ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

kasa magana mamin tayi salma ko da tasan cewa da ita yake wani abu ya tokare mata wuya,tuni qwalla ta ciko mata ido,cikin rawar murya tace
”abdallah ni kake cewa kaska”
yayo wani dan qaramin murmushi irin na gefan bakin nan
”mene don ance miki kaska,ita ba halittar Allah bace kamar yadda kike”
kai ta girgiza tare da cewa
”na gode abdallah”
fuu ta zagayeshi ta wuce
mami ta soma kiranta tare da yunqurin binta,da sauri ya sha gaban mamin yana murmushi

”qyaleta don Allah mami,indai salma ce zata dawo”
harararshi ta danyi
”saboda ka saba mata haka ko,to saddiqa na daki saura itama ka wulaqanta tan kaji abdallah”yarfe hannu hayi cikin gajiyawa
”again mami?”kafin ta bashi amsa saiga saddiqar ta fito tana sakin hannu rigarta wanda ta tattareshi saboda alwalar data daura
bakinta a waahe take fadin
”oyo yo ya abdallah”hannu ya dan daga mata
”????????qanwa,yaushe ke kuma kika zo?”
murmushi ta saki hade da kashe ido daya cikin sigar son jan hankali

”cikin awa ta ta kusan hudu nake da zaman jiranka,kuma naga na kiraka nace maka zanzo”
ya dage kafadunshi
”nayi,tsammanin mami zaki gaida ko qanwata”
”ni gunka nazo”tace cikin salon shagwaba
”kuma kinga yanzun bani da time,time din mami na ne,jiya na dawo kinga baici ace mun gama hirar yaushe rabo ko,da zaki yi tafiyarki next time na baki appointment”yana murmushin mugunta qasan zuciyarsa ya fada,duk da yana jin yadda mami keta zungurinshi amma sai yayi kamar baiji ba

saddiqa gwanar girman kai da ganin ta isa ce,ki tayo tafi qarfin abdallah ya mata haka,son haka ta figi gyalenta wanda shi da babu duk daya
”abdallah….wai da ka fuskanci ina sonka shine ya baka damar takani yadda kaga dama,to wallahi aji na ya wuce nan”
murmushi ya kuma saki wanda ya qarawa kyansa kyau da kwarjini

”ni kaina nasan ke me aji ce”qufula ta sake yi don tuni ta fuskanci magana yake yaba mata a fakaice
”to indai don son da kake taqama ina maka ne daga yau na daina son naka sai me?”
”fine kin huta wallahi,kin kuma burge abdallah”wani zafi taji ranta na mata tuni ta durfafi fita ba tare da ta yima ko mamin sallama ba kamar yadda salma tayi

da sauri mamin tayi yunqurin binta,ya sake shan gabanta da hanzari
”pls mami ki qyaleta itama,wallahi hutu ta zabarwa kanta,hukuncinta yayi dai dai”
wata iriyar harara ta maka mishi
”matsa min abdallah agun tun ban sabar maka ba”
baice uffan ba ya janye gefe ya bata hanya,sai yayi komawarsa saman dining yayi zaune abinshi yana kallonsu

tana cimmata sai ta saki kuka,mamin tadan daddaki kafadarta a hankali
”meye kuma na kuka haka saddiqa da girmanki”ba don mamin bace da sai ta daka mata harara,amma sai ta toge tace
”haba mami,don kawai ana sonshi zai tsaya yana wulaqanta ni,yasan fa koni wace,su waye ke sona,to an daina sonshi din ma”
”ya isa daina kukan haka,ki barni da shi kinji”

da qyar ta lallaba saddiqan ta tafi,ta iso kan dining din inda abdallan ke zaune hankalinshi kwance tamkar babu abinda yayi,kujera ta ja ta zauna
”abdallah so kake kawai ka dauko min magana,kasan Allah akan haka zamu saba ni da kai?”
”ya salaaam….mami me kuma nayi da kike fadin wanna maganar mara dadi?”
”ka sani sarai abdallah yadda muke da yaran nan,ka san kuma irin magan ganun da ake tayi a kanka ko?,to ni na gaji gaskiya,ka zabi wadda kake so acikinsu kawai kowa ya huta abun ya isa haka”

”for god sake mami,ni babu wadda fa na taba cewa ina ina so duk cikinsu,yanzu mami anan kinga matar aure,kinga wadda ta cancanci zama surukarki matar danki qwaya daya abdallah,ni ban gani ba mami kuma kema na san baki gani ba”
ajiyar zuciya tayi don ta sani gaskiya abdallan ya fada
”amma wulaqancin bai da amfani abdallah,gwara arabu cikin mutunci da salama”
”mami ai bani na kawosu ba,kuma ni ba wulaqanci na musu ba,zuciya sukayi suka tafi”

murmushi tayi cikin zuciyarta,idan banda abun abdallah ai kora da hali ka musu,tace cikin zuciyarta
”tunda kace duka basu maka abida fa?,itadai nutsatstsiya ce ai ko”
yadan yatsine fuska
”ai nutsuwa kam akwaita,amma ba kamun kai,itama ina tabbatar miki mami gobe ko jibi zaki ganta da uban tana tana sum sum sum,marabarsu kadan ce ai”
”abdallah
abdallah,Allah ya shirya min kai”
”ameen mami na”

takaici ne ya rufeshi jin sallamar zubaida,ta qaraso tana wani satar kallonshi
”mami barka da dare”
”yauwa zubaida”filet ya zara ya bude warmers ya zuba abincin ya haura saman mamin abinsa
zubaidan binshi tayi da kallo yayin da ami ta dafe goshinta ????????‍♀
abdallah na bata damuwa da yawa kan yaran mutane
”ya akayi zubaida?”
maganar mamin ce ta janyo hankalinta daga kallon saman inda abdallan ya haye ya barta

”bab….ba komai mami,cewa nayi dama sai da safe”tace cikin in ina
”Allah y bamu alkhairi,ki gaida nene yau duka bamu hadu ba,insha Allahu zan shigo gobe”
”zasu ji”ta fice daga bangaren cike da takaici

a kwance ta tadda ahi saman three sityer wanda saboda tsahonsa kansa na daya hannun kujerar qafafun na daya hannun har sun zarta sosai
yasan qorafi zata yi don haka yayi saurin riga ta
”nidai,mami banji dadin dawowar nan tawa ba sam,duka yaran nan sun hanani sakewa,gaskiya daga yanzu kada wadda ta sake shigowa indai ina nan har sai na fita kawai”
”to uba na”
dariya yake ciki ciki don yasan tunda ta fadi haka ya quleta ne kuma ba zata sake cewa komai ba

????????????????????????

a fusace huwaila ta fito daga dakin nata,kai tsaye qofar dakin inna hadiza ta durfafa,a fusace ta saka hannunta ta yaye labulen tana fadin
”fito hadiza,wallahi na gaji na wannan iskancin da ake min cikin gidan nan ni da yara na”
inna hadiza dake kwance kan kujerarta da daurin qirji ta miqe ta soma qoqarin zama tare da jawo dankwalinta tana fagamniyar qulle danqararren kanta tare da fadin

”ai ni na girmewa fitowa saidai ashigo a sameni”
ba tayi wata wata na ta gado falon wanda saura ladan ta take qafar binta dake kwance saqe saqe,tayi saurin janye qafar tata tare da fadin
”Allah ya isa na wallahi”saidai bata ji ba kasancewar cikin masifa take da hayagaga

”hadiza,ki jawa diyarki
binta kunne,iskancin da take cikin gidan nan ya soma isata,haka kawai sai ta kama lubabatu ta dinga jibga,babu dama ta dauki aron wani abu nata”
”ahaf,kince haka kawai sannan kin dawo kin warware maganarki kince tana daukan aron abun ta,to ke da ita ku bude kunnuwanku da kyau,indai lubabatu bata daina daukar aron kayan binta bazan hana binta jibgarta ba,wutsiyar raqumi ai tayi nesa da qasa,mu yanzu cikin gidan nan babu sa’an mu don arziqi ba qarya bane”

kallon tara saura huwaila tayi mata,kana ta saki guda
”aikin banza….hara ra aduhu,arziqin nan fa da kike ta taqama da shi a sa hannuna ya samu,amma da yake butulu ce ke had kina da bakin goranta min,baya ga butulcin da kullum kwanan duniya kike min na hanani morar duka wani abu da jamila ta kawo cikin gidan nan,to bari kiji wallahi ki bini a hankali,don wallahi duk abinda kike taqamar da shi a yau idan naso sai na warware miki zarenki tas ta yadda baki isa ki maidashi ba”

hindatu dake parlour tana yiwa mama tsifa ta dubeta
”mama…kunnenki yana jiyo miki abinda nake ji kuwa?”
duk da cewa,zamcan ya duketa amma sai tace
”ina ruwanki hindatu?manzan Allah yace yana daga cikin kyawun musulincin mutum ya bar abinda babu ruwansa”gilma na cin hindatu amma dole haka ta ja bakinta tayi shiru tana addu’ar Allah ya kawo mata ya maryam,kai qila ma sai ta kira ta ayau din cikas din kawai mama da zata hanata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button