ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

sauka tayi kawai ta janyo,abun salla ta shimfida sannan ta kalli mero
”ya kamata kije kiyi sallah ko,don lokaci yayi”
”shi kuma abdullahin fa?”
”zaiyi shima”ta bata amsa tana tada kanbbarar sallah,sai data kusa raka’a uku kafin meron ta tashi ta fita tana yiwa abdallah sallama
roba ta saka ta masa alwala sanna ta juyar dashi bangaren gabas,kafin ya idar ta zuba abinci cikin plate ta ajjiye,bayan ya gama ta dora mishi kan,fillow a saman cinyanshi don hisham yace a dinga barinshi wani lokaci ya dinga ci da kanshi don hannun ya dinga motsawa ya dinga jin qwarinshi sosai,ta koma saman kujera ta ta samu roba daya ta zuba ganyan magaryan tana gyarashi tare da cire qayoyin jiki

shirun da taji alamun bai fara ci ba ya sanyata dago kanta,hada idanu sukayi da sauri ta janye idonta,ta rasa dalilin da a kwanakin nan bata iya hada ido da shi na tsawon lokaci,jikinta yaci gaba da bata kallonta yake,a sace ta kuma daga kai zata saci kallonshi suka sake hada ido,ya lumshe idon nashi da sauri ya bude,sign ne da ta lura yana yawan yi mata amfani da shi idan suka hada ido,batasan me yake nufi ba saidai a duk lokacin da yayi hakan takan tsinci kanta cikin wani irin feelings,wani irin abu ne cikin qwayar idanun abdallan da bata taba ganinshi cikin idanun wani ba

ta janye idonta tana fadin
”kaci abinci kada ya huce”kai ya girgiza mata alamun a’a,babu yadda bata masa ba amma yaqi,qarahe sai daya bar abinda take yi din ta dawo kan katifar ta karbi plate din,ta debo ta miqa mishi,babu musu ya bude bakinshi ya karba yana kallon fuskarta,ganin ya karba sai ta ajjiye cokalin tana fadin ”bismillah to”tana maida fuskarta gefe
a tausashe taji an kamo habarta ana qoqarin juyo da fuskarta,qin kallonshi tayi kamar yadda shima sam ya hanata sakewa har sai da suka sake hada ido,ture plate din abincin yayi da hannunshi guda kana ya jawota ta fada jikinshi.

tayi ta qoqarin tashi,saidai ya hanata,har mamakin yadda ya iya riqeta haka tayi,kamar zata yi kuka tace
”abdallah,bafa mu kadai bane cikin gidan nan ka sani”shiru taji,alamun bazai kulata ba,tilas ta haqura da yunqurin tashin tayi luf cikin jikinshi,ya lalubi hanninta ya saka nashi ciki ya jade yatsunsu guri guda tare da sauke ajiyar zuciya wadda ta haddasa mata sauyawar yanayin jikinta gaba daya,ta runtse ido tana jin fitar numfashinshi.

kuyi haquri da wannan

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[1:55pm, 9/24/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

          4⃣6⃣

Annabi Muhammad S A W yace:duk wanda yaje gurin boka ko dan duba haqiqa ya kafircewa abinda annabi muhammad tazo da shi,hakanan ba za’a karbi sallarsa ta kwana arba’in ba(ba yafe masa su akayi ba,kuma ko yayi Allah baya buqata baxai karba ba,babu wani abu da zaka/ki aikata ya zama kaffarar wannan zunubin da kikayi face ki tubarwar Allah tuba na haqiqa ba tuban muzuru ba,kuma kada ki yarda qafarki ta sake kusantar gurin bama zuwan ba,shin me kike tsammani idan Allah ya dauki ranki a gun ko a hanyar zuwa kota dawowa?,Allah ya kare mana imsninmu,ya,cire mana dukkan wani qulli dake zuciyoyinmu game da ‘yan uwanmu musulmi)

Manzan Allah S A W yana cewa”ka tuna Allah lokacin da kake cikin jin dadi da yalwa,shi kuma sai ya tuna da kai lokacin da ka shiga qunci da matsi da wahala(ba wai ka xauna kara zube ba don kana cikin jin dadi da wadatar rayuwa,ba zaka tashi addu’a ko tuna Allah da girma yake ba sai bala’i da masifu sun maka katutu,wannan kuskure ne babba,Allah yana fushi da bawan da baya roqarsa haka annsbi S A W yace mana,Allah kasa mu dace)

Saukar numfashinsa ne ya alamta mata bacci ya daukeshi,ta zare jikinta cikin dabara ta maye gurin da fillow,fuskarshi tarwai,kyawunshin nan mai daukar hankali yana nan,ta zuba masa ido tana tuhumar kanta na wasu ‘yan lokuta,ta janye idonta ta lumshesu hadi da sakin ajiyar zuciya,mero ta fado mata arai,sai ta ja siririn tsaki kana ta sauka daga katifar,hijabinta na kanta don haka abun sallah kawai ta gyara ta zauna akai bayan bayan ta samu roba daban ta saka ganyen magaryar qwalli bakwai aciki,a nutse tayi bismillah cikin madaidaiciyar murya ta soma karanta suratul baqara cikin robar da ta zuba ganyan magaryar da ruwa aciki,da ka take karatun cikin daddadan sauti mai cike da nutsuwa,don surar na daya daga cikin surorin data haddace saboda muhimmancin surar.

cikin barcinshi ya dinga jin tashin sautin karatun,sai ya gaza bude idonshi duk da ya farka,sosai yake jin dadin karatun,wani yanayi mai dadi na ratsashi,sannu a hankali ya dinga daga idanun nashi har ya kammala budesu gaba daya,ya zubesu fes kan fuskarta
kallonta yake da yadda bakinta ke motsawa cikin gwaninta da ita karanta alqur’ani da bawa kowanne harafi haqqinshi,ba kadan ba ta burgeshi,komai nata mai kyau ne da nutsuwa,saita tunasar da ahi ahima wani bangare mai girma daya manta ko ya saki na karatunshi ya daina tilawa.

kan idanunahi ta kammala,ko kadan batasan yana kallonta ba har ta gama ta karanta falaq da nasi da suratul ikhlas aciki ta girgiza ahi sosai har ruwan ya soma kumfa ta samu murfi ta rufe,ta zare hijabinta saboda zafin data fara ji sakamakon rashin kitso,Allah ya bata yalwar suma kamar yadda ala sana salin fulani ke da ita,ta zare ribbom dinta ta fara sake qoqarin tattara gashin guri gida donta daureshi,bin sumar tata yayi da kallo,don iya zamansu bai taba ganin gaahibta haka ba,ba qaramn hirgeahi abin yayo ba,yana son mace mai yalwar gashi sosai,shi ua sanya yawancin lokuta a zamanin quruciya shi yakewa mami tsifa,rabi wasa rabi tsifa da haka suke gamawa,ya dan lumshe idonshi kana ya bude saboda wani abi da ya soki zuciyarahi da tunawa da mamin da yayi,qaunarta da kewarta ta zamar masa sabuwa.

ci gaba yayi da kallonta ganin yadda ta daureahi ta kuma nannade jelar kamar alkaki,ta juya don sake sanya hijabinta suka hada ido,gabanta ya fadi
”shikenan ya gama qaremin kallo”ta fada cikin zuciyarta,murmushi ya sakar mata ganin yadda take faman qoqarin sala hijabinta
”dubeta,kamar ba mijinta bane ni,banga marabarki da mutanen qauyen nan ba kam,dama ina da ikon miqewa yau da sai na baki kunya fiye da haka yarinya”ya fada shima cikin zuciyarshi,fatanshi daya kada ta gudu,aikam addu’arsa bata ci ba don tana gama sanya hijabin ya gudu a dakin.

a bakin bishiyar darbejiya ta sameau zaune ita da mero
”sannu maryamu,na kiyo ki ai kina karatu,har mero zata shiga nace ta qyaleki,hala abdullahin kike wa”
”eh inna wuro”
”ai yana da kyau kam haka din,qur’ani dama ai waraka ne”
”wani baccin ya koma?”mero ta fada tana kallon qofar dakin nasu,sai data waiwaya itama ta dubi dakin kana ta dubeta ta girgiza kai
”amma aka barshi shi kadai,da fitowa akayi da shi ko inna wuro?”inji mero ta fada tana duban inna wuro
”lallai kam yasha iska shima,duk da akwai fanka,amma ta Alla tafi lafiya”

kafin maryam ta kai ga miqewa har mero ta miqe ta fara yin gaba,da sauri maryam tace
”amma inna bazan iya dorashi kan kujerar ba ni kadai,ga mustafa baya nan”itama miqewar tayo
”muje,zaki iya in sha Allahu,ai jikin ya qara qwari ba kamar da ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button