A ZATO NA COMPLETE

Mun gama makarantar da sakamako mai kyau, amma ba wanda zai shigar damu jami’ar Ahmadu Bello ba. Da yake Remedial Studies ne muka yi, idan Allah ya taimakeka ka fitar da sakamakon da ake so, za’a baka gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello, matakin karatu na aji biyu, to mu Allah bai kaddara zamu samu ba. Amma mun sake rubuta jamb, mun kuma samu sakamako mai kyau both a jamb da kuma post-utme. Cikin ikon Allah duk suka bamu course din da muke so, nursing.
Nan muka koma gida muka fara shirin tafiya. Sai da muka tsaya aka yi bikin Kulsum. Kasancewar wanda zata aura ya dage akan yana bukatar ayi aurensu, yasa aka daura musu auren, da sharadin zata nemi gurbin karatu anan Umyuk, kuma zai barta tayi, yace ya amince.
Bayan bikin, muka je muka yi registration. Na koma gida na kara kimtsawa na sati daya, na tafi makaranta.
Mun shiga aji na uku muka hadu da Umar, ya raka kanwarshi registration lokacin. Shi NDA ta Kaduna yayi, ya samu ya gama, ya fara posting dinshi kenan muka hadu. Allah Ya taimake shi yana da hanya, shi yasa suka barshi a nan Zaria basu jefa shi waje mai nisa ba.
Babu bata lokaci muka fara soyayya ni da shi. A duk tsayin rayuwata, wannan shine karo na farko da na tsaya nayi wata soyayya da wani da namiji, ban taba ba kaina wannan damar ba.
Lokacin da ina gida da, na fara tsayawa da wasu. Sai dai, ban san dalili ba, duk wasu kalamai na so da zan ji sun fita daga bakinsu, sai inji ina karyata hakan. Wannan dalili yasa zancen ma baya yin nisa, ake watsewa. Daga karshe dai na fahimci cewa ban yarda da soyayyar bane. Duk lokacin da zan ji wani ya ambaci true love, to zan ce maka bata existing sai cikin littafan novels da fina-finai. Janan ta kan ce saboda ban samu wanda raina ya kwanta dashi bane, ko kuma ina jin tsoron commitment ne. Koma dai wannene, ban damu ba.
Shi kanshi Umar din, lokacin dana fara amincewa dashi, ba so bane, it was more like burgewa ko kuma abokantaka. A lokacin I was in a desperate situation, you know irin lokutan nan da zaka ji kana bukatar wani a kusa da kai, bayan abokai da yan uwa of course, sai kuma ya kasance na samu duk wani abu da ake bukata a wajen namiji a tattare dashi Tattali,kulawa da saukin kai. Irin free-spirited mutanen nan ne, duk inda zaku zauna dashi, in shaa Allah zaka ji ya shiga ranka. Sai dai rawar kai da ba’a rasa samarin yanzu da ita, wanda shima sai da muka yi nisa da haduwa dashi sannan na fara karantar hakan, amma nasan cewa lokaci ne, zai daina, tunda ina matukar yin kokari wajen ganin cewa duk lokacin da yayi kokarin yi min maganar banza na dakatar dashi. Hakan yasa lokuta da dama zamu yi fada burum-burum dashi, daga baya dai zai sake dawowa mu shirya.
Bayan wannan sai kuma daga baya da naji na zama very comfortable a tare dashi, ba kamar sauran samarin da nayi a baya ba. Ina jin shi kamar Janan, yadda zan zauna inyi hira da ita babu wani boye-boye, shima haka zan zauna inyi hira dashi. To ko bana son shi, a ganina wannan kadai ai zai ishi rayuwar aurenmu ko? Tunda mun fahimci juna sosai. Balle ma ina son shi. Duk da cewa maganar aurena dashi tana sa inji wani unsettling abu a cikina. Kodayake, har yau bai ma fara zancen auren namu ba, nafi tsammanin kila sai bayan mun gama karatu sannan, and I’m totally fine with that.
Shekararmu ta farko a makaranta babu sauki, yanayin karatunsu mai zafi ne, duk da cewa mun yi wanda yaci uban wannan a SBRS, still, yana mana wahala. Ni a cikin hostel din makaranta na zauna. Yayin da Janan take zaune tare da matar Yaya Bilal anan cikin samaru.
Yaya Bilal yana aiki da kamfanin jaridar daily trust ne. Kasancewar kamfanin yana Abuja ne, yasa yake tafiya can duk ranar lahdi da yamma ko litinin da safe, ya dawo ranar Juma’ah da yamma. Ban san dalilin da yasa bai tafi da amaryar shi ba, tunda naji Janan tace yana da gida acan Abujar. Ban kuma taba tambayarta ba koda wasa. Daga bakinta dai naji tace ashe ma gidan da suke zaune, mahaifin Ameerah ne ya sai musu gidan. Duk da abin ya daure min kai, ban tambayeta dalili ba shima.
Na sha jin korafin bata jin dadin zama da matar Yaya, ban taba fahimtar dalili ba sai da watarana daya da muka je gidan.
Muna cikin shirye-shiryen exams ne, Janan ta saba shigowa makarantar a ranakun weekends, muje library mu yi karatu. Ranar tana zuwa, Yaya Bilal ya kirata yana tambayar tana ina, ta fada mishi. Ba’a jima ba sai gashi yazo, ashe Anty Ameerah ce bata jin dadi, yace zai je ya dauko family doctor din su Ameerah din, muje mu tayata zama kafin ya dawo, a karo na barkatai, naji lamarin nasu ya daure min kai. Nan dai muka tarkata muka tafi.
A kofar gidan ya ajiye mu ko ciki bai shiga ba, ya juya, mu kuma muka shiga ciki. Gidan nasu dan madaidaici, mai kyau. A kalla mun dauki fiye da mintuna goma sha biyar muna doka kararrawar sanar da zuwan bako gidan. Ina tunanin ba wanda yake cikin gidan ba, hatta da wanda yake makotaka dasu, yaji wannan bugu da muka dinga yi. Yadda Janan tayi, very calm and collected, babu alamun wata damuwa a tattare da ita, yasa na gane cewa wannan ba shine karo na farko da irin haka ta faru ba.
Sai da aka kara kusan mintuna biyar sannan naji motsin taba kofa, aka bude kofar falau, cikin sanyin jiki duk muka shiga cikin falon. Ance wai shimfidar fuska tafi ta tabarma, duk da irin kayan alatun da suke cikin falon, hakan bai sa naji ni very welcomed ba a gidan. Ba’a bamu wajen zama ba, babu sannu da zuwa balle ga ruwan sha, haka aka barmu tsaye a tsakiyar falon dakin. Sai Janan ce ta min nuni da kujera, tace in zauna bari taje ta dauko min ruwa. Jiki a sanyaye na lalubi kujera na zauna, cikin nuna girmamawa na gaidata. Sai data gama shan kamshi sannan ta amsa, ya saukin jikin dana mata ma Allah bai bata ikon amsawa ba. Dama na gama shaka da ita, daga nan nima na maida kaina cikin wayata na cigaba da karatuna. A zuciyata kuma cike da mamakin wannan mata. Ita ba wata babba ba, saboda daga ganinta shekarun data bamu kadan ne, ita ba wata dangin sarauta ba balle ince ko jinin sarauta ne a jikinta, amma kice dole sai kin shimfida mulki? Duk da cewa yes, tana da kyawu Masha Allah, kuma daga yadda naji, mahaifinta mashahurin mai kudi ne, kila hakan ne yasa take dagawa. Na girgiza kai kawai.
Ko kallon ruwan da Janan ta kawo min ban yi ba, Allah-Allah nake Yaya Bilal ya dawo, in narko wani excuse din in karawa bujena iska don ba zan iya zama a haka ba Allah ya sani.
Muna zaune mu duka ukun, babu wanda yake cewa wani ci kanka, har rana ta daga sosai babu alamun Yaya. Gashi ko TV ba’a kunna ba a falon balle mu ce zata dauke mana hankali. Gabadaya naji na takura, ban iya dogon zama irin haka babu hira ko wani abu to discuss ba. Rawar kai na da tsokanata basa barina zama waje daya.
Janan ce ta katse dogon shirun daya mamaye dakin ta hanyar tambayar ta, ‘Anty ko za’a dora abinci yanzu ne?’.
Budar bakinta sai cewa tayi, ‘daga gida za’a kawo mata abinci yau, bata son jin kamshin gas ko risho’, da dai na samu na hana kaina daga kama baki in ce to?!, sai na bame bakina na kara tura kaina cikin wayata.
Allah ya taimakemu Yaya ya zabi daidai wannan lokacin ya fado falon kamar an jefo shi daga sama.
Tayi tsalle ta afka jikinshi, mu da muka dago da niyar yi mishi sannu da zuwa sai kasa muka yi da kanmu a rikice saboda ta’asar dake gudana. To ta’asa mana! Ba kullum bane kake ganin irin wannan ‘intimate moment’ a gabanka ba. Sai daya gama tsotse mata baki da fuska, sannan muka jiyo alamun tashin muryarsu kasa-kasa, hakuri ya dinga bata kan cewa bai samu ganin likitan nasu ba, kuma har gidanshi yaje, amma ko zata daure su tafi asibiti yanzu? Ta wani lankwashe murya kamar wata yarinya karama, tana cewa ai ita so tayi ya zauna kusa da ita kawai, bata wani bukatar likita.
Nayi kokari na danne dariyar data kusa kamo ni, irin wadannan ‘cheesy lines’ din ai nayi zaton a films kadai suke amfani da novels, ba a ainihin rayuwarmu ba.