ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

hakanan maryam taji wani abu ya takoreta,ta dade tana qaryata kanta akan irin abunda takeji idan mairo ta rabi kanta da sunan kishi ne saidai a yanzu a yadda abun yaqi barinta ta tabbatar cewa kishin ne
baifi saura awa daya a kira magariba ba inna wuro ta dawo gaggauce don bata kaiwa magariba a unguwa

itama dai da mamakin take kallona abdallah dake tsaye kan maryam ya harde hannayensa a qirji yana kallonta kamar wanda aka baiwa gadinta
”bawan Allah?,Allah mai iko,kaine a tsaye da qafafunka?”
kyakkyawan murmushin nan nasa ya saki kana ya qarasa ga innar yana karban daurin buhu dake hannunta ya sa mata shi daga gefe
”ni ne inna wuro”
tana kame da bakinta tace
”bari malam yazo yaga ikon Allah,Allah gwanin iyawa ya amshi addu’ar bayinsa,kai Allah mun gode maka,sannu bawan Allah,Allah ya qara lafiya”
”ameen ameen inna”
ta dubi maryam dake zaune
”ita kuma wannan fa,meron ta barwa girkin kuma?”

Ya juya ya dubi maryam da ta dan hade rai don tasan yanzun innar zata sako wani abu kuma daban,ita kam gani take sam bata sonta yanzun tafi son abdallah da mero kawai
dariya ta tasowa abdallah,bai iya hadiyeta ba sai da ya dan dara
”inna targade tayi,Allah ma ya soni ya rufan asiri saura kadan tayi iyo cikin rijiya”
cikin tsoro innar ta zaro ido
”rjiya?,garin yaya ni ‘yasu mairamu?”sai ta sake yin fuskar shanu ita ala dole sai ta nuna haushi take ji,sai abdallah ne ya bata amsa
”ina tsammani santsin lakar can ne,ba shiri inna na qarasawarkewa naje na tarota”
”to Allah ya rufa asiri”ta fada tana dan masa magana da ido,shi ma ya maida nata amsa ta hanyar langabe kansa da daga hannunshi alamun ban haquri

mairo ko dake bakin wuta cikin zuciyarta take cewa
”shi kuma baya tashi warkewa sai ranar da wani abun zai sameta,haka ma fa bakinsa yayi”
(hmmm,abdallah na maryam)

????????????????????????

Washegari da hisham suka wayi gari cikin garin ni’ima cikin kuma gidan inna wuro,dukkansu tare suka zauna karin safe,kowanne ka dubi fuskarsa zuwa zuciyarsa cike take da farinciki mara misali,hira suke a tsakaninsu har suka kammala,maryam ta kwashe kayan ta gyara gurin

tsoho alhaji yace
”to alhmdlh abdullahi,kaga dai yadda ubangiji ya karbi addu’armu cikin lokaci qanqani”
kanshi a qasa yace
”hakane,malam naga darasi cikin rayuwa sosai,naga abunda da can bansan da shi na sai da Allah ya jarrabaceni da lalura,rayuwa abar tsoro ce haka duniya ma abar tsoro ce,darasi ne babba na koya cikin lalurar da Allah ya jarabceni da ita”

”gaskiya ne,dama wani abun baka saninsa ko gane shi sai ka shiga wata jarabtar,Allah ka bamu ikon cinye jarrabawarsa”
dukkaninsu suka amsa da ameen
tsoho alhaji ya dubeshi
”yanzu sai shirye shiryen tafiya gida kenan”
murmushi ya saki kana yace
”banjin barin garin nan da wurwuri haka,garinku ya yimin malam sosai,yaci sunanshi ni’ima,bazan taba mance wa da garin nan cikin tarihin rayuwata har abada,baya ga haka neman aure nake malam cikin garin naku”

dum kunnenta taji gaba daya yayi tamkar ba zata iya ci gaba da sauraren komai ba,sai ta rasa gane a wanne bigire take a zaune?,duk wata laka ta jikinta ta daina aiki,so take ta tashi ta bar dakin amma haka ya gagara
”a cikin karkaran nan tamu kuwa?”tsoho alhaji ua fada cikin mamaki,cike da tabbatarwa ya gyada kansa
”eh malam”

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[5:05pm, 10/4/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

    ▶5⃣5⃣

Daga abdullahi dan mas’ud Allah ya yarda da shi yace:Manzan Allah S A W yace ”duk wanda yayi nuni(fara aikatawa) akan wani aiki na alkhairi yana da kwatankwacin ladan wanda ya ya kwaikwayeshi(ba tare da an tauyewa kowa cikinsu daga ladansa ba”(haka yake ga wanda ya qirqiri wani aiki na sharri kuma wani koyi da shi shima yana da zunubi kan duk mutum daya daya aikata irin aikin kwatankwacin zunubin wanda ya aikata aikin)

An karbo daga abu ayyubal ansari Allah ya yarda da shi yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa”duk wanda ya raba tsakanin uwa da danta,Allah sai ya raba tsakaninsa da masoyansa ranar qiyama”,a wata ruwayar ta abi musa yazo da lafazin ”Allah ya la’anci wanda ya raba tsakanin uba da dansa,da dan uwa da dan uwansa”

tuni ta miqe sabida kunnuwanta ba zasu juri jin abinda zai fada ba,saidai kafin ta kai ga ficewar har tsoho alhaji ya sake tambayarsa
”wacce yarinya ce abdullahi ka gani din,yar wajen wace?”
”ba wata bace ba malam,ta gida ce,mar……..”
cike da gaggawa ra qarasa ficewa daga dakin don tuni zuciyarta ta riga ta bata sunan wadda zai kira din,dakin inna wuro ta wuce ta haye can quryar gadonta gami da cusa kanta tsakanin filalluka
”me abdallah yake so na masa ne da zai fahimceni,wacce hanya zan biyo masa da zai fahimce ni?ta yaya abdallah zai nemi auren wata?watan ma mero?eh tasan bazai wuce ita din ba don duka take takensa ya gama nuna mata haka”tambayar data ringa nanatawa kanta kenan

tana nan kwancen kimanin minti talatin da wani abu ta jiyo maganarsu,muryar inna wuro ta fara jin
”Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku,ni dama tuwo na maina ne,da kai da itan duka daya ne a guna”
wani irin abu taji ya tsirga mata da bata taba jin makamamcinsa ba,babu shakka kishi bala’i ne,bata sake gasgata kanta cewa tana kishin abdallah mai tsananin zafi ba kamar ranar,take ta yankewa kanta daga yau bata sake kwana a garin tunda ta gama iya abunda zata yi din,cikin qanqanin lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta

Duk yadda inna wuro ta so fa fito ta qiya,gani take duka basu sonta,har,hisham wani irin haushinsa take ji,ko kowa zai goyawa abdallah baya ai bai kamata shima yabi yarima yasha kida ba,kwanciyarta tayi kan gadon tana jin yadda jikinta ke fudda hucin zazzabi ta kuma qi yarda ta gayawa kowa,sallar magariba da isha ne kawai ya tasheta daga gadon shima din sai taga innan ta fita a dakin

????????????????????????

Daga alwalar sallar asuba ta hada da wankanta baki daya ta dawo dakin inna ta canzq kayan tunda ta debo kayanta ganin hisham yazo tasan dole tare da abdallah suke kwana bazaiyiwu kuma tayi ta ziryar dauko kaya ba shi yasa ta debo duk abinda take da buqata

abin sallah ta saka tayi raka’atanil fajr wadda falalarta Manzan Allah S A W yace tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi,bata ko jira tayi azkar ba ta koma gadon ta sake nadewa,tanajin inna wuron na tada ta tayi banza da ita duk da idanunta biyu,ta baza kunnuwanta ne a tsakar gida ko zataji fitarsu abdallah ta shiga dakin ta dauki abinda ya mata saura

Tun tana azkar tare da tsumayin fitowarsu har wani dan qaramin bacci ya sacera sabida rashin isashshen bacci da bata samu ba jiya

Da addu’a ta tashi,ta zabura ta zauna kan gadon ganin rana ra gama fitowa sosai,ta,duba agogon dakin qarfe sha daya har da rabi na safe,takaici ya lullubeta,duka lissafinta iwar haka ta tsufa a kano,ta soma yaye bargon jikinta cike da takaici
sallama aka yo cikin tsakar gidan,kunnenta ta kasa sosai don tantance da gaske ne ko irin mafarkan da ta saba yi ne,kamar kuwa ansan tantamar da take yi aka sake rangada wata sallamar

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button