ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

wasu cikin yaransa masu wayon ne wadanda baiwa kafi ba suka haura can hayinsu don nemo jama’a don su kam,basu da maqota daga su sai ginakin dake kusa da su,kimanin awa guda sai gasu sun dawo jiki a sabule don ko kare bai yarda ya biyosu ba balle bil’adam,qarshe ma jama’ar qauyen hayin nasu bigewa sukayi da farinciki kowanne gida suna taya junansu sam barka na mutuwarsa,don ba qaramin tsanarsa sukayi ba,dalili kenan da yasa ya baro cikinsu ya dawo hayin ruwa

Kafin cikar awa uku da mutuwarsa saiga gawa ta fara kumbura tana fidda wari mai azabar doyi da wasu irin tsutsotsi,hakan ya sanya kowa ya fara hada karonsa dom gujewa muhallin nasa,tawagarsu guda suka yo qofar gida kowacce cike da zulumin kada fa su rasa hanya kamar kowanne lokacin,saidai cikin ikon Allah yau kowa idonsa abude yake tar,dukkan wani duhu ya yaye,hijabin da malam din ya sanya musu ya kau,kuka zahariyya ta fashe da shi zuciyarta fal da tsoron Allah tausayin kansu da kuma tausayim taragutsan yaran da malam din ya bari,yarane da basu ji ba basu gani ba,son zuciya irin na iyauensu ya jawo musu fitowa ta rubabbe kuma rusashshen taatso,kowacce iriyar rayuwa zasuyi a gaba oho?,ta dubi iyayen kana ta tsaya a gabansu tace
”ku dakata,ina da magana da ku”kowacce kuwa sai tayi tsam ruqe da hannun yaranta tana kallonta
”magana ce zan muku kan wadannann yaran wadanda son zuciya da bijeriwa Allah yasa muka sama musu uba wanda bai dace da su ba,wadan nan yaran haqiqa jarabta ce Allah ya hadamu da ita ko ince hukunci ne tun a gidan duniya da Allah yayi mana kan bijirewa umarninsa da mukayi,hanya daya ya kamata mubi wadda zamu nunawa Allah mun karbi jarrabawarsa shine mu ruqe ‘ya’yan,muyi musu kyakkyawar tarbiyya,don Allah don annabi kada mu barsu su lalace su zama kamar yadda ubansu yake,kada mu bari tarbiyyarsu ta gurbace kamar yadda ta ubansu take,kada mu bari su zama guba cikin al’umma,don Allah muyi iya yinmu kan rayuwarsu,yadda malam ya mutu kawai izina ce a garemu baki daya,kada mu bari wataran su zama silar da za’a la’ancesu a la’ance mu koda ta Allah ta kasance akanmu”
babu wadda jikinta bai mutu ba,haka suka mata godiya kowacce idanunta shabe ahabe da hawaye zuciyarta cike fal da nadama da dana sani tana kada kan yayanta saboda yadda warin cikin gidan ke fitowa waje tana kama hanyarta

A haka duka suka fashe saura ita da habiba,hannunta habiba ta kama tana fadin
”mu tafi zahariyya,nikam sai yadda Allah yayi dani,bani da kudin da zasu isheni naje har abuja,amma zan fara da zuwa katsina inda dangina suke,daga can nasan zasu maida ni gida”haka suka kama hanya suna tafe suna kuka,idan ka,gansu sai ka tsammaci,mahaukatane suka gudo daga gidan gajiyayyu

Da qyar habiba ta samu mai motar daya yadda zai kaita katsina bayan ya mata tambayoyi ya tabbatar ba mahaukaciya bace sabida dauda da yadda take buga tsami,don sai sukai sati basuyi wanka ba haka gashi ba suturar arziqi garesu ba,haka al’adar gidan malam ko ince boka na hayi take,shima driver din a boot ya saka ta bayan ya lafta mata kaya don kada passingers su ganta ko suji doyi su fasa shiga

Da qyar ta qarasa jikin get din gidan ta dinga bugawa,ibrahim daya daga cikin security din shi ya fara bude yar qaramar qofar gidan yana cewa waye,turus yayi ganin mace mai siffar mahaukata tsaye a gabansa,baki ta waahe jajayen haqoranta suka bayyana tana fadin
”yauwa ibarahim,sannu ashe ka dawo aiki”kai kawai ya gyada mata
”eh na dawo”
”nene na tana ciki kuwa”rai ya hade mata kana ya girgiza kai
”bata nan”
”to mami fa,hajiya bintu”
”tana ciki”sai ta fara qoqarin shigewa tana fadin
”alhamdulillah”tsawa ya daka mata kana ya tsaidata
”hala irin mahaukatan nan ne da ke gudowa daga turu ko”
sai ta dubeshi
”haba ibrahim,na kama sunanka din,na kama na nene,na kama na mami kuma kace min mahaukaciya,zahariyya ce fa,zahariyyan nene”cike da mamaki ya zuba mata ido,yakai a qalla kusan minti goma yana qare mata kallo kafin ya ganota ta hanyar idanunta,tab aikam ko giyar wake yasha bazai barta ta shiga ba,mutanen da suka so hallaka iyayen gidansa mutane na gari,haka kawai ta dawo ta sake wargaza zaman lafiyar gidan bayan sun samu nutsuwa da kwanciyar hankali,yarinyar da bata da mutunci,bazai iya tuna sau nawa tasanya hannu ta tsinka masa mari ba a matsayinsa na soja,ko ranar da zasu sallameshi ita da uwarta bai manta irin zagin,cinmituncin da suka dinga dura masa ba,wata yazo qarshe amma da suka tashi korarsa hanashi salary din watan sukayi,wanda hakan ya zama sanadiyyar rasa danshi(hmmm,ka shuka alkhairi dai sai kaga da kyau)

murna ta fxatonta zaice ta shiga sai taga ya hado gurar sama data qasa ya hadeta gu guda
”wallahi ko cewa akayi idan baki shiga ba mutuwa zakiyi saudai ki mutu,na baki minti biyar kibar qofar gidan nan,don duka ahlin nene yanzu basa cikin gidan nan,sun shiga duniya,kema gwara kici gaba da bin sahunsu”yaja qofar ya rufe,zubewa tayi a gun tana kuka haiqan don tasan bata da wani gata kuwa

minti biyar na cika ibrahim ya sake leqowa ya sameta zaune,baice uffan ba ya fara qoqarin ciro bindigarsa yana saitata a kanta
”bari na kasheki kinga an rage iri”habawa,kamar ba mai ciki ba haka ta dinga fella gudu har ta fita babban titi,tsayawa tayi tana haki da waige waigen ko ya biyo sahunta,daidai lokacin da motar gida mahaukata ke zagaye tana kame tababbun masu rangwamen gata dake yawo kan titi suna kaisu gidan mahaukata din basu magani bisa umarnin gwamnati,cikin sa’a kuwa suka hangota,ba bata lokaci suka mata tara tara suka damqeta suka cusata cikin motar,ihu take tanason ta subuce musu fadi take
”wallahi niba mahaukaciyya bace da hankalina,gidanmu naje aka biyoni da bindiga shiyasa na gudi titi”wannan surutan nata suka qara musu amanna kan mahaukaciya ce

????????????????????????????
Cikin kwanakin kusan babu abinda yake damunta illa kewar abdallahn ta kawai

Kewarsa take gaba dayansa bawai wani abu daban ba,don kusan bayan kowacce awa uku zai kirata ya debe mata kewa da daddadar muryarsa,mamar kowanne lokaci yauma suna maqale a waya tana kwance ta gama shirin bacci
”baby,anya kuwa zan iya cika kwana goma nan kuwa,na hisham zan baro na taho?”a shagwabe tace masa
”sabida me?,ka barshi kawai ka qarasa din”
”baby na gaza jurewa wlh,kewarki na son kasheni,bansan kuskure na tafka da na tafi ba baqarami ba sai yanzu,kuma yadda nakeji na tabbata kema haka kike ji”
”wata qila ma na fika”ta fada a hankali,kamar ya taka rawa haka yaji saboda farinciki,son da maryam ke nuna masa irin wanda yake fatan samu ne daga macen aurensa,bashakka shikam dan gatan mami da maryamu ne
sai da suka raba dare suna musayar zafafan kalaman qauna kafin suyi sallam

Da wannan damar mami itama tayi amfani ta samo mata masu koya mota har gida matar ke zuwa tana koyawa maryamun,a haka lubabatu ta nace har itama ta fara koya,cikin sati guda sai gashi maryamun ta fara qwarewa,matar kam jinjina mata tayi don lallai kam na qaramar basira take da ita ba

????????????????????????????

Tun jiya abdallah ya sanar da ita suna hanya in sha Allahu,saboda tsabad murna adaren kasa komawa bacci tayi,zama tayi ta dinga lissafe lissafen abubuwan da zasuyi a gidan gobe,tunda ba zasu shigo ba sai kusan magariba,har yace da yasan haka zata masa taqi komawa bacci da bazai gaya mata ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button