ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Tayi nisa sosai cikin saqe saqe da tunani taji dumin mutum a bayanta wanda sam bata san lokacin da ya shigo din ba,a zabure ta miqe zata sauka ya damqeta da hannu daya
”kiyi a hankali kada ki fama ciwon naki”ya fada cikin salon rainin wayo,kasa motsi tayo abdallah zai kasheta kam wallahi,sai kuma ya hade rai
”kikaci gaba da kuka zuwa anjima idanunku zasu kumbura,kinga idan anzo dinner sai ki tanadi amsar basu”ya miqe tsam daga gadon ya fice abinsa adakin bako waiwaye,ajiyar zuciya ta saki,sai da ya fita din sannan taji kamar ta bishi ta rufe da duka,gaba daya ma shi babu abunda ya shalleshi,babban isue da ya kamata ace yana cikin rashin nutsuwa amma ko a jikinshi.
????????????????????????
Bayan ta kammala sallar magariba mami ta shigo
”yaya maryamu jikin,dinner din zai yiwu kuwa?”
kanta a duqe ta amsa mata da eh don kawar da zargin da mamin keyi na wani abu ya faru da ita,amma a zahiri ba don wannan zargin da mamin keyi ba da cewa zata yi bazata iya zuwan ba,saboda har yanzu zuciyarta cikin qunci take,nan mamin ta sakata ta shiga tayi wanka duk cikin dakin,mai makeup ta tadda na jiranta,hakanan tanaji tana gani ta zauna aka zuba mata kwalliya ta gani ta fada aka sata ta shirya cikin wedding gown irin ta larabawa fara tas mai dige digen adon zaiba kadan kadan,rolling aka mata sak irin na larabawan wanda iyakarsa saman qirjinta,hill shoes shima da earings sarqar hannu data qafa duka ruwan zaiba ne.
Kada kaso kaga kyawun da maryam din tayi,kusan duka cikin event din bikin da suka gabatar wannan itace shiga mafi kyau da tayi.
Tana zaune nan cikin bedroom din shiru kamar yadda mami ta umarceta,qofar taji an turo wanda kafin ma ta daga kanta taga waye qamshin turaren data jiyo ya sanar mata,saboda haka taci gaba da dauke ganinta daga bakin qofar,tsayawa yayi kawai ya zuba mata ido cike da sha’awa da burgewa,tayi masa kyawu fiye da tunani,bai qara amanna da kyawun da Allah ya bata ba irin yau,kasa controlling din kanshi yayi ya miqa hannunshi da nufin shafa lebenta da yaci jambaki maroon colour,har ya kusa da ita kome ya tuna kuma sai yayi saurin janye hannunsa ya daidaita nutsuwarsa hadi da cunkushe fuska
”ki tashi muje mu ake jira”
sai a sannna ta daga kai ta kalleahi cikin sakannin da basu wuce uku ba ta qare mishi kallo
eh yes ta yadda abdallah mai kyau ne,sanye yake cikin jacket mai bala’in tsada da kyau fara tas da ita komai nashi farine idan ka cire necktied dinshi takalmi da agogonshi duka ruwan zaiba kalar nata shigar sak,kau da kanta gefe tayi don bata son fiya hada inuwa da mutumin da ya yiwa rayuwarta karan tsaye
”kayi naka wuri nima nayi nawa”sunkuyowa yayi saitin fuskarta har numfashinsu na gware
”kin manta a idanun duniya mu masoya ne da mukayi auren qauna,qwarai ni airen qauna nayi amma ke da aka yiwa auren dole na fada miki dole ki ari acting na ma’abota so ki dorama kanki matuqar kina buqatar cikar burinki,wannan ne magana ta da ke na qarahe,harshe na ya gaji da yi miki tuni”
Kanta ta sake kaudawa ta yadda babu yadda zai iya ganin hawayen dake qoqarin fita a idanunta,cike da zafin rai tace
”saidai kayi dukkan abinda kaga zakayi,kaga,nifa na gaji da wanna game din naka,kawai ka sallameni a yanzu na san inda dare yayi min”
”idan anqi fa?”
ya fada bayan ya miqe tsaue ya goye hannauenshi a qirjinsa yana leqa dan qaramin bakinta dake raahin kunya
”tilas ma ka sakeni tinda nace bana so bana yi akai gaba wataqila asamu mai tayawa”
Yaji zafin maganarta amma son biye mata balle a gamu da matsalar da tafi ta baya
”lallai kam yarinya wuyanki yayi kauri,naga alama kinga makwancina da yawa,don kin samu kamar ni abdallah na nuna sonki har na aureki kikeda bakin fadin haka,kinsan kalan ‘yammatan dake rububi da fatan na zame musu miji ba tare da aisin kwabo na ba ma?”
A sukwane ta juyo tamkar mai jiran ya gama fada,ido cikin ido tace masa
”ni ba irinsu bace,na sha ban ban dasu nesa ba kusa ba,baka yimin ba sam ko kusa ko alama,kuma na fada na gaya maka bana sonka bana buqatar igiyar aurenka a kaina,ka ssakeni mana dole ne,kaje ka auri masu rububin naka,idan ka taya akace ba’ayi ai sai ka matsa ga masu yi inda kake da muhalli,bawai ka tsaya ka nace a inda babu muhallinka ba”
Mamaki kam kusan kasheshi yayi a tsaye,gadan gadan ya nufota yana fadin
”ba irin mu mace ke kalla kai tsaye tace bata son mu ba duk isarta da tsadarta,bamu cewa muna so ace ba’a son mu,ni abdallah na miki alqawari sai na azabtar da zuciyarki da kalar soyayyar da baki taba yiwa wani da namiji irinta ba”bai bata damar furta komai ba ua sirute gaba daya ita da wedding gown din nata harda ‘yar purse dinta marching na kayan,dike doke da zille zille ta fara tana fadin ya saketa ita ba ‘yar iska bace yana sauka daga step din benen zuwa falon mami na qasa yana fain shi kuma tantirin dan iska ne sai yaya kenan?
kafin su qaraso falon tuni ta soma jiqa fuskarta da hawaye,ajjiyeta yayi saman kujera ya dora qafansji daya saman kujerar kusa da cinyarta yana huci kadan kadan,sai da ya gama qare mata kallo kana ya bude ‘yar jakarta dake hannunshi yaci sa’a kuwa ya samy tissue turare da powder,cirosu yayi ua cilla mata
”ki gyara fuskanki nan da minti biyu”
cikin muryar kuka tace
”idan naqi fa?”
wani dan gajeran qayataccen murmushi irin na gefan baki yayi idanunahi sun kada sunyi ja don ta soma bashi headach bai taba fuskantar irin wanna trouble ba daga gun mace,idan suka botsare basu da dadin sha’ani saidai ka bisu ta yadda suke so ka ka musu jan ido.
”meyi baya fada,kiqi yin kiga mai zai faru a aikace kinga ai yafi dadi akan na fada miki da baki”ya sauke qafanshi ya nufi fridhe ya ciro sassanyar ruwan swan na madaidaiciyar roba ya soma daddaka,sai da ya shanye tas ya juyo inda take,tuni har ta gyara atsoronta na kada ya hanata takardarta,tamkar ya qyalqyale da dariya sai kuma ya maze yasha mur
tana shirin miqewa ya hangi igiyar takalminta ta kwance da sauri ya duqa don daure mata zata ja baya ya riqe qafan gam ya soma daure mata,lokacin mami ta ahigo tana fadin har yanzu basi fito ba me suka tsaya yi ne?,yanayin data gansu ya matuqar burgeta ta sake amanna da soyayyar dake tsakaninsu,tayi murmushi tana tunanin tana tsakiyarsu basu taba nuna mata soyayya suke ba saima fada kullum ashe ninketa suke baibai.
Compound di ya cika babu laifi da jama’a,wanda kusan rabinsu duka ‘yan uwane irin mugun na jikin nan sai daidaikin maqota da abokai,tayi mamkin yadda adan taqaitaccen lokaci irin haka ma aka tara jama’a mai dan dama har haka,ko ina ka duba gurin walwali yake da decoratiom na farin yadi da wasu fararen fitilu,komai na gurin fari ne hatta da kayan mahalarta taron farine
tayi mamaki da ganin raliya da nasir lubabatu qanwarta batulu harda hindatu da jabir,to wama ya gaya musu wa ya gayyacesu?,daga sashi guda kuma nene ce da adnan sai zahariyya,idanun zahariyya da nene na kan abdallah duk wani motsi nashi suna ankare da shi,fatansu daya suga mummunan sauyi tattar da shi,yayin da adnan ya tattara nashi ma mujiyar kan maryam wanda babu abinda yake sai aukin hadiyar yawu,cikin zuciyarsa yana yiwa nene Allah ya isa da ta hanashi mallakar maryam din har abdallah ya sameta,gefe guda kuma yana tainewa abdallahn yana fadin duk taurin ranshi ne ya jawo,amma yaci alwashin da zarar burinsu ya gama cika kota tsiya kota arziqi sai ya mallaki maryam din,ko nenen na so ko bata so,kai baiqi ya kawar ma da duk wanda zaice zai kawo masa cikas ba,zubaida na gida nene ta qulleta cikin dakinsu kana ta qullen bangaren ma baki daya,ta rantse ta maya babu inda zata fito har a watse.