bar wayarta haka..hakuri ta bashi tareda mishi bayanin ta fita parlor wayan kuma ta barshi daki yana caji..hira sosai suka shigayi irin na masoya Billy na kwance tana jinsu har bacci ya dauketa basu dena wayan nan ba inda yawanci hiran nasu bai wuce akan tahowa shima da zasuyi a gobe ba don dashi za’ayi Mother’s Eve..daga nan zasu kwana Saturday bayan daurin aure zaa wuce mishi da amaryarshi..sosai yake farin cikin hakan sbd abunda yake hange daga nesa ne yake dab da karasowa kusa dashi…ga su Mummy suma da suketa faman shiri wai zasuyi traditional event dinsu na Igbo ranan da aka kawota..shi gaba daya ba son harkan events din nan yake ba wlh..a takaice Bobby bai kashe wayarshi ba saida yaji ta fara bacci snn ya saki smile tareda kashe wayar cikin ranshi yana ayyana very soon shima zata fara bacci a kusa dashi kilan ma a jikinshi..tunanin hakan da yayi saida yasa ya saki wani murmushi na musamman yana shafa gashin kanshi.
Mother’s Eve…
Misalin karfe 12 da wani abu Mummy da jama’arta gaba daya suka sauka garin Gombe..gida guda Waziri yasa aka ware musu ita da ‘yan uwanta da kuma sauran mutanenta..Aunty Sumy ma gayya guda tayi na kanta abunka da babbar yayar ango.
A 6angaren oga Bobby kuma gida suma Waziri ya bashi ya sauka tareda abokanshi..duk yanda yaso Waziri ya bari suje hotel hanawa yayi yace dole saidai su zauna gidan daya basu tunda yanada girma zai daukesu gaba daya shi kuma basu gane ba hayaniya ne baiso shiyasa yaso suyi lodging a hotel tunda kowa separate room za’a kama mishi so babu wanda zai dameshi amma nan ko bai hada daki da kowa ba yasan dole zai hada da Nur da yakeda shegen tsokana da rawar kai kmr shine angon..shi duk randa akace yau ana auren Nur baisan irin giggiwar da zaiyi a matsayinshi na groom ba..gaskia idan haka ne Miemie ta shiga uku..kawai sai ya saki murmushi yana girgiza kai.
Karfe shidda da wani abu suka gama shiryawa duk suka shiga motocinsu wasu suka fara tafia hall da za’ayi event din shi Kuma ango da some of friends dinshi irin su Nur suka tsaya gidan da zasuyi picking amarya..dama tun kafin zuwansu an kammala mata shirinta tayi kyau sosai cikin coffee lace dinta daketa walwali..daurinta yayi daidai dana amarya ga kuma gashin goshinta da aka sa musu gel akayi wani coiling dinsu suka kwanta luf a goshin nata..fuskanta na rufe da wani net da ake iya hango fuskan nata daga ciki..Billy ce ta fito da ita tareda walida cousin dinta..ita tana daga baya tana dage nata gown dinta dake jan kasa walida kuma na daga side dinta suna tafia a tare…tun daga cikin mota Bobby ke kallonta gabanshi har wani faduwa yayi sbd kyau da yaga tayi..she looks extremely gorgeous har baisan da wane kalma ma ya kamata ya danganta kyawun da tayi dashi ba..relaxing yana cigaba da kallonta hannunshi daya dafe da saitin heart dinshi da yaji fitowa zaiyi daga kirjinshi sbd mugun bugawar da yake…Nur dake zaune driver seat yana ganin sun fito ya fita daga motar da sauri yana kallonsu baki a washe yake fadin”MashaAllah Tabarakallah..Lamido kece kuwa?..”murmushi tayi tana sunne kai daidai lokacinda suka karaso wurin..Nur da kanshi ya bude mata baya inda Bobby ke zaune har yanxun yana dafe da zucia ta karasa a hankali ta shiga cikin motar kafin ya kulle kofa shima ya koma driver seat..Walida da Billy suka shiga motar Hamma Najeeb da bai dade da zuwa ba suka farayin gaba kafin shima Nur ya tada nashi motan su tafi…wani irin tsit cikin motar yayi yanda kasan babu wani abu mai rai da motsi a ciki..ga kuma kamshin perfumes dinsu da ya baibaye ko ina a cikin motar..ta mirror Nur ya kallesu yaga yanda har yanxun Bobby ke jingine jikin kujera ya wani lumshe ido ita kuma tayi kasa da kai tana wasa da purse dinta..murmushi ya saki yana girgiza kai cikin ranshi yace”strange couple”…har suka isa hall din babu wanda yayi mgn cikinsu..shidai Nur yana gama parking ya bude motar ya fita don ya basu space su dan tattauna before azo a shiga dasu ciki kuma..kmr abunda Bobby ke jira knn ya bude idon a hankali tareda karkatawa gaba daya yana kallonta…dagowa itama tayi ta kalleshi sai kuma ta saki murmushi tareda dauke kanta..a hankali ya matsa kusada ita tareda kai hannu ya yaye net da aka rufe face dinta dashi..nan take beautiful face dinta da yasha light make up ya bayyana..Bobby lumshe ido yayi ya furzar da iska kafin ya sake bude idanun a kanta..hannunshi yakai ya kamo nata da yasha red and black henna ya shiga shafa lallen a hankali yana kallonta..dagowa itama tayi tana kallonshi sai kuma ta kasa cigaba da kallon nashi sbd faduwar da gabanta yayi..idonshi taga yayi wani iri shiyasa bazata iya juran kallonsu a haka ba…hannun nata yakai bakinshi ya manna mishi peck a hankali kuma yana cigaba da kallonta yace”u look…”kasa karasawa yayi ya dago fuskan nata yana kallon eyeballs dinta yace”u look.. extraordinary..beautiful..kishi nakeji wasu su kalleki a haka”..hannunta takai itama tayi cupping nashi fuskan tana binshi da kallon da tasan bazai iya resisting ba tace”kayan hakuri it’s just for today”..kai ya shiga gyada mata yana murmushi yace”yes.. it’s only for today..daga gobe ana daura mana aure shknn u have become mine”..kai itama ta sake gyada mishi tana murmushi alaman yes..kasa hakura yayi saida ya janyota ya hadata da jikinshi sbd yanda yaji kmr fizgarshi akeyi zuwa gareta..hannu takai itama ta zagaye bayanshi dasu a tare suka sauke ajiyar zucia..voice dinshi na breaking yace mata”I..love..you”..lumshe ido tayi itama a hankali tace”I love u too”..dagota yayi daga jikinta yana sake kallon face dinta da har yanxu baiji zai iya gajiya da kallonta ba..itama kallonshi tayi sai taga ya kara haske yayi wani irin kyau da tunda take dashi bata ta6a ganin yayi mata kyau haka ba..shadda ne a jikinshi getzner sai sheqi yake milk colour da aikin coffee a jiki..hula da shoes dinshi suma duk coffee hatta links dinshi coffee colour ne..kallonshi kawai take tana sakin murmushi cikin ranta tana godia wa Allah daya mallaka mata such a handsome man as her hubby..he’s looks so cute da har ta kasa dauke idanu a kanshi saida Nur yayi knocking musu kofa duk suka dawo hayyacinsu…bude kofar tayi da sauri ta fita don wani kunya da taji ya rufeta..shima ya bude side dinshi ya fito yana sakin murmushi dake sake fito da annurin face dinshi…su Billy da abokan ango ne sukayi arranging kansu suka sanya bride and groom a tsakiya snn aka sakar musu sauti suka fara shiga ciki…wajen ya cika ya tumbatsa da mutane ba daga brides family ba ba kuma groom’s family ba dan suma sunzo da yawansu ne tamkar dama a Gomben suke da zama…tun da suka shigo idanun kowa ya dawo kansu kmr dai yanda ya saba kasancewa a every gidan biki amarya da ango na shigowa all attention yake komawa kansu..duk Wanda ya kallesu sai ya sake sbd tsabar haduwan da sukayi..hannunta na rike cikin nashi suke takawa a hankali ita kanta a kasa yayinda nashi kan ke daidai sai sakin murmushi yake..sunyi matukar dacewa da juna ne sosai ba kadan ba..hatta Mummy da Ammi da kowa take zaune inda aka tanadar mata tareda jama’arta kallon ‘ya’yan nasu sukeyi full of love..they look so perfect together..they look takeaway kaman a daukesu a gudu..Lamido dai sake nutsuwa tayi na musamman sbd warning da Ammi ta kora mata wai idan ta kuskura tazo tayi mata rawar kai sai taci ubanta..wnn dalilin yasa ta sake nutsuwa tana takawa daidai har suka karasa inda aka tanada dominsu..bayan sun zauna bridesmaids dinta suma suka zauna a side din da aka tanadar musu likewise abokan ango..bayan sun zauna mc ya fara gabatar da surutanshi kmr dai yanda aka saba..aka bukaci bride and groom da su fito kan stage..tasowa sukayi a hankali Bobby na rike da hannunta suka fito stage din..maman amarya da ango aka bukaci da su fito su nunawa ‘ya’yansu so..nan take Mummy da Ammi suka fito kowacce cikin shiganta na alfarma..yanda Ammi tayi kyau mutane da yawa sai sukayi mamakin wai ita ta haifi Aysha yayinda itama Mummy mutane da dama sunyi mamakin ganinta matsayin mahaifiyar Bobby sbd kyawun da tayi…Mummy tana zuwa batasan sanda ta rungume Aysha ba sbd farin ciki aikam wurin ya kaure da tafi da surutun mc..bayan nan sukayi musu watsin kudi snn suka koma..daya bayan daya ake Kiran mutane suna zuwa su watsa kudi su koma su Hajia Aunty Sumy da Aunty Munubiya dama sauran aunties dinshi na both familyn Mummy dana daddy duk sunyi ankonsu iri daya kuma sun taka rawar gani sosai…qawayen amarya su Billy suma ba’a barsu a baya ba sun taka rawar gani sosai sunsha liki suma tareda besty da bai dade da sauka ba…lokacin da aka fara rawa Aysha jikinta har rawa ya farayi sbd so take tayi amma idanun Ammi dake kanta sun hanata kata6us..ga kuma shi kanshi Bobbyn daya kama hannunta ya rike gam sbd gudun kada tace zata shiga tayi rawar don yasan halin kayanshi amma duk hakan bai yiwu ba don aunty Fiddausi da kanta tazo ta dauketa tace a ware musu fili zasuyi rawa aikam duk aka basu wuri dj ya saka musu waqa amma sbd kunya Aysha sai taji ta kasayin rawar kasancewar su biyu ne a wurin..kunyan su Mummy taji ya kamata don haka ta kasa zagewa tayi kaman yanda tayi jiya sai da su Billy suka shigo snn ta dan samu tayi tunda tasan ba ganinta za’ayi sosai ba..can su Aunty Sumy suma suka shigo sai kuma ga su Husna da Miemie da batasan yaushe suka zama qawaye ba..Yusra da Ilham suma duk inda sukayi suna tare don sosai suma suka rakashe a bikin Addah da Uncle Bobby..Ammi dai na zaune tana kallonsu tana daria wato ita dai Fiddausi har gobe bazata gane cewa ta girma ba knn…a fannin su Nur abokan ango suma ba’a barsu a baya ba dan sosai suka taka rawar gani a wurin mutane sai jinjina Kara irin nasu suke…lokacinda aka bukaci su fito suyi rawa Bobby yasha kallon rawa hadda na hauka wajen Friends din nashi especially Nur daya dage sosai yana dilliqar rawa shi ko kunyar students dinsu dake wurin ma baiyi..shi kuwa duk yanda akayi dashi kan yayi rawar kinyi yayi wai shi bai iya rawa ba saida aunty sumy tazo da kanta ta kama hannunshi ta shiga juyawa dashi kuma dukda hakan baiyi rawan da sukeso yayin ba…in summary dai taro yayi kyau Kuma yayi tsari sosai mutane sunci sunsha sun Kuma yi rawa yanda ya kamata..(kunsan dai duk bikin da ba’aci abinci anyi rawa ba bai amsa sunanshi biki ba).
Sai kusan karfe karfe goma na dare aka tashi daga taron mutane kowa ya nemi motar da yazo ya shige ciki aka fara maidasu gida..su Mummy da ahalinta suma duk motocinsu suka shiga suka wuce gida yayinda Ilham da Miemie suka dage kan su saidai a barsu a nan tunda gobe daurin aure..Aunty Sumy batayi musu musu ba ta kyalesu tunda taga yanda jininsu ya hadu dasu Husna don haka ta wuce tareda alqawarin zata aiko Sab ya kawo musu kayansu na gobe.