ABADAN COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ABADAN COMPLETE HAUSA NOVEL

Tafe suke mero na nunnuna musu gurare,duk da wani gun ma maryam dauke kanta take ba kalla taake ba,saidai abdallah ya bada hankalinshi sosai bisa dukkana alamu hakan na masa dadi kuma yana fahimtar baya nanta,mero kan makar ta taka rawa don murna,yau gata ka larabawan birni,duk inda suka gifta sqi an bisu da kallo har wasu ma su tambayi meron
”’yan uwanmu ne,wannan yaya na ne”haka take fada cikin washe baki,wasu mazan har hannu suke bawa abdallah,ba qyama yake basu nashi hannun suyi musaba,kodama can shi cikin aqidunshi baya qyamar maras shi,duk wanda kuwa sukayi musabahar farinciki da murna kamar yayi me,musamman idan ya shinshina hannunahi yaji qamahin turaren abdallan,da yawa idan mero tace bashi da lafiya baya iya magana addu’a suke masa sosai Allah ya bashi lafiya.

sannu a hankali suka ci gaba da ratsa qauyen mai cike da ni’ima kamar yadda sunanshi yake,ko ina ka duba shuke shuke ne koraye shar,a yadda taji mero na gaya wa abdallah haka qauyen nasu yake ko ba cikin damina ba,cikin mintina goma suka iso bakin rafin,ruwa ne mai kyau yake guda na ciyayi baibaye da da bakinshi,wasu fararen dutsina da jajayene reras a zube a gun tamkar ana sane aka shiryasu,saidai ikon Allah yafi gaban haka ai.

Gab da bakin nan maryam ata ajjiyeshi,suna iya,hango shanu daga daya,bangaren sunata kai kawo,mafi yawancincinsu fararene qal sai kuma ruwan qasa jifa jifa,shegen surutun mero sai data gaya musu hatta da mai shanun,na wani dan garin ne saidai duk da dukiyar shanun da Alah ya bashi,matashine don bazai wuce shekara talatin ba,don ko auren fari baiyi ba,gefe ta matsa maryam ta zura qafafunta cikin ruwan tana kallon yadda yake gudana,tunanin mama da hindatunta ya fado mata,don kusan babu wanda suke waya da shi a yanzun ,hisham ne yace ta haqura din kada nene ta bayar da nim dinta ayi tracing nasu,da hakan ma saidai abinda take ji yana sukuwa azuciyarta da ranta tana jin kamar yafi haka,duk da zubar da meron keyi hankalinshi na kanta,ya fuskanci akwai abinda ya taba zuciyarta.

ji yayi kamar ya miqe da ya fuskanaci hawaye take sharewa a idanunta,mero ya yiwa nuni da ‘yan qananen fararen dutsinan dake gun,ta dauko yan,madaidaita ta miqa masa ga zatonta zai dinga cillawa ne cikin ruwa har tana fadin
”ai ka danyi nesa kadan da ruwan ko na matsar dakai gaba kadan?”kai ya girgiza mata alamun a’a.

ya dauki daya ya cillashi ga maryam,ya sauka abayanta,sai tayi sauri ta waiwayo take kuwa suka hada ido,idonshi daya ya kashe mata kana ya daga mata gira alamun tambaya,sai ta kawar da kan nata ta maida kan rafin,ganin haka ya sa ya sake ciro wani ya jefeta wannan karon ta sani shine sai tayi banza taqi juyowa,da daya da daya sai da ya qarar da su duka amma taqi koda motsawa bare ta waigo gareshi,mero na tsaye a bayanshi tana kallonsu tuni tayi nisa cikin duniyar tunani har ta manta da a inda suke.

Gabanta ya yanke ya fadi,da sauri ta waiwayo,abdallah ta gani a qasa ya fado daga kan wheel chair din idonshi na kanta,a sukwane ta miqe daga inda take zaune dan tahowa inda yake,take santsin,bakin rafin ya debeta tayi baya luuuu zata koma cikin ruwan
”maryam!”
muryar abdallah da take a shaqe ta daki dodon kunnenta ba zato babu tsammani,cikin ikon Allah ta turje bata kai ga fadawar ba ta dawo gaba ta kwasa a guje ta dira a gabanshi cike da tsananin mamaki,ko ina na jikinta rawa yake,sai hawayen idonta da take ta yiwa waigi ya balle baki daya,ta rasa me ma zata yi,hawan mero tayi da bala’i ta inda take shiga bata nan take fita ba,dn me tana gani zata barshi ya fado akan me?,duk masifar da take taqi kallonshi yayin da ahi kuma ya zuba mata ido yana karanta al’amura da dama daga gurinta
”shshshhhhh”din ta taji yace yasa ta rage masifar da take, a hankali a hankali,daga qarshe taja bakinta tayi shiru
”ki taimakamin na koma kan kujerar tukunna madam”
ya gaya mata karo na farko taji,muryarsa ta fita sosai,wani abu taji yana ratsa ta tako ina.

har yanzu jikinta bai bar rawa ba don haka qarfinta ya gaza kaiwa har sai data haqura mero ta taimaka mata suka maida shi,bata sake cewa komai ba ta soma turashi suka fara barin gurin tana goge qwallarta lokaci lokaci,ta kasa tantance yanayin da take ciki,gaske ne koko mafarki,yau abdallah ke magana da bakinshi?.

Dab da zasu fara shiga cikin mutane taji yace
”bai kamata ki shiga cikin mutane kina kuka ba ko?,dakat kadan ki daidaita yanayinki”
bata qi shawararshi ba ta tsaida wheelchair din din ta ciro dankwalin atamfarta ta goge fuskarta kana ta maida dankwalinta,amma maimakon hawayen ya tsaya sai wasu sabbi,ma dake bulbulowa har mero ta iskosu
ya limshe ido ya maida bayansa sosai ya kare da kujerar yana fadin
”ya salam,to me aka yi miki?,idan don warkewar baki na ne ai godiya zaki ma Alah ko,tunda dama shine mai kowa mai komai,idan kuma don fdowar da nayi ne ai gani sumul,ba ba abinda ya gutsireni mijinki baiji ciwo ba”
batasan ta harareshi ba sai data ji yace
”maida idon kada kija min asara,don ba qaramar asara bace idan na rasa wadann nan golden oily eyes din ba”.

A nutse suka ci gaba da tafiya kamar yadda suka zo,saidai canjin yanayi da aka samu,a dazu mero keta faman zuba cike da farinciki abunta abdallah na kalle kalle babu bakin magan,wannan karon kuwa tasbihi hailala da salatin annabi ke fita a bakinshi zalla,yayin da maryam ke cikin wani irin yanayi,jin ta take kamar an rage mata wani nauyi daga cikin nauyin da aka azawa zuciyarta,mero kuwa amsa kuwwa muryar abdallah ke maya cikin kunnenta,dadin muryar ya kasa barin dodon kunnenta,tsabar kulawa da qauna da take iya hangowa daga dukkan kallo da ikin abdallah da kewa maryamu,da gaka suka qarasa gida ana qwala kiran sallar magariba.

mrs muhammad ce????

????????????✍????✍????✍????
[7:29pm, 9/25/2017] Huguma????: ????????????????????????
????????????????????????
???? ABADAN????
????????????????????????
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????

WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
????????????????????????
????????????????
????????????
????????
????
© HASKE WRITERS ASSOCIATION????
home of expert and perfect writers

        4⃣7⃣

Manzan Allah S A W yace:shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku

mala’iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur’ani a cikinsa

A bakin murhu suka tadda inna wuro tana kwashe tuwo,sallamarasu ce ta janyo hankalinta bakin qofar shigowar
”kun dawo kenan mer…..”’sauran maganar ta maqale wa inna wuro ganin har da abdallah cikin masu sallamar,marar hannunta da take kwashe tuwon ta saki ta miqe tana fadin cikin dafe qirji
”Allah qaadiran ala mai yasha’u,bawan Allah?”ta fada tana kallonsa tare da qarasowa gabansu.

murmushi yayi yana kallon innar ganin ta kasa magana
”babu mamaki cikin ikon Allah inna,nine da bakina nake magana,yau Allah ya amince min”
kiran sallar magariba ya katse su
”inna muyi sallah tukun”ya dubi maryam dake tsaye guri daya tana faman goge qwalla lokaci zuwa lokaci
”gimbiya a dauran alwala,inna ki mata magana tun dazun nace tabar kukan nan taqi”inna wuron dake daura da maryam din ta dafa kafadarta
”haba meramu,farincikin da zaki nunawa ubangiji shine ki masa godiya ba wai kika ba,share hawayenki ki daurawa mijinki alwala”
”to inna”ta fada cikin rawar murya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button