ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da taga alamun fitarta sanna ta janye idanunta,cikin fitar hayyaci ya kama fuskan tata don baison ta daina kallonshin sabida wasu zafafan abubuwa da yake karanta daga qwayar idanunta wanda shi kansa yasan bata san da su ba,satar amsa yake samu sosai ba tare da saninta ba,tana son qaace fuskarta yace
”ko na aure duka matan duniyan ma meye naki a ciki”
cikin fushin da batasab ya fita ba tace
”wallahi kuwa,tunda ni dama yar amshin shata ce ba,na kusa sanin inda dare ya yimun,su mero na kusa ai baka da damuwa”

Dariya taso kamashi hanin tsabar miskilanci da qarfin hali irin na mutum,ga gaskiya amma ka qita qiri qiri
”gaskiya ne”ya fada yana kamo hijabinta da take qoqarin,ficewa a dakin
”alfarma daya nakeso kiyimin don Allah,ruwa zaki dan duma ma min ki kaimin bandaki,idan inna ta tambayeki kice mata zafi nakeji duk da nasan halin innan sarai ba zata tambaya ba,amma idan da takura ki barshi sai naje nayi haka”
bata bari ta kalleshi ba don gaba daya ya gama kunyatata,har ga Allah ta dauka da wasa yake ba wankan zaiyi ba ashe shi da gaske yake gaya mata sai qeya ta turo masa
”salon ta zaci wani abun mukayi”
”to haramun ne koma me mukayi din,’yar qauye kawai,ita innan ai ba yarinya bace,tafiyarki kawai zata kalla idan ma wani abu ne ta gane,idan baki wasa ba ma sai na gaya mata munyi wani abun inga ya zakiyi”
tayi imani,kadan daga aikinshi ya kum kunyatata saboda haka kufce ta fice ta hada masa ruwan wankan

yar halak inna kam dauke kanta tayi abunta tana faman jan mero da hira,maryam din ma zama tayi can gefe tayi tsuru tsuru cike da kunya tana son ganin reacting na inna wuri saidai babu abinda ta fahimta don hirarta kawai innar take,kafin ma abdallahn ya fito ta shige daki abunta ta kama wasu sabgogin,sai gun ya rage daga ita sai sister mero(lol)
maryam ta dan dubeta
”wai nikam na tambayeki mana?”
”ina jinki”meron ta fada cikin tsoro tsoron kada ko wani abun maryam din zata yi mata
”bakisan cewa haramun bane shiga guri ba tare da kayiwa masu gurin sallama ba”shiru ta danyi don babu inda ilimin nata yakai,na salla dai ta sameshi baina baina
”ai ina yin sallama,kune bakwa ji da wuri”
”waya gaya miki idan kayi sallama cewa akayi ka cusa kanka kawai,sallama na nufin neman izini,koda kayi sallama addini cewa yayi kada ka shiga sai an baka izini,haka Allah ua fada cikin qur’aninsa mai girma”yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah kada kushiga wami gida da ba naku ba face sai kunyi nemi izini kuma kunyi sallama abisa ahlin gidan,wannan shine yafi alkhairi a gareku ko zaku fadaka,idan baku samu kowa a gidan ba kada ku shiga har sai an baku izinin shigar,idan kuma akace da ku koma to ku koma,wannan shine yafi tsarkakewa a gareku”kin fahimceni naga kina raba ido zancan Allah na karanto miki cikin qur’ani”kai ta gyada mata kawai

sai ta dora”kinga zancan Allah na gaya miki ko?so daga yau kada ki sake fado mana daki ba tare da na baki izini ba”sai ta dauke kanta can wani bangaren kamar bata jita ba,ran maryam ya dan sosu mai yarinyar ke nufi
”dake fa nake mero”ta fada cikin dan zafi zafi
”to ai abdullahi ne yaci na shigo ko”
”ba ruwa na na gaya mii daga yau kada ki sake sai na baki izini,ko shi ina iya hanashi shiga,idan kuma baki ji ba ni da ke ne”
sai ta danji tsoro don maryam din bata taba mata magana irin haka ba,a sanyaye tace ”to”

????????????????????????

”duk abinda ta faru ko baki fada ba bintu na sani ba cikin hayyacinki kike ba,amma ki kwantar da hankakinki duk abinda yq samu bawa da sanin Allah,kuma abinda nakeso da ke,bana son ko kadan ki nunawa nene kinsan wani abu game da abinda ke faruwa din,abu na farko da zamu fara yi shine zamu raba sadaka makarantu makarantu na alarammomi a samu cikin addu’a,koda zamu nemi abdallah ba zamu nemeshi a bayyane ba saboda na tabbata babu wanda yasan halin da yake ciki koda qasa batasan wanne hali yake ciki sabida da ta sani da tuni na tabbatar an baza labarin cikin shafukan jaridu da mujallu,sabida haka yadda Allah ya rufawa al’amarin asiri muma cikin surri zamu ci gaba da bibiyarsa har Allah ya warware mana wanannan daurin gwarmai din,addu’a zaki duqufa yi masa babu dare ba rana domi, addu’ar mahaifiya karbabbiyace kan ‘ya’yanta”

”na gode qwarai kawu,Allah ya qara girma ya bar zumunci”
”ameen bintu kamar diya kke a gareni,irin hiyayyar da kika yiwa iyayenki irinta kike mana,hakanan kowa naki ne babu wanda baya morar arziqinki komai dukiyarka kuwa,to don me taqi matsalar ta taso ba zamu shiga ciki ba,abinda nake dak qara jaddada miki shine ko a fuska kada ki nuna mata abinda suka miki ya sakeki,kici gaba da binta ahakan,nayi imani addu’armu Allah bazai wofantar da ita ba”
”na gode kawu”haj bintu ta fada idanunta fal da qwalla zuciyarta kuma cike da taqini da qauna cikin rahamar Allah

????????????????????????

Kamar wani mahaukaci haka ya fado dakin futu futu da shi,tana kwance kan gadon dakin an tallafo bayanta da filo,tun daga ranar da mugu yayi mata wannan dukan bata qara iya yin komai da kanta ba saidai a yi mata,ga baki na magana ga ido ga kunne amma dai qafafun da gangar jikin basa aiki

”yaya,adnan ka samota?”ta tambayeshi cikin zaquwa
tsaki yaja ya zauna a gefanta cike da bala’i yace
”nifa na gaji,wallahi nene na gaji babu inda zan sake komawa,zuwana biyar dajin amma na kasa gane gidan sama ko qasa na nemeshi na rasa,shikenan mu haka zamu qare cikin wahala,wallahi baqin jininki muka debo wallahi,haba da Allah malam hauka ake?”
kwantar da murya tayi tamkar ita ce uwar ma
”haba adnan,zahariyya yar uwarka ce da baka da kamarta fa,ka daure kai kuwa mana da alamu wallahi tana cikin mawuyacin hali na neman taimakonmu”

a fusace ya kalleta kamar mai shirin sharara mata mari
”jaka ce ta yimin gula a ciki?idan na koma wanann na zama alade,ke idan na koma ma Allah ya tsinemin,dazu fa ina tsammanin kurace ta tasanmin badan ina cikin mota ba da tuni yanzu na zama dan gari a lahira haka kawai akan wata banzar zahariyya da budurwata ma ta fiye min ita,nafsi nafsi fa kawai nene ehe”ya fada yana miqewa ta bishi da ido

janye janye janyen lokoki ya fara yi mata,da sauri tace da shi
”meye haka adnan,kasan fa na hanaka yimin bincike cikin daki ko?,akwai surrukana da ajjiye ajjiye na fa”wani kallon banza ya juyo yayi mata yana fadin
”dama kin kwantar da hankalinki don yau ranar diban kaso na ne,zan dibi duk abinda nakeso don ma fuskanci wannan tafiyar babu nasara,odan yaso duk ranar da kika samu nasarar kashe abdallahn ki nemo ki sai muci ganimar tare”iya bakin qoqarin hanashi da bakinta tayi amma a abanza,kallon tsiya ma bata isheshi ba balle yasa ran na arziqi,tana kallo ya dinga balle lockers dinta yana kwashe duk wata kadara tata yana hadewa cikin wata ‘yar jaka,kaf ya kammala ya tako gabanta yasa hannunshi ya tsinke sarqar gwal da ke wuyanta wanda garin fincikar har biyo shi tayi sabida rashin qarfin jiki,kuka ta fashe da shi
”kada ka yimin haka adanan,nifa mahaifiyarka ce,ni nasha wuya gun haihuwarka na kawoka duniya”dariya ya sheqe da ita
”gaskiha nene kina da mantuwa,kefa kika ce farauta halak ce kuma ba’a barin ruwan gangare ace sai an dawo za’a diba,wanda ya samu dama ya dama,duk inda ka hadu da arziqi kayi qoqarin yagar rabonka don yanzu duniya sai kana da shi ake yi da kai duk fa hudubarki ce wanann,to kawai yau daya don ta dan ratsa da ke zaki hau raki,ai dama malami yanason ya koyawa dalibinsa karatu yaga yana aiki da shi pratically

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button