A ZATO NA COMPLETE

~Am really, very, very sorry. Please ku yi maneji da wannan, in shaa Allah gobe zaku samu dogon feji.
☆⋆27⋆☆
Ranar Lahdi a cikin makaranta na yini. Tun wajen karfe goma sha daya na safe na tafi wajen Aylah, tsohuwar room mate dina wadda muka zauna da ita last year. A wajenta na yini, muka sha hirar yaushe gamo da ita. Da yammaci kuma na tafi wanke kaina saloon din cikin makaranta.
Tashin hankalin dana shiga cikin yan kwanakin nan, ba muhimman al’amura kadai na banzatar ba, har ma da kananan irin wanke kai da yanke farce na manta. Ban ankara ba sai da naji kaina yana masifar tashi, sannan.
Da yake akwai wata mata dana saba zuwa wajenta tun ma muna cikin makaranta, nasan duk da cewa yau Lahdi ce tana nan saboda musulma ce ita. Don haka kai tsaye na wuce shagonta. Abinda naci karo dashi ne a gabana daga shiga cikin shagon, ban shiryawa ba.
Adi, Raheemah da Salamah a zaune akan kujerun jira da aka tanada a shagon, yayin da ake wa Adi karin gashin kanti a kanta. Muka tsaya muka danyi kallon-kallo dasu, kafin muka kauda kanmu mu duka, babu wanda ya nuna alamun yasan wani. Na dai musu sannu, nima kuma na samu waje can gefensu na zauna.
Rabon da in gansu su dukansu, tun azumin farko da naje gidansu, gashi yanzu har muna tunkarar watan Zhul-Hijja nan da yan kwanaki.
Ina nan zaune ina wasa da wayata kawai, ina sauraren hirar da suke tayi da yake mu kadai ne a cikin shagon. Tsantsar gulma ce suke yi, wadda nafi kyautata zaton akan Haleemo ce, babu kunya balle tsoron Allah. Wani karin abin haushin shine, Raheemah tana fita domin ta dauki kiran da aka yi mata a waya, suka ajiye hirar Haleemo gefe suka dasa tata. Na girgiza kaina cike da takaicin halayya irin tasu, ku a tsakaninku kuna a matsayin yan uwa babu aminci da amana, ina ga wadanda ba yan uwansu ba kuma?.
Kafin kace me, naji na kosa da zama wajen, da ba don na riga na shigo wajen ba da wallahi baya zanyi.
Allah ya taimaka ba’a jima ba wata daga cikin yan aikin wajen tazo ta kama kaina. Ta tambayeni retouching zanyi ko kuma wankewa kawai? Nace mata wankewa, don ni koda wasa ban taba sanyawa kaina relaxer ba. Yanayin natural santsi da laushin shi yafi yi min.
Na cire gyalena na ajiye a gefe, muka koma can gefe inda ta wanke min shi tas, muka koma tayi drying. Tana gama gyarawa, na sallameta na kara gaba na barsu acan.
Ina fita na sake cin karo da Haleemo, wani mutum daga ganinshi babba ne ya sauketa a mota, itama dai kallon-kallon muka yi, na tabe mata baki na wucewa ta.
Sai da nayi sallar magriba anan sannan na koma cikin asibiti.
*
Washegari da safe bayan duk mum gama ayyukan da suka kamata muyi a cikin ward, su dressing, bada magungunan yara majinyata da sauransu dai, duk muna zaune a nurses station. A yanzu wani yaro da ake yiwa blood transfusion muke monitoring dinshi duk bayan mintuna sha biyar, don haka muke zaune kusa da wajen.
Wasu matrons ne su biyu daga can gefenmu, suna ta zuba hirarsu. Da alama daya daga cikinsu ce aka yiwa aure, yanzu haka tana kan yin hutun amarcinta ne.
Sister Mairo ce take cewa “… Ai ina gaya miki, daga zuwanta sai ga mata a kicin washegari tana girka abinci, ba fa nata ita kadai ba, wai har uwargidan da ‘ya’yanta saboda uwargidan ta tashi da ciwon ciki. Nace to a haka za’a ci amarcin ne? Me zata ji, me zata karas? Allah na tuba duk wanda bai ji dadin kwanakin nan bakwai na aure ba, ai bai ji dadin amarci ba!”.
Daya sister din da ban san sunanta ba ta kwashe da dariya, tace “maganinta kenan ai. Nan muka zo, wace irin nasiha ce ba’a mata ba akan Alhaji Mati? Amma ita ta nace ta kekashe kasa, wai mutum mai mata ko wanda ya taba yin aure is more responsible, waye da waye, gashi nan ai tun ba’a je ko’ina ba, zata zama yar bauta. Ai ni wallahi inaa, Allah ya tsare ni wallahi. Ko a lokacin da Abban su Humairah yake ihun mata biyu zai aura ban ko daga ido na kalleshi ba balle in wani daga jijiyar wuyana, abu daya na sani koma mata nawa dai zai aura, anan zasu zo su sameni dai. Sai na gama tsintar abinda zan tsinta, na gama morewa mijina yadda naso sannan in bar mata sauran. No biggie!”. Suka sake sakin dariya.
Ina kallon yadda Janan take watso min wani irin kallo daga can kasan idanuna. Ban san abinda take sakawa ba a cikin ranta, bana kuma fatan in sani. Don haka nayi shiru, kunnuwana duka biyun akan hirarrakin da su sister Mairo suke yi, wanda yawancin hirar akan ire-iren abubuwan da suke yawo ne a cikin raina.
Har dai lokacin da zamu sake duba yaron nan yayi, muka dauki abubuwan da zamu bukata ni da Janan muka je muka duba shi tare da rubuta cigaban da aka samu game dashi, muka fito.
Muna fitowa, muka ci karo da Dr. Na Abba, ya ja ya dakata yana kallonmu cikin murmushi, “hey, ‘yanmata!”.
Ni da Janan muka maida mishi martanin murmushin tare da gaida shi ya amsa. Janan ta dan yi gaba kadan, ni kuma na dan dakata haka nan muka gaisa. Bamu ja hirar da tsayi ba, saboda yace yana da patients amma yayi min alkawarin sake zagayowa zuwa anjima, nace mishi babu damuwa. Ya wuce, ni kuma na daga kafa na karasa wajen Janan muka cigaba da tafiya zuwa wajen da muke zaune.
Zuwa lokacin da muka koma, su Sister Mairo sun canza hirar da suke yi zuwa ta sana’o’in hannu.
Muna sake komawa wajen yaron a karo na hudu, muka tarar an gama mishi transfusion din. Saboda haka bayan munyi handling din bayanan yaron wajen likitan daya duba shi, ni da Janan muka wuce masallaci domin raka Janan tayi sallar azuhur.
Bayan tayi sallar, muna kan hanyar dawowa, Janan ta kalleni, tace “na yi zaton zaki sayi wani abu ki ci tunda ba azumi kike yi ba yau?”.
Tunda muka fito waje sai lokacin tayi min magana. Na girgiza mata kai a sanyaye, nace “bana jin yunwa!”.
Daidai lokacin mun je wani dogon corridor, Janan taja ta tsaya tana fuskanta ta. Tace “kada ki ce min rashin son auren Yaya da kike yi, yana da nasaba da maganganun da su sister Mairo suka dinga yi dazu?”. Na zuba mata idanu kawai ina kallonta.
Tace “Na’ilah, haba don Allah! Wa yace miki rayuwa zata tafi a haka ne? Da dai nayi shiru in ga iyaka gudun ruwanki ne, amma da alamun baki da niyar tsayawa a matsaya daya, don haka na gaji da kallonki haka nan. Duk kin bi kin kwarzabi kanki Na’ilah, kin hana kan ki sukuni, kin hana kanki kwanciyar hankali, haka ake yi dama? Wai a kanki ne mai mata ya fara neman auren budurwa ne? Shi Yaya Bilal din ba mutum bane? Mutum ne shi, guda dayan shi sukutum. Amma ke kin hana kanki kwanciyar hankali, kin hana na kusa dake samun nasu kwanciyar hankalin saboda wani dalili naki mara fa’ida!”. Tayi shiru tana ajiye numfashi. Har yanzu ban ce mata komi ba, ban ma yi yunkurin tanka mata ba.
Tayi kwafa, “to naji. Ina ce kin ce baki son Yayan? Kin ce ya kyale ki? Ba ya kyale ki din ba? To kuma menene na sanya kanki cikin damuwa? So kike yi ya dinga bin ki duk inda zaki je, kina wulakanta shi Na’ilah? Meye haka kike yi wai?”.
Nan ma na sake yin shiru, haka kawai naji kwalla ta ciko min idanu, na sadda kaina kasa ina sauraronta tana zuba bayanai. Ni kaina a halin da ake ciki yanzu, ban san me nake tunani ba, ban kuma san me nake so ba. Ina son Yaya Bilal ya cigaba da kirana, ya cigaba da kulawa da ni, ina son in kasance dashi. Sai dai a duk lokacin da tunanin zama da kishiyoyi musamman irin su Ameerah da Raheemah ya fado min cikin raina, sai inji duk wani abu da nake ji game dashi ya bi iska.