A ZATO NA COMPLETENOVELS

A ZATO NA COMPLETE

A rayuwar makaranta, musamman wadanda suke zaune a cikin hostel, babu abinda idanunka ba zasu jiye maka ba. Babu tabara, rashin kunya da banzatar da kai da ba zaka gani ba.

Kai ne iyayenka suka taso ka tun daga wani gari, suka kawo ka wani, domin me? Domin fa kayi karatu ne, idan kuma kayi kai zai yiwa amfani ba wani ba. Amma sai kazo, ka biyewa kawaye da samarin banza ayi ta bushasha da dibar albarka, har ma ka manta da abinda ya kawo ka. Ka ci amanar kanka, ka ci ta iyayenka, ka kuma yaudari kanka. Tunda daga karshe dai, su wadanda ka rike din, zasu zo su maka tawaye, kawaye da suka zuga ka su yaye maka baya su koma gefenka suna maka dariya, samarin banza da suka daure maka gindi su samu wasu da suka fi ka, su kyaleka. A lokacin ne kuma idanu zasu raina fata, an barka da carry overs in ma kayi rashin sa’a da spilling, daga nan idan shaidan ya maka huduba, ka koma bin lecturers domin gyara takardu. Idan kuma hakan bata samu ba, a barka da hamma, kayi babun badinihu, baka ga tsuntsu baka ga tarko, sai zare idanu. Lokacin ne kuma zaka yi dana sani.

Yanzu ita Murjanatu da muke magana a kanta, yar spilling ce. Kamata yayi ace yanzu ta gama nata aikin tana internship kamar yadda sauran yan ajinsu da suka gabata suke yi yanzu haka anan Shika din, amma gata nan.
Yanzu haka har nayi shirin kwanciya barci na kwanta, bata dawo dakin ba. Sai wajen karfe goma sha biyu da rabi na dare sannan ta turo kofar dakin ta shigo. Ina kallonta ta cikin dusu-dusun hasken dakin ta kwanta akan katifarta. A raina na nema mata shiriya da ita da sauran masu hali irin nata, Allah ya nuna musu hanya madaidaiciya.

F.W.A

☆⋆13⋆☆

“Assalamu Alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuhu, ina fata kin wayi gari cikin koshin lafiya ya ke ma’abociyar haske dake haskaka fadin zuciyata bakidayanta!”.
Kamilalliya, kuma tattausar muryar ta fada, cikin wani irin huskinesa da sexiness da… da… abubuwa da dama.
Jin muryar kadai ya haifar min jin wasu abubuwa, wadanda nafi fahimta a cikinsu shine faduwar babu gaira babu dalili da gabana yake yi, sai kuma wata irin kasala, sauran na kasa fahimtar ko meye kuma.

Karfe tara na safiyar ranar asabar, sai dana kusa tuntsirawa kasa lokacin da vibrating din da wayata tayi ya tashe ni daga daddadan barci da nake yi. Sai dai ba wannan bane yasa nayi suman zaune ba, ko kuwa kwance zan ce? Sunan wanda yake kiran ne da yake tsalle yana rawa akan screen din wayata ya kusa sumar dani. Mamakin ya wuce misali, haka fargabar ta wuce misali, nayi zaton mafarki nake yi, hakan ne yasa na kurawa wayar idanu tana ta ringing, wakar Chainsmokers da cold play ta ‘something just like this’ tayi-tayi har ta katse. Ba’a dauki wani lokaci ba aka sake kira, nan ma dai naci gaba da kallon wayar. Sai a karo na uku ne na samu kuzarin kifta idanuna, sannan na daga wayar na kara a kunne.

Muryar data fara dakar kunnena rendered me speechless, na kasa magana. Na tabbata a lokacin da za’a dauki abin gwajin bugun zuciya, za aji zuciyata tana gudun fanfalaki.
Na sha ayyana yadda muryar wannan bawan Allah zata kasance, har mafarki na sha yi. Amma muryarshi da naji yanzu, ban taba tunanota ba, ban taba mafarkinta ba, ban taba jin mai kama da ita ba.
Na hadiye yawu mukut! Da kyar na iya warto murya da natsuwata da suka fara shawagi a saman kaina suna kokarin dagula min lissafi.
Cikin rawar murya dana rasa dalilinta, na amsa. Zata iya yiwuwa saboda yadda muryarshi ta sanya zuciyata tsalle ne, ko kuma saboda yadda muryar tashi ta sanyayar min da jiki ne, zata kuma iya yiwuwa saboda yadda abin yazo min a bazata ne, za kuma ta iya yiwuwa duka abubuwan ne.

Yace “wow, Masha Allah, ban taba tunanin muryarki zata kasance haka ba, lallai tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya tsara ki, ya baki murya wadda zata iya shagaltar da mutum ga yin abu, shin ko ya zaki kasance a fili?”.
Sai naji kunyar maganganunshi sun kama ni, don haka na buge da gaida shi. Ya amsa, ya kara dorawa da, “To daga farko dai sunana Muhammad M.B, ni bahaushe ne sannan ina aiki a Abuja, ban sani ba ko malamar ta ganeni?”.
Nayi yar dariya, “na gane ka mana, Mr. Mysterious!”.

Ya saki wata irin tattausar dariya data sa na kara narkewa akan katifata, jin muryarshi nake kamar ana min busar sarewa a kunne, yace “da gaske nayi zaton sai na zauna dogon bayani, shi yasa tunda gari ya waye nake ta hardar abinda zan fada miki, ki ce da ban wahalar da kaina ba?”.
Na gyada kai ina dariya kamar wata sakara, “gaskiya kam, da ka kira tun da wuri”.
Yace “yadda zan katse miki barci? Yanzu ma naji kamar daga barci kika tashi, sorry, na katse miki barci. Na kasa daurewa ne wallahi. Ina fata banyi laifin komi ba?”.

Na girgiza kai kamar yana kallona, “ko kadan baka yi laifi ba, zan ma iya cewa kayi daidai!”.
Ina jin ajiyar zuciyar daya sauke, “good. Don ba zan so ace daga wayar farko ba na fara yin laifi ba gaskiya”. Duk muka yi dariya.
Daga nan duk muka yi shiru, baka jin sautin komi sai karar dake fita daga cikin wayar kawai. Zuwa can yayi gyaran murya, yace “to Malama Na’ilah, kamar yadda nasan cewa kin san dalilin da yasa na tunkareki tun farko har ya kawo ga wayar da muke yi yanzu, magana ce ta so. Wadda nake so, kuma nake fatan idan Allah ya yarda ya amince, zata kaimu ga aure na sunnah. Magana ta gaskiya ban fito da wasa ba, kuma nayi niyar dana bayyana a gareki, muka samu fahimtar juna ni da ke, ba zanyi sanya ba zan fara zancen aurenmu, in samu in killace ki a dakina kafin kwado ya min kafa, me kika ce?”.

Daga jin sautin muryarshi da yadda yake fitar da haruffa daya bayan daya, kasan cewa kaji mutum wanda yasan ciwon kanshi, wanda yasan me yake yi, ya kuma san yadda duniya take ci. Naji ya kara shiga raina. Nan nayi mishi bayanin cewa yanzu dai karatu nake yi, sannan kuma akwai wanda muke tare dashi a halin yanzu dai, ban boye mishi komi ba, na fada mishi komi da komi. Shi kuma ya burgeni daya saurareni tunda na fara magana har na gama bai katse ni ba. Hakan ya kara min wata martabar shi a cikin idanuna.

Sai dana gama, ya nisa yace “naji dadi kwarai da baki boye min komi ba game dake, sannan maganar karatu a wajena ba matsala bace, koda ace baki fara ba, zan iya daukar nauyinki har ki gama, balle kuma duka-duka Allah na tuba menene ya rage a cikin karatun naku yanzu? Sauran kadan ne. Zancen wanda kuke tare kuma, wannan ai lokaci ne zai nuna mana ko ke din ta wacece. Illa iyaka, mutum ya zage damtse, ya shiga filin dagar neman ki sai aga wanda yake da nasara!”.
Nayi dariya sosai da maganganunshi, da alamu Allah ya hore mishi iya sarrafa maganganu matuka. Shima ya biye min muka yi ta kyakyatawa kamar wasu kananun yara. Sai dana nutsa sannan nace mishi, “to Allah dai yayi mana zabin mafi alkhairi”.
Ina dire aya ya cafe da; “in shaa Allahu ma kece alkhairin”, ko yawu bai bari na gama hadiyawa ba.
Nace “to Allah ya yarda”.
Yace “ameen… Tunda yanzu mun yi wannan magana, ina fata mun fahimci juna ni dake? Kina da wata tambaya da kike son yi game dani?”.
Nace “na fahimci komi, tambaya kuma bana tunanin a yanzu akwai ta, amma idan ina da ita nan gaba, zan yi maka”.

Yace “zaki iya yi a koda yaushe, tunda yanzu na ji muryarki, ina tabbatar miki da cewa sai kin gaji da ganin kira na a wayarki, don zan so ace kullum cikin sauararen muryarki nake!”.
A zuci so nayi in ce, “ai nima hakan take”, amma a fili sai nayi dan murmushi kawai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button