ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Awa daya tsakani ta sake jiyo innar
”ki fito ki lallabe min kan nan tunda ba zaki ci abincin ba,inaga azumin yammaci zuwa dare kika fara”
abdallah ya kalli innar qasa qasa yace
”inna dama bata ci abincin rana ba?”
baki ta tabe
”ina fa taci ta dorawa kanta nunqufurci”
ya marairaice fuska kamar yqdda yakewa mami idqn yanason wani abu
”amma inna banda zama da yunwa fa”
”qyale shu’uma,cikinta ai da kanta zata nema idan yunwar ta rarakota”
kai ya kada yana jin ba dadi cikin zuciyarsa
”a’ah inna”
”ka qyaketa nace bawan Allah,ai ba wani ya hanata ci ba”

kwanukan ya dauka ya danna kekansa ya nufi dakin,a kwance ya taddata,amsa sallamarsa tayi tana qoqarin boye hawayen fuskarta don kada ya gani,ta miqe tana gyara hijabin jikinta zata fice a dakin
”dawo ki zauna”taji ya fada,haushinsa take ji fal cikin zuciyarta don haka ta masa shiru,taku biyu ta qara ta sake jin muryarsa mai cike da dakewa da kwarjini
”zan saba miki idan kika sake koda taku guda”cak ta tsaya kana ta dawo da baya tayi zaune kan ledar dakinta bayan ta cusa fuskarta tsskiyar cinyoyinta,keanukan ya tura mata
”dauki ki cinye banason inga komai cikin kwanon”ba tare data kalli kwanon ba tace
”bana ci na qoshi”
”tunda bakici ki fadi me kike son ci?”
”na qoshi nace”
”baki isa ba”ya fada kanshi tsaye,yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata da gaske har cikin zuciyarsa bazai barta ba sai taci

”me zaki ci nace”ya kuma tambayarta cikin dakewa da ginshira
”fura mai kwakwa da shawarma”tana sane ta fadi hakan don tasan mawuyacine a nan a samu abinda ta fada din
baice komai ba ya danna keken ya fice

Awa guda ya dawo da baqar leda
”karbi kici”taji yace da ita
ta miqa hannu ta amshi ledar fuskarta a qunshe,ga mamakinta duk abinda ta lissafa din ne a ciki
babu yadda ta iya haka taja ledar ya tasata a gaba da zazzafan kallonshin nan yace a gabansa zata ci
sosai ta bata masa lokaci duk don ya gaji ya fita amma sai ta lura baiko damu ba gyara zamanshi yayi ma,tamkar ma nishadi yangarta da zaunar da shi din da tayi take sashi
duk motsin da tayi idanunshi na kanta musamman dan qaramin bakinta mai dauke da pink din lips dake motsawa yana rauna shawarmar cikin rashin son cin abincin,wani abu ya darsa cikin zuciyarshi wanda ya sashi limshe idanunsa,ji yake kamar ya kamaau ya tsotsesu tas,wani,barin na zuciyarsa ke gaya masa loka cine

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

       5⃣2⃣

Manzan Allah S A W ya hana bacci bayan sallar magariba haka nan ya karhanta zance/hira bayan sallar isha’i

daga nana Aisha R A tace na kasance ina wanke janaba daga tufafin Ma’aiki S A W sai ya fita sallar asuba da tufafin alhalin akwai ragowar danshin ruwan a jiki

a wata ruwayar ta muslim kuma yace nana aisha tace”na kasance ina kankare janaba daga tufafin Manzan Allah S A W (kamar busashen maniyyi kenan)sai ya saka ya fita salla da tufafin

wannan shafin sadakarwa ne gareki dungurun gum baki dayansa SADNAF bama ke kadai ba har da ‘ya’yana AFFAN DA IKRAM Allah ya rayasu ya yiwa rayuwarsu albarka,Allah ya bar zumunci

Idanunsa suka sake sauka kam yatsunta da take gutsirar shawarman da ita,yanayin yadda take ci kawai ya isa ya gaya maka kan tilas take ci din,don dama asalam ba cimarta bane da biyu tace ita don take so ga zatonta basai samo ba
ba qaramin kyau suka yi masa ba,kasancewar yana gan da ita yasanya ya kamo hannunta
”yaushe kika yi wannan abun?”
ya fada yana kallon qwayar idonta,sai ta soma qoqarin zame hannin nata ba tare da ta bashi amsa ba
”maryam”ya kira sunanta can qasan maqoshi kamar maijin barci,nan ma bata amsa masa ba ya kuma fuskanci bata da niyyar amsa masa din,sunkuyo da kanshi yayi ya tura yatsunta guda biyun cikin bakinshi ya soma tsotsa a tausashe har yana lumahe iso tamkar wanda ya samu wani abu mai dadi

wani irin abu ta dinga ji yana tsirga mata tun daga tafin qafarta har qwaqwalwarta,take jikinta ya mutu baki daya hakanan ta rasa kuzaron hana shi sai idanunta ma da taja ta rufe tana ajiyar zuciya qasa qasa

A hankali ta bude idanunta jin ya daina shan hannun,wata iriyar kunya ta kamata kamar qasa ta tsage ta shige,ashe ita ua zubawa idanu tana kallonta bata sani ba
”uhmmm,madam,zan iya ci gaba?,na kamar kema kina enjoying ko?”ya fada yana kashe mata idonsa na hagu,bata san me zqtq ce ba don ya gama kunya tata saboda hakq kawai saita fara hawaye tare da qoqarin zame hannunta saidai ko daya ya janata ya kama hannun ya riqe tsam ya kima zuba mata mayun idanunshi har tayi mutsumutsinta ta gana tq bada kai ta hanyar haqura tayi qasa da kanta kawai

Hannun ya sake mata bayan ya gama kallonta iya son ranshi,jikinsa gaba dayq ya gama yin laushi muguwar kasala ta lullubeshi
”ta yaya zan iya wanka qarfe takwas na dare,kinga ina zaman zamana kin jawo min ko?”
rasa inda zata tsoma ranta tayi,sam abdallah bai da kunya kwata kwata,lamuranshi yake gaba gadi,ko ita qaramar yarinyace ai ta gane abinda yake nufi bare da hankalinta
”ka jawowa kanka dai tunda bani na kirawoka ba”ta fada can qasan maqoshinta
”erhmmm,me kike cewa?”ya fadi yana matso da kunneshi,shaf ta mance yadda abdallan ke da shegen ji kamar maciji

”najiki sarai abinda kika fada,amma ba komai Allah zai saka min,nima na kusa aure in sha Allahu nan kusa na huta”wani abu ne ya takareta har batasan lokacin da dago kanta ba bayan ta dubeshi tace
”toni me ruwana,idan ka tashi ka aure matan duniya ma baki daya sannan ne zansan ka cika jarababben ma…….”sai ta kasa qarasa fada saboda nauyi da maganar tayi mata da kuma yadda ya tsatstsareta da mayun idanunshi wanda bai gajiya da kallonta da su

ta cukuikuye hijabinta gu daya ta miqe da sauri zata fice adakin,hannu daya yasa ya fincikota atausashe sai gata gabadaya ta fada saman cinyarshi
”babu inda zaki sai kin qarasa fadar abinda ke ranki”
kai ta girgiza gabanta na faduwa cike da danasanin fara furta maganar
”na gama magana ta ai”
”qarya kike,akwai saura”batasan sanda ta rantse ba
”wallahi babu”
”ummh,sanannan ne zaki san na cika jarababben mayen mata ko?,dama can ni mauen mata ne ai ko kin manta?idan baki sani na kuma to kibi a hankali don ta kanki zan fara maitar tawa kafin na sallameki”

tamkar tace wayyo Allah haka taji,kansu sake cewa komai an dago labulen dakin,mairo ce riqe da laptop din abdallah
”yaya abdullahi wai meramun kitson da….”sai ta kasa qarasawa sakamakon ganin maryam din kwance kan cinyar abdallahn,shi kuma ya mata rumfa da faffadan qirjinsa,hakanan sai maryam din ta samu kanta da sake narkewa kan cinyar abdallahn ta saki jikinta tare da saka idanunta cikin naahi sosai abinda bata taba yi ba,hakan yasa ya kasa daga idonshi ya kalli mero din baison yayi missing kallon kyakkyawan oily brown eyes dinta ba dake matuqar jan hankalinshi,ganin ba wanda ya dago ya kalleta yasa sakin labulen bayan ta ajjiye masa laptop din ta fice a dakin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button