A ZATO NA COMPLETE

Ina tunanin sai lokacin Yaya Jameel ya kula da nice a cikin falon, yace “a’ah! Wai dama Na’ilah ce?”.
Na daga kai a hankali ba tare dana kalli inda yake ba.
Yace “ke kuma sai kawai muji labarin aurenki daga sama babu sanarwa kamar saukar aradu?”. Mutanen falom suka saki dariya da jin haka, nima sai dana dan murmusa.
Yace “da gaske fa! Da har munyi fushi ai, daga baya dai na hakura. Allah yasa ranar asabar din zamu je daurin auren wani abokinmu, tunda shi nashi da safe ne ba kamar naku na rana ba, in Allah ya yarda zamu yi kokari mu leka”.
Na gyada kai a hankali, nace “Allah ya yarda”. Ban tsaya jiran jin wani yace wani abu ba, na daga kafa na fita daga cikin falon da sauri Janan tana bina a baya.
Muna fita, Allah ya taimakeni naga dan adaidaita sahu, na tsayar dashi da sauri na haye. Ko tsayawa muyi sallamar kirki ni da Janan banyi ba, dan adaidaitan yaja muka tafi.
A cikin adaidaitan, na saka fuskata cikin hannuwana, ina kokarin slowing down irin gudun da zuciyata take yi. Nayi tunanin na manta da Yaya Bilal a cikin raina. Nayi zaton na binne shi a cikin raina gabadaya. Ashe I was wrong. Innalillahi, na shiga uku. A haka zanyi auren?.
Cikin wannan tashin hankalin na sauka garin Gashua washegari. Ganin su Fatsu da kuma yan biyun Sailu da suka yi wayo bul-bul abinsu, shi ya sanya gabadaya na manta da ganin Yaya Bilal da abinda hakan ya haddasa min a cikin raina.
Tunda na sauka ban huta ba, Fatsu bata bari ko rintsawa inyi cikin sauki. Ina sauka, masu gyaran jiki suka tare ni da kayansu na tsuguno da turaruka. Washegari kuma aka yi su dilka da halawa. Kwana biyun nan da nayi, ba karamin gyara na sha ba. Ni a karan kaina sai da naji canji a jikina ba na wasa ba.
Ko a ranar da zan tafi, tare muka tafi da wata mai gyaran jikin, zata cigaba da gyaran data fara har zuwa ranar da za’a kaini gidana. Daga Maiduguri tazo, diyar wata aminiyar Fatsu ce wadda suke mutunci da ita sosai.
*
Tun ana saura kwana uku biki gida ta fara cika da yan’uwa na nesa. Mutanen Gashua da yawansu sun zo, sauran kuma sun tsaya a gida da yake suma can kalar nasu bikin zasu yi.
Janan ana saura kwana biyu fara biki tazo, muka hadu dasu Kulsum da sauran abokanmu muka cigaba da planning harkar bikinmu.
Da yake akwai dakuna biyu manya spare a cikin gidan, nan aka gyarawa yan biki. Duk da haka, ranar da aka fara harkokin bikin, sai da wasu bakin suka dangana da dakin Anty Alawiyya da namu dakin. Su Hajiya Ramata kam kane-kane tayi, babu wanda yayi gigin tunkarar dakinta ma saboda yadda ta cune fuska.
Ranar bikin ma haka ta yini tana ta shiga da fita tana zubda habaici, sai dai duk cikinmu babu wanda ya tanka mata. Muka cigaba da gudanar da bikinmu.
Wani abin mamaki shine, har ranar da muka yi walima, babu wanda muka gani ya leko daga cikin dangin anguna. Shi dama ango sai ranar daurin aure muka yi dashi zai zo, kwana uku ne kadai aka dauka ana shagulgulan bikin Koda na mishi korafi, cewa yayi kada in damu, zasu zo ne. Har ranar daurin aure shiru.
Maganar tafiya ma bai sake tada min ita ba, kuma a yadda muke tunani, an daura aure ranar asabar, jirginsu zai tashi ranar Lahdi da yamma. Dana taba tambayarshi yadda za ayi, naga yana neman manna min hauka, wai me yasa na cika wutar ciki ne da gajen hakuri? Na ga an daura auren ne ya dauki kafa ya barni ne? In zuba idanu mana in ga abinda zai faru. Na bashi hakuri a lokacin, na kuma kawo idanun na zuba mishi kawai.
Ranar assabar, ranar da za’a daura aure. Karfe goma sha biyu na safiyar ranar za’a daura auren a babban masallacin juma’ah dake nan cikin unguwarmu. Da safen muna can gidansu Kulsum saboda yadda gidanmu ya cika da jama’a babu masaka tsinke.
Na lume akan katifar Inna a can uwar daka, duk da uwar kwalliyar da nasha, da kuma zufar da ake yi, hakan bai hana ni fita ko nan da falo ba. Tunda garin yau ya waye, ko in ce tun a daren jiya ma, nake jin wata irin faduwar gaba akai-akai. Zuwa yanzu gabadaya jikina yayi sanyi lakwas kamar an watsa min ruwan sanyi a jiki.
Idanuna kur akan agogon bangon dake cikin dakin makale a jikin bango. Duk wucewar dakika daya, da karuwar faduwar gabana take wucewa. Har lokacin da hannuwan agogon suka hau kan sha biyu, suna nuna karfe sha biyu ce daidai a wannan lokacin. Jikina ya hau rawa yana kadawa, shikenan, na zama danyar nama.
Karfe goma sha biyu da rabi, na jiyo muryar Malam a tsakar gida da sauran muryoyi. Ban san abinda yake faruwa ba, ban kuma yi yunkurin tashi inji mai yake faruwa din ba, na cigaba da zamana. Sai da Inna ta shigo dakin ta ganni, tace “kina nan ashe? Ai an daga auren zuwa karfe hudu na yamma”.
Daga farko ajiyar zuciya naji ta ziyarce ni, kafin na kalleta a rikice, “me yasa?”.
Tace “wallahi nima Malam bai fada min ba, kawai dai yace sun ce an daga”.
Ina ji da yawa suna fata da addu’ar Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, a zuciyata nace ameen.
Idan haka ne, kenan yana nufin sai gobe sannan za’a tafi Zaria da ni. Tsarin dama shine idan aka daura auren yanzu, zuwa bayan azzuhur kuma sai yan kai amarya su dauki hanya. Nayi kokarin tuntubar angon nawa ta waya inji yadda ake ciki, waya bata shiga. Tun da yau tayi ban samu wayar shi ba, nayi tunanin ko network ne ya hana tunda a jiya da rana da muka yi wayar mu ta karshe dashi, yace yau da sassafe zasu taho da abokan shi.
Na sake kokarin tuntubar babban amininshi, Salisu inji ko me yake faruwa, wayar shi ta karaci kara har sau biyu bai daga ba. Daga karshe na maida wayar cikin jaka.
Haka kawai naji wani kuzari ya shige ni, na mike na fito tsakar gida, muka cigaba da harkar mu ni da ‘yanmata na.
Kafin yammar tayi, gabadayanmu mun canza kayan jikinmu. Ni da Janan muka saka yadin da Ummahnsu ta dinka mana, su kuma sauran yanmata suka sanya ankon da muka yi.
Duk kokarin su shirya suke yi, saboda saurin kada anguna su zo damar hoto ta wuce su. Angunan da har yanzu banji wani yace yaji daga garesu ba. Har yanzu muna gidan Inna ne.
Bayan gotawar karfe hudu da mintuna kadan, muka jiyo sautin guda daga cikin gidanmu. Naji kafafuna sun yi wani irin lakwas, na fara kokarin zamewa kasa da sauri na jingina da bango.
Duk da haka, sai da naji wasu irin black spots suna kokarin dabaibaye idanuna lokacin da wata zabiya, irin marokan nan, ta fado gidan tana rangada guda.
“Ina amarya, amarsu ta ango! A zo a bani tukuicin wannan daddadan sako da zan isar, nima kakata ta yanke saka. Wa ya sani ko daga kanki sana’ar roko ta barni? Allah ya yarda, alkawarin Allah ya tabbata, aure ya dauru….!!”.
✌✌✌????????
*☆⋆33⋆☆*
Marokiya bata kula da halin hargitsi da amarya ta shiga bane da alama. Sai data gama jan kirarinta, ta kara gaba. Duk cikinsu bana tunanin wani ya kula da halin da nake ciki ma gabadaya.
Tana fita, wani marokin ya leko shi har da yar karamar gangar shi a hannu, ya tsaya daga soro yana zuba nashi kirarin.
“Ina amarya, tazo ita kuma ta bani kujerar makkah. Ranar farinciki da murna ga masoya, Allah ya nufa, alkawarin Allah ya cika, aure ya dauru tsakanin Muhammadu Bilal da Malama Na’ilah!! Allah ya bamu ikon dawowa badi war haka mu sake shafa wata fatihar ta ‘ya’yanku! Eh, a gayawa amarya, maroki dan na Halimeme na jiran nashi kason, ango Bilalu ya burge shi da sababbin kudi babu ko kari, farare tas bugun Abuja!….”.