ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

A darare take zaune gefan gado tana bin dakin da kallo a haka ya fito ya sameta,da sauri ta dauke kanta don yaune karo na farko data taba ganinsa haka,rigar wankan jikinsa ya kunce zaren dake riqe da ita ta fadi a gun ya zama daga shi sai gajeran wando,cikin qunquni tace
”nikam naqi jinin rashin kunya”
a hankali ya tako gabanta ya durquso inda take a zaune har tana jin qamshin sabulun wankanshi da ragowar dumin dumin ruwan da yayi amfani da shi
”me kike fada?”ya tambayeta da wata iriyar murya ta daban,baya ta dan ja tana sake tsuke fuska don kusancin nasu yayi yawa
”nikam babu abinda nace”dagowa yayi yana dariya
”da kin sake kin maimaita yarinya yau da kinga yadda ake ruwan rashin kunya,yau da saidai mami tayi jinyarki ni kuwa na gudu abuja kinga ko fada ba zata samu damar yi min ba”sarai ta fuskanci me yake nufi,wai gabuntar dan fari ke damun Abdallah ko tabarar auta?,ta rasa wanne ne daga ciki,sai kuma ta tuna cewa itama ‘yar farin ce take ta bawa kanta amsar saidai tabara ce kawai irin ta auta.

Babu wanda ya sake cewa dan uwansa komai har ya kammala shiryawa,itakam sai dauke kanta kawai tayi wani sashen don harkarsa yake kamar shi daya ne cikin dakin,wannan karon ma t.shirt din ya sanya saidai baqa ce long sleeve haka ma three quater dinashi baqine,wani kyau suka yiwa farar fatarsa,ya fesa turarrurrukansa,ga tunaninta ta dauka zai bude musu qofa ne su fice sai taga ya soma sauko da wasu tsadaddun akwatuna baqaqe masu kyau qana nan set ne guda uku ya ciro biyu babban da qaraminsu ya ajjiyesu
”bismillah madam,a hadamin kayan tafiya”ya fada yana dauki pillow daga saman gado ya jefar a saman rugs din dakin ya kwanta rub da ciki yana kallonta
”ammafa mami tazo nemanmu dazun kana bacci”,girarsa ya dage
”ba matsala nasqn ba wata damuwa bace indai mami ce,bamu da damuwa da ita” qi tayi duk don ua qyaketa ta fita hakan yasa ya janyo wayarsa ya kira mamin ya tambayeta
”a’ah,ba wani abu ne,dama baqi ne suka zo matan baffa salisu ne kuma sun tadda kana bacci,har mun gaisa ma sun wuce sauri suke suna zasu”
”ok mami”ya fada ya katse wayar yana duban qwayar idonta
”sarkin kuka,komai kuka komai kuka,bayan qiri qiri baki da gaskiya”ya fada cikin zuciyarsa yana murmushi,bai ce mata komai ba har ta gaji da kallon da yake mata ta miqe ta isa ma’ajiyar kayanshin don yanzu kuma bata da wata dabarar ta kubce masa.

Tsaye tayi a gun,ta rasa ma wanne zata dauka masa,kaya ne bila’adadin iya ganinta,a sanyaye tace
”wanne da wanne zan dauka maka”
”na baki zabi,nikam,bani da ta cewa”ya fada yanajin dadin yanayin da suke,ji yake kamar ya riqe lokaci suyita zama a haka,a hankali ta dinga zaban kayan tana shiryawa cikin akwatin,tsit dakin yayi lokacin da take aikin,duk wani kotsinta yana binta da ido don,ba qaramin burgeshi take ba,komanta cikin nutsuwa,ta gama da suite suite ta saka masa yadi biyu shadda biyu tunda tasan tafiyar tasa majority sai yafi amfani da suite din,sannan ta saka masa na shan iska,ta kammala ta rufe qaramin kuma ta saka masa sauran tarkace na buqatar yau da gobe,shi kansa yanayin yadda ta tsara masa kayan ya burgeshi qwarai,komai a tsari,ta gama shima ta zuge tana fadin
”an gama”,sai da ya lumshe idonsa ya bude kana yace
”thank you verry much,shukran jazilan”
ya tashi ya zauna soasai yana fadin
”bari na qarasa daya nau’in godiyar ko”kafin tace komai ya jawota jikinsa,irin saqonnin dazu ya fara aika mata har suka so sufi na dazun zafi,nauyin da saqon nasa ya mata ya sata sakin kuka amma bai fasa ba don yana jin shine hanya daya data rage masa na samun sauqin abinda yake ji cikin zuciya da gangar jikinsa.

Kukan wayarsa ne ya ceceta,da qyar ya iya miqa hannu ya dauka,sunan mami ya gani na yawo ya daga kana yayi shiru
”abdallah,maryam tayi baquwa fa”bazai iya magana ba don yasan da yayi din tana iya harbo jirginsa don haka yace
”uhmmmmm”tuni ma ita ta kashe bata jirayi amsar sa ba,ya dubi maryam da ta dunqulr guri guda,duk da abinda yake ji sai da ta bashi dariya,sai kace wanda yake shirin yin mai gaba dayan duka ta wani tsure
”raguwa kawai,abinda baikai ya kawo ba kin gaza daukeshi”ya fada yana miqewa itakam ko daga kai ta kalleshi bata iyawa saboda azabar kunya haushi da tsoro
ya fito yana tsane jikinsa har yau tana nan inda ya barta,wayarta itama ta dauki tsuwwa da sauri ta daga hindatu ce ke kiranta
”adda maryam,jiran kusan minti arba’in”
tayi qoqarin daidaita muryarta saidai duk da haka a sanyaye take
”gani nan hindatu”ta kashe wayar ta miqe tana daidaita kanta

Sai data juya baya kana tace cikin cool voice
”bani key din zan fita ana jirana”
”dubeki,a hakan zaki fita,shiga toilet kiyi wanka”
ido ta zazzaro duk da bata kallonshi,kamar yasan zaro idon tayi kuwa yace
”eh,ko ba zakiyi ba kije ki daura alwala muyi salla azahar tayi mu samu ladan jam’i nasan yanzu masallaci sun riga da sun idar”
son fitar take don haka ta koma ta daura alwalar,kaya ta samu ya ajjiye mata da ido ta dubi kayan ya fahimci tambaya take
”ki sauya kaya na jikinki sunyi squeezing da yawa ko”ya bata masa ba tare daya dubeta ba,ba musu don itama ta yarda haka dinne ta debi kayan ta koma toilet ta canza ya jasu suka bada sallar azahar,suna idarwa ko ko addu’a bata tsaya yi ba ta dauki key din dakin da ya dora sama dressing mirrow,shima baice komai don yasan yau kam ya samu dama mai yawa,binta yayi da kallo har ta fice

A falo ta taras da hindatu da mami nata hira abinsu kamar wadanda sukayi shekara da sanin juna
”sai yanzu adda maryam har ina shirin kkmawa inda na fito”inji hindatu da sauri ta mata alamar don Allah tayi shiru don hindatu qanwar abdallah ce yanzun ta bata kunya,ashe mamin ta kula suka hada ido kunya ta kamata,sai yanzun ta gane wayo wato abdallah ya mata da ya sata canza kaya,tunda mami ai zata iya gane ba da su ta shiga ba,mamin gwanar kawaice da basarwa sai kawai ta miqe ta koma samanta ta basu gu
ajiyar zuciya ta saki tayi harr da idanunta,hindatun dai tace
”ko kunya bakwaji adda maryam,kubar mamanku zaune ita daya ku qule daki kuna cin soyayyarku”ido ta zare mana
”yi mana shiru mara kunya ‘yar lukuta kawai,wai hindatu haka kika koma?,kina kallon kanki a madubi kuwa,lallai jabir shima da shi da ya barki kika yi qiba irin haka”
dariya tayi”ni da shi duka bamu ganin qibarmu,amma kowa sai ya ce mun zama ‘yan lukutaye ni da shi”
”eh gaske”maryam ta fada tana kallon hindatun yadda ta koma,tayi bul bul ta sake zama fara,hira tayi hira qarshe ma dakin,maryam din suka koma,sai da suka shafe aqalla kusan awanni biyu suna hirar yaushe gamo.

Har kusan qarfe uku na rana suna hira kafin tayi haramar tafiya,a falon suka sake taras da mami hannunta dauke da poil paper ta nufi dakin abdallah hindatu tayi mata sallam,cewa tayi ta jirata ta koma sama ta dawo dauke da turaruka ta bata,hannu bibniyu hindatu ta amsa ta mata godiya kana maryam ta rakota.

Wata sabuwar matrix ash colour taga ta saka muqulli ta bude,baki maryam ta kama
”ah,lallai yarinyar nan jabir na shagwabaki,yanzu shikam ya yarda ya bawa hindatu mai shegen rawar kai mota take ja?”dariya hindatu tayi
”kai adda maryam,an girma da yanzu,idan da rabo ma nan da wata bakwai sai kizo suna”
duka ta dan kai mata
”eh lallai hindatu baki da kunya,laifin jabir ne”sai da ta shiga cikin motar ta zauna kana tace”zan biya gida fa na gaida mama,me zan ce mata?”take kewar gidan duk ta kamata,tana son taga mamanta sosai,watanni kusan nawa ta share rabonta da ita,tun ranar da aka fiddota zuwa fidan mijinta
”kice ina gaidata sosai da sosai,sannan nima ina nan zuwa”
”amma adda maryam duk ranar da zaki din zaki biyo min ko don Allah”ta fada taba yin kalar tausayi duk don tazo mata din,murmushi tayi
”kai hindatu”
”eh mana,baki fa taba zuwa min ba adda”
”to naji,zanzo insha Allahu”
”yauwa adda ta”ta fada tana dariya ta eufe murfin motar kana ta tada ta taja,bata bar gurin ba tsayawa tayi taga irin driving din hindatun,sai da ta fice a daga gidan kana ta saki yar qaramar dariya tana girgiza kai
”hindatu,hindatu”abinda ta fada kenan cikin zuciyarta ta juya ta koma cikin gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button