ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

da qyar suka kutsa cikin rumfar tasu,mamansu ce zaune bisa kujera fuskarta dauke da tashin hankali,sai anty kubra qanwar mamansu,inna hadiza da baba huwaila sai jamila dake gefansu tana zuba ruwan bala’i har daurin zaninta na kwancewa anty kubra na maida mata da raddi
baba huwaila ke riqo,jamilan ta fincike kana ta zabga mata harara
”kinga malama ki qyaleni kawai,wallahi babu inda zani sai da lefena koda motocin daukar amaryar zasu shekare,a qa’ida ai lefe nawa ne kuma sai in zuba ido a take min haqqina,wallahi babu wanda ya isa ko duk duniya gatanshi ne yau sai kun fiddo lefen nan”
”qwarai kuwa haqqinki ne ai”babarta hadiza ta fadi cike da nuna goyan baya,wani abu ne ya tsirga wa huwaila,wato tsiyar ma har da ita a ciki yau

‘yan mata biyun dake tsaye bakin qofa cikin ‘yan daukar amarya suka hada ido,cikin tashin hankali dayar ta cewa ‘yar uwarta,muryarta can qasa”mun shiga uku malika,wacce iriyar mace ya jabir ya kwaso mana”babu mai amsar duk cikinsu,saboda haka jiki a sanyaye suka zame,suka fice daga gidan

hindatu dake jiran qiris ta saki jakar hannunta tana huci ta qaraso gaban jamila
”rufe mana baki matsiyaciyar banza matsihaciyar wofi ‘yan taka hayen arziqi,lefen banza lefan wofi,mj jabir ma yanzu bai ishemu kallo ba balle abinda ya fito daga hannunsa,idan kinsa ranki a inuwa ma zamu fito muku da gayuar tsiuarku ba sai kinzo kina haushi kina ragewa kanki daraja ba idon dangin miji ba”
sai ta,hau ihu
”e hooo,munji dai duka haushin rashi ne ,kaya dai sai kun bada su”
”ai dama zamu bada din amma ba saboda wannan hayagagar taki ba,zamu baku ne saboda mu a gun mu ba yanke talauci jabir ya bamu ba,kune nake tsammanin zai iya zama yanke talauci a gunku”
hannu inna hadiza ta saka zata zabga mata mari,tuni ta tare ta kana ta sake taku uku zuwa gabanta tana huci da nuna ta da yatsa
”kada ki kuskura wallahi,don idan a baya kin saba tabani ina qyaleki ta yanzu babu wannan maganar,idan kuma kika yi gigin aiwatar da hakan wallahi ko kadan bazaji kunyarkk ba daga hannu zanyo nima in nuna miki salon nawa iya marin,tsohuwar banza wadda shekarunt basu dade ta da k…..”

tsawa mamarta ta daka mata”kada ki kuskura kici gaba,zo ki wuce ki debo musu kayansu kawai idan na isa da ke”yarfar da hannun inna hadizan tayi a fusace ta shiga dakin maman inda anan kayan ke ajjiye ta soma fiddo da su tana watsosu falon
”kada fa ta barnata muku kaya kuyi mata gana”
”ina ruwanki,da muka zo da ke wanne taimako kika iya yi,tunda dai sun fiddosu ai shikenan”inji jamilar
takaici yasa huwaila jiyawa ta bar dakin

a warwatse haka hindatu ta dinga jefomusi su tas tun mama na mata magana har ta gaji da qyaleta,bayan kuma ta gama tace wallahi ian basuyi gaggawar kwashesu daga rumfar tasu ba zasu ga qasqanci,duk iya ikancinsu sun sqn halin hindatu sqrai bata iya fushi ba,don haka cikin rawar jiki suka dinga kwashewa ciki harda uwar amarya inna hadiza

sai da suka gama sannan taji kuka yazo mata cikin dakin nasu da ta shiga da niyyar rage qincin zuciyarta,sai ta tadda maryam nayin nata,kasa lallashinta tayi hala suka hada kai suka dinga risgar kukan da qyar anty kubra ta sha kansu

haka suka kwashi amaryarsu suka kaita gidan da aka shirya shi da sunan maryam din,wanda hatta kayan gado fiye da rabi kudinta ne ta baiwa baban nata ya hada da na gurinsa aka siyesu,abu daya ne inna hadizan tasa aka jado aka dawo musu da shi kayan kitchen,duk da haka sun cire manya manyan warmers masu tsada da maryam din ta siya cikin albashinta

????????????????????????

kwana biyu gidan yayi da ragowar baqin su inna hadiza da basu ida tafiya ba,kwanakin biyun nan daidai suke da shekara goma na tsanani gurin maryam,kallo daya zaka mata ka dauke kai,hatta da mamarta wannan karon ta kasa daurewa zuciyarta sai da ta taya diyar tata kokawa

????????????????????????

ciwon kwana na hudu bayan sallar la’asar raliya ta iso gidan,maryam na kan dadduma bata kai ga tashi ba tunda tayi sallar la’asar,suna hada ido ta soma share qwalla,itama raliyan sai ta kasa daurewa duk da alqawarin da tayi ma nasir din bazata zo su hada kai suyita kuka ba

kusa da ita ta zauna suka soma aikin kuka wanda mama dake dakinta bata ji shigowarta ba sai rishin kukansu,leqowa tayi don ganin waye”ashshsha,haba raliya,abu da ya riga ya wuce kuma,don Allah ya isa haka,tashi ku shiga daki”ta fada tana karbar fadil daga gunta ta fice ta bar musu rumfar

da taimakon ambato Allah da take ta samu zuciyarta ta rage zugin da take
”raliya me n yiwa jabir haka da zafi?,wace iriuar qiyayya ce wannan ya gwada min,idan yasan tun farko baya sona me yasa bai gayamin ba tunda ba tilas aka mishi ba?”
girgiza kai kawai raliyan take
”maryam,ke kanki idan kika ga jabir sai kin tausaya masa,kallo daya zaki masa ki tabbata ba’a cikin hayyacinsa yake ba,kinsan me ya fafu ne?,lafiya suka zo gurin daurin auren amma kafin a kai ga gama taruwa ana zaune kawai su nasir suka ga jabir ya sume,mintina kadan ya dawo hayyacinsa,kinsan abinda bakinsa ya fara fada?,jamila nidai jamila nake so wallahi,zan iya rasa rayuwata idan ban mallaketa ba wallahi,abbanshi uazo yabi ba’ason maganar sai yace shi wallahi baisan wata maryam b ai tab cewa yana son wata mai suna marym ba,abbanshi ya dauka iskanci ne ya hau maa fada yace bazai maidashi mutumin banza ba,

abu kamar wasa sai ga jabir ya sake sumewa jin an hanashi jamila,da babanku yaga haka sai yace wa abban nashi ya barshi ai dake da jamilan duka daya ne”ajiyar zuciya maryam din ta ski mai tafe da hawaye,idon raliyan ciki natan tace
”maryama don Allah ki dinga saka abir a addu’o’inki,don ya hadu da jarabta,jiya nasir ya debeni muka je gidan,kinga yadda ake zaman?,yadda kika san bawa da uban gidansa,jabir ya zama abun tasayi,da jamila ta yi magan sai kiga ya zabura,tana saman kujera kwatankwacin bawa da uban gidansa”

a maimakon haushi takaici da tsanar jabir sai tausayinsa ya maye gurbi,take taji fiye da rabin quncin zuciyarta ya tafi,bata jin komai a ayanzu sai tsantsar tausayinsa,lallai ya fada cikin jarrabawa mai girma,sun dade tare da raliyan suna tattuna lamarin har daf da magariba sannan tayi musu sallama ta tafi

Bayan sallar isha’i baban su ya shigo falon nasu,bayanin da yayi musu kusan tishi ne kan wanda raliyar ta musu,ya rife da cewa”dln haka ke maryam sai kiyi haquri ki fidda wani mijin,tunda ke da jamilan duka daya ne ‘yar uwarki ce”lamarin baban nasu na daure musu kai saidai ko daya maman tasu bata bari suyi maganar da ita kan yadda yake nuna wariyar launin fata qarara su da sairan yaran gidan,daga haka ya kade rigarshi ya fice yace idan ta samu wani mijin ta sanar masa

Mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[9/17, 12:50 PM] 80k: ????????????????????????????
????????????????????????????
???? ABADAN????????
????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
????????????????????????????
????????????????????????????
WRITTEN BY
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

    ▶7⃣

WACE CE MARYAMA?

Maryama diya ce ga amina da kuma malam mahmud,za a iya cewa itace diya ta farko da suka fara haifa shi da ita,asalin su fulanin kano ne cikin wani qauye da ake kira da gaya dukkansu shi da amina mazauna garin ne,yanayin nema ya dawo dasu cikin garin kano

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button