A ZATO NA COMPLETE

Gidan shiru, haka falon babu kowa hatta da TV a kashe take. Na san kila sun tafi makaranta, wannan ko kuma suna daki suna barci. Muka fada kicin muka fara aikin daya kaimu.
Bamu yi minti talatin cikakke ba, muka ji an bude daki an fito. Ba’a jima ba Salama da Haleemo suka shigo kicin din cikin kayan barci, na kallesu na kauda kai cikin girgiza kai. Haka suke yawo wani lokacin a gidan cikin kaya masu bayyana jiki, a ganina duk da a gidan Yayarsu suke ai hakan bai kamata ba. Ba fa kowane mutum bane na Allah.
Haleemo ta dan dakata data ganmu a kicin din, sai kuma ta maze ta kallemu, wai “sannunku!”. Muka yi banza ni da Janan muka kyaleta kamar ba damu take ba. Salama tayi dariyar mugunta tana bude firjin, tace “Allah ya kara, uwar sanabe da neman gindin zama!”. Ta dauki abinda zata dauka ta fita daga kicin din ta bar Haleemo a tsaye.
Kame-kame ta fara, “uhmn, Na’ilah nace., ni fa ban san wannan gayen saurayinki bane! Shi ya fara zuwa wajena, kuma sai daya ne, na rantse da Allah…”.
Na katseta ta hanyar juyawa ina watsa mata harara, nace “ni fa kinga Haleemo, idan na raina kasuwa ko sako bana badawa cikinta. Ban tambayeki alakar ki da tsohon saurayi ba ba, ko kallon banza ban miki ba, saboda baki kai matsayin da zan zauna ina cacar baki dake akan wani saurayi ba wallahi. Alfarma kika min babba da kika lallaba kika hillace shi, godiya ma yakamata in miki, don haka ki kwashi jikinki ki bar nan wajen wallahi, duk abinda mutum yayi dai ai kansa ya yiwa, walau mai kyau ko marar kyau!”.
Ta saki baki tana kallona, sai kuma ta juya ta bar kicin din da sauri. Naja dan siririn tsaki.
Da yake kwabin doughnut din da muka yi babu yawa, nan da nan muka gama soya shi. Muka fara na cin-cin din, zuwa lokacin rana ta fara yi.
Ni kadai ce a kicin din lokacin da Raheemah ta fado kicin din kamar wata kububuwa, Janan ta leka waje zata samu wani yaro ta suka can bakin titi.
Na gaidata a kaikaice, hankalina yana kan fulawar da nake murzawa.
Maimakon ta amsa, sai naji ta ja dan tsaki, “uhumm, ihunka a banza kenan! Ina amfanin wadda za’a kwace saurayi a hannunta tana zaune? Hakan yana nuna aikin banza ne, kuma abu mai wahala ace za’a iya kwace miji! Don ma dai mutum yaji ya sani, idan ma saboda mijina ne ake min zarya ana min shige da fice a gida, to wallahi mijina yafi karfin haka. Nima kuma nafi karfinshi!”.
Allah sarki, naji maganganunta sun bani takaici sun kuma bani dariya, na girgiza kai a hankali ina dan murmushi. Banda tsabar hauka da rashin tunani, har ta wani kalleni tace wai zanyi kwacen miji? Tsakanin ni da ita ko wa yayi kama da wanda zai yi kwace? Na sake girgiza kai.
Ta kama kugu tana wani jijjiga jika ganin ban tanka ta ba, tace “ke Baiwar Allah dake nake, aha! Ni dai na fada na sake fada miki, mijina yafi karfinki!”.
Na juya na kalleta ina murmushi, “ai na fiki sanin haka, saboda haka ki kwantar da hankalinki, mijinki naki ne ke kadai, ban iya snatching ba wallahi!”.
Sai ta hau wasu tsalle-tsalle cikin masifa, “dariya ma kike min kenan? Ke wallahi na ga alamun iskancin ki yawa yake yi fa! Ke har kin isa ki zauna kina min ba’a? Wacece ke, yaushe aka haifeki? Aikin banza dana wofi!! An ga mijina mai kudi an makale mishi kamar maganadisu, ana ta wani shige da fice a gida har da rashin lafiyar karya. To ta Allah ba ta mutum ba wallahi, kuma duk dan iskan da yace zai kara dani wallahi shi zai ji jiki. Haka nan za’a koma gida aci gaba da cin tuwon datsa miyar kuka tsanwa, mu dai mun fi karfin mutum!!”.
Na janye robar hannuna gefe ina kallonta, raina ba karamin baci yayi da maganganunta ba, amma na danne, nasan so take take raina ya baci in biye mata. Na fuskanceta sosai, ina watsa mata wani wulakantaccen kallo, babu shiri ta shiga taitayinta. Nace “na farko, ban san abinda na miki ba da zaki zo haka kawai ki hau zagina, sai dai bari in tabbatar miki da wani abu daya, I’m not into your husband! Hakan da kike yi ya tabbatar min da cewa ko dai kema kwacen mijin kika yi, ko kuma dama can kwacen samari da mazaje a jininku yake. Kowanne ne dai wannan matsalar ku ce, don ni ban saba ba, ban iya ba, kuma ba zan yi ba. Ke gida da dukiyar miji suka dama, dama don su kika aure shi. Mijinki baya cikin yan kayana, ki godewa Allah, da ba don haka ba wallahi da sai na sa kin zubda hawaye, don haka baiwar Allah, ki shiga taitayinki. Gida ne, daga gobe idan kika kara ganina a cikinshi ki min duk abinda kika ga dama!”.
Ta daga baki zata yi magana, amma ta kasa. Tayi haka yafi sau uku, kafin tayi kwafa a fusace ta juya ta bar kicin din da sauri, na ja tsaki ina furta “sakarkaru” a kasan raina. Raheemah sakara ce, daukar zugar kanne da kawaye yana nema ya jefa rayuwar aurenta cikin garari da matsala. Wani abun ban dariya da takaici shine, zasu zuga ta ta wa miji ko danginsa rashin mutunci, ta hau kai ta zauna, su kuma su koma gefe suna mata dariya da ba’a, me amfanin hakan kenan?
Muna gamawa na koma daki na bar Janan zata gyara kicin din ta kuma hade kan kayan. Na wuce mutanen gidan a zaune su duka, muna kallon-kallo dasu daya bayan daya. Ni har mamaki nake, anya kuwa karatu suke yi? Ita dai Raheemah dama tun daga karatun diploma tace ta yanke karatu, su kuma su Salama da suka zo suka zaune a gidan da cewar karatu suke yi, ba makarantar suke zuwa ba. A sati idan suka je sau uku, to wannan shine highest. Babu aikin da suka iya sai kinibibi da gulma. Ban san daga ina Raheemah take samun idea din wai saboda Yaya nake zuwa gidanta ba, abin is so absurd. Tunanin hakan a karan kaina idan nayi sai inji kaina yana juyawa. Na dauki kudurin daga wannan lokaci, ni da gidan Yaya sai dai ziyara amma banda kwana. Ziyarar ma da ace har in gama karatuna in bar Zaria ban kara yin ta ba, da naji dadi.
Karan wayata ya katse min tunanin da nake yi nayi nisa a tunani ko karan ban ji ba sai daya kusa katsewa. Yana katsewa aka sake kira, na dauka naga Yaya Mudatthir ne, don haka na daga. Bayan mun gaisa da tambayar mutanen gida, yace ya ba wani abokinshi da zai je Kaduna gobe sako zai kawo min, zai tsaya ya kwana a Kano sai ya taho da safe, ina ganin zan iya fitowa bakin hanya in karba? Nace mishi ehh, yace to ya bashi lambar wayata zai kira ni. Nace to, tare da mishi godiya, muka yi sallama.
Komawa nayi kan katifa na kwanta zuciyata cunkushe da tunanika, har Janan ta dawo dakin hannu dauke da plate shake da abubuwan da muka yi. Ranar su muka yi ta ci ko abinci bamu nema ba.
Washegari talata aka tashi da azumi. Bayan mun shirya, mun saka uniform dinmu, muka wuce asibiti. Allah ya taimaka wanda zai kawo sakon muna fita ya mana waya, don haka muka tsaya muka amsa muka wuce asibiti. Hostel kawai na wuce na ajiye su ko dagawa ban yi ba, muka wuce ward dinmu.
F.W.A
☆18☆
Azumi bai taba bani wahala irin na ranar Alhamis ba. Muna dawowa daga hutun sallah zamu zana wata irin exams da suke kira ‘council exam’, wannan exam ita zata yi deciding din kasancewar ka nas a cikin wannan shekarar ko kuma akasin hakan. Don haka hankulan kowa a tashe yake, karatu kowa yake yi babu sassautawa balle takaitawa. Ga projects da suka sako mu a gaba. Kafin mu gama projects uku zamu yi, bayan mun gama TP dinmu munyi daya, yanzu haka preparation din proposal muke yi cikin wannan azumin. Ga kuma wani da muka fara cikin wannan satin. Yanzu haka dawowata daga cikin makaranta kenan ganin supervisor dina, wani inyamuri mai dan banzan rashin mutunci. Allah kadai yasan wahalar daya bani yau. Nayi zarya zuwa department dinmu ta kai sau goma yau, yana cewa inje in dawo, hawa bene ma kadai ya isheni. Cinyoyina masifar ciwo kawai suke yi, ga rana, ga azumi. Tun ruwan ranar Lahdi da aka yi ruwa ya mana duka, ba’a sake yin ruwa ba har yanzu, dama daminar ba karfi tayi ba.
Komawata ofishin Mr. Akafyi a karo na kusan goma, na riga na rantse na kuma maya, wannan karon idan naje ya sake cewa inje in dawo, to warewa ta kawai zanyi, in yaso na dawo washegari. Don na gaji.