ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Sam taqi dubansa,hidimad gyara gurin da suka kammala cin abinci kawai takeyi,ya san tana sanen rayi haka
”idan kinsan wata baki san wata ba yammata,duk abunki sai na dan more kan na tafi”ya fada cikin zuciyarsa yana danne danne waya,kansa ya dago kamar wanda ya tuna da wani abu da gaske ya dubeta
”af,maryam,taimakamin ki dauko mim wasu takaddu cikin cupboard please”kamar ba zata je ba haka taji saboda kunyar idon mami amma sai taga mamin ma ta sauko daga kan dining din ta koma cikin falo tayo zamanta kan kujeru,ba tare da tace komai ba ta miqe ta nufi inda ya aikata din.

Ta kusa aqalla minto goma tana dube dube cikin dakin nasa amma sam bata ga abinda yake fada din ba,dole ta juyo ta fito don ta sanar masa,a kusa da maminta tadda shi yana zaune yana nuna mata abu a waya,ta dan rusuna kadan”ban gansu ba”tace da shi,ba tare da ya dago ya dubeta ba yace
”ki sake dubawa dai da kyau,suna nan ciki ko locker din mirrow dina”a yanzu kam jikinta ya fara bata aiken bogi ne,don iya dubawa tq duba ko ina din,amma sabida bata son musu yasa ta miqe ta koma.

Ko minti biyu batayi da komawar ba ya dafe kai yana fadin
”af,na manta asge na sauya musu gu shi yasa ta kasa ganinsu,bari naje na dauka”ya fada yana satar duban mami,bata ko dubeshi ba har ya miqe yayi hanyar dakin,binsa tayi da kallo tana murmushi can qasan ranta tana fadin”dama ai bazan hanaka kebewa da matarka kuyi sallama a abdallah”,tattare itama ya nata ya nata tayi ta haye sama abinta

A hankali cikin sanda ya tura qofar dakin ya shiga,tana duqe ta duqufa neman takardu
”har yau maryam ke yarinyace na yarda da hakan ba wuya a miki wayo”ya fada cikin xuciyarsa
jingina yayi da qofar ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta son ranshi,sai datq gaji da dubawa kana ta dago,ta juyo da niyyar fita amma hankalinta na kan gado tana dubawa ko nan ya ajjiye,dalili kenan da yasa bata ganshi ba har sukayi karo,baya ta ja da sauri,tana yarfe hannunta tace
”na duba ko ina ban gansu ba nikam”.

Hannun nata ya kama yana fadin
”ba wasu takardu dama,son ganinki kawai nakeyi dama kafin nawuce,ma tabbata idan ba haka ba bazaki bari na ganki din ba sai a gaban mami”
so take ta qwace amma ya gwada mata qarfi irin na ‘yan maza sai da ya kaita gefan gado ya zaunar da ita kana yayi tsalle ya fada gadon,kwanciya yayi ruf da ciki,kanshi ya dora saman cinyarta ya saka hannayenshi ya zagaye qugunta,ya gama kanainaye jikinta bata da ikon motsi
”ummm,baby,har yau bansan matsayina a gunki ba baby kin barni cikin duhu fa?”ta dan hadiye wani abu,yana nufin yace har yau bai fuskanci komai daga gareta na ko so yake sai ya qureta ya sata fadin abunda bata yi niyya ba
”ka riga da ka san matsayinka tuni a gurina ba tun yau ba”shiru ya danyi kana yace”na riga ni kuma da na manta baby,pls ki sake gayamin”.

Shiru ta sake yi don ya sakata cikin kokwanto biyu,idan ta buda baki abinda duk zata gaya masa ta tabbatarwa kanta qarya take a yanzu,idan kuma ta fadi gaskiyar wanne kallo zai mata,jin taqi cewa komai ya saka shi juyowa da sauri ya koma rigingine duka akan cinyar tata yana kallin fuskarta,sai tayi saurin runtse idonta,murmushi yayi ya saka yatsanshi ya lakace mata hanci
”yar qauye kawai,shi kenan tunda kin barni cikin duhu,idan kuma na mutu kafin na dawo burinki ya cika kenan ko?”
bata san lokacin da ta bude brown oily eyes dinta ta watsasu cikin nashi ba tana zazzaro su,shima kallon nata ya tsaya yi can qasan zuciyarsa wani sanyi na ratsashi
”mutuwa kum….”sai ta kasa idawa ganin yana sake fadada murmushinsa yana lumshe ido,idanun nata ta sake ja ta rufe ba tare da ta qarasa din ba
”a hakan ake so ace ba’a sona?,bansan lokacin da kika koyi yima kanki da kanki qarya ba”.

Bugun zuciyarta ya qara gudu jin yadda ya kama tafin hannunta yana mata tafiyar tsutsa,wani abu take ji yana bin jikinta,da hanzari ta janye hannun ba tare da ta bude idon ba,yana qoqarin sake kamowa tace
”ka bari,ba dadi”
”da dadi”ya fada cikin wara iriyar murya
cikin lokaci qanqani gaba daya yake son burkita mata tunani,hot kises ya dinga aika mata da su wadanda bata taba koda kin labarin irinsu ba,romancing dinta yake sosai kamar ba abdallah,duk da jikinta na amsar saqon amma a tsorace take matuqa hakanan bakinta bai mutu ba da fadar kalmar ”ka bari abdallah,bana so,ka bari don Allah”
ko kadan bai saurareta ba sai da ya ragewa kansa zafi,kallonta yayi idanunshi sun juye tamkar bugagge muryarshi ta koma can qasa sosai,a rufe idanunta suke gashin kanta da ribbom din ya dade ta zamewa ya warwatsu har fuskarta,wata kasala yakeji sosai a jikinsa don haka ya koma ha kwanta kamar dazu kanshi bisa cinyarta kwanciyar rigingine yana maida numfashi.

A hankali ta dinga bude idonta kamar mai tsoron cin karo da wani abun,ta dube abdallah dake kwance daidai kan cinyarta,idanunsa na a rufe numfashinsa na sauka a hankali,ta rabbatar bacci ne ya daukeshi,so take ta miqe amma ta kasa saboda gaba daya ya sakar mata nauyinsa,sai ta miqa hannunta ta dauki ribbom dinta ta hada gashinta guri guda ta dauki dankwalinta ta mayar,fuskarsa taci gaba da kallo,wani kyau baccin yayi masa sosai kamar ba mai bacci ba.

Ta riga ta yarda kyau kam Allah ya bawa abdallah shi,irin kyawun da ba kowa Allah ke azurtawa da shi ba
kusan awanni daya da rabi ya samu yana baccinshi tana zaune tamkar mai gadinsa duk motsinsa na kan idanunta,a haka taji an soma knockong qofar,ta fara qoqarin tureshi daga jikinta jin muryar mami ne amma qememe yaqi,tamkar ma yana sane sai ya sake kanannadeta abinsa yaci gaba da baccinsa,a hankali mamin ta murda qofar jinta abude yasa ta dan turo kadan tana sallama,amsa mata maryan tayi sai ta leqo da kanta,karo na biyu ta soma yunqurin maida shi gefe ta kasa cikin jin kunya,murmushi mamin ta mata kana ta mata alamar tayi shiru ta zauna kada ta tasheshi ta ja qofar ga rufe musu,ta sake kallon fuskarsa gumi taga yanayi duk da sanyin rabar dake dakin,tattausan tafin hannunta ta saka tana share masa tare da hura masa iskar bakinta,caraf taji an kama hannun naga an riqe,tsoro da kunya suka kamata sai tayi wuri wuri da ido,ya bude idonsa a hankali ya sumbaci hannun kana ya tashi zaune yana ambaton ”la’ilaha illal lah muhammadurrasululluh sallallahu alaihi wa sallam” yana miqa

ya dubeta tana qoqarin miqewa yace mata
”sannu baby am sorry na danne miki cinya ko”bata ce komai ba tana qoqarin fita cikin zafin nama ya rigata isa bakin qofar ya saka key ya qulle,ta kalleshi cikin alamu na tambaya kafin ta furta tambayar ma ya bata amsar
”babu inda zaki je,idan kinga kin bar dakin nan nazo tafiya ne”sai ta bata fuska kana tace
”to waishin ma ni matarka ce?,bayan kace temporary ne”
girarsa ya dage kana yace”yes har yau matata ce ke,dole kici gaba da yimin abinda nakeso kafin lokacin da maryara zata iso”kasa magana tayi shi kuma ya zare key din ya jefa aljihun three quater dinsa
”daga tashina a bacci kinsani magana my mero”,jin ya ambaci sunan meron ua sake hasalata
”ai ba meron bace,sabida haka kada ka sake kira mana sunanta,kayi qoqari mu rabu lpy”shikam da yar qaramar dariyarsa ciki ciki ya zari towel dake saqale kan murfin cupboard ya shige toilet

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button