ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

A hanzarce ta miqe da gudu ta koma cikin bandaki gqulli,tsaye tayi jikin qofar bandakin,takaici ya sake cikata data bi jikinta da kallo,yanzun qila gwanin kallon mutane ya gama qare mata kallo,ta waiwaya ga babban madubin dake maqale a bangon bandakin ta kalli kanta,daga cinyarta ne kawai zuwa qirjinta a rufe amma ko ina na jikinta awaje yake,tuni qwalla ta cika mata ido,ta koma ta sake keqashi ta jikin qofar,yana kwance bashi da niyyar tashi,danne dannensa ma yake a waya abinsa
”idan zaki fito ki fito abinki,ni zuwa nayi mu gaisa kuma na tambayeki,ba abinda kike zata bane”yq fada yana sake gyara kwanciyarshi

taja baya da sauri din gani take yana kuma hangota ne,idan banda rainin hankali irin na abdallah a haka zata sake fitowa?,kuma haka ake shiga dakin mutum ba neman izini bakasan ma ya shigo ba
tana tsakq da neman mafita taji ana knocking qofarta,kafin ta kai ga amsawa taji muryar mami na fadin
”maryam,baki tashi bane?”
gyara muryarta tayi kana tace
”na tashi mami na farka tun dazun”
”ok to bude min”
rarraba ido ta fara yikamar wadda ta yiwa sarki qarya,gaba daya ta rude,abdallah so yake ya ja mata abin kunya,haka kawaj mami ta raba musu daki ta gansu kuma tare,ita ga towel a jiki ta fito daga wanka,ta matso jikin qofar sosai yadda abdallah zai iya jinta cikin rawar murya tace

”kaga abinda ka jawo mana ko,yanzu meye haka don Allah”
tana kallo shi yana dariya
”ni ban jawo komai ba,kwato ne ni balle kice idan an ganni a dakin za’a jefeni ko ayimin bulala,ki fito kawai ki canza kayanki ki bude mata”haushi ya qara kama ta ganin yadda ya maida abun ba seriouse ba,cikin qunan rai tace
”Allah ya sawwaqe wallahi na fito ka gani a haka”
yayi wani irin juyi yai ruf da ciki saman gadon yana fadin
”mu shekara a haka mana yammata”

”maryam,me kika ce?”inji mami,sai tsoro ya sake kamata kada dai ace taji muryoyinsu,ta dan daga muryarta tace
”am…am…cewa nayi…cewa nayi dama ina bandaki ne wanka nake”ta fada cikin tsoro
”ok,to shikenan nari na shiga gun abdallah dukkanku baku karya ba shima daga cemin zaije wanka shiru,idan kin fito ki samemu a dining”ajiyar zuciya ta saki da taji alamun mamin ta tafi

Miqewa yayi ya sauka a gadon jin mamin ta soma qwaqwasa qofar dakin nashi,tana kallonshi ya murza key ya bude dakin,lallima SAMUN WURI(by maman farida),har ma wani key ya saka mata a daki kamar nashi dakin,bata tanka masa ba har ya fice don kada kulashi y sake dawowa ba qaramin dan neman magana bane kadan daga aikinshi

Yana fitowa suka hada ido da mami,duk sai ya dububurce,kunyarta yaji ta kamashi ganin yadda ta harde hannunta aqirji ta zuba masa ido,sai ya soma shafa qeyarsa,dariya ma ya bata ta kama hannunshi suna tafiya dining tace
”yaushe abdallah ya fara kunyar maminshi?,hala maryam ce ta koya masa?”baice komai ba sai murmushi da yayi

Cikin atamfa ta shirya super sharaton kalar lemon green da milk,ba qaramin kyau tayi mata,duk da ba wani makeup tayi ba amma hodar data shafa tabi fuskarta sosai ta qawata farar fatarta,ta sanya dan kunne sa sarqa na fashion lemon green

Tun daga nesa ya kasa kaucewa kallonta,wani kishinta da sonta na ratsashi,tayi masa kyau matuqa da gaske don bata yafa mayafi ba ma,tayi hakan ne sabida mami,tasan zata iya ganin baiken yafa mayafin da tayi bayan su biyu ne cikin gidan

Ta rusuna ta gaida mamin cikin kunya da girmamawa,ta amsa tana murmushi tare da dubansu
”nikam ai gaba dayanku kun fini kyawun gani,fatarku tayi kyau kamar ma ba’a qauye kuka zauna ba,lallai su inna wuro sun iya kiwo,dole ne kam mu nuna godiyarmu”dukkansu dariya sukayi ta ja kujera ta zauna tana gaida aliyun,ta qasan ido yake dubanta kana yayi qasa qasa da murya
”baby kinyi kyau fa ”banza tayi da shi kamar bata jishi ba,bata mantashi ba bai kunyar idon mamin yanzun sai ya jawo mata abun kunya tana zaman zamanta

Duk da haka bai qyaleta ba ganin taqi kulashi,hannu ya dinga sawa cikin kwanonta yana cinye mata chips dinta,nan ma qin biye masa tayi,saidq mami ta kula tukun
”a’ah,abdallah ya haka?,ga naka cikin olate nan kuma ma naga tare muke ci da kai ko?,don me yau zaka matsa mata”shi kansa sai ya danji kunya da ya tuna tare fa suke ci da mamin ko yaushe amma yau ya manta da ita

Ringin na wayarta ta jiyo wadda ta tabbata abdallah ne ya kunna mata don ta ajjiye ta ne kawai bata kai ga kunnawar ba,ta miqe daga cin abincin ta nufi dakin
sunan hindatu ta gani kan screen dinta,dan uwa mai dadi,wani farinciki taji ya kamata ta haye kan gado kana ta amsa
”yar uwa rabin jiki”inni hindatun,dariya maryam ta saki sannan ta qarashe mata
”banga mai kamarki ba”
”da gaske adda maryam kun dawo ya abdallah ya samu lafiya?,yanzu mukayi waya da mama ta gayamin mamin abdallah ke fada nata jiya bayan dawowarku,wallahi kinganni bani da lpy amma har naji na warke”
”eh da gaske mama take hindatu yanzu haka muna gida,ya gida ya mai gidan……”
katseta hindatun tayi cikin zumudi
”inaa,wlh adda maryam,bazan iya zama ba,ki duba hanya gani nan zuwa”tun kafin ta amsa ma ta katse wayar,ta dubi wayar tana murmushi
”hindatu uwar rawar kai da karadi,har yau ba’a canza hali ba”

Tana fitowa sukayi karo da baaba uwani na fitowa daga kitchen,cike da murna baaba uwani ta kalleta
”a’ah maryamu”
”baaba uwani”itama ta amsa mata fuskarta dauke da murmushi,sai da suka bata mintina suna hira a gun kafin ta wuce

ko da ta koma dining din tuni su mami sun kusa kammalawa,daman ita tuni taji ta qoshi zuwan hindatu kawai yasa ta qoshi,don haka jujjuya abincin kawai take
”har yanzu banga abun kirkin da kika ci ba maryam”
”na qoshi mami”ta fada tana mirmushi
”ko a ni’ima ma haka takeyi mami,batason abinci”inji abdallah cikin salon jan fada

Ya dan ja kujerarsa baya alamun ya qoshi yana hamdala abayyane
”mami,tun jiya fa aka soma turo min saqon komawa gurin aiki,don watanni da muka diba sun cika,so jiya bamu jima da dawowa ba saiga tex dinsu,zamu zauna da mr presdent gobe a abuja insha Allahu”
shiru mami tayi na dan lokaci kana tace
”anya Abdallah ba za’a haqura da aikin nan ba kuwa?”
murmushi yayi kadan bayan yayi miqa
”ba komai mami,ai duka aikin taimakon al’umma ne,idan lokacin barin yayi za’a barshi,yanzun aikin da na fara nakeso na idar da shi,alhj hamza mai qusa ina da zargi mai qarfi akansa”
”Allah ya taimaka,yanzun yaushe zaka tafi”
”da la’asar in sha Allahu,jirgin yamma ne”
”Allah ya kaimu”
satar kallon maryamun yake yaga ya yanayinta yake saidai sam taqi yarda su hada ido

mrs muhammad????

????????????✍????✍????✍????
[7:06pm, 10/6/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

      ▶5⃣7⃣

Daga sahal dan sa’ad Allah ya yarda da shi yace”wani mutum yazo wajen manzan Allah S A W,sai yace,ya manzan Allah,nuna min wani aiki wanda idan na aikatashi Allah zai soni mutane zasu soni?,sai manzan Allah S A W yace: KA GUJI DUNIYA(dadin dake cikinta da qyale qyalenta) Allah zai soka,sannan KA GUJI ABUN HANNUN MUTANE MUTANE ZASU SOKA
ruwayar ibnu maaja

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button