ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Kitchen ta shiga kai tsaye da zummae dora musu girkin dare,saidai abun kunya ta tadda mami harta kammala ta adana cikin warmers baaba uwani na gyara kitchen din,cikin kunya ta fito ta koma dakinta,wanka ta shiga tayi kana ta fito ta sauya wasu kayan,doguwar riga ta sanya ta atamfa wadda ta kamata daga sama daga qasa ta bude sosai,ta mata kyau qwarai cikin ragiwar dinkunanta ne na fitar biki da bata kammala sakawa ba.

Mami na gaba abdallahn na gefanta,security din abdallah ne guda biyu riqe da akwatunansa,yayin da ita kuma ke binsu a baya a haka suka isa harabar gidan inda dalla dallan motocin da gwamnati ta sakewa abdallah guda biyar ke jiransa wadanda da su zasu rakashi airport su kuma su wuce abujan su hadu a can.

Duk suka shafa addu’an da mami ta gama jero masa kana ta dan matsa don basu damar sallama,hakan yakeso don dama tun dazun idanunshi na cikin nata,moment nasu na dazun kawai ke masa kai kawo,ji yake kamar ya dawo da hannun agogo baya,hannunshi ya miqa mata idanunshi fal so qauna da bege,a kunyace ta miqa masa nata hannun,cikin motar ya janyota a tausashe,saura kadan ta fada cinyarsa ya rungomota jikinsa kana ya miqa hannu ya rufe murfin motar driver najin haka ya kunna motar ya jata,mami na can suna magana dasu ibrahim sai gani tayi har motocin sun fice.

Gam gam ya hade hannayensu waje guda kana ya kwantar da kanshi kan kafadarta,yadda bata ce komai ba shima haka,kowannensu da abinda yake saqawa ranshi a haka har suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake nan kanon dabo
Ahankal motocin suka koma tafiya kasancewar sun fara shiga cikin airport din,sai a sannan ya fara magana
”ina fata zaki cika zuciyarki da soyayyata kamar yadda tawa take cike da taki kafin na dawo,duk da na sani cewa ko a yanzun ma nasan cike take din saidai dama da aka hanata,abu daya da zan gaya miki maryam am sorry to say bazan iya cika miki alqawarin da na daukar miki ba,bazan iya sakinki ba maryam har ABADA ke din tawa ce”ya qarashe maganar yana daga kansa dagq kafadarta,wata farar envalope fara qal ya ciro daga aljihun suit dinshi ya bude tafin hannunta ya saka mata,dai dai lokacin da motar tasu ta tsaya aka bude masa murfin.

”Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo dani,kimin addu’a don muhimmin aiki zan gabatar wanda koda shine aiki na qarshe da zan aiwatar insha Allahu sai na gabatar da shi,alhj hamza ya jima yana cutar da society dinmu,ya dade yana ha’intar qasarmu yana lalata rayuwar matasa maza da mata,yana shigo da mugayen makamai da qwayoyi,in sha Allahu wanann karon qarahensa yazo,ki saka ni a addu’o’inki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam”
wata muguwar faduwa gabanta taji yayi,a hankali ta furta
”Allah ya tsare,Allah ya bada sa’a”saidai bata san ya ji ba ko baiji ba don ya fice da hanzarinsa ganin sun kusa makara yana baiwa driver din da ya daukosu umarnin ya fara maida masa ita gida sannan su kama hanya,binsa tayi da kallo shi da security dinsa har ta daina ganinshi,drivern ya dawo ya rufe murfin kana yaja motar

Batasan dalili ba kawai dai taji zuciyarta ta hade envalope din da ya bata tayi tsakiyar hannunta tana jin qamshi na fita daga jikinta

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

      ▶5⃣8⃣

Daga abu hurairah R.A yace:Manzan Allah S A W yace”na haneku da yin hassada,domin hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cin karmami(yayi,itace)

Cikin motar laqwas jikinta yayi gaba daya,tana jin wani abu mai kama da kewa na shigarta kamar wadda aka cirewa wani muhimmin abu daga sassannin jikinta

Dakin ta ta wuce kai tsaye ta fada gado tayi ruf da ciki,kasala take ji da canjin yaynayi cikin jikinta,sai taji gidan ya mata fayau kamar ita daya ce a ciki,ganin matuqar taci gaba da zaman a haka kasalar zata rufeta da gasken ya sanyata miqewa ta fito kai tsaye tayi sashen baaba uwani

A tsakar gidacta tatar da ita kan tabarma tana gyara zogale,kan tabqrmar ta isa itama tasa hannu tana tayata suna hirarsu,qarar wayarta ya katse musu hiran kiran raliya ne,tana murmushi ta daga sanan ta mata sallama
”maraaba da dawowan diyana”cikin sauti mai dauke da farinciki ta maida mata amsa
”uwar gida kuma amaraya agidan muhammad nasir”
dariya itam tayi cike da nishadi
”a wannan kirarin ai sai ku,ku da ludayinku ke kan dawo”
sai da suka gama zolayar juna kamar yadda suka saba sannan suka fara gaisawa

Hira sukayi mai tsawo wadda har baaba uwani ta kammala gyaran zogalen ta kwadanta basu gama ba

Har bayan magariba tana gun baban suna hirarsu,sai sallamar mami kawai sukaji
”zuwa nayi na duba dama,nayi zaton bai dawomin da ke ba”
kunya ta kamq maryam din ta sunkuyar da kai tana murmushi,tana idar da sallar isha’i ta yiwa baba sallama ta koma bangarensu

Ta kammala shirin naccinta tsaf ta haye gadonta,saidai ko guda baccin da take da muradin yi bata ji alamunsa,wata iriyar kewa da madaici na daban take ji na damunta,juyi take tun daga farkon gadon zuwa qarshensa,tayi hakan yafi sau a qirga,tana son qaryata kanta kewar abdallah take saidai ta gaza,sai ta tsinci kanta da muradin jin muruarsa saidai ko kadan ba zata iya kiransa ba,hasalima bata tunanin akwai lambar wayarsa cikin wayarta,ta miqe a hankali ta jawo side drower ta ciro envalope din da ya bata dazun,dawowa tayi kan gadon ta kwanta ruf da ciki,a hankali ta farketa,kudi ne sababbi fil a miqe yan dubu dubu masu yawa suka fado,yar qaramar takarda ce maqale jikin bandir na kudin,ta cirota ta budeta,karo na farko da idaninta suka ci karo da kyakkyawan rubutu wanda bata yaba ganin kamarsa ba
”kiyi amfani da su idan buqata ta taso miki,love you so much my sugar”
dunqule takardan tayi ta dorata saman kudin

Ta sake bude cikin envalope din take taci karo da wata takardar fara qal mai adon furanni wadda ba shakka itake tashin qamshin nan,ajjiye envalope din tayi kana tasa hannu biyu ta ware nadin da aka yiwa takardar,sallama ce a farkon takardar cikin kyakkyawan rubutu da harshen larabci

qoqarin mantawa da wanda kake so is like trying to remember some one you never meet,i know we feel d same baby saidai bansan me ke yawo cikin zuciya da ruhinki ba,dont let your ego stop u from doing whats right,duk abinda nayi nayi ne saboda ke,duk abinda kike gani na miki laifi a akansa saboda ke na aikata,sonki ne sanadi baby,i cant express my feelings a kanki baby,ban taba sanin haka so yake na sai a kanki,zan iya cewa kai tsaye ke kika koya min so,nasan kina tunanin na auroki ne kan tilas,ba haka bane na aureki saboda sonki da qaunarki da nake,nayi tsammani zaki qini zaki qi sona hakan ne yasa ban nemiki kai tsaye ba,but sorry for hurting u baby

kalmomi na sun bata ranki hakan ya sa kika riqeni,na sani na kuma san na fada,but banda ke baby baki ciki amma duk da haka am sorry again for my words and action last time,ina sonki baby ina sonki,am not with you to play games,ina fatan komai zai gyaru kafin dawowata,bazan iya jurar rasaki ba bazan iya ba,zanso ace ko yaushe kina tare da ni,baby ina da qarfin buqata tun ba yau na na sani,idan kika qi ni bazan iya sakinki ba duk tsanani matuqar ina raye amma ina fatan bani dama nayi aure,koda babu komai tsakaninmu ganinki da zamanki a matsayin matata kawai ya wadatar da ni,ke ta dabance baby ki yarda,inajin komai nawa daban duk lokacin da muke tare,am feeling safer when iam wrapped up in your arms then ever before,duk lokacin da nake kusa dake baby am overwhelmed with happiness,kin soni kin ceceni kin kubutar da ni kin kuma tserar dani,shin wannan ba so ne ba baby?bai isa a kira waannan so ba?,so mai ma kuwa mai tsada,so mai cike da sadaukarwa da fansa?,kin min abinda ‘yammata da yawa suka kasa min,na haqiqance u are what i have been waiting for my whole life,so na haqiqa so na gaskiya,kina sona ba tare da kinsan ma kina sona din ba baby

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button