ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

”huwaila tayani gani,kinga su kuma wadan nan ina suka samo kayan alfarma haka”
da sauri ta juyo don ganin abunda lubabatun ke nuna mata,idanunta suka sauka kan kayan fadon da buhun shinkafa catoon na taliya mscaroni da couse couse wabda mami ta hada mata da su irin kayan da Abdallah ke rabo na musamman duk azumi sadaka ga mahaifinsa mafigayi alh abdul kareem mai nasara

”kinga inda ake abu,kare ya san ana abu a gidansu,tunda gashi yana gani a qasa”
wannna zancan ne ya dauko hankalin hadiza kan kayan
”mtswew,aikin banza aikin wofi,kayam haram din da aka samu ta hanyar haram har wani abun fariya da alfahari ne?,kwadayi dai ai mabudin wahala ne Allah na tuba nawa akayi”
”kamar ku kenan da ruwan ya qarewa dan kada ko?” wani irin ashar hadiza ta lailayo ta narkawa huwaila
”ai wallahi qaryarki tasha qarya,tuni na gama fahimtarki dama huwaila,sai kima kinsan cewa ba’a ja da masu kudi”
tsaki ta ja kana ta turo daurin dankwalinta gaba
”yo Allah na tuba ina abun yake,ina qudan yake ballantana romonsa?,game ce anyita kuma yau anzo game over din,sai kusa haquri masu rano su dara daga inda kuka tsaya’ta antaya qeyar yaranta daki ta bar hadiza abakin qofar tana ci gaba da zage zage kamar zata tada jinnu,ta gama da huwaila ta kalli qofar dakin mama ta yi nata,ita kadai ita da yaran nata tamkar wasu sababbun tabi

hindatu kam babu abunda take sai sheqa dariya cikin dakin suna aikinsu maryam ta dan dubeta kana ta kau da kai ta ci gaba da ahimfida zanin gadon dake hannunta kan sabon gadon maman
”ko kema shirin bin sahun nasu kike irin wannan dariya haka”dariyar na ci gaba da cinta tace
”ai wallahi adda maryam ki gode Allah,kinsan wannan bala’in tun jiya ake zuba shi cikin gidan nan”
”amma ina baaba,bai tsawatar ba?”
”ya tafi gaya duba inna gwaggon baba,kuma ko yana nan ma ma zai tsawatar din akai?,mowarshi aka taba fa,jamila ce ta dawo gida jiya wujiga wujiga”

sai da gaban maryam ya fadi,a hanzarce cikin fuskar mamaki ta kalli hindatu
”garin yaya?”
”to yaya jabir yace baya yi ta taho gida har dactakardar sakinta kyawawa guda uku,a kuma karbe duka wani abu na dukiya ko kadara da ya mallaka mata,amma in fada miki baaba hadiza da yake jahila ce ba ilimi a take suka hau dan sahu ta maidata wai zata bashi haquri a daidaita,wallahi in taqaice miki ko zama bata yi ba bayan dawowarta sai ga jamilar ta biyo sahunta,da duka ya koro ta daga cikin gidan da qyar ta qwaci kanta,to kuma bala’i sai ya koma kan inna huwaila wai itace sila tunda dama ta taba cin alwashin sai ta wargaza komai”
hindatu ta sake qasa qasa da muryarta kada mama ta jiyota
”in taqaice miki adda maryam jiya dai har gun bokan da sukaje ya raba tsakaninsku da ya jabir sai da suka tona abinsu,cikin hargagin fadansu”

sai jikin maryam yayi sanyi,ta bar abinda take yin din tayi zaune gefan gadon,tabbas tasan ba’a yi mata adalci ba,saidai rabuwar aure ai ba dadi gareta ba,espicially yaran gidansu da dukkaninsu babu wani mai qwarin gwiwa kan aurenshi kullum cikin jeka ka dawo suke,to ga wata kuma sabuwata samu
”kinga ya maryam,kada kice fa zqki wani damu,sakayya ce Allah ya miki ita da gaggawa haka”ta fadi ita tana ci gaba da dame gadon aikin da maryam din ta saki

”a’ah,maryamu kin gaji ne,idan ba dama sai na aika hindatu ta kiramin laure ta tayamu”
girgiza kanta tayi alamun a’a
”mama haka abu ya faru da jamila kuma dai?”
”uwar asugwi din ta fesa miki din kenan ko”maman ta fada tana qarasowa cikin dakin,ta kama kunnen hindatu ta dan murde har sai da ta saki aiririyar qara tana dafe hannun maman
”don Allah mama kunne na,zaki tsinke kunnen autar taki fa ki rage mata kudin sadaki”
”ai gwara in tsinke kunnen tunda ya iya jiyo gulma ya fadawa addarshi”
da qyar hindatu ta zame a hannun maman

jikinta babu qwari haka suka dinga aikin,har ga Allah bata ji dadin mutuwar auren ba,tunda yau babu wanda,zaiso ace nashi ne kullum a bazawara,sai magariba uka kammala aikin komai yayi neat da shi,ta cire kaya jikinta ta daura zani da hijabi tq fito bandakin tsakar gidansu tayi wanka,tsakar gidan shuru da shi qwal kowa yana daka da mugun abinshi a zuciya,girgiza kai kawai tayi cikin zuciyarta tana fadin Allah ya gyara,sam rayuwar gidan nasu a karkace take kowa da inda ya dasa tasa alqiblar

tana cikin sallar isha’i kiran abdur rahim ya dinga shigowa wayarta,hindatu ce zqune kan kujerar dq wayar ke kai don haka ta daga,bata ankare ba taji sun shiga hira da hindatu,dama gata gwanar surutu,sai da ta idar sannan ta miqa mata wayar,kasa dagawa tqyi saboda kunyar ama dake gurin,itama maman na ankare da ita amma tayi kamar batq gani ba,dn tasan maryq din ba boye mata zata yi ba,cikin zuciyarta take addu’ar Allah yasa mijin aure ne diyartata ta samu

su ukun cikin kwano daya kamar ko yaushe suka ci tuwonsu na masara miyar busashshiyar kubewa,santi kawai maryam ke ti wa mama don tayi missing girkin maman sosai,mama gwana ce ba baya bace gun tsara girki musamman namu na gargajiya

zumudi yasa hindatu ta kasa shiru jin addar tata taqi tada zancan mutumin da ya kira din dazun
”wai adda maryam abdur rahim din dazun fa yace saurqyinki ne,kuma naji shiru baki ce komai ba”
hara rarta tayi
”wannan baki naki hindatu kamar ba’a gasa miki shi ba?”
dariya suka sa su dukka ukun,tilas yanzun ta yiwa mama maganarshin tunda tun ajiyan yake jadda da mata aure yake son yayi bada wasa ya zo ba,a kunyace ta yiwa maman bayani,farinciki fal zuciyar maman
”Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,ya kade dukkan sharri da fitintinu,addu’a ce yanzu kawai abunyi gareki maryam”
”insha Allahu mama,sai a tayamu muma da ddu’ar”ta fada cikin karyewar murya wanda ke nuna raunin zuciyarta,tausayinta ya kama maman

”addu’a ta zama dole akan musulmi,ballantana uwa ga ‘ya’yanta,wacce garkuwa kike da ita da zaki basu wadda ta zarce addu’ar,uwar ma irina mai yara mata da take musu fatan samu mazaje na gari nagartattu,babu sallar da zan idar da ita maryama ban muku addu’a ba,ku kadai nake da su fa”
wata iriyar qauna hade da tausayin mahaifiyar tasu suka lullubeta,haqiqa uwa ba wasa bace,wata ni’ima ce daga ubangiji,cikin zuciyarta take fata insha Allahu wannan karon zuciyar mqhqifiyar tasu zata wanke daga dukan wani quncin rashin auren nata,hawayen da suka tqru suka fara sauka a idanunt cikin dabara take sharewa don kada maman ta gqni hankalinta ya tashi

kiran abdur rahim ne ya sake shigowa,wannan karon ba tare da jinkiri ba ta daga don so take ta kaucewa idon amman kada tqyo tozali da hawayen da takeyi
”ranki ya dade lafiya kike kuwa?”ya tambaya a sanyaye
”lafiya nake me kaji?”
”muryarki ce naji tamin kama da ta masu kuka”
duk da yanayi da take ciki sai da murmuahi ya subuce mata
”idan banda abun abdul har yaushe kasan muryata da zaka tantance kuka nake yi?”
murmushi ya saki har tana iya jiyo sautinshi
”na dade da sanin muyarki maryam,ke dince baki sani ba,kina gidanku ko?”ya qarashe maganar da tambaya,cikin mamaki da sigar tambaya itama ta maida masa amsa
”wa ya gaya maka?”maryam,kina shakka cikin son da nake miki ko…..any way….naje gidanku ance min baki nan kina gun mamanki”

a wani mamakin ya kuma sakata,son iya saninta babu mai shigowa gidan su mamin ta sauqi
”ya akayi kasan gidan da nake zama taya kuma ka iya shiga da sauqi irin haka?”
”maryam,duka abdul ba mai daukar abunda yake so da sauqi bane,yana bashi muhimmanci ne afili da boye,ina fata kin fahimceni?”
”jinjina ga irin wanna son da abdul yake min”
”jinjina ga zuciyar data sadaukar min da kanta”sai duka suka yi murmushi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button