ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

ta fito daga kitchen zata ja ruwa a rijiya,a wannan karon kam ta kamashi dumu dumu yana kallon nata,saboda wani tsabar qarfin hali irin na abdallah tare suka hade rai hakanan kowa ya janye idonsa daga kan dan uwansa ta ita ta wuce bakin rijiya shi kuma ya bude shafin gaba na qur’anin hannunsa ya shiga sabuwar sura suratul jinni bayan ya gama suratu nuh daga sama yaje gangarowa qasa surori kadan suka rage masa ya hada saukarsa don yau yake son kammalata gobe juma’a za’ayi sadaka wa mabuqata

ta debi na farko cikin rijiyar mara katanga don kowa yasan yadda bakin rijiyar qauye yake a bude take kuma daf da qasa ta kai rumfar girki ta sake dawowa ta zuba cikin botiki duk yana satar kallonta ta gefan ido don baiso ta kuma kama shin kuma gashi bai gajiya da kallon nata,ta daga botiki kenan santsin lakar dake bakin rijiyar wadda ta jiqu da rya ya debeta,luuu gaba daya ta tafi tayi kan rijiyar
”maryam”ya fada cikin wata iriyar gigitacciyar murya idanunta a rufe tana ambaton sunan Allah,zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje da kanta,ta gama saddaqarwa yau kam sai yanda Allah yayi da ita don ba makawa cikin rijiyar zata yiwa masauki don

qafarta ce ta fara gjrdewa wani zafi ya kuma ratsata ta saki qara,jikin mutum taji ya fada gaba dayanta kana aka janyeta gefe,a mamakance ta bude idonta saboda ta gama bayarwa zata jita tsamo tsamo cikin ruwan rijiyar ne,sai kuma ta sake haduwa da wani abun mamaki da yaso sandarar mata da jinin jikinta

Abdallah ne tsaye bisa duga dugansa kan qafafunshi kamar yadda yake a da,ta dan janye jikinta daga gareshi da fuska mai dauke fal da mamaki tabi tsawonsa da kallo,tabbas shine abdallah ne,the gentle giant man din nan,abdallah dai abdallah mami,kasa daina kallonsa tayi don har yau tana jin kodai mafarki ne daga irin mafarkan da saba yi,baya dai ta sake ja saidai wani zafi daya ratsa qafarta ya sata durqusaqa tana fadin”wash”wasu hawayen farinciki suka aulmiyo daga idanunta

Cak taji ya dauketa baki daya bai direta ko ina ba sai kan kujerarsa da ya tashi ya ajjiye ta a kai bayab ya dauke alqur’anin dake kai ya maida man window din dakin inna wuro,reshe sai ya juye sa mujiya a maimakon abdallah dake kallonta a sace dazun,yanzun ita ke binshi da kallo baki sake kuma kai tsaye

Gabanta ya dawo ya durqusa baiko damu da rairayin dake gurin kada ya bata masa kaya ba,ya kama kyakkyawar qafarta da yake tunani anan ta gurde din
matsawa wani guri yayi sannan yace
”nan ne?”bata fahimci ma da ita yake ba don ta tafi cikin duniyar mamaki,saida yasa bakinsa ya hure mata brown oily eyes dinta da suka qara sheqi sakamakon sabuwar qwallar dake ciki tana yawo,bata kai ga fitowa ba

”kada ki cinyewa mero ni mana,ina ne gun ciwon?”ya tambayeta yana sake duban qafar tata
”abdallah ka warke?ka fara tafiya fa abdallah ko baka gani ba?”kyakkyawan murmushi ya saki kana ya dago ya dubeta kana ya sake maida kansa ga qafarta
”na sani kuma na gani,tun shekaran jiya na warke maryam,ranar da kika kwana a qijina,ranar da tsoho alhaji ya baki magani kika shafan da hannayenki masu albarka”

qwallar ta subuce ta zubo ta ido daya,muryarta so cool tace
”amma abdallah kaci gaba da zama a maysayin mai lalura?me yasa ka boye samuwar….”
”shshsh!”ya fada bayan ya sa qwayar idonshi cikin nata
”akwai dalili,sannan yanzun ba muhallin nganar bane”
kai ta girgixa ya gane so take ta fake ne ta masa borin nan nata,don haka ya rigata ta hanyar matse inda ta gurde din,ai kuwa tuni ta saki abinda takeso ta fada din ta maida gurbinsa da fadin
”wayyo qafata”tare da runtse ido ta kuma damqe hannun abdallahn,sake surarta yayi daga kan kujerar ya maida ta kan rabarmar kabar dake shimfide kusa da kujerar ya ajjiyeta,zama yayi ya miqe qafafunshi ya jawo qafar tata kan cinyarsa,idanu a warwaje tace
”me zaka yimin haka abdallah,kada ka fama min ciwo”ta fada a tsorace don tasan irin wannan gurdewar ta taba irinta taja bakinta tayi shiru taqi gayawa mama,sai data yi kwana uku maman ta lura,ta takura mata sai taje an duba mata,da taje ashe targade ne,taqi yarda a gyara mata qarshe sai da maman ta kaita da kanta,ai kuwa har suma tayi kafin a gama gyaran din qafar ta gama yin tsami,shi yasa yanzun ma ta tsorata kada taje irin wancan ne

Bai tanka mata ba kamar yadda bai kalleta ba ya kama gurin,kamawar farko ra saki qara tayo jikinsa baki daya ta nanade shi saboda azaba,kasa ci gaba yayi saboda irin riqon da tayi masa ma baki daya ua zare masa lakar jikinsa,tuni ta fara hawaye tana roqonsa kada ya sake taba mata wlh zafi
shiru yayi yana kallonta yadda taje faman kuka kamar yar baby,sai kukan ya bashi sha’awa saboda duka eye lashes dinta sun jiqe sa hawaye sun sake zara zara

Tazara ya sake bata ya faki idonta ya kuma damqar ciwon,ta qara shigewa jikinsa gumi yana karyo mata tare da wani sabon kukan,har cikin xuciyarsa yake jin kukan amma yasan idan ya qyale mata gaba zafin da zatajin sai yafi haka don ya gane targade ne a qafarta,qarfinsa yasa bai qyaleta ba sai da ya gyara,tuni ta jiqe sharkaf da gumi da hawaye harda majina,ya kalli fuskarta sai yaji dariya tazo masa duk fuskar ta hada ja,miqewa yayi ya nufi daki ta bishi da kallo don har yau mamakin takawarsa bata saketa ba,ya fito da handkherchief mai kyau da kansa ya dinga goge mata fuskar har sai da tayi tsaf kana ya gyara mata zaman ya miqar mata da qafarta ya jinginata da bango

gabanta ya dawo ya zauna dirshan,ganin yadda take jefa masa harara ya sashi daukar qur’aninsa ya bude yaci gaba da tilawarsa a zuciya
sai ta tsinci kanta itama tana qare masa kallo,ko ta ina abdallah cikakken namiji da samun irinsa sai an tona,kyau zubi da tsarinsa kadai ya isheshi ya godewa ubangijin daya qerashi

Komai nashi daidai yake,babu abunda yayi kodan ko yawa a tare da shi
”ya dai yammata akwai magana ne?”taji ya fada,kunya ta kamata ta rasa na cewa sai kawai ta soma qoqarin tashi,hannunta ya riqe yana fadin
”take it easy”sannan ya maidata ya zaunar
”idan kin tashin me zakiyi,ina kuma zaki je?”
”girki na dora kuma ban kammala ba,gashi yamma na dada yi”
sai ua dinke girar sama da ta qasa kana yace
”tab,ai kuwa yai saidai kada kowa yaci abinci cikin gidan nan,babu girkin da zakiyi”baki ta saki tana kallonsa yadda yabi ua hade rai tamkar wanda ta zaga,sai taga ya ajjiye qur’anin bayan ya saka alama ta inda zai tashi ya nufi rumfar girkin,kallo ta bishi da shi,sai ta tsinci bakinta yana furta
”ahamdulillahil lazi bini’imatihi ta timmus saalihaat kana ta limshe idonta tana sake gaskgatawa da miqa dukkan imaninta ga Allah,shine mai kun fa ya kun,yadda duk yakeso haka yakeyi haka kuma za’ayin”

Tana kallonshi yana tura wutar iccen tuni hayaqi ya bulbuleshi sai gashi ya fito da sauri daga rumfar idanu jajur hawaye na diga,dariya taso kamata,dama idan banda rigimar sa ina shi ina wutar icce,wataqila ma tunda gake bai taba zuwa gaban murhu ba balle ayi batun girki,yana goge qwallan yana fadin
”kai kai kai,yanzu baby haka kike shaqar wannan abun kamar kanka zai juye,gaskiya daga yau kin gama”dauke kanta tayi kamar bata jishi ba bayan kuma ta gefab ido take satar kallonshi

Baikai ga zama ba nero tayi sallama ta shigo gidan,turus tayi ta tsaya tana kallon abdallah,gani take kamar ba shi ba,sam ta kasa dauke idonta daga kanshi
”wannan kallon fa?”yace da ita sai ta sunne kai wai ita kunya,qarasowa tayi tana fadin
”yaushe ka warka abdullahi?”
”kinga ga girki can inna ta bari jeki qarasa tukunna kya zo muyi hirar”
miqewa tayi ta isa nufi cikin rumfar tana sake mamakin warkewar tasa har ta gaza boyewa tana zaune a rumfar girkin tana waiwayensa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button