A ZATO NA COMPLETE

Na sameshi da daya dalibar da aka hado mu wajenshi da ita a zaune akan lumtsumemiyar kujerar ofishin suna kwasar hirar abinsu. Dama ina jin kishi-kishin cewa mutumin irin yan adawa da musulmai ne, duk mai saka hijabi da nikabi, apparently shi a wajenshi makiyi ne. Nayi kwafa a kaikaice, wato ita wannan da yake tasha izgar doki aka ta fiddo cinyoyi da hannuwa waje, zai iya bata lokacinshi kacokam a kanta, tunda zai iya taba ta yadda yake so, duba da irin zaman da suka yi. Duk da akan teburi ne, sai da yayi yadda yayi yake taba hannunta.
Na gaida shi ya amsa yana wani cijewa, Allah kadai yasan iya dauriyar da nayi ban sakar mishi tsaki ba. Da ace ina da hanyar da zan bi a canza min supervisor, wallahi da da gudu zan bita, a canza min shi in huta. Sai dai a babbar makaranta kamar wannan, babu wani abu da yake zuwa ta sauki ba tare da hanya ba. Wadanda suke samun wannan garabasar it’s either iyayensu suna da kudi, ko sun san wasu da suka san wasu manyan a cikin makarantar, ko kuma ke kinsan wasu manya a cikin makarantar, ta nan ne kawai zaki samu yanda kike so. Ire-iren mu mu ya-ku-bayi, da bamu san kowa ba kuma kowa bai san mu ba, haka nan muke cije duk wani wulakanci ko kaskanci da za’a nuna mana, muyi ladab, domin mu samu mu gama karatunmu cikin sauki ba tare da an janyo mana wata matsala da zata fi karfinmu ba.
Kusan mintuna na talatin a ofishin shi, yana min bayani amma rabin hankalinshi yana kan yarinyar dake gabanshi, abin ban takaici shine daga gani yayi diya da ita in ma ba jika ba. Nayi Ala-wadai a cikin zuciyata, na samu ya sallameni ni dai na bar musu ofishin, in yaso ma su cinye kansu kowa ma ya huta.
Bayan na fita daga makaranta na tsaya a banki da niyar cire wata naira dubu daya da nayi tanadinta a cikin akawun dina. Abin ban haushi da takaici sai da layi yazo kaina bayan na sha uwar rana da jira, wai kuma suke ce min ‘insufficient balance’, haushi yazo min iya wuya. Na gwada ciro naira dari biyar, shima a lokacin suka ce babu. A matukar fusace na karasa hostel. Na san ko hauka nayi ba zan cewa Baba ya turo min kudi ba. Ni yanzu haka taraddadin yadda zan ce ya turo min kudin jarabawar da zamu yi nake yi. Kudi ne kusan naira dubu hamsin da doriya.
Na haye kan katifa na kwanta kawai na lumshe idanuna, gajiya, tunani, yunwa, zafi kai komai ma, suka taru suka min rubdugu sai dana rasa ina zan jefa kaina inji sauki a ciki. Sai da yamma tayi likis, ban ma sani ba sai da Esther ta fara tambayata wai yau ba zan yi dafe-dafen karya azumi ba? Sannan na mike ina dingishin wahala. Sauran kayan miyar da suka rage min basu da yawa, dama nufina idan na ciro kudin in tsaya a kasuwa in siyo kayan miyar in kuma karo wasu abubuwan, to kuma ga abinda ya faru. Sauce nayi, na dafa farar spaghetti da zan ci da ita. Nasan zasu isheni in sha ruwa in kuma yi sahur.
Na sauka kasa dakin wata student da take saida ruwan sanyi da kankara, na sayo. Zobon dana yi saura jiya na kara gyarawa na juye a cikin jug. Naje na dauro alwala na dawo na zauna akan abin sallah ina lazumi har aka kira sallah. Na dauko dabino kwara uku da Yaya Bilal ya bani ranar talata, irin yan makkah dinnan gida hudu, nasan har azumi ya kare ina ci, na ci. Sai da nayi sallah sannan na ci abinci.
Ina gama sallar isha’i naji wata irin gajiya da kasala ta saukar min, haka nan na daure nayi tarawihi. Zuciyata na rada min in kwanta kawai in huta, it has been a long day, yayin da wata take kara karfafa min jiki akan in dai daure in tafi karatu. Bayan dogon nazari da saka da warwara dai na daure na warci wayata da littafai na tafi aji. Kwana biyu ko zaman kallon ma bana yi. Yawancin fina-finan da nake kallo kafin, ko lokacin sallar tarawihi ake yinsu, don haka na ajiye su gefe. Idan na samu lokaci ina hawa YouTube in kalla dai. Yanzu ma nasan idan na shiga common room ba karatun zanyi ba, shi yasa na fara zuwa class.
Karfe sha daya tana yi, na fara haramar hada kan kayana. Na rungumi littafan dana dauko na fito daga cikin theatre hall din. Yanayin wajajen musamman da dare, zaka ji shi shiru, babu zirga-zirgar komi sai ta ababen hawa da basu cika yin wajen hostel din ba sai da can babban titi sai kuwa dalibai da suke zuwa aji ko kuma masu dawowa. Na kan ji yawancin mutane suna korafin tsoron wucewa ta wajen da dare, sai dai ni ban taba ganin dalilin da zai sa naji tsoron ba. Naga a cikin waje mai tsaro muke, idan ba wani Iko na Allah ba, babu abinda zai faru da mutum.
Idan nayi addu’ata na shafa ni kam shikenan, sai in jona earpiece in done kunnena, in rufe komi kwata-kwata sai karatun da nasa, ko kida ko kuma wa’azi. Babu irin yanayin da nake matukar so irin wannan. Na kan ji ni free, without worries.
Yanzun ma abinda nayi kudirin yi kenan, musamman yadda ranar yau ta kasance min. Ji nake kamar inyi tsuntsuwa in ganni akan katifata. Sai dai banyi nisa da fara tafiya ba, kiran Muhammadu na ya shigo wayata. Ina jin wannna muryar tashi yana ambatar “baby na!”, I was a goner. Mantawa nayi da komi dake cikin duniyar nan, har ni kaina kuwa, sai shi kadai. Rakiya ya min har cikin dakin da nake, muna ta hirarmu cikin raha, kafin muka yi sallama dashi. Na cire kayana na sa na barci na dauro alwala nazo na kwanta.
Karfe uku alarm din dana sa ya buga na tashi, na fita na dauro alwala na zo na fara nafilfili har lokacin sahur yayi, nayi na sake tado wata sallar har dai aka kira sallah nayi na zauna ina karatun Al-Qur’ani kafin lokacin fara shirin shiga cikin asibiti yayi.
Kamar yadda nayi tunani, maganar kudin jarabawa bata zo min da dadi ba. Yadda Baba ya rufe ido yana masifar shi bashi da kudi, ina nema in tatuke shi, abin ya bani mamaki. Tun bayan kudin school fees daya turo min, naira dubu goma ta sake hada ni dashi. Yanzu kusan wata na biyu kenan a Zaria, amma ba halin in daga baki inyi maganar kudi sai ya hau zagina. Ko provision yawanci Yaya ne yake turo min su, sai kuwa kudin da yake turo min jifa-jifa, dasu nake amfani in sayi kayan bukata. Bayan doguwar wayar da muka yi dashi a ranar Assabar kenan, daki na koma na kwanta. Esther ta tafi weekend gidan kawunta, Maimunah kuma bata ma dakin tun jiya, babu wanda yasan inda ta tafi. Don haka ni kadai na kwana a daki.
Nayi lamo akan katifa cikin tunani iri-iri, kala-kala, ban taba jin karatun nan ya fita a raina ba sai yau. A raina na raya wai da wanne ake so inji ne? Abu ne da bai taka kara ya karya ba, wanda na tabbata yafi karfin Baba, amma kullum cikin ja wa kanshi babu yake, kullum babu, kuma babun a kaina kadai take.
Yawancin matsaloli irin haka idan suka taso dama sai dai in tuntubi Yaya da maganar, idan bata fi karfinshi ba ya maganceta, in kuma tafi sai ya kai ga dangana da su Malam. To ita kuma rayuwa ba zai yiwu taci gaba a haka ba, ba zai yiwu ace kai kullum cikin bani-bani da a maka-a maka kake ba, kowa ma dama zai ji ya gaji.
Sai dai idan nayi duba ta wani bangaren, sai inga yaushe na cika bani-bani kamar yadda Baba yace? Tsakanina dashi kawai kudin handout ne, sai abinda yaga dama ya dan lafo min ciki kawai. Dama can yawancin hidima da dawainiya Yaya ne yake yi, idan aka samu ya biya school fees da kyar, ya hado min provision, to sauran fa sai dai yadda hali yayi, sai na sha matukar wahala ya kuma yazga ni yadda yaga dama sannan zai turo min na bukatun yau da gobe. To maganar gaskiya na gaji yanzu, yanzu haka kwanciyar da nayi ina tunani, tunanin hada kan kayana nake in koma gida kawai, azabar ta isa.