ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

qarfe shida suka fita meena event center suka gabatar da wata qwarya qwaryar dinner,ta maryam ce ita da qawaye da iyayenta,su hindatu kuwa tuni jabir yazo ya dauke matarshi suka wuce dinner,fir maryam tace ma abdur rahim bata buqatar wata dinner,su din ma da zasuyi sai sun dawo,hindatu da jabir na mata dariya sukayi tafiyarsu,bashi kuwa ya dawo da ita gida ba sai daya saura na dare,maryam din zata soma mata fada tayi shigewarta bargo tayi kwanciyarta
”hindatu rawan kan amarci ya fara tabaki kenan”cewar raliya wadda ke gyara kwanciyar fadil,suna jinta tana musu dariya

????????????????????????????

tun qarfe biyar da rabi na yammacin ranar asabar motoci suka cika layin har suka musu kadan,tilas ya sanya wasu motocin suka dinga parking a bakin titin unguwar,moto cine na kere sa’a waccan tana wace wannan haka wannan ma haka,a nutse kowa ke zaban wadda zai shiga kasancewar tare za’a tafi,sai hindatu ta raka maryam din tukunna.

”da Allah malama kihi ki foto,kunzo kun sanya uwarku a tsakiya kuna neman sata kuka,ina cewa ba’a kanku aka fara aure ba,haba da Allah”inji yayar mama hajiya aysha,hindatu da maryam dinne duqe gaban maman,maryam ta soma qoqarin taahi amma kuka yaci qarfinta ya hanata,sanye take da atamfa riga da simple zani an lullubeta ruf da wadataccen mayafi,hajiya aushan ce ta taimaka mata ta miqe ganim da gasken ta kasa miqewar,addu’o’in fatan alkhakri ta biyo yayan nata da shi.

caraf sukaji an damqe hindatu,jamila ce a zabure kamar mahaukaciya sabon kamu surutai take zage zage da sumbatu kala kala
”shegiya tsinanniya,wallahi babu inda kika isa kije,gidan mijina nawa ne ni kadai,wallahi bazan baki damar cin irin daular da naci ba don uwar ubanki”ganin abin na gaske ne daya daga cikin qannen malam amadu sailuba ta qaraso ta daga hannu ta zabgawa jamilan mari
”saketa ‘yar iskar yarinya mai kama da ‘yar Allah bani,dul abinda kika aikata akayi muku shuru ba’ace muku komai ba bai isheku basai yau ranar da Allah ya tashi nina muku kuskurenku,shekara nawa kuna cutar amina baiwar Allah ta taba tadakai ta kalli waninku,tunda aka fara bikin nan baku,bar mutane an zauma lafiya ba,uwarku dai ta cuceku wallahi,kuma ki saketa tun kafin ki debi haqoranki a hannu,idan tsiyace kowa ma ya iyata”ba shiri ta saki hindatun taja da baya sai gata yaraf a qasa.

da gudu inna hadiza ta qaraso gurin,hannu ta dora a ka cikin qaraji tana fadin
”huwaila amina dake kanki sailuba,zaku kashemin ‘ya,munafukai tsinannu,dama ai na dade da sanin kun fi son amina saboda ‘yar garinku ce,to Allah ya fiku kina ranar daukan fansa na tafe”
babu wanda yabi ta kanta,hssalima zamewa kowa ya dinga yi ko ruwan da za’a kwarawa jamilar an rasa me miqowa,su kansu sauran ‘ya’yan nata na qofar gida suna jallin yadda motocin sukayi farin dangon daukar amare,kwalliya kowaccensu taci tare da fatan daya daga cikin mamallakan motar ya taya

ta dubi sailuba sata zo wucewa tana sauri don kada ta rasa motar tafiya
”da Allah sailuba miqo min ruwa na kwarawa jamila kinga bata numfashi”kallon banza tayi mata
”kici mutuncinmu kici na uwarmu kice zaki moremu,saidai ki nemi wata ta baki wallahi badai ni ba”ta buga qafa tayi ficewarta,tilas ta saki jamilan ta debo ruwan ta sheqa mata kana ta jata zuwa cikin daki tana fyace majina.

Gwanin sha’awa motocin ke tafiya cikin tsari da nutsuwa,sam babu irin mahaukscin gudun nan da ‘yan kai amarya keyi,mitoci ne kimanin guda arb’in banda na security guda goma

wani matsananciyar faduwar gaba take fama da shi idan ta tuna izuwa gidan aurenta fa take tafiya,addu’o’i ne fal cikin zuciyarta na samun sa’a da nasarar sabuwar rayuwar da zata fuskanta

????????????????????

sau uku tana sako qafarta waje da niyyar fita saidsi ta kasa,sakamakon mutanen dake giftawa bata da buqatar kowa ya ganta,aiki ne na sirri wanda bata da buqatar haduwarta da wani,wayarta ta fara vibration jikinta na rawa ta daga,muryar nene ta cika dodon kunnenta
”kada fa kiyi kuskuren da zaki jawo mana bacin aiki,wannan ce damarmu ta qarshe”murya can qasa take fadin
”na gama aiwatar da komai nene,fitowata ce ke neman gagara mutane na kai kawo a gun”
”kada ki kuskura ki wuce mintina talatin baki baro area din ba,wuce hakan na nufin bacin komai”din din din wayar ta katse,hankalinta ta msida sosai kan hanyar ficewarta,wuf ta faki idanu ta fice ta nufi bangaren nasu cike da farincikin nasarar aikinsu

????????????????????????

Qarfe goma da rabi ne na dare,gefan lallausan gadon dakin nata take a cure guri guda,tafiyar yan kawota da mintina ashirin yayyafi ya fara sauka wanda ya haddasa sanyi da garin yayi hade da qamshin qasa,bai kankama ba ruwan hakanan yayyafin bai tsaya ba,kusan tunda suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba

hayaniyan data soma ji cikin paflour na muryoyin maza daban daban suka qara mata fatgaba,ta runtse idonta tana jin yadda zuciyarta ke dukan uku uku kamar zata yi tsalle ta fito

”ko baka fadi ba ba shiga muma za muyi ba don an dade da daina wannan”ta jiyo muyar wani daga cikinsu,tun tana jin hayaniyar tasu sama sama har taji dif alamun basu cikin sun fice kenan

da gudu gudu sauri sauri ya qaraso cikin parlojt din saboda ruwan da ya sake danyin qarfi,duk da haka ya jiqa masa fararen kayanshi,ya tsaya ya kulle ko ina ya rage yawan qwayayen dake kunne kana ya doshi dakin kai tsaye

a hankali ya tura qofar dakin kana ajjiye tarin ledojin dake hannunshi,qamshin dake dakin kawai ya isa ya tabbatar maka rana ce ta musamman,tsaye gayi hannunshi harde a bayanshi,sai ya lumshe idonshi yana zuqar qamshin qasa hade da turaren jikinsa da na dakin baki daya yadda suka hadu suka fidda wani qamshi na musamman kuma na daban,gwagwarmayar da ya fada kacin samunta ta zama mallakinsa ya dinga dan tunawa,a hankali ya bude idanun nashi ya tsaya yana qarewa shigar tata kallo

gaba daya jikinsa ya saki lokacin da wani tunani ya darsu a ransa wanda ya qada maaa qwarin gwiwa da azamar isa gareta,tamkar mai tausayin gadon haka ya hau ya dinga rarrafawa har ya isa gareta kana yayi zaman dirshan a gabanta

sannu a hankali ya dinga yaye mayafin dake kanta har ya cimma nasarar cireshi duka fuskarta ta bayyana,saidai ya cimma idanunta aruntse ne,ya karyar da kai yana ci gaba da kallon fukartata irin kallon da bai taba samun dama ya tsaya yayi mata shi ba,kyawunta yaci gaba da fito masa muraran,sosai ya shagala har baison abinda zai shiga tsakaninsa da yanayin

Qememe zuciuarta taqi amincewa da daina mugun tseran gudun da take,gashi ya sata agaba,nauyi da kunyarshi sun hanata bude ido,jin shirun yayi yawa ya sanyata yanke shawarar bude idanun nata ko yama fita adakinne ma bata sani ba

da kadan da kadan ta dinga budesu har sai da suka kammala buduwa tar,da qafafunshi ta soma tozali a hankali ta dinga daga kan nata har ya sauka bisa fuskarshi da ruwan sama ya jiqa har ruwan da ya soma taba kanshi ke diga kadan kadan,batasan lokacin data ta wuntsila gefe ba cike da TSORO RAZANI DA FIRGITA BA sakamakon wanda ta gani

ABDALLAH ne cikin daren nan cikin gidanta kan gadon aurenta?,idanunta ke mata gizo koko meye?,me yake faruwa ne?,hauka ce ta samu qwaqwalwar abdallah ko bashi bane bama gaba daya aljanu kesan mata wasa da qwaqwalwarta da tunaninta,ina abdur rahim da ya bar abdallah ya keto dakinsu na sunnah?
dimbin tambayoyin da suka nemi jirkita mata qwaqwalwa kenan tashi guda ba tare da tasan duka amsoshinsu ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button