ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

tuni har mero ta debo ruwa cikin buta tazo gaban abdallan ta ajjiye ta koma bakin rijiyar ta ja wani ta fara daura tata alwala,dukkansu nan bakin qofar dakin innar suka shimfida karauni biyu sukayi sallar magaribar,shiru ya ratsa tsakar gidan kowanne na tasbihi cikin zuciyarshi banda mero da moysa bakinta kawai takeyi duk motsin abdallah ta cikin hasken qwan solar na kan idonta,har maryam ta fuskanci haka,dauke kanta tayi don ji da tayi ranta na aon baci taci gaba da tasbihi da yatsunta.

Ranar har sha daya na dare suna zaune suna hira,hiransu suke sosai shida inna wuro da yake jinta kamar maminshi.

Yana jin kewar mamin nashi sosai har bazai iya fadar adadi ba,mero ma tsakiyarsu tana sanya musu baki yayin da maryam taja bakinta ta tsuke,lokaci lokaci abdallah yana satar kallonta,ji yake tamkar ya jawota jikinshi ya rungume ko ya shiga zuciyarta ya jiyo damuwarta,shirun nata bai masa dadi sam,don haka sha daya na cika yace da inna wuro yana jin bacci zai kwanta
”nikuwa kamar mu kwana nan hirar yau tayi min dadi abdullahi,gashi yau kaima da bakinka akeyi da kai”mero ta fada yana kallonshi baki a washe,murmjshi kawai yayi ya girgiza kai,bata bar gidan ba sai da taga sun shige dakin kana ta waiwayo ta yiwa inna wuro sallama ta fice cike da jin dadin jin daddadar muryar abdallah da yau ta morewa.

sanye yake da jallabiya milk mai gajeran hannu yana zaune saman katifar tasu hannunahi dauke da qaramin al’qur’ani,daya hannun kuma riqe yake da wayarshi ya kunna torch din yana haskawa,ya sake satar kallonta sha biyu har da kwata amma bata da niyyar kwanciya,hakanan kuma ta kashe musu qwan solar dakin saboda ta lura da yadda yake ta nacin kallonta,tana zaune dirshan bisa dadduma sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja,ya saka zare kan shafin da yake na karatun qur’ani ya shafa addu’anshi,ya tabbata koya kirata kam ba zuwa zata yi ba indai ba cewa yayi yana buqatar wani abu ba.

”madam,a ataimakawa bawan Allah da ruwa mana”ya fada murya qasa qasa kamar mai rada har yasa tsigar jikinta tashi,ta ajjiye carbin kana ta miqe ta isa inda catoon na ruwan gora ke ajjiye ta ciro daya tare da cup ta hawo gadon,ta tsiyayo ta sake matsowa gabanshi ta miqo masa,jadawa yayi harda hannun nata ya riqe gam yana son saka qwayar idonshi cikin nata,ta soma qoqarin qwace hannun nata saidai ta kasa garin hakan har fiye da rabin ruwan ya zube a katifar.

Ta dago da niyyar dubanshi idanunta cike da qwalla da ya rasa ta meye,take idanunsu suka hadu,da sauri ta janye nata idanun don bata iya dauke nauyin idanunshi cikin nata
”ka sakemin hannu kaga duk ka…..”
”bazan sakeki ba,sai kin gayan meke damunki,tunda bakina ya budu baki,barni nayi magana da ke ba sai wasu ke tayani hira?”
ta sake kau da kanta kana tace
”to me kake so muce ko ince maka ne?”
”bana tunanin baki san me zaki gayan ba maryam,nasha hango maganganu da dama boye cikin idanunki,kin hana bakinki ya furta kina cutar da zuciyarki hakanan babu gaira babu dalili ba tare da ta yi miki laifin komai ba”
kamar wadda ya doka sai ta soma hawaye,ita kanta batasan me yake saurin karya mata zuciya ba
”subhanallah,kuka…kuka kuma maryam me na miki”babu amsa don haka ya janyota ta fada jikinshi ragowar ruwan ya zube mata ya jiqa mata gaban dan yalolon hijabin jikinta wanda takansa duk dare idan zata kwanta,dama ba wani kauri gareahi ba,yauqi ne da shi da rashin kauri take kuwa ya manne mata a jiki.

”yi shiru ki gayan matsalarki,bazanso saki kuka ba maryam cikin irin wannan lokacin,baki cancanci haka ba”
”ka sakeni ni babu abinda ke damuna,ka qyaleni”
kai ya girgiza hakanan mutum,bazai yita kuka ba komai na da dalili”
ta tabbatar indai abdallah ne bazai saketa din ba don ya mata riqon tsauri ne don haka tace
”kayana,ka jiqamin kayana ka sakeni na canza wasu”
idanunshi ya kai kan gaban jijabin nata cikin hasken torch din wayarshin,wani abu ya tairga mishi har qasan qafarshi,ya kai,hannunshi gaban hijabin yana fadin
”bari na cire miki”
kan tayi qoqarin hanashi har yaje,gaba dayansu wuta ta dauke musu shi da itan gaba daya,sai ta sakar masa wani kikan harda dan sauti
”am so sorry my dear”kawai yake fada ya cire hijabin ya cillar gefe daya ya sake mannata kan qirjinsa,yana kin sautin kukanta bai hana ta ba don yasan koma mene idan tayi kuka sosai zuciyarta zata sassauta,tun sautin na fita kadan kadan har ta koma ajiyar zuciya kana numfashinta ya fara sauka a hankali alamun bacci yayi awon gaba da ita.

murmushi ya saka mai qayatarwa qasa qasa yace bayan ya leqa fuskarta
”rigimammiya,kin hana zuciyarki sakat”yana gyara mata kwanciya,ya fuskanci duk ranar da ta kwanta a qirjinshi bata dadewa bacci ke daukanta wani lokacin ma har taso makara gun tashi,ya saki ajiyar zuciya qasa qasa yace
”u dont know how u make me feel duk sanda kike jikina”ya dora kanshi saman habarta cike da wata iriyar nutsuwa.

????????????????????????

A shirye take cikin riga da wando na pakistan ruwan madara tayi rolling da mayafinsu,zaune take kan kujera ko motsi batayi kanta a duqe tana kallon yatsuntsa,ya sake dubanta tini har ta fara zub da qwallar tata abinda bai son gani
”kina son fita amma kinqi ki gyara ni,nikam yau babu wanda zaimin wanka idan bake ba,see you ko tausayina baki ji,kin gwammace mustafa yayi ta yimin bayan bako ina yake wanke min ba wani gun ni nake da kaina”
maryam cikin muryar kuka ba tare da ta dago ba
”taya zan wuce bandaki ni da kai yi maka wanka inna wuro na kallon mu,haba mana abdal….”
”fine,muyi zamanmu ko baby na ni dake yau cikin daki,babu mai cewa don me ko”qara narkewa tayi tana faman hawaye don tana jiyo muryar inna wuro na jajjabin rashin jin motsin daya daga cikinsu,duk da tasan kara da alkunya bazata bar inna wuron tayi magana ba ko zasu shekara cikin dakin.

Narkewa yayi shima cikin filallukan dake kan whellchair dinshi dariya na cinshi,ya sani cewa ba zata taba iyawa ba,ko kaya na shan iska bata yarda ta gani jikinsa kuma duka ua gama karantota,ta daukeshi kamar wani muharraminta
sallama mairo tayi tana daga labulen dakin
”yaya abdullahi muna ta cigiyarku shiru?”ta fada tana kallonashi tana kuma kallon maryam
girarshi ya dage guda daya
”eh,muma muna ta cigiyarku,daman ke nake jira ki taimaka min inyi wanka,yau meramu ta gaji”ya ambaci sunan ta irin salon da yaji suna fada
zuciyar mero qal ta rufe fuskarta da tafukan hannunta,da sauri maryam ta dago babu shiri ta dubi abdallah qirjinta ya buga kamar an dakeshi da guduma,ido daya ya kashe mata kana ya dauke kanshi ya maida kan mero wadda take fadin
”kai yaya abdullahi”cikin salon nuna jin kunya.

kan mero ta bude idonta har maryam ta taashi ta kama wheelchair din tayi hanyar fita da shi,sai data bude idon nata raga dakin wayam har sun fice,jiki ba qwari jtama ta fice a dakin
inna wuro bata a tsakar gidan don haka tayi maza ta tura suka shige bayan gidan
”take it easy mana madam,kada ki fadar da bawan Allah”inji abdallah cike da dariyar mugunta da yake qunsheta
tana tsaye ya soma cire kayanshi ta dauke kanta qirjinta na lugude,saura gajeran wandon daya rage wanda yake bari a jikinsa idan zaiyi wanka,gaba daya ta rude don bata yarda taga jikinshi har kamar haka,hatta da cinyoyinshi dake cike da gargasa sun fito,ganin yana niyyar fidda shi shima yasa ta qarasa rudewar gaba daya,batasan ta dafe hannunshi ba
”ayya mana abdallah ba kyau fa don Allah”ta fada cikin son fashewa da kuka
dariya sosai ta kamshi amma ya hade rai yayi kicin kicin
”to me naki,dazun fa adaki kika gayan babu ruwan wani da wani,kema me ruwanki da ni ko na cire din,ba wanka zaki tayani ba?,kimin wankanki kawai ki maida ni daki,wai haka ma ake jinyar mutum?,oh ni abdallah sam baki iya jinya ba”ba bakin maida amsa girgiza kai tayi yaci gaba da kiciniyarshi,a guje ta kwasa ta fice a bayin dariyar da yake boyewa tilas ta fito,mamaki take bashi tamkar cikin qauyen aka haifeta ko kuma shi din ba mijinta bane,kunyarta ta mata yawa ta maida shi kamar wani dodo,Allah yasa komai na wanka na gabanshi don haka ya qyaleta yayi abunshi tunda hannunshi na kaiwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button