ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

sai taji,maganar ta mata wani iri taya za’a dauketa adanqata ga mutumin da ba’a binciki wayeshi ba,sanna kuma uwa uba daga haduwarsu jiya sai tace ya turo magabatansa,tilas sai an nuna masa an gaji da zamanta dama
sai ta lanqwashe murya tace
”baaba,ina ganin an dan badakamar wata guda ko fiye kafin ayi masa maganar turowar,sanna baba ka gafarceni ayi binciken inaga haka sai yafi kyau”
”hmmm,karatun boko ya bude miki ido mero”ya fada yana murmushi
bata ji dadin yadda ya fassarata ba,don ita tayi ne da zuciya daya,tayi ne don gujewa auren jeka nayika
”shikenan tunda kin zabi hakam,amma kada kiyo kuka dakowa idan shima ya kama gabansa kafi wata gudan,maganar bincike kuma tunda ya gaya miki unguwarsu na baki wuqa da nama kiyo kinga kin hutashaheni ma”

hawaye ni ya silalo mata,bata taba jin inda ‘ya takewa kanta binciken ma’aurinta ba,amma yata iya jaka tata qaddarar rayuwar take,ta kuma godewa Allah da bai sata ta kauce hanya ba duk da yadda ta tsinci rayuwar tata cikin tsangwama
”na gode baba,Allah ya gara gima”ta fada aladabce
”ameen ameen,idan kin fita ki turo min iwar taki”

tare suka karya da lafiyayyen qosai da kunun tsamiya wanda yasha lemon tsami,sosai tayi namijin qoqarin fidda dukkan damuwa daga zuciyarta suka karya din cikin wawala
sun tattauna da mama kan atamfofi da take so ta dinga sarowa maman idan tadauki albashinta na wannan watan ko falle bibbiyu ne ta fara saidawa agani idan zasu karbu,albarka maman kawai ta shi mata tare da mata kyakkyawan fata

sai la’asar ta fara shiri tafiya,hindatu tace
”ki jirani adda maryam mu fita tare zanje duba jamb dina,tun jiya naji sanarwa ta fito”
”to kiyi,maza ki shirya don so nake naje nayi abincin dare,jiya duka baaba uwani na dorawa aikin”
”gaskiya kam,don ma muta nene masu karamci da mutunci”
inji mama dake ta hadawa mami su kuka daddawa kubewa man shanu da sauransu

qarfe biyar sukayo sallama da mama ta fito don raka su,jamila ce tsaye a tsakar gidan sanye take dai da swiss lace dinta tun na shekran jiyan,mai tsada ne amma gaba daya ya yamutse yasha squeezing,fuskar nan ta hqutsine kamar dakalin kashi sqboda tsabar bqcin ran da take,ciki da baqinciki uwa uba kwana biyun nan bata saurari wanka ba,gabanta hadiza ce riqe da kwanon da yasha uwar lamba shinkafa da wake da manquli ce aciki da barbaden yaji
”haquri fa zakiyi kici tunda dai na ba gidanki bane,mu bamu da wani miyar nama da zamu zuba miki,kina kallo haka suma qanna naki suka ci”
”idan naci wannam abun Allah ya tsinen hadiza,wai ma meye amfamin kudaden da na ringa satowa ina kawo miki duk ina kika kaisu?,kinje kin rabawa garadan soro sun cinye kuma gashi nan auren da ake ta tattali din ya tsinke….”
da sauri hadizan ta kaiwa bakin kamilar dula kin zata mata tonon silili cikin jama’a
”don ubwnki sharri zakimin”
”ba wani sharri wlh gaskiya ce da bakina sai a hanani fadan gaskiya ta…”

binta ce ta atse cece kucen ta fito dakin,inna hadizan hannunta dauke da wayar jamilan wadda ta tasamma dubu dari biyu da hamsin tana ta digar ruwa
”kinga aikin da kulu ta miki”ta fada tana miqa mata wayar
hannu jamia ta dora aka ta kurma ihu tana fadin kulu ta kasheta,ita kadai ce ta rage mata kadara shine don baqar zuciya zata tsoma mata ita a ruwa wallahi to ba zata yarda ba
kukan kura tayi ta banka dakin nasu da gugu inna hadizar tabi bayanta tana fadib kada ta nakasta mata yarinya amma ina kota kan uwar bata bi ba
tsaki hindatu taja tana fadin
”jarababbu,ku kashe kanku dai”

naira talatin talatin suka biya zuwa caffe din dake qasansu,su taradda gun cike da dalibai masu duba jarabawarsu,hakan ne ya dan janyo musu jinkiri,sai da suka jira har kusan shida sannan suka samu sarari,babu jimawa aka gano result din hindatu,ba ita mai jarrabawar ba hatta maryam tayi farinciki ainun,don makin hindatun ya kai dari biyu da biyar,sai da ta rakata ta samu ota sanna itama ta tari tata ta wuce gidan

????????????????????????

kamar yadda layukan suke shiru gidan shima yake shiru lokacin da ta isa

tana shirin shiga ita kuma na shirin fita kunnenta maqale da waya,cikin dinkin fitted gown take na material ruwan zuma,dan siririn dankwalin kawai ta nade wuyanta da shi,ganin ta nufota gadan gadan yasa tayi hanzarin matsawa gefe dob ta lura idab batayi hakan ba tsaf zata bangajeta ne ta wuce,saddiqa ce uwar girman kai da dagawa,duk da hakan bata tsira ba sai data yi mata kallon biyi babu taja tsaki bayan ta cire wayar a kunnenta sanna ta wuce

su biyun kuma na kwance cikin kujerun falon wato abida da salma kowa na sabgar gabanshi,abida na charting salma na danne dannen laptop da bata san me tak yi ba,sai t v plasma din falon dake ta zuba aiki babu mai kallonta,babu wadda ta amsa sallamarta cikinsu,bata damu ba sam don ba yau ta soma ganin hakan ba,har zata wuce daki sai ta jiyo motsi cikin kitchen din haka ta sauya akalar tafiyar tata can,baba uwani ce ke wanke kwanuka,ta qaraso kitchen din dafe da bakinta
”ayyah,baaba uwani ayimin afuwa na barki da wahala jiya da yau”murmushi tayi tana taunar goro
”haba ‘yar nan ai an zam daya babu komai,ke dai ya kika barosu?”
”lafiya baaba suna gaidake”ta amsa mata tana karbe soson wanke wanken
”to madala muna amsawa,inace yanzu kika shigo gidan?”
”eh baaba”
”to amma shine zaki wani,karbi wanke wabke,bani in qarasa kije ki huta ga kiran sallar magariba can anayi”
”a’ah baaba,haba gaskiya bazan baki ba,ki huta kema nasan tun jiya kike dawainiya”

”hmmm,wallahi ke dai bari ‘yar nan,inda ace abdullahi ne sai ni sai hajiya aikin da sauqi,tofa ina wadan can marasa kunyar yaran kawai sun isa su saka ka gaji,ga daya ta dadu,wancan tace ita kaza za’a dafa min waccan tace kaza”
wani takaici ya kama marya
”kuma kika dafa baaba?”
”to ya za’ayi meramu sai haquri”
ta ajjiye kwanon hannunta
”bana jurar raina babba baaba,babu wadda zaki sake dafawa komai saidai idan maami ta saka ki,duk mai buqatar wani abu ta shigo ta dafa ai itama tana da hannu”

sai da suka qarasa komai sannan suka bar kitchen din tare bayan baaban ta gaya mata mami na asibiti da azahar ta fita zuwa bayan isha’i zata dawo,yadda ta barsu a falin haka ta dawo ta taradda su babu wadda ta motsa don tayi salla

tara saura ta fito din ta debi abincinta,zaunen dai suke duka su uku wannan karon kowacce taci ado,abida cikin matsatstsun riga da wando,salma cikin fitted gown,saddiqa kuwawata gown ce wadda bata da hannu duka saman qirjin a waje,mamaki ya cikata tamkar irin matan gidan nan dake tsammin dawowar mai gidansu a lokacib,babu tababa zaman jiran dawowar abdallah suke,takaici ya isheta kamar ta rufesu da duka,duk su suke jawowa abdallan ke daukar kansa on top,yake rage qimar mata,koma meye sune sila

tasa kanta gaba zata wucesu dauke da plate din abincinta
”ke malama a bawa mutane abinci ko su zasuyi serving kansu?”
a nutse ta waiwayo
”su waye mutanen?”ta tambayi salma cikin gatse,amma da yake sam ba ganewa take ba sai tace
”mtseeww,gani kuwa kina kallona”
”ayyah,to ai na dauka a qoshe kuke ko”
ta shige dining area din ta zuba mata ta ajjiye mata

”ni da kika raina sai nayi magana zaki zuban?”inji abida
maryam ta dubi plate din hannunta
”sai kayi magana zansan kana so ai,ga wannan kici na zuba wani”ta fadi bayan ta ajjiye mata shi a gabanta,ba bata lokaci tasa qafarta ta shure shi take yayi dai dai a gun,wanda ba don tayi saurin ja da baya ba har a jikinta zai samu masauki
”lallai ne ba qaramun raini ne tsakanina da baqauyar yarinyar nan ba”cikin qanqanin lokaci ta yar da wayar hannun ta ta miqe tayo kanta,qyam ta tsaya hannayenta harde da qirjinta tana kallon abidan,qarasowarta dab da ita ta daga hannunta saidai kafin ta aiwatar da komai muryar mami ta karade falob
”kai,meye haka abida?”dolenta ta sauke hannun nta cikin hayaniya take fadin
”wallahi mami sai na hora yarinyar nan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button